Showing 123001 words to 126000 words out of 255051 words
yace.
"Ka bata hakuri, ka kuma..."
"A'a Malam, wallahi na gaji. Nima fa ina da aikina ba masinja ba ne. Haka kawai sai a takuran da kaiwa da kawowa wurin fa
ɗ
ar saƙo. Toh na gaji fa, ana cin lokacinm
u nisa Princess. Haba, aure ko wata ba'a yi ba an ban sabon aiki?"
Har
ɗ
e hannu Hussein ya yi a kirji yana dubansa fuska dauke da murmushi, ya maida idanunsa sararin samaniya yana ganin yanda ake zuba walkiya da kuma iska. Ba ta
"Give me her di
gits."
Ba Hisham ba da mamaki ya kusan kaiwa ƙasan gwuiwa, hatta shi
ɗ
in da ya nemi lambar sai da ya ji fa
ɗ
uwar gaba, ya nemi tsoro da fargabar abinda hakan zai haifar ya rasa, ji yake kamar akwai abinda ke danneshi.
"What did you say?" Hisham
ya fa
ɗ
i kusan a birkice. Maimakon ya amsa sai ya fiddo wayar ya ajiye saman mota ya bude murfin zaman direba ya shiga ya soma kokarin tayarwa. Ganin haka Hisham ya dauki wayar bayan ya fiddo tasa wayar, hannunsa har rawa yake yana mai jin wani farin ciki,
fatansa yake so ya tabbata. Lambar Ramlat na Mtn da Airtel duka sai da ya
ɗ
uramasa, kowanne ya
ɗ
an danna kira amma sai ya kashe bai bari ya shiga ba, so yake dai lambobin su fada cikin Log.
Ta cikin gilas ya miƙa masa wayar.
"Shegen sama, g
ashinan ba ruwana kuma idan Hajiya ta gani, wallahi kar ma ka ambaci sunana. Ban yi saving ba, idan ka ga dama ka sanya Rabe a kan sunan ko Talle Mai Wanki."
Dariya sosai Hisham ya ba shi, suka hau yi can kuma ya
ɗ
an lumshe ido ya bude.
"Zan ram
a
ɗ
aya bayan
ɗ
aya wallahi, ka yimin duk abinda ka ga dama yanzu. Sannan ni ba da wata manufa ma nemi lambar ba kar ka yi zaton akwai wata bayan Zeenat, wai don na ragemaka zirga-zirgar ce. That's it."
Hisham dai dariya ya yi bai ce uffan ba. Suka yi
sallama ya ja motar ya nufi Rijiyar Zaki.
***
Washegari direba ta sanya ya kai yara makaranta, ko bakomai tana son yin baccin safe kadan sannan ta yi shirin Ofis. Ga garin ya yi luf sakamakon ruwan da aka samu a daren jiya. Wannan ne ya bata dama
r komawa bacci mai dadi bayan tafiyarsu. Ba ita ta farka ba sai da wayarta ta Soma ringing.
Duk yanda ta kai ta share hakan ya gagara don mai kiran bai yi
ɗ
aya ya haƙura ba. Da wani irin takaici ta mike ta ja tsaki kafin ta duba sunan dake yawo sam
a screen. Hilal. Ɗagawa ta yi da sallama.
"Ayya na tasheki a bacci kenan. Shikenan ma yi magana anjima. A yi bacci lafiya."
Bai jira cewarta ba ya katse kiran, murmushi ta
ɗ
an yi ta kara maida kanta cike da kasala. Wayar dai ta ƙara ringing, a
dolenta ta miƙe zaune. Lambar Salisu na ofishinsu ke yawo saman screen. Ta
ɗ
aga da sauri.
"Ramlat, kina ina ne?"
"Haba Yalla
ɓ
ai, ba sallama ba komai?"
Ƴ
ar dariya ya yi sannan ya yi sallamar suka gaisa, ya
ɗ
ora.
"Kiyi hakuri, abin ne
naga gwara na sanar da ke shiyasa shaf na mance da wannan batun."
Cikin rashin nutsuwa ta zuro kafafunta ƙasa.
"Lafiya Salisu?"
"Ji nayi Oga Ɗalhatu na maganar an miki sauyin wurin aiki, za ki koma
ɓ
angaren Chairman, a matsayin secretary
ɗ
insa."
Kirjinta ya bada dam! Koda ace ranta a
ɓ
ace yake jiya, ba ta mance irin shu'umin kallon da Chairman Aliyu Dikko ke watsamata ba. Ba ta son ta munana zato game da abinda ba ta da tabbacinsa kamar yanda take ganin baƙin jama'ar ma'aikatar da ke
gulmar Chairman din da cewa
ɗ
an iska ne. Don haka sai ta kyautata zato.
"Ko kina da masaniya ne Ramlat? Naji ba ki ce komai ba?"
Dan murmushi mai sauti ta yi.
"Banda ka fa
ɗ
i bani da labari Salisu. Yanzu ai zan shigo ofishin In sha Allah.
Sai na ƙaraso."
Daga haka suka yi sallama, shiru ta yi na
ɗ
an lokaci, so take ta gani ko za ta iya fahimtar manufar yin hakan, sai dai duk iyakar tunaninta ba ta gane komai ba. Tasan dai ko mene ba alheri ba ne tunda mutumin Hajiya ne.
Miƙewa
ta yi ta shiga wanka, a gaggauce ta shirya cikin doguwar rigarta na Atamfa, mai kawai ta shafa kafin ta zura hijabinta dogo ta dauki duk abinda take
ɓ
ukata ta fito. Sai a sannan ta tarar da missedcalls har uku duk daga mutanen Department dinsu ne. Ba wand
a ta bi, ta karasa ta gaida Hajiya dake zaune suna hira da Ladidi.
"Yau dai babu niyya. Daga jin sanyin gari kin shantake."
Dariya ta
ɗ
an yi.
"Wane sanyi? Ai da saura ruwan Hajiyarmu. Bai kankama ba tukunna!"
"Allah Ya bamu damina ma
i albarka dai." Fadin Hajiya, suka amsa. Ta gaidata karo na biyu kafin ta dubi Ladidi su gaisa sannan ta karya a gaggauce ta fita. Ba ta iya ta sanarwa Hajiya sauyin da aka yi mata ba, bar wa cikinta ta yi har sai ta je ta ji asalin abinda ke wakana.
***
AKWAI WATA AI just published "BABI NA TALATIN DA HUƊU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/WcD6L9EP0ab
🕯
️
*ƘARFEN ƘAFA*
🕯
️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
34)
AKWAI WATA A ƘASA...
Gaban Notice Board ta soma tsayawa, shakka babu dagaske Salisu yake, ajiyar zuciya ta sauke bayan kammala karanta bayanin sauyin da ta samu. Sati mai zuwa za ta fara sabon duty dinta.
"Allah Yasa hakan ya fi alheri." Ta fadi a fili sannan ta kara
sa cikin ofis dinsu wanda kiris ya rage ta bar shi. Bayan sun gaisa ta zauna.
"Za dai mu yi kewarki anan Ramlat, ko ba komai kin fi wasu a nan."
Fadin Oga Ɗalhatu, aka
ɗ
an dara idan ka cire Halima da hassada da bakin ciki ya cikamata zuciya, yan
da ta ke jin tsanar Ramlat a yanzun har ya fi na baya. Ta jima tana burin kasancewar mai aiki a ƙarƙashin Chairman duk kuwa da cewa hakan bai rage ko ƙara albashinta ba, amma dai tasan alhairan da ita za ta kwantar da kai ta samu wurin Chairman, ba lallai
ne ita Ramlat ta yi ba.
"Ki dai bi sannu don kinsan ko waye shi."
Cewar Halima tana yamutse fuska.
"Kedai ba ruwanki, zato zunubi. Kuma kin fi kowa sanin Ramlat da halayyarta." Fadin Zuhra kenan.
Ramlat kallonta kawai ta yi ba tare
da ta tanka ba, tsaf ta gama gane wacece Halima da kuma irin takun saƙar da take yi da ita wanda ita kam ba ta ga dalilinsa ba.
Da wannan damuwar ta dawo gida ta sanar da Hajiya halin da ake ciki.
"Toh ke meye naki na damuwa? Sauyi ne fa kawai,
idan batun kamun kai ne ai na yarda da ke bana jinki a wannan
ɓ
angaren. Allah Yasa hakan ya zamemaki alheri."
Ta amsa da amin.
Bayan Magriba suna zaune tana koyawa yaranta Homework, Maigadi ya yi sallama a bakin ƙofar suka amsa. Jin saƙon wai
ana sallama da Ramlat ya ba ta mamaki, ta dubi Hajiya, itama kallonta take tana murmushi.
"Ka ce tana zuwa."
Bayan tafiyarsa ta dubi Hajiya.
"Haba Hajiya, mutum da bansan ko waye ba, yanzun ai ba'a irin haka, da ace ya san ni toh ba zai r
asa lambar wayata ba. Ta nan zai neme ni."
Harararta Hajiya ta yi.
"Kuma ya zama dole ki fita ba, naga alamar kin fi kaunar zama a haka babu aure, toh ya isa. Nima kamar Babanki Dakta, ba zan ƙara biyemaki ki kori masu zuwa wajenki ba. Idan ma a
baya an yi bai wuce na tausayawa marayunnan ba. Tashi maza ki je."
Kamar ta yi kuka ta ce.
"To wa zai ƙarasa koyamusu?"
"Jeki, nasan duk da
ɗ
ewa ba za ki wuce awa
ɗ
aya ba. In Sha Allahu ma ba su kai ga yin bacci ba. Tunda kin sallami Affan ai
da sauƙi."
Miƙewa ta yi ranta duk ba dadi, hijabi kawai ta zura ta kama hanya su Ummi na kiran a dawo lafiya, a tahomusu da alawa. Harara kawai ta watsamusu ta yi gaba ta bar Hajiya da dariya.
Sai dai me? Wanda ta gani ya matuƙar shayar da ita m
amaki, sakin baki ta yi kafin kuma su yi dariya a tare.
"Kai Yaya Hilal, yaushe ka zama baƙo a gidannan? Kuma fa ko Malam Bala bai fadamana wanda ke sallamar ba."
Dariya ya yi. Sanye yake cikin shaddarsa ruwan toka, ya karya hularnan ta zannah
Bukar ta zauna caras a kansa. Yana daga cikin mota zaune a inda ya fiddo ƙafarsa
ɗ
aya waje.
"Ke din ce sai da hakan, farko na so kiran wayarki sai kuma na fasa tunda nasan dai zai wahala ace a wannan lokacin ba kya gida. Malam Bala kuma ni na roƙeshi
akan kar ya ce ni ne saboda yau zuwan naki ne ke
ɗ
aya."
Ta
ɗ
an sadda kai ta yi shiru, ta san tatsuniyar gizo ba ta wuce na ƙoƙi. Abu ne da ba ta jin har abada za ta iya aminta da shi.
"Ɗan zagayo mana ki zauna."
Ba tare da musu ba ta zagay
a ta bude motar ta shiga, kamar yanda ya bar ƙofa a bu
ɗ
e, itama hakan ta yi. Gaidashi ta soma tare da tambayar iyali da wajen iyayensa. Ya amsa mata cike da annashuwa.
"Kin
ɓ
uya da yawa, ta ko'ina gujemin kike kamar rai da ajali. Na rasa hanyar
ɓ
ullo
maki. Sai na kiraki ki share ki ƙi
ɗ
auka, daga baya na samu text dinki wai ba kya kusa ne nayi hakuri. Anya kuwa?"
Kunya ta kamata, ashe dai ya gane. Ita kuwa dalilinta na yin hakan a ganinta mai ƙarfi ne. Kokarin nesanta kanta da shi ta ke yi ta kowa
ce hanya don ba ta son jawowa kanta magana.
"Ka yi hakuri."
"Na yi, amma ba duka ba. Ramlat, Maman Ummi, Ansar da Affan. A karo na biyu ga Hilal nan, bai kuma zo da niyyar yaudara ba. Aure ne ya kawoshi idan har kin amince."
Ajiyar zuciya t
a saki don dama ta san maganar kenan, jikinta ya yi sanyi da irin wannan soyayyar ta Hilal gareta. Ta dubeshi, shi dinma ita yake kallo babu ƙaƙƙautawa. Ɗan kauda idanunta ta yi.
"Ko da can ma ba ka zo min da niyyar yaudara ba balle kuma yanzu. Asali
ma ni ce na yaudareka. Ka yi hakuri Yaya Hilal. Don Allah ka yi hakuri."
Ta ƙarashe a raunane, ita sam ba ta san ta
"Ka yi hakuri."
"Ba hakuri za ki bani ba, dalilinki na guduna za ki fa
ɗ
amin. Idan da wajen da na kuskuro na gyara."
Gir
giza kai ta shiga yi, kwalla ta soma ciccikomata idanu. Hilal wane irin mutum ne mai matukar sanyi da hakuri? Wace irin soyayya yake mata da ya kasa ganin laifinta?
"Akwai abubuwa da dama da ya kyautu na gujeka dominsu. Ba ka ta
ɓ
a yimin laifi ba, ba z
an iya kallon danginka a karo na biyu ba a matsayin matarka. Bayan abinda ya faru wa kake tunanin zai ƙara kallon Ramlat matsayin matar kirki? Wallahi da kaina na fa
ɗ
a, bani da kirki, ban yi halin hakuri da dattako na iyayenmu ba. Ka yi hakuri Hilal, mu ƙa
ddara ba'a rubuto aure tsaka.."
Ta kasa ƙarasawa saboda kunya da kuma irin hararar da ya watsamata. Can kuma ya numfasa ya runtse ido. Da ace ta san yanda yake jinta a rai da ba ta ce haka ba, a gefe guda kuma bai mance irin kalaman da iyayensa suka y
i gareshi ba muddin ya ce zai aureta ko bayan ransu ne. Kansa ya yi zafi da yawa.
"Ka yi hakuri."
Ta kara nanatawa, a wannan lokacin tuni hawayen sun zubo. Ya bude idanunsa da suka ka
ɗ
a ya dubeta.
"Bana jin har abada zan manta da ke Ramlat
, you are my first love. Ki daina bani hakuri, da ace zan iya da tuni na rarrashi zuciyata. Aurenki da Aliyu na dauki hakan matsayin rubutaccen al'amari wanda ba makawa sai ya faru. Albarkar auren gashinan mun gani (yana nufin yaranta), don haka ni wallahi
tuni na yafe abinda kika yi gareni. Idan da naki a sannan, nima ai akwai nawa tunda ni na naace akan sai na aurekin ko ba so. Kar ki saurin yanke hukunci a kanmu, na baki nan zuwa sati kiyi tunani mai kyau, koda ba ki kirani ba, da zarar lokaci ya cika za
n kawo kaina."
'Allah Sarki.' Ta furta a ƙasan ranta. Da wannan suka rabu ya bata kayan maƙulashe na alawa da biskit da ya siyowa yara. Ta kar
ɓ
a gami da godiya suka yi sallama ta shige ciki.
Hajiya zaune a falo ta a gyangya
ɗ
i ka
ɗ
an-ka
ɗ
an, yaran
sun ƙurawa talabijin idanu su na kallon Angrybird.
"Waye ne ya zo?"
"Yaya Hilal ne."
Hajiya ta mike zaune.
"Yaronnan dai dagaske ya ke yi."
Ramlat ta zauna jikinta a sanyaye.
"Na rasa ya zan yi Hajiya, ya dage aurena ya ke
son yi. Na rasa hanyar
ɓ
ullomasa ya fahimci illolin da hakan zasu haifarmin a danginsa da wurin matarsa."
"Nima bana goyon bayan aurenki da shi, sai dai bamu san abinda Allah Ya
ɓ
oye ba tunda har ya kasa hakuri ya dawo karo na biyu. Shawara ki dage da
addu'ar neman za
ɓ
in Allah, duk abinda Ya yi mai kyau ne."
Jinjina kai ta yi cike da gamsuwa.
***
A kwana a tashi ba wuya a wurin Mai Rahma, bikin Munir ya taho. Ana gobe za'a yi
ɗ
aurin aure ƙalilan daga mutanen Daura suka iso don Hajiya ba ta
yi gayyata ba duba da cewar ba'a jima da bikin A'isha ba.
An daura aure lafiya, a daren aka yi shirin tafiya dinnerparty. Ramlat da yayyunta mata har A'isha da Amrah wacce basu daukarta bare cikinsu, ankonsu iri daya na wani leshi peach colour. Ko
wannensu riga da skirt ya zauna
ɗ
as a jikinsa.
Motarta daga ita sai Amrah don Yaya Munir ya ce babu yara. Suna tafe suna hira, anan take ba ta labarin sauyin da aka yi mata wurin aiki, ta kara da fadin.
"Tsorona daya, rashin sanin taƙamaiman man
ufar wannan Chairman
ɗ
in. Ina tsoron ya kasance wani mugun abin ne."
Amrah tana taunar cingam din da ya zamemata ciki tun tana laulayi har a yanzun da cikinta ya shiga watansa uku.
"Kar wannan ya dameki, ai kinsan kanki. Daidai gwargwado kin san
mutuncin kanki kina kuma karewa. Addu'a za ki yi ta yi akan Allah Ya kareki daga sharrinsa. Ba abinda zai faru amma shakka babu dai akwai wata a ƙasa!"
Jinjina kai Ramlat ta yi.
"Wallahi ko ba ki fa
ɗ
a ba Amrah, ni ban ta
ɓ
a ganin mace mai irin kis
hin na wannan matar ba."
Amrah ta
ɗ
an muskuta.
"Af, kin ce za ki nunamin hotonsa."
Ta yi murmushi.
"Mu ƙarasa tukunna."
Daga nan suka fa
ɗ
a wata hirar ta daban har ta ke sanarmata da kiran da Baba Dakta ya yi mata. Amrah banda dariy
a da hamdala ba abinda ta ke yi.
Wurin ya cika sosai, mafi yawa dangin Amarya Hunainah ne.
"Ke me ya kawo waccan wurin nan?"
Cewar Amrah tana kallon Salma kanwar Bilkisu.
Idanun Ramlat ya kai gare ta. Ta
ɓ
e baki ta yi.
"Au ke duk
hirar da su Maman Twins suke yi ba ki ji ba? Cewa fa aka yi itama Bilkin za ta zo. Ita gwanar kissa."
Suka yi dariya suka karasa ciki basu kara kallonta ba. Salma ta bisu da harara ta ja dogon tsaki gami da fadin
"Munafukan banza!"
Koda sun
ji basu tanka ba.
Sai da suka samu wuri suka zauna kafin Ramlat ta fiddo wayarta ta lalubo hoton ƴan biyun da ta dauka ta miƙa wa Amrah. Sakin baki da hanci ta yi tana kallonsu.
"Wow! Ke wai Twins ne? Toh ai banda gilashin da ke idanun daya, b
a za ka ganesu ba. Lallai wallahi ban ga laifinta ba, dole ta yi kishi. Amma kika ce babba ce?"
Amrah ta ƙarashe fuskarta
ɗ
auke da tsantsar mamaki. Dariya ta ba Ramlat.
"Dattijuwa ma kuwa don idan ma ba ta yi sa'ar Hajiyarmu ba, kadan ya yi mata
saura ta yi. Ke kin gani kinsan wuff ta yi da shi."
Suka yi dariya can kuma Amrah cike da tausayawa ta ce.
"Wallahi nidai sai naga kamar ba banza ta bar shi ba. Wannan kyakkyawa ya tsaya a auren sa'ar uwarsa? Gaskiya jikina na bani akwai wata a ƙ
asa Ramlat."
Ramlat ta gyara zama don ta sosamata inda ke mata ƙaiƙaiyi.
"Ke kenan da ba ki ma ga matar ba. Ni banda duka wannan kinsan cikin biyunnan na hoto ba wanda ban hadu da shi ba?"
"Me kike nufi?" Amrah ta tambaya da rashin fahimta.
Ramlat ta