Showing 57001 words to 60000 words out of 255051 words
sauyuka masu dama a rayuwar auren masoyan.
***
Handout ne a hannunta tana haskawa da fiti
lar waya. Ta bararraje a kan gado daga ita sai karamin vest da gajeran wando. Mace ce mai gashin jiki, ga zufa. Duk da kasancewar ta bude winduna ta daga labulayen dakin, hakan bai hanata jin zafi ba, karatun ma ba shiga yake ba. Aliyu kuwa tunda ya sa ƙaf
a ya fita da maraice, har yanzun karfe takwas na dare ba shi da niyyar dawowa.
Ta miƙe tana jan tsaki ta hau rage kaya ta fa
ɗ
a wanka. Wankanta na biyu kenan daga Magriba zuwa lokacin. Ta goge jiki, wannan karon bata bi ta kan undies ba, ta zura kar
amar rigar bacci mai jikin cotton, duka-duka tsawonsa iyaka guiwarta ne. Ta tufke gashinta wanda rabonsa da relaxer tun na aure. Hakan yasa ya kakkarye, kitso kawai take buƙata yanzun.
"Haka za'a rayu babu wuta? Nepa ma ba samu ake ba? Tab."
Ta furta a fili, za ta iya cewa tun tasowarta ba ta san matsalar wuta sosai ba a gidansu. Koda zasu rasa wuta, na ƴan kwanaki ne. Yanzun kuwa a gidan Aliyu ta haura wata bata ga kyallin wuta ba. Ƴan Nepa sun musu zagaye ya fi kirga akan su biya kudi sai
dai Aliyu ya ce bai da halin biya, suka gaji suka yanke jonin direct din da suka yi.
Banda wannan ma lamura da dama sun sauya, idan ta ga Aliyu ya yi cefanen kaza toh fa wata ribar mai tsoka ya ci a kasuwa. Naman miya na neman kakare musu. Duk wata
cima ta jin dadi ya ja baya. Ta miƙe a hankali ta fito zuwa falo ta na kallon farfajiyar gidan. Motar Aliyu na nan kamar yanda ta zata don a yanzu sai ya shafe kwanaki biyu na bai fita da mota ba sai mashin da ya siya, duk a dalilin jarinsa ya karye.
Jingina ta yi jikin window ta kurawa hasken farin wata idanu tana tunani. Tunanin gidansu take, tunanin yanda aka yi watsi da lamuranta. Abba ya hanata taka gidansa, duk sadda ta ce za ta je sai ya ce mata duka-duka yaushe ma aka yi auren. Karshe ya rant
se idan ya ga kafarta a gidan yanzu zai sa
ɓ
amata.
*"Kewarku nake Abba, kewa sosai, babu wanda ke zuwa gidana, daga dangin Aliyu har ku, ya kuke so nayi da rayuwata? Har yanzu ba ku bar fushi da ni ba?"*
*Tana jin sadda ya yi murmushi mai sauti.
*
*"Kiyi hakuri Ramlatu, muna sonki ne, da ba ma sonki ba zamu tayaki son abinda kike so ba kinji ko? Ki shekara tukunna, ki shekara. In sha Allah a sannan ko ba ki fadamin ba, ki taki da iznin mijinki ki zo mu gaisa. Hakan ya miki?"*
*Ba haka t
a so ba, sai dai kuma babu yanda ta iya, ta amsa da toh yayinda kwalla suka cikamata idanu. Ba za ta iya fadawa Abba cewa Aliyu na shan taba ba har a gidan kuma a gabanta, tasan dariya zai yi mata. Don haka suka yi sallama bayan ta bada saƙon ya gaida Haji
ya domin ba ta daukar wayarta.*
Ramlat ta sauke ajiyar zuciya,
ɗ
umin da ta ji a saman fuskarta ya tabbatarmata da zubar hawayenta, ta sa hannu ta share. A yau ta tsinci zuciyarta da kewar ƙawa kuma aminiyarta Amrah. Gashinan dai makarantarsu
ɗ
aya, a
binda suke karanta ma
ɗ
aya, sai dai koda wasa Amrah ba ta ta
ɓ
a bata fuskar da za su gaisa ba balle magana ta ha
ɗ
asu. Ranar da ta ta
ɓ
a kuskuren yi mata magana, nan take Amrah ta yi mata Allah Ya isa idan ta kara nunawa ta santa. Wannan ne ya bata haushi har
ta kasa
ɓ
oyewa ta sanar da Aliyu, sai da ta yi danasanin fadamasa da ta yi don zagin Amrah ya yi, irin ashar din da idan wani zai ce mata Aliyun ya iya, za ta musanta.
*"Babu ke babu ita! Babu ke ba ita! Kika kara ma kulata nima ban yafe ba!"*
Kalamansa sun mata tsauri, ta yi danasanin furtawar da ta yi, kusan ma ba ya ganin mutuncin kowa nata yanzu, daga ta soma batun kewar gida zai ce ai basu damu da ita ba.
Tunaninta ya katse sadda ta ji ana ƙoƙarin bude ƙyauren gidan. Ta sa hannu ta
share hawayenta gami da goge gumin da ya tsastsafo a goshinta. Maimakon ta ganshi da mashin, sai ta ganshi shi
ɗ
aya, abinda ya daure mata kai bai tsaya rufe kofar ba ya soma kokarin nufo cikin gidan. Tabbas dai Aliyun ne kamar yanda farin wata ya haskamat
a fuskarsa da kuma t-shirt fa jeans din jikinsa.
A gaggauce ta koma daki ta sanya dogon hijabin sallarta kuma na zuwa makaranta har ƙasa ta fito rike da fitilar wayarta. A barandar kofar falon suka yi kici
ɓ
us.
"Oops! Baby sorry. Ina mangareki
ko?"
Ta hau murza idanunta, kirjinta ya shiga bugun tara-tara. Ga abu dai a gabanta amma ta kasa gaskatawa, hakan yasa hannu na rawa ta dago ta haske fuskarsa ido a waje.
"Aliyu?" Ta furta cikin tabbatarwa da kuma alamar tambaya lokaci guda, k
afafunta ta ji sun hau wani irin mazari, kwakwalwarta ta kasa daukar abinda ta gani a fuska da yanayin gangar jikin Aliyun.
"Bani hanya Malama." Ya kara fadi cikin muryar ƴan maye. Ba ta da niyyar kaucewa ya kuwa bangajeta ta fadi ƙasa ya shige yana
kundumar ashar. Ta kama le
ɓɓ
anta biyu da hannunta na hagu kamar mai kar
ɓ
ar punishment a makaranta, kukan take yi amma gani take kamar idan ta bude bakin ihu ne zai fito madadinsa. Tunawa da ta yi kofar gidan a bude yake ya sanya ta miƙewa ta je ta rufe. A
hanzarce ta koma ciki, a falon ta sameshi ya zube anan kasan tiles yana maganganu barkatai marasa ma'ana da tsari.
"Aliyu? Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Aliyu me zan gani? Me..me...me?"
Ta kasa ƙarasawa tana sheshshekar kuka, ta zube a
gabansa.
"Aliyu ka ce mafarki nake, don Allah ka daina yimin irin wannan wasan. Na yarda na sani taba kawai kake sha, ka bar yimin wasan maye, wallahi ba zan iya dauka ba. Na shiga uku ni Ramlat."
Ta ƙarashe tana mai riko hannunsa. Cikin wani i
rin dariya na shaƙiyanci ya kamo tufkar da ta yiwa gashinta da iyakar karfinsa har ta saki ƙarar azaba.
"Keee, au baby...don uwarki da kika aureni ba ki...san...ina..hawa...sama...ba? Baby...kin cinyemin ku
ɗ
ina...na talauce...amma na tsira da hawa ga
jimare..."
Ta yi nasarar ƙwatar gashinta, da wani karfin zuciya don kuwa yanzun ba ta jin kowane karfi a jikinta ta mike za ta gudu daki, ba zato ta ji ya riƙe kafar sai ga ta yiff! Ta fadi saman tiles, baki da goshinta suka ƙumu a ƙasa. Kan ka ce me
sun yi suntum! Kuka sosai ta soma.
"Ka kyaleni Aliyu! Don Allah ka rabu da ni karka kasheni!"
Ta firta jikinta na mugun rawa, za ta iya rantsewa ba ta ta
ɓ
a yin ido hudu da mutum yana maye ba sai a ranar. Ta fi gani a akwatin talabijin.
Jikinta na rawa bai fasa rabata da hijabi ba kuma ya ketamata t-shirt din dake jikinnata ba, ya shiga sarrafata ya dora dukkan karfinsa a kanta. Fadi yake.
"Shege G-Baba...ya ce na yi son raina dake na huce....Baby farar ƙafa gareki...ubanki bai ban
komai ba....Hahaha..uban Muhibbat har gida ya ba..."
Bai karasa ba sakamakon hanka
ɗ
ashi da ta yi ya bugu jikin kujera, ta mike a guje ta shige
ɗ
aki ta rufe da muƙulli. Anan cikin duhun ta zube ta shiga rera uban kuka, innalillahi wa inna ilaihir raaji
un kuwa, ta ambata ya fi dubu. Aliyu mashayi?
Wani irin dunkulewa ta yi a wurin ta shiga risgar kuka. KEWA, yau kewar iyayenta da ƴan uwanta take ji. A yau ta yi dakacen biyewa za
ɓ
in ranta. Tausayin kanta ne ya lullu
ɓ
eta. Ta yi kukan mai isarta, ta
na jin yanda yake surfamata ashariya ta uwa da uba mara kyawun sauraro, ya gaji da bugu ya kife anan, tana jin fita da saukar munsharinsa. Miƙewa ta yi kanta na wani irin bala'in sarawa ta zura doguwar riga, ta tattare takardun ta kwanta saman gado,yanda t
a runtse idanu haka ta budesu. Baccin ya tafi, damuwa da bakin ciki sun tararmata sun tsaya a ƙahon zuciyarta. Nan da nan zazza
ɓ
i ya sauka a jikinta, haka ta kwana tana rawar
ɗ
ari.
***
Sanyin asuba da kuma iskar dake ka
ɗ
awa ce, ta tasheshi daga ba
ccin da ya shimfi
ɗ
e yana yi, ya bude ido gami da tallafe kansa da ya yi mishi wani gingirigim. A hankali hasken wayar Ramlat ta taimaka mishi wurin gane inda yake kwancen. Zumbur ya mike tsaye, komai ya dawo mishi tiryan-tiryan. Bai mance yanda ya sha magu
ngunan mura na saka maye a tare da su Sa'ad ba a club. Ya je musu da
ɓ
acin ran yanda a yanzun kasuwancinsa ya ja baya babu wani albarka, har ta kai ya rage facaka yanda ya dace, suka duramasa abin maye, ya yi ta sha babu kakkautawa duk domin ya ji sanyi.
Bai kuma mance yanda suka kawoshi gidan ba, yana da tabbacin mashin dinsa ma can ya bari.
Wani wawan tsaki ya ja, ya gaji da wani
ɓ
oye-
ɓ
oyen banza. Shi da gidansa? Ai dole ma wataran ta san halinsa. Maimakon ya kwankwasamata, sai ya wuce dakinsa ya
kara shimfidewa saman gado, babu tunanin tashi sallar Asuba.
A gefen Ramlat kuwa, dakyar ta iya lalla
ɓ
awa ta yi alwala ta yi sallah, jiri sosai ke kwasarta, ta mike ta koma saman gado, kwanciyarta ba jimawa ta ji amai na yunkurin tasomata. A guje ta
fa
ɗ
a ban
ɗ
aki ta shiga yunkurin sai dai banda ruwa ba abinda ke fita. Ta gaji da yunkurawar ta wanke baki ta fito. Kifewa saman gadon ta yi ta shiga rera sabon kuka, tunaninta kawai mutuwa za ta yi. Babu wani mai sanyaya zuciyarta a yanzun, Aliyu tana fush
i da shi, fushi mai tsanani. Gani take ta tsaneshi, ba kuma za ta iya ci gaba da zama da mutum mashayi ba.
***
Motsin bude ƙyauren gidan ne ya farkar da ita daga azababben baccin da ya kwasheta ba tare da ta shirya ba. Rana tarr a saman kanta,
Allah Ya taimaketa ma babu makaranta, Asabar ce. Ba laifi jikin da sauki sai dai ciwon kan bai sauka ba, bakinta babu
ɗ
an
ɗ
anon komai. Wanka ta fa
ɗ
a. Doguwar riga jallabiya kawai ta zura ta daure kanta da
ɗ
ankwalinsa.
Cikin faduwar gaba ta bude kofar
falon, don bata da tabbacin fita ya yi ko shigowa. Ganin ba kowa sai wayarta da kaya a yashe saman kujera ya bata tabbacin shi ne ya maido su wurin. A hankali ta taka ta dauka ta kai daki, gaban madubi ta kara tsayawa tana kallon yanda goshi da bakinta suk
a kumbura suntum. Hawaye ta shiga fitarwa, ba ta isa ta je wa Abbanta da wani zancen ba akan Aliyu. Sai dai kuma shi kadai ne ke sauraron ta, banda shi ko waya ta kira su Zulaihat sama-sama suke amsawa.
Kicin ta koma ta dafa ruwan shayi da kayan kam
shi kamar yanda Hajiyarta ke yi, ta zauna tana sha. Ba ta jin cin komai don haka ko kulolin tuwon da ta yi ba ta kalla ba balle ta iya
ɗ
umamawa.
Babu abinda ta iya gyarawa a gidan, nan falon ta na
ɗ
e tana rawar sanyi, ciwon kai ya fi na baya. Ruwan s
hayin da ta sha shima haka ta amayar da shi. Bacci wahalalle ya kara daukarta, ba ta ji ƙarar shigowar mashin dinsa ba, sai jin hannunsa ta yi saman goshinta. A firgice ta farka, ganinsa ya sanya ta zabura za ta ruga
ɗ
aki. Ya riketa gam a jikinsa, kawai sa
i ta fashe da kuka jiki na rawa.
"Don Allah ka yi hakuri ka rabu da ni, na tsaneka Aliyu, meyasa ka
ɓ
oyemin munanan halinka? Wallahi ba zan iya ci gaba da rayuwa da kai ba."
Ya
ɗ
ago fuskarta yana mai riko ha
ɓ
ar.
"Baby wannan shi ne so? Do
n kin ganni a halin da ƙaddara ta jefani shi ne za ki gujeni? Baby maimakon ki ji tausayina ki tayani addu'a? Meyasa kika zo kusa da ni? Kalli yanda na ji miki ciwo? Baby baki da lafiya, jikinki zafi, muje ki sanya hijabi na kaiki asibiti. Kinji?"
C
ikin karfin hali ta fincike jikinta ta fa
ɗ
a saman kujera tana sheshsheka.
"Kar ka kara kirana da Baby. Wannan kuma ba ƙaddara ba ce, son zuciyarka ne! Kana sa
ɓ
awa Allah kana kiran hakan kuma da suna ƙaddara? Wallahi sam ban yarda ba!"
Kalamanta
sun soma yi mishi zafi sai kuma ya danne, lalla
ɓ
ata kawai yake don ba ta jin dadi, don kuma wani abu da ya ƙudurta a ransa game da itan. Wannan tasa ya gane fa
ɗ
a da zafi ba nashi bane. Ɗakinta kawai ya shiga ya fito da dogon hijabi ya taho da wayarta.
"Haba, ashe wayarki ba chaji shiyasa na yi ta kira bana samunki. Muje idan mun fita na bada chaji. Ki tayani addu'a, akwai wani ciniki da zan yi yau, idan ya fa
ɗ
a har kaza zan siyomana, na kunna mana inji. Rashin wutar ya isheni."
Maimakon ta ji s
anyin kalamansa, sai ta kasa jin hakan. Asalima baƙaƙen maganganun da ya jefeta da su a daren jiya har da zagin iyayenta sun fi komai tsayuwa a ƙahon zuciyarta. Ta ha
ɗ
iye komai ta danne, ita kanta yanzun tana bukatar a duba lafiyarta, tana jin jikinta kama
r babu jini balle ruwa, kamar ma a yau
ɗ
in za ta mutu.
***
"Congratulations, kina da ciki wata biyu."
Kalaman da ke fitowa daga bakin likitiyar suka sanyata jin hanjin cikinta kamar zasu tarwatse.
"Ciki kuma? Dama haka ake cikin?"
Abinda ta fadi ya sanya daga Aliyun har Likitar dubanta, shi Aliyu ko fuskarsa kadai ka kalla za ka san yana murna da hakan duk da cewa yana auna yanda nauyi zai ƙara hawa kansa.
"Yes ciki, haka report ya nuna. Yaushe rabon da ki ga al'adarki?"
Tsabar rudewa ma ta mance da wani batun al'ada, ita tun zuwanta gidan Aliyu ba ta ta
ɓ
a ganin jini ba. Shima Aliyun sai a sannan ya ankara da hakan. Maimakon ta yi murna, maimakon a ga tana dariya sai ta rike cikin tana kuka kamar wacce aka fadawa ranar da
za ta mutu.
"Bana so, wallahi bana so! Dr ki zubar da shi."
Wani wawan mari Aliyu ya dauketa da shi. Ta rike ƙuncin a zabure ta mike tana dubansa cike da dumbin mamaki.
"Haba Malam, matarka ta sunnah? Ita za ka mara? Wane rashin hankali
kenan? Koda ta yi kuskure ba ka ganin yarinya ce, bai kyautu ka lalla
ɓ
ata ba? A ina aka ta
ɓ
a marin mace, matar ma ta sunnah?"
Bai ko kalli Likitar ba wacce haushi da takaicinsa ya kamata. Ta zagayo ta kama hannun Ramlat da gaba daya ta gigice kukan
ma ya tsaya cak. Ashe dai akwai marin da ya fi karfin kuka.
"Please get out. Ka bamu wuri."
Yana huci ya yi kwafa gami da hadata ita da Ramlat din ya watsamusu wani banzan kallo, har ya kai ƙofar ya juyo ya hau magana.
"Kika kuskura kika
yi gangancin zubarmata da ciki, daga ke har ita sai na yi shari'a da ku!" Daga haka ya fice gami da banko ƙofar da ƙarfi har iskar na bugunsu. Dr Sadiya ta zauna kujerar da Aliyu ya mike, sannan ta maida Ramlat din mazauninta suna fuskantar juna.
'G
a ta a haka yarinya mai hankali da nutsuwa, sai dai da alama ba ta yi dacen miji ba.' Cewar Dr Sadiya a ƙasan ranta. Tausayin Ramlat ya kamata,ta danne ta soma yi mata nasiha.
"Ramlat ke fa musulma ce, cikinki koda shege ne ya haramta ki zubar balle
kuma cikin sunnah. Ba ki yi kama da mutuniyar banza ba, ba kuma ki yi kama da mata ballagazazzu ba wadanda basu je makaranta ba. Ko mene ya yi zafi a rayuwarki, ki dinga tunawa da Allah. Shi ne Mai yaye dukkan wani azaba. Ki kwantar da hankalinki, idan ma
haihuwa kike tsoro ki miƙa lamuranki ga Ubangiji, In sha Allah sai kiga kin haihu lafiya. Mutum nawa ne za ki ga su na neman haihuwar ba su samu ba? Wata ma da kudi za ki ga ta zo nan tana neman maganin da za ta sha ta samu ciki. Wata kuwa har kuka take yi
tana fa
ɗ
in yanda miji da danginsa ke wulaƙanta ta duk akan ba ta haihu ba. Ke kuma da Allah Ya ba wa cikin ma na sunnah ki ce bakya so? Kenan kina nunawa Ubangiji ba ki yi murna da kyautarSa ba?"
Ta girgiza kai tana share hawayen da sai a sannan suk
a zubo, so ta ke ta ce ba haka bane, so ta ke ta ce yaron ko yarinyar da ke cikinta, ba ta so su dauki
ɗ