Showing 201001 words to 204000 words out of 255051 words
da
ɗ
awainiya."
Ya murmusa yana shafa sumar kai. A hankali ya kai hannu ya bude dayan murfin na motarsa. Dubanta ya yi.
"Da
n zagayo ki zauna ki ban aron koda mintuna biyar ne, magana zamu yi."
Ta yi shiru ba ta tanka ba, karshe ma ta daure fuska don ta san wani sabon rainin hankalin ne.
"Please." Ya furta a sanyaye, sai ta ji ba za ta iya jan musu ba don haka ta zaga
ya ya bita da kallo har ta shigo ta zauna. Shiru ya biyo baya har dai ta ƙosa amma ba ta ce komai ba, shi kuwa yanda ta ke hura hanci ke ba shi mamaki da dariya. Ya
ɗ
an murza karan hancinsa kafin ya soma magana cikin nutsuwa.
"Satina sama da biyu a Ad
amawa, ba ki samu damar yimin ko gaisuwar juma'a ba, why?"
Ranta ya sosu ainun.
"Ina tunawa da wadanda suka tuna da ni. Bana sanya ka layin wadanda suka zamemin wajibi na nema balle na gaida."
Ɗ
if ya yi kamar mutuwa ta ratsa, ta daurewa zuc
iyarta ba ta kalleshi ba sai dai ta ji wani irin sanyi a zuciyarta ko ba komai ta
ɗ
an huce daga maganar da ya gasamata. Sai ta tsinci kanta da murmusawa. A hankali ta saci kallonsa don ganin yanayinsa, ga mamakinta murmushi sosai yake haƙoransa a waje, ya
juyo rabin jikinsa ya tallafi ha
ɓ
arsa da hannunsa
ɗ
aya yana kallonta. Ta kauda kai.
"Hakan ma na gode sosai. Kin burgeni. Rashin wancan mutumin ne yasa ki ka sauya har ki ke gasan magana ko? Hum, za ki huce."
Ba ta ce uffan ba hakan yasa ya gama
shan ƙamshinsa ya
ɗ
ora.
"Alhamdulillah, na sadu da iyaye da yan uwana lafiya. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijin Talikai. Wannan yana
ɗ
aya daga cikin dalilan da har abada Hussein ba zai mance da Ramlat ba. Na je Mubi kuma na je Maiduguri
. Ban ta
ɓ
a zaton zuwan rana makamancin hakan ba, komai ya faru bisa jajircewarki akan dukkan lamurana. Na gode. Ina kara godiya da fatan alheri gareki. Har abada ba zan mance da halaccin da ki ka yi gareni ba. Allah Ya ba ki abinda kike so kuma ya ke sonk
i."
Ta dubeshi, idanunsa a lumshe har lokacin murmushin ya ke, ganin zai bude yasa ta janye nata idanun kirjinta na bugu. Ta rasa wane irin so ne na Hussein a zuciyarta. Son da ba ta jin ya kai irin wanda ta yiwa ALIYUNTA. Idan Aliyu da dadin kalamai
ya rinjayi zuciyarta, ta rasa da me Hussein ya rinjayi nata zuciyar.
"Zan tafi."
Abinda ya ce kenan.
Ta sa ƙafa kawai ta fice ta rufe mishi ƙofar ba ta ce uffan ba kamar yanda bai tanka mata ba har ta yi gaba abinta. Murmushin ya ƙara yi g
ami da lasar lebbansa. Allah kadai Yasan sirrin da ke cikin zuciyarsa. Ya sauke ajiyar zuciya ya tashi motar ya fice.
***
Hajiya Zeenatu ta rausayar da kai ta ƙara duban Hajiya Batool da ta saki baki tana kallonta, murmushi ta saki ta ce.
"Kin
a mamaki ne?"
Hajiya Batool ta furzar.
"Kema ai kin san dole akwai mamaki Zeenatu, shi Hussein din ne ya sauyamaki mota? Har ya ke tambayarki abinda kike da buri a yanzu? Kuma ya amince da ku bar ƙasar babu wata gardama? Anya kuwa Zeenatu ba wani
tarkon ya ke shiryamaki ba? Ƴan uwansa kuma sun yarda da zamanku tare? Anya babu lauje cikin na
ɗ
i?"
Ɗ
aure fuska ka
ɗ
an Hajiya Zeenatu ta yi.
"Me kike son ki ce? Na fiki sanin Hussein, bai iya yaudara ba. Ko a baya balle kuma a yanzu. Duk isar mut
um bai isa ya kawo mishi wargi ba balle ya yi ƙarya dominsa."
Hajiya Batool ta tsaya kawai tana yi mata kallon sakarya.
"Ke ba wannan ne damuwata ba, wasu shegun ƙuraje ne suka fesomin a cinyoyina. Ba ƙaiƙayi balle zafi, su dai gasunan ne kuma s
una
ɗ
urar ruwa."
Hajiya Zeenatu ta katse tunanin Batool, kusan ma katse zancen ta yi don ba ta son ji.
"Ya kamata dai ki je asibiti. Tunda dai ko ba komai za ku ci duniyarku da tsinke yanzun."
Suka sa dariya gami da cafkewa duk kuwa da cewa
r jikin Hajiya Batool bai gama gasƙata sauyawar Hussein ba.
***
Tsaye suke a farfajiyar katafaren shagon na A&Z, Hisham sai faman shan ice cream yake a roba yayinda Hussein ya maida hankali ga danna waya. Tattaunawa suke yi game da abinda ya ke son
shiryawa akan Hajiya Zeenatu. Shi Hisham ma duk haushi ya ke ba shi don haka ya ja guntun tsaki.
"Kai nifa wallahi haushi ka ke ban idan kana zancen matarnan. Ban ta
ɓ
a zaton ko second
ɗ
aya za ka iya ƙarawa da ita a gida
ɗ
aya ba. Ban zaci za ka ƙara w
ayar gari ka gan ta kuma ka bar ta a gidanka ba. Da kunnenka ka ji ita Halima na yimin rantsuwar cewa akwai sa hannun matarnan a abinda ta aikata. Na ji, babu kwakkwarar hujja mai ƙarfi da kotu za ta kama Hajiya Zeenatu da shi akan hakan, amma kai kana da
hujjojin da za ka iya
ɗ
aukar kowane mataki a kanta ba dole sai hukuma ba. Kafin na furtamaka cewa Zeenatu ce ta sa Nos Khadija aikata kisa, kai ka soma furtawa kuma ka sa na nemi gidan yarinyarnan da kaina na nunamata hoton Zeenatu ta tabbatarmin cewa ita
ce. Me ya yi saura? Me kake jira bayan komai ya fito fili."
Hussein ya yi murmushi gami da zaro hankicif a aljihu ya miƙamasa.
"Goge bakinka, ya
ɓ
aci."
Hisham ya harareshi kafin ya warce ya goge ice cream din da ya
ɓ
atamasa gefen baki tsaba
r masifa.
"Ba na abu kai tsaye, na fi kaunar komai da cikakken hujja Hisham. Sannan ma tsaya, me kake nufi game da Matata? Ina sonta fiye da yanda ta ke sona. Har abada ba na jin akwai wani ko wata da ya isa ya raba ni da Zeenatu. Zan iya yin komai d
on ganin na sanya ta farin ciki. Kar ka damu da komai, komai da na fada ko kuma ya faru, ba komai bane. Abinda zai faru a gaba shi ne abin kallo. Shi ne abinda zai fi burgeka a lamarin soyayya."
Hisham ya bishi da kallon ta
ɓ
a
ɓɓ
e, sai dai wacce ya gani
tsaye bayansa ta jikin gilashin motar Hussein, yasa ya gano dalilin sauya maganar Hussein din. Shigowarta wurin kenan daga gidan Hajiya Batool, a waje ta yi parking ta ajiye motarta don ba jimawa za ta yi ba tana sauri ta koma gida ta girkawa mijinta abin
ci, wani abun ta mance a
ɗ
azun dole ta dawo
ɗ
auka.
Hussein wanda ya yi kamar bai ganta ba, ya ci gaba da magana.
"Kar ka yarda da maganar mutane, Zeenatu ba za ta ta
ɓ
a kisa ba balle har ta sanya wani ko wata ya yi yunkurin yi. Na fika saninta. D
on haka duk wanda ya fa
ɗ
amaka Zeenatu ita ce silar shigar Ramlat wannan yanayi, karya ce."
Wani gumi ta ji ya yankomata, ta yi saurin juyamusu baya ta sharce. A hankali ta saita nutsuwarta kafin ta juyo ta tako inda suke tana murmushi.
"Ah, ku na
nan?"
Sai a sannan suka yi kamar lokacin suka ganta.
"Sannunki, yaushe ki ka zo?"
Ta maida duba ga Hisham tana jifansa da wani irin kallo kafin ta maida ga Hussein.
"Yanzu na shigo, mantuwa nayi zan dauka. Sannu abokinmu, ya gida?"
Hisham ya sauke ajiyar zuciya, dakyar ya ƙaƙalo murmushi ya jefamata.
"Lafiya kalau Uwargidan Hussein."
Ta gyada kai.
"A gaida mutan gida."
"Za su ji."
Daga haka ta yi gaba, Hisham ya bi bayanta da harara. Murmushi Hussein ya yi
.
"Hararar fa?"
Tsaki Hisham ya ja.
"Kai dai ban san sadda ka koyi makirci ba."
Dariya kawai Hussein ya yi, shi kadai ya bar wa cikinsa abinda ya ke shiryawa.
***
"Resigning?" Darakta ya maimaita da mamaki da kuma jin wani irin k
aryewar zuciya. Cike da ladabi Hussein ya jinjina kai.
"Yes Sir."
Kwata-kwata abin bai mishi dadi ba, samun mutum irin Hussein da ya iya gudanar da kasuwanci da amana da kuma ƙwarewa abu ne mai matuƙar wahala. Kwandala idan ba ta Hussein ba ce ba
zai ta
ɓ
a ci ba kamar yanda duk wani marar gaskiya da ha'inci, nan da nan ya ke ganoshi kuma a take ya yanke masa hukunci kafin ya sanarmasa.
Hussein bai katse tunanin Darakta ba don dama ya san za'a rina, wai an saci zanin mahaukaciya, Darakta Sa'ad
mutum ne da ya ke kaunarsa kamar
ɗ
an da ya haifa. Don ma Hussein din bai fiye son shigewa mutane ba, da ya tabbata zumuncinsa da Daraktansa sai ya fi haka.
"Meye uzurinka amma?"
Darakta ya tambaya ransa ba dadi. Murmushi sosai Hussein ya yi ya
na jinjina wannan kaunar.
"Adamawa zan koma da zama, cikin dangina."
Da mamaki ya ce.
"Dama kai din
ɗ
an Adamawa ne?"
"Eh."
"Ikon Allah."
A karshe dai suka yi magana mai tsawo kafin Darakta ya dakatar da shi zuwa lokacin da za
i samu wanda zai maye gurbinsa. Da wannan suka ajiye magana.
***
"Wai nikam Alhaji na rasa gane kanka. Ban san me zai sa zuciyarka ta sauka daga dokin fushin da ka hau ba."
Kawu Modibbo ya daure fuska sosai yana kallon Anti Amarya.
"Me kik
e son ki ce?"
Anti Amarya ta sauke ajiyar zuciya.
"Ya dace ace zuwa yanzu ka watsar da makaman yaƙinka kamar yanda ƴan uwanka suka watsar. Ya dace ace yanzu gabar da ke tsakaninka da su Dada ya wuce. Ko maƙiyin Dada ya kira ya tayata murnar gani
n Hussein amma kai kam na..."
"Ni kike fa
ɗ
awa maganar banza da wofi?! Ke kinsan waye ni kuwa? Idan har kina so ki tsira da mutuncinki da kuma aurenki, ki yi gaggawar fita a idona! Wannan ne gargadi na karshe da zan maki game da lamarin Amina da iyalin
ta. A wurinki ki ke ganin komai ya wuce, amma ni har abada ba zan ta
ɓ
a bari wata alaƙata shiga tsakanin ni da yara da ba'a san asalinsu ba! Aminu dai ya zo ya kawomana karuwarsa ya kuma tafi ya bar munda bara gurmi a cikin zuri'armu. Na ji! Amma ba wanda y
a isa ya yi min dole kan na kar
ɓ
e su. Shi kuwa Tahir yau ko ni ko shi tunda ya za
ɓ
i zama da su a kaina! Zan nunamasa ni ne nan ubansa!"
Kawu Modibbo na kai wa nan ya mike ya nufi
ɗ
aki, ransa idan ya yi dubu ya
ɓ
aci, ga Bokansa ya tabbatar masa babu sa
uran ƙofar da wani asiri zai shiga jikin Hussein da sauri sai dai a sannu. Yanzun ya gama gane ba iyakar tsana kawai ya yiwa zuri'arnan ba, har da bakin ciki da kuma jin tsantsar hassadar yanda ba su rayu a wulakance kamar yanda shi da Innarsa a baya suke
fata ba. Sai ya kasance koyaushe sai dai ya yi ta jin labarin nasarorinsu. Ga dai yaransa nan amma kowanne da kalar shashancin da ya sa gaba, kalilan ne a yaran suka kama dahir. Wato dai suka yi karatu kuma su ke aiki, aikin da bai kai darajar na AlHassan
ba. Ko iyaka nan aka tsaya ya san za su yi mishi dariya, abinda ba zai jure ba kenan.
***
"Ya akai
ɗ
an uwa?" AlHassan ya fadi kai tsaye daga
ɗ
ayan
ɓ
arin. Hussein ya kara gyara zaman wayarsa duk kuwa da cewar tuƙi ya ke yi.
"Lafiya, batun maganar
da muka yi, yaushe za ka zo?"
Murmushi mai sauti AlHassan ya yi.
"Ai ka ji, dama sai da na ce maka ka yi hakuri mu taho tare komai zai fi bada ma'ana, yanzu gashinan tun ba ka tafasa ba za ka ƙone."
Hussein ya
ɗ
an cire hannunsa saman sitiy
ari ya shafi sumar kai yana murmushi kafin ya mayar.
"I'm sorry, ka san.."
"Ko ba ka fa
ɗ
a ba na sani. Na san kuma dalilinka. Hakan ma ya yi daidai. Fadamin, me ka zo ka tarar?"
Tiryan-tiryan ya ba shi labari, AlHassan ya yi dariya.
"Alh
amdulillah. Wannan ma nasara ce. Zeenatu get ready."
Suka
ɗ
an ta
ɓ
a hira abinsu suka yi sallama.
***
Da yammacin ranar juma'a, tana zaune saman kujera suna hira da Baban Hanif, damuwa karara ta bayyana saman fuskarsa.
"Mamin Affan, ban san
dalili ba, amma gabana faduwa ya ke, sai na ga kamar zan rasaki, sai naga kamar duk wannan rawar ƙafartawa zai zama mafarki."
Ta
ɗ
ago kai da zummar ba shi amsa da
ɗ
an murmushi saman fuskarta, ya yi daidai da bude ƙaton kyauren gidan, motar Hisham ce t
a shigo sai dai a gefensa mai zaman banza, Hussein ne.
Kauda idanu ta yi gami da danne bugun da kirjinta yake ba tare da fuskarta ta nuna ba.
"Me zai sa ka fargaba? Akwai wani lamarin da ya fi karfin addu'a? Komai na Allah ne."
Ya jinjina k
ai, har sannan bai ji zuciyarsa ta sake ba. Yana son fa
ɗ
amata sakamakon da binciken tarihinta ya ba iyayensa amma ya danne a ransa har zuwa sadda zai kammala nashi binciken ya gane gaskiyar lamari.
Daga cikin motar kuwa, Hisham ji ya yi wani murmu
shi ya su
ɓ
uce masa, abinda ya fi dadi, ya ji na zuwan da ya yi da Hussein gidannan. A farko Hussein bai yi niyyar zuwa ba, sai dai kwadayin ladan da ke cikin ziyartar iyaye da ma yan uwa da asibitoci a ranar juma'a yasa shi cewa su je din. Sai da suka soma
zuwa gidan iyayen Hisham din suka ci abinci kafin su zo gaisuwar surukai kuma yan uwa a wajensu yanzun. A farko Hussein gardama ya ke mishi kan zuwa ziyartar Kawu Modibbo da Hisham ya ke so su yi a ranar, sai dai shigowarsu gidan da mummunan tozalin da ya
yi ya sa shi yin
ɗ
if har hakan ya ankarar da Hisham shima ya kai idanunsa garesu.
"Muje ko?" Hisham ya katse tunaninsa yana kara nazartar yanayin sauyawar fuskarsa. Babu annuri.
"No, shiga ka fito."
Dariya mai karfi ta kama Hisham sai dai
dakyar ya ha
ɗ
iye, idanun Hussein din akan Baban Hanif yana son tuna inda ya ta
ɓ
a ganinsa.
"Ah, wai Hajiya Ramlatu kake kallo? Kai wai dama Haris ne? Bari na je mu gaisa."
Hussein a sannan ne ya watsawa Hisham banzan kallo kafin ya ja tsaki, kusa
n a tare suka fito daga motar. Baban Hanif na ganinsu ya taso da fara'a ya karaso. Maimakon Hussein ya tsaya kawai sai ya yi gaba yana shan murr ko inda suke bai kalla ba. Baban Hanif ya bishi da ido sadda hannunsa ke cikin na Hisham su na musabaha. Ramlat
ta dora kafa daya kan daya tana fitar da wani irin murmushi mai kama da yaƙe. Sauyawar Hussein ya mugun kasheta da ba ta mamaki.
"Ranki ya dade, girman kujerarki."
Sai a sannan ta sauke ƙafar ta gaida Hisham fuska a sake. Daga bisani shima ya y
i ciki.
Kusan mintuna sha biyar suka kwashe a cikin gidan kafin Ramlat ta shigo. Kici
ɓ
us suka yi a bakin ƙofar. Kallon da ya watsamata ne yasa ta hadiye gaisuwar a fatar bakinta. Ganin shi bai ba ta hanya ba kuma bai ce uffan ba yasa cikin dakiya bay
an ta saukar da kanta ta gaishe shi.
"Ba girin-girin ba dai, ta yi mai."
Ya fadi a sanyaye amma zafin maganar ya fi komai buga zuciyarta. Ta dubeshi, ya kauda kai ya bi gefenta ya wuce. Ta bi bayansa da kallo cikin rashin gane inda zancensa ya d
osa.
"Ah Hajajju, har kin gama ta
ɗ
in?"
Ta juyo ta dubi Hisham tana murmushin hadiye damuwa.
"Har za ku wuce?"
"Eh kinsan da yake ba iyakar nan muka tsaya ba. Yau dai ladan juma'ar muke kwadayi."
Ta jinjina kai.
"Allah Ya saka
da alheri."
Ya amsa da amin. Wani wawan hon da Hussein ya yi sai ya ba Hisham dariya.
"Kinga bari na tafi kafin na ba shi haushi ya koma Adamawa a ƙasa."
Ta yi dariyar da ta tsaya a fatar baki. Hanya ta ba shi ya wuce.
***
BANKWANA
DA MASOYI....
I just published "BABI NA HAMSIN DA BIYAR" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1015298066?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-U
mar&wp_originator=APuHCxKNugEN8dtZunyL4O%2FJKBns%2FO08vTjSCIlxF7AhR%2BRuxyUYJF8vGaw9PlhcYs%2Fd5Guq41cilqJPUF4w8sQuGhQdsC6bSLWR4oVKhbuxPFsqscrPZn1s%2BR6QxkUd
🕯
️
*ƘARFEN ƘAFA*
🕯
️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir R
aheem.
55)
"Na kasa gane kanka. Wai me ya sauyaka haka?"
Hussein wanda ke jin kirjinsa har wani zafi yake ya kasa magana sai guntun tsaki da ya ja.
"Allah Ya kyauta. Amma idan har dagaske kana son Ramlat toh ya kamata ace zuwa ya
nzu ka bada kai bori ya hau. Bana son wannan zurfin cikinnaka alhalin ni na sani wallahi ko mijinta na farko sai an yi dagaske zai kamo ka a son da ka ke mata."
Nan ma dai shirun ya kara samu maimakon amsa, Hisham dole ya ja baki ya yi shiru don ya so
ma jin haushi.
"Zamu je Yakasan?"
Ya tambaya bayan ya yi tuƙi mai
ɗ
an tazara daga gidan su Ramlat. Ajiyar zuciya ya saki ya dubeshi da jajayen idanun da
ɓ
acin rai ya rinar.
"Ba zan iyaba. Mu yi hakuri ko zuwa gobe ne, ba ta