Showing 18001 words to 21000 words out of 255051 words
Milk shadda ya sanya da aka yiwa aiki daidai da zamanin, ya dora hula brown da ratsin milk din. Dogo ne don har ya fi ta da ka
ɗ
an, ya
na da hasken fata. Tafiyarsa ma kadai za ta burge mutum. Yana da
ɗ
an duhun lebba, gashin kansa a cike luf-luf wanda ya taho har gefen fuskarsa ya ha
ɗ
e da
ɗ
an ƙaramin gemunsa. Lafuzzan Aliyu ma kadai abin burgewa ne.
Murmushi ta yi wanda ya taho tare
da hawaye, ta yi azamar sharewa lokacin da Maryam ta dafa kafa
ɗ
arta. Ta kai duba gareta.
"Ina za ki?" Sai sannan ta waiga ta gansu tsaye a ƙofar gidan yayinda ita kuwa ta
ɗ
an yi gaba. Tabbas tunanin Aliyu ba zai kasheta ba. Ta yarda matar mutum kab
arinsa don haka ta haramtawa rai da gangar jikinta tunaninsa tunda har shima ya fahimci Hilal ne za
ɓ
in Allah a rayuwarta, kamar yanda shima ya samu daidai shi.
'Allah Yasa hakan kake nufi.'
Ta furta a ƙasan ranta.
Sun wuni cur a gidan K
awu Kabiru tare da iyalinsa, tun Ramla na ƙin magana da fa
ɗ
awa tunani har dai ta yi watsi da komai sai dai ta kasa yakice kalmar Ina sonki da Aliyu ya furta. Da zarar ta tuno a karon kanta sai ta saki murmushi.
Sai yamma suka bar gidan.
Haka
ta ci gaba da rayuwa gidan kakanninta tare da su Jidda, duk kuwa hakan bai tafiyar da tunanin Aliyu ba. Abinda ke tsorata ta bai wuce yanda so da kaunarsa ke neman rinjayar zuciyarta ba. Har yakan maida tunanin Hilal gefe guda ya ajiye.
Sai da ya r
age sauran kwanaki uku su koma makaranta sannan duk aka watse kowannensu ya koma gidansu, nan ma ji suke kamar kar a rabu.
***
"Wai ke ba za ki bu
ɗ
e kofar ba? Me kenan hakan? Ba'a isa a fa
ɗ
amaki ki ji ba?"
Muryar Maman twins ta bu
gi kunnuwanta, ta share hawayenta ta tattara hotunan ta maida mazauninsu sannan ta bude kofar fuska a ha
ɗ
e.
Shigowa ciki Maman Twins ta yi tana fadin
"Allah Ya shiryamana ke Ramla, bansan sadda za ki rabu da wannan bakin ran naki ba. Haba jama'a!
To sai ki fito Hajiya na nemanki."
Ta miƙe ta bi bayanta zuwa falon. Hajiya sosai ta bu
ɗ
e mata wuta kan ba ta son irin haka, dole ta ba Hajiyar hakuri itama Rafee'ah ta bata.
Kafin su bar gidan sai da ya kasance komai ya wuce kamar ba su yi
ba.
***
Kwanci tashi asarar mai rai, cikin ikon Mai Duka bikin A'isha ya taho gadan gadan, ana saura sati ƴan Daura suka dinga cika gidan. Wasu a can Yakasai wasu kuwa anan wurin Hajiya.
Ana saura sati a sanya A'isha a lalle Ramla ta
ɗ
auk
i katukan daurin aure da na wuni ta kai ofishinsu. Ranar da ta kama Asabar kuwa, takanas ta shirya yara sai gidan Muhibbat wanda daga nan zasu wuce gidan Ramla rabon kati. Mutane biyu masu muhimmanci a
🕯
️
*ƘARFEN ƘAFA*
🕯
️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem
07)
Daga ita sai Affan suka fita. Unguwar Gwammaja nan suka soma nufa gidan Muhibbat don ta tabbatar idan ta shiga gidan Amrah za ta
ɓ
ata lokaci, ko ba komai an dade ba'a hadu ba dalilin
tafiyar da Amrah ta yi zuwa
Lagos tare da Maigidanta wanda rabin aikinsa a can ne.
"Don Allah ina iya
ɗ
aukar fasinja?"
Muryar
ɗ
an sahun ta katse tunaninta, ta kai duba ga wanda ke tsaye shima yana kallonta yana jiran amsa, abubuwa da dama hakan ya tunamata, ta daure ta du
bi mai adaidaita fuska a ha
ɗ
e.
"Ba haka muka yi da kai ba. Ko ka mance shata na
ɗ
auka?"
Kafin mai adaidaita ya ce wani abu mutumin ya kauce gami da bata hakuri. Wannan tasa
ɗ
an sahun fisgar abin hawar da alama ransa bai mishi dadi ba. Ta ƙara ri
ƙ
e Affan kar ya tuntsira ba ta ko damu da yanda
ɗ
an sahun ke shirga uban gudu ba. Hankalinta ya tafi ga tunani. Meyasa abubuwa da dama suke ƙin
ɓ
acewa daga kwanyarta? Ba ta jin har ta mutu za ta mance da Aliyu.
***
_*ABIN ƁOYE*_
Tafiya na ka
ra yin nisa, makonni na shu
ɗ
ewa zuwa watanni, har ta kai lokacin da Ramla suka kammala aji na hudu a Sakandire suka wuce SS2 kai tsaye. A wannan lokacin idan ta ce ta huta daga tunanin Aliyu tasan ƙarya ne. Motsinta da komai ya zama shi, ramarta na tada ha
nkalin Hajiya.
"Na tsammaci ko kujiba-kujibar bikin Rafee'ah ne ke ramar da ke yanzu kam na tsorata. Ki fadamin mene damuwarki? Ko ba ki ga yanda kika bi kika lalace bane? Idan ma tunanin aure kike ki tattara ki ajiye a gefe tunda sanin kanki ne Abba
nki ba zai aurar da ke ba sai kin kammala Sakandire. Wannan ai shirme ne. Kalli yanda ko abin kirki ba ki yi ba a jarrabawa, ni ban ga amfanin wayar da Abbanki ya siyamaki yanzu ba, na tabbata kuma zai kara dauke hankalinki ne kurum daga karatu!"
Duk
wannan bambamin da Hajiyar ke yi, Ramla na zaune tana fidda hawaye ga wayar da Abba ya damƙamata Nokia mai tocila rike a hannunta, ƙala Hajiya ba ta ce ba sadda aka yi budurin ba ta wayar sai bayan fitar Abban ta ke fitar da abinda ke ranta. To itama ta ga
ji! Ta gaji da tunanin mutumin da ba ta san inda za ta ƙara ganinsa ba. Tunaninsa na ta
ɓ
a walwalarta, ya kasance ba ta murna da kiran Hilal, ba ta murna idan ya yi mata aike ta hannun Yaya Munir. Yakan tambayeta ko lafiya ta
ce ba komai. Duk a rashin sanin
cewa yanzun ba shi take da muradi ba, soyayyar wani can da ba ta san inda za ta ganshi ba, ya fi komai dagula lissafinta.
"Shikenan, kin yi shiru ina magana kin rabu da ni! Tunda haka kika za
ɓ
a ki yi ta zama da kuncinnaki, sai dai wallahi kin ji na
rantse muddin wannan shekarar a zangon karatunki na farko (1st term) naga ba ki tsinana abin a zo a gani ba, da kaina ba Muniru ba, zan kwace wayar na kuma hanaki fita. Shashasha kawai!"
Ta dawo nutsuwarta sa'ilin da Hajiyar ta miƙe za ta fice daga fa
lon. Da sauri ta ƙarasa ta sha gabanta, kallon da Hajiyar ta mata sai jikinta ya yi sanyi, ta sunkuyar da kai tana ci gaba da kuka a hankali. Tsakanin
ɗ
a da uwa sai Allah, ba ta san sadda ta ja hannunta ba suka zauna saman kujera.
"Menene Ramlatu? Ku
n samu matsala da yaron ne?"
Ta na nufin Hilal, ta tsinci kanta da gya
ɗ
a kai.
"Amma mun shirya, don Allah kiyi hakuri Hajiya. Na miki alƙawarin chanjawa, wannan karon ba zan ƙara ba ku kunya ba a karatuna."
Jikin Hajiya ya yi sanyi, nan ta
shiga yi mata nasiha akan kar ta sake ta sabarwa da kanta haka.
"Don kin yi fa
ɗ
a da mutum bai zama dalilin da za ki sauya rayuwarki ba. Kenan ko kun yi aure haka za ki dinga yi? To kul! Shi rashin jituwa idan an yi nan take ake yiwa juna sulhu kuma a
nemi gafarar juna. Idan ba mai fahimta bane sai ki bari idan ya huce daga baya ki nemi gafararsa. Wannan damuwar bana so, kar ki ƙara."
Ta amsa da to gami da godiya. A ranar ta yi kokarin sauyawa kuwa, ta rage kulle kanta a
ɗ
aka tana tunane-tunane, gi
dan yanzu daga ita sai Auta A'isha tun bayan bikin Rafee'ah. Hakan da ta yi sai ya kwantar da hankalin Hajiya. Ita kuwa duk abinda take daurewa take gudun matakin da Hajiya za ta dauka a kanta.
Yau wunin gidan Rafee'ah zasu yi tare da Auta A'isha.
Tun safe suka shirya Abba ya ragemusu hanya ya basu kudin mota. Sai da direbansa ya taremusu abin hawa drop har gidan
Rafee'ah sannan suka rabu. A hanya suna tafe tana yin game na snake a waya, kusan a lokacin kaga budurwa da irin wayarta ba karamar babbar
yarinya bace. Wannan ta sa take latsawa cike da jin ta isa.
A daidai junction suka tsaya, ba ta ankara ba ta ji an zare wayar daga hannunta. Cikin razana ta juyo har tana shirin fasa ƙara, yana kan mashin yake dubanta yana dariya. Kirjinta ya buga
da ƙarfi, ta kasa gaskata cewa shi
ɗ
in ne. Hakan ya sa ta lumshe ido ta kara budewa. Ya sauya, ya yi wani fresh, wannan karon ƙananan kaya ne cikinsa. Bakin jeans da riga green wanda ya kar
ɓ
eshi sosai.
"Barkanki."
Ta yi kasa da kai gami da amsaw
a murya na rawa.
"Yauwa."
Ta
ɗ
ago ta mika hannu.
"Bani wayata."
Ta ƙarashe a kasalance, sai dai wani irin annashuwa take ji can ƙasan ranta, ta kasa daina murmushi. Kullum adduarta Allah Yasa ta ƙara ganinsa.
"Allah Ya kar
ɓ
i addu'ata, b
a zan bari ki tafi ban da lambarki ba."
Maganarsa ta katse tunaninta, ta saci kallonsa ya shiga latsa wayarta. Daidai nan aka basu hannu ya ce ma
ɗ
an sahun su tsallaka sai su yi parking. Ba musu akai hakan. Ya danna kira wayarsa ta dauki ƙara, ta saci
kallon wayar, wata ƴar ƙaramar waya ce Lg flip mai murfi ya fiddo. Wayarta ya miƙamata gami da kasheta da kallo.
"Nagode, Allah Ya kaiku lafiya."
Daga nan ya ja mashin
ɗ
insa sabo fil ya yi gaba, suma suka wuce. Ranar wuni ta yi cikin annashuwa,
ji take kamar an mata albishir da aljanna.
Tun daga wannan ranar suka yi wani irin
ɗ
inkewa da Aliyu. So da kauna mai karfi ya shiga tsakaninsu, duk kuwa a sannan
ta ji cewar ya yi aure har tsawon sati hudu. Kishi mai tsanani take yiwa matarsa kuma
ƴ
ar uwarsa MUHIBBAT.
Duk yanda ta kai ga
ɓ
oye alaƙarta da Aliyu abin ya ci tura don tuni Abin Ɓoye ya fito fili.
***
"Gwammaja daidai ina?"
Muryar
ɗ
an sahun a zafafe ya katsemata tunanin baya da ta fa
ɗ
a. Ta sauke ajiyar zuciya tana mai
gyara Affan da ya fara bacci ta hau yin kwatance har suka isa kofar gidan Muhibbat. Ta sallami
ɗ
an sahun ta tashi Affan, ya kuwa farka suka kama hanya.
Gidan Muhibbat take karewa kallo, gani ta yi kamar koyaushe ƙara ƙawatashi ake da sabbin furann
i da kuma abubuwan
ɗ
aukar ido. Da sallama suka sanya kai falon.
Matar gidan ba ta nan sai masu yi mata hidima su biyu sun shantake suna kallon fim na AfricanMagic Hausa. Sai kuwa yaran Muhibbat su biyu a saman kujera wasa. Babban zai yi sa'ar Ansa
r yayinda ƙaramin ya girmi Affan da kadan. Fuskarta ba baƙuwa ce garesu ba, aka gaisa, Mujahid da Ammar suka gaidata. Fuska a sake ta amsa kafin ta dubi Affan.
"Ba gaisuwa?"
Ganin haka ya sunne kai yana wangale baki.
"Bari a kirata." Cewar
ɗ
aya cikin masu aikin tana nufar sama, yayinda
ɗ
ayar ta mike ta nufi kicin. Toh kawai Ramla ta ce tana mai ƙarewa gidan kallo lokaci guda tana kara jinjina arzikin mijin Muhibbat.
'Kin manta itama daidai gwargwado suna da rufin asiri?' Wani
ɓ
angare
na zuciyarta ta tunatar da ita wacece Muhibbat.
_*Mahaifinta Justice AbdulRazak Buba, tsohon alƙali ne a wata babbar kotu ta ƙasa. Ƴan asalin garin Kano ne gaba da bayansu, duk a zuriar Marigayi Malam Buba shi ne fitaccen mai arziki wanda sunansa ya
shahara har wasu a zuri'ar kan ara su yafa. Babban family house ne wanda kusan duk ana tare wuri guda. Muhibbat ita kadai ce
ɗ
iyarsa mace wacce yake so kuma
yake matukar ji da ita. Ita ce kuma wacce kaddarar aure ya fa
ɗ
a mata wanda a yanzun ya zama tarihi.
*_
Ƙ
amshin turaren da ya mamaye falon ne ya ankarar da ita zuwan Muhibbat. Ta
ɗ
ago kai tana dubanta lokaci guda suka sakarwa juna murmushi mai nuni da tsantsar kauna da farin cikin ganin juna. A gefe guda kuwa kamanninta da ALIYU take ƙara gani zahira
n wanda har Muhibbat kan riki
ɗ
emata zuwa kamannin Affan wanda ke matukar kama da mahaifinnasa.
Fara ce mai matsakaicin tsawo, tana da siririn jiki sai dai ba mai muni ba. Gashinta luf-luf ya kwanta har saman goshinta. Mace ce mai hakuri kuma mai yawa
n fara'a. Ba ta daukar lamura da zafi. Cikar kamala dai Muhibbat ta kai, jaruma ce har gobe a idanun Ramlat, yayinda bata fasa yiwa kanta kallon zalamammiya kuma mai laifi a idanun Muhibbat ba.
"Kai Madam, kinga yanda kike ƙara mulmulewa kuwa? Anya
nan gaba za ki nuna kin san mu?"
Muhibbat ke wannan kalamin sa'ilin da take zama da kamo hannun Affan, lokaci guda tana ƙarewa Ramlat kallo cikin dariya.
Harararta ta yi da wasa gami da jan guntun tsaki.
"Kin ji wata magana, ina hutu a wuri
na nida koyaushe ina hanyar Ofis? Hutu ai sai ku Hajiyoyi."
Suka dara.
"Ba ki kyauta ba, shi ne kika bar Ummina da Ansar a gida? Wannan autan na ƙagu ki yi aure a mishi ƙanwa ko ƙani mu ga ta autantaka."
Ta
ɓ
e baki Ramlat ta yi sa'ilin da ta
ke kur
ɓ
ar ruwan da aka ajiyemata.
"Ke kika san wannan, ni kam ai na rufe babin aure har abada."
Jiki a sanyaye Muhibbat take dubanta.
"Kar ma ki fara wannan tunanin, shi aure lokaci ne. Idan ya zo ko bakya so sai mun wanke ki mun kaiki. Kuma
da yardar Allah ma kina so za'a yi shi. Duka-duka ashirin da nawa kike?"
Murmushi mai ciwo Ramlat ta yi, ta basar da zancen ta hanyar janyo jakarta.
"Kar ki dameni da wannan zancen, ni kar
ɓ
i wannan."
Ta miƙa mata envelope da ta ciro,
ɗ
aya n
a kamu da yini ne da za'a yi a Meena Event Centre yayinda
ɗ
aya na dinner party ne da ango ya shirya a Marhaba.
"Allah Sarki mai sunan Mamana za'a fada kwaryar manya, toh Allah Yasa zamu gani. Ya kawo na ƴan baya. Ko Affan?"
Ta ƙarashe gami da ru
ngume Affan wanda tuni ya sake yana dariya. Murmushi Ramla ta yi, zuwa yanzu masu neman ta yi aure dariya ma suke ba ta wasu lokutan.
"Akwai fa taro da za'a yi na family, har jikoki gaba daya. Ba ki da labari?"
Ta girgiza kai.
"Ba wanda ya
fadamin, to wa zai fada?"
Harararta Muhibbat ta yi,
"Ai dole a fada ko don yarannan. Ina jin nan da sati biyu zasu gudanar. Zan biyo mu tafi tare da yarana."
"Toh." Shine kawai abinda Ramlat ta ce, ba ta wani jima sosai ba ta mike. Duk yand
a Muhibbat ta so ta tsaya ta ci abinci ta nuna akwai wuraren da za ta je kan ta koma gida. Dole Muhibbat ta cika Affan da kayan zaƙi kala-kala ta takomata har farfajiyar gidan suka rabu. A hanya tana tafe tana tunaninta. So da kauna tsantsa idan an ajiye n
a ƴan uwantaka a gefe, Muhibbat ta nunawa Aliyu. A yanzun sai soyayyar ta koma kan yaransa. Har ta tsayar da adaidaita suka yi cinikin unguwar Gaida ba ta bar tuna tarin laifuffukan da ta aikata ga Muhibbat din ba.
***
*Son Zuciya*
Zaune tak
e ta zuba uban tagumi ta yi shiru, kai ta
ɗ
aga tana kallon ƙaton enlargement na hotonta da Aliyu. A ƙasa an rubuta sunansu. Aliyu Abdussalam Buba da Muhibbat Abdulrazak Buba. Za ta iya cewa ita ke son shi, son da take mishi ya hanata ganin aibunsa.
T
un suna yara suke shakkar ha
ɗ
a inuwa da shi, don ko kusa ba ya wasa da su. Mutum ne wanda ya fita zakka a zuri'arsu, don kuwa a iya saninsu Aliyu giya ce da kwaya kawai za'a ce yana sha su ƙaryata. Ya soma shaye-shaye a
ɓ
oye ba tare da sanin mutan gida ba.
Hakan ya samo asali ne daga manyan
ɓ
atattun yaran masu ku
ɗ
i da yake abota da su a sakandire, Innarsa Amina bafulatanar Gombe, mace mai hakuri wacce ba'a ta
ɓ
a yin kace nace da ita ba duk kuwa da tarin facaloli da kuma kishiyoyinta biyu da take tare da su.
Aliyu
ɗ
a na fari a wurinta hakan yasa koda wasa ba ta sakewa da shi. Kusan rayuwarsa ya yi ta ne a hannun kakarsa Abulle matar Marigayi Malam Buba. Da wuya ka ganshi cikin gidan Mahaifinsa Abdussalam sai dai sashin Abulle wacce ta dauki son duniya ta
ɗ
ora
akan Aliyu. Wannan tasa a duka yaran Malam Abdussalam, Aliyu ne kadai ke makarantar manyan masu ku
ɗ
i irin na yaran Justice bisa jajircewarsa akan shi ba zai yi makarantar da za'a rainashi ba. A sannan sai da Mahaifinsa ya ji kamar ya mishi duka don shi mu