Showing 51001 words to 54000 words out of 255051 words

Chapter 18 - KARFEN KAFA complete

bai kashe kidan ba duk kuwa da hango iyayensa maza da ya yi zaune a saman tabarma ƙasan ƴar rumfa a farfajiyar gidan. Duk sadda irin hakan ta kasance,

tattaunawa suke game da wani abun mai muhimmanci.

Kallonsa suke har ya kashe motar ya fito zai nufi cikin gida ba tare da tunanin gaishesu ba. Idan da sabo ya ci ma su saba.

Malam Abdussalam cike da takaicin halin

ɗ

annasa ya sunkuyar da kai.

"Kai! Aliyu?!"

Fadin Kawu AbdulRashid wanda ke bi wa Malam Abdussalam a haihuwa. Aliyu ya maido akalar tafiyar garesu.

"Gani. Sannunku."

Yanda ya gaishesu kerere ya fi komai baƙanta ransu. Daƙuwa Justice ya wurga mishi.

"Ungo wanna

n! Yanzu kai tsabar iskanci da rashin kunya mu kake yiwa gaisuwa irin na ƴan iska?"

Nan ya gane kurensa, sai ya durkusa yana shafar suma. Dama ya riga yasan har gobe dattijon haushin sakin da ya yiwa

ɗ

iyarsa yake. Yana cikin farin ciki yau, don haka b

ai shirya wani abun ya

ɓ

ata ransa ba.

"Ku yi hakuri." Ya ce kai tsaye cikin tausasa murya. Banda warin taba ba abinda ke tashi a jikinsa. Sun gaji da magana daya akansa.

"Allah Ya shiryeka Aliyu, Yasa wataran ka sauya." Cewar Kawu AbdulRashid ransa

na zafi.

Nan Justice ya shiga magana.

"Yarinyar nan mun ji labarin abinda ta aikata, kuma ta yi a bakin duniya duk don ta aureka. Ta yi laifi, ta yi kuskure. Mahaifinta ya damƙa amanarta gareka, da kunnenka ka ji kalamansa."

Aliyu ya gyada

kai cikin son tuna abinda Abban ya furta gareshi ranar da ya karbi sadakin Ramlat a hannun magabatansa.

*"Ramlatu amana ce Allah Ya ba ni, yanzu kuma amanar za ta koma kanka. Ban ce lallai sai ka kyautata mata ba, ban kuma ce lallai sai ka yi mata ada

lci a rayuwa ba, duk wannan hakki ne da ya rataya a wuyanka ko ban fa

ɗ

a ba. Ka ji tsoron Allah a lamuranka, kar ka manta zai tambayeka duk wani abu da ka aikata a rayuwa."*

Bai mantawa a lokacin murmushi ya yi kawai.

*'Ba dai haka ka so ba Abbanm

u. Sai dai ba za ka hana abinda Allah Ya yi ba.'*

Nan take ya ce a cikin ransa.

"Don ubanka ina magana kake dariya? Wane raini kenan?"

Kalaman Justice suka katse tunaninsa, ya ankara da murmushin da yake zabgawa har haƙoransa na bayyana.

"Ayi hakuri." Ya kara fadi.

Kowanne ya tofa albarkacin bakinsa kan ya riƙe amanar yarinya, daga nan ya yi musu godiya ya mike da uzurin Abulle na nemansa. Mahaifinsa ya bishi da kallo gami da addu'ar shiriya. Yaran ka haifa ba ka isa ka saita hala

yyarsu ba.

Kici

ɓ

us suka yi, ba haka ta so ba. So ta yi da sauri ta bar dakin Abulle kafin ya cimmata. Shigarta dakin Abulle don kai mata goron da ta dauko a dakin Daddynta. Jin Abulle na mitar Aliyun ya zaunar da ita zaman jiransa ya sa ta katse hira

rtasu ta yi mata sallama ta fito tana sauri ta bar bangarennata. Sai dai kuma ba yanda ta iya tunda gashinan gabanta. Ta daure ta ha

ɗ

iye komai dake tasomata.

"Ina wuni Yaya Aliyu."

Bai san yana da kunya ba sai a yanzun, ya kauda kai daga kallont

a.

"Lafiya. Ya kike?"

Ba tare da ta amsa ba ta wuce da sauri ta yi hanyar kofar sashinsu. Bayanta ya bi da kallo, Muhibbat kenan. Ya sa kai dakin Abulle.

Salati ta shiga yi kafin ta hau yi mishi fadan sigari da ya sha. Ta

ɓ

e baki ya yi, ya m

ance da hakan shaf bai jefa alawa bakinsa ba, bai kuma fesa turare ya tsaye a waje na mintoci ba kafin ya hau mota ya tuƙo. Ya mance rabon da ya shigo gidan yana warin taba.

"Wai ni don Allah ki bar kunnena ya huta. Shikenan don kin ji warin abu a ji

kina sai ya kasance sha na yi? Ko a addini an hana irin wannan yanke hukuncin. Idan ina sha tsawon lokacin nan ba za ki sani ba sai yanzu? Mtsw, Abokina ne ya sha, shi na ziyarta shi ne ƙamshin ya biyoni."

Hakan da ya fa

ɗ

a sai kuma ta gyara zama ta ha

u jijjiga kai.

"Kuma fa hakane. To ka kara kiyayewa dai. Ra

ɓ

ar abokai

ɓ

ata gari ba naka bane. Na soke abotar. Yanzu dai ya batun lefe?

Mahaifinka cewa ya yi na farko an maka, na biyu kai za ka yi. Duk da haka Alƙali da sauran kawunnanka sun

ɗ

an ba ka

wani abin ka ha

ɗ

a ka yi."

Murmushi ya yi.

"Lefen Baby ina son ya fi na kowa. Ina son a bude a kirashi da lefe. Masu yi mata habaici da zagi a kan aurena su daina. Don haka da kaina naji zan hada abina koda ace hakan na nufin karyewar jarina."

Baki sakaka Abulle ta saki tana kallonsa kafin ta magantu.

"Um um dai Zakina, ba za'a yi haka ba. Ƴar dangi ma ba ka ce hakan ba sai akan bare? Ina rabaka fa."

Ya yi dariya.

"Abulle tawa ni kadai, Baby ai ta isa na yi mata komai. Koda kuw

a komai nawan zai ƙare a kanta."

Ta ta

ɓ

e baki.

"Fadi dai sunanta na zahiri, shi zan fi fahimta. Ramlatu ko? To naji, ungo nan."

Ta daga filo ta fiddo damin kudi ta mikamasa. Ya karba ya zura a aljihu.

"Wai nikam me zai hana ka mayar da

yarinyarnan

ɗ

akinta ne? Naga dai tsiraicinka yafi rigar aro ta mutane."

Miƙewa ya yi tsam!

"Sai da safe Kakus. Kwanta ki yi bacci abinki. Nima na tafi nawa lissafin."

"Ai fa, ba dama a dauko magana sai ka kauce. Toh har gobe ban ga wata

ɗ

iy

a da za ka kawo na ji ina sonta a raina ba irin Muhibba."

Daga kafada ya yi alamar ke ta shafa ba kuma tare da ya komai ba ya fice daga dakin. Ko a ransa bai ƙara tada zancen Muhibbat din ba.

***

"Kai Allah Ya rayamana mai sunan Abba."

Fa

din Zulaihat kenan cikin waya tana murmushi ranta fari ƙal. Ramlat na daga kicin tana dahuwar indomie ta ji wannan kalamin. Anan ta fahimci sunan Abba

ɗ

an Rafee'ah ya ci. Kwalla suka tarar mata, a yanzu ba ta rabo da hakan. Tunda aka daura aurenta da Aliyu

, komai ya daina yi mata dadi. Ba kuma don ba ta sonsa ba, har gobe tana jinsa a ranta. Wuyarta ya kira wayarta ko kuma ta kirashi, za ka ganta cikin farin ciki da annashuwa. Kalamansa masu taushi da dadi, wanda ke nuni da nutsuwa da kuma cikar hankali, su

n fi komai yi mata dadi a ranta. Sai dai ba ta nufin ta rabu da yan uwanta a dalilinsa, duk suna amsamata idan ta yi magana, sai dai irin amsawar da gwamma kar su yi. Babu fara'a babu sakin fuska. Sama-sama suke amsawa kamar ba sa so.

An kwaso kayan

ta kaf a gidan Hilal, a daren jiya ya zo har gidan ya riski Abba a falonsa. Sun jima suna magana sannan ya tafi. A hirar Zulaihat din da Hajiya ta ke jin cewa hakuri ya ba shi. Hakuri bisa sakin ƴarsa da ya yi.

"Ke wane rashin hankali ne za ki kunna

gas har abu ya ƙone haka? Gobara kike son jazamana? Ko mu dinma kashemu za ki yi?"

Ta waiga ta dubi Zulaihat s'ilin da ta sanya hannu ta kashe gas din.

"Hajiya ta ce ki yiwa Mijinki magana za'a je a yi jere don Abba ya ce a satinnan za ki tare.

Ya kawo muƙulli."

Tana kaiwa karshe ta fice a kicin din, kawai sai Ramlat ta fashe da kuka. Haka to za su ci gaba da yi mata?

Indo ta risketa tana kuka, ganin ta dage wurin rarrashinta duk kuwa da haushinta itama ta ke, ya sa ta daukar wayarta t

a bar kicin din. Abincin da ba ta ci ba kenan.

***

Akwati takwas cif Aliyu ya shaƙe da kaya na gani na fa

ɗ

a. Yakasai gidan su Hajja aka kai lefen kamar yanda Abba ya bada umarnin a yi.

"Anya Rabi'atu wannan yaron ba ya cin haram a aikinsa?

Wannan wane irin kaya ne ya shaƙowa yarinyarnan?"

Hajja da mamaki ya kasheta a zaune ke wannan furucin cikin waya ga Hajiya. Hajiya ta yi murmushi mai ciwo.

"Ko ya ya dai Hajja ai ita yarinyar ta fi kowa sanin yanda aka haihu a ragaya. Tunda y

a kawo lefe an kar

ɓ

armata shikenan. Ta je ta yi ta sakamishi."

"Kai Rabi, na rabaku da irin wannan fushin fa. Meyasa Khalid ya biyewa yarinyarnan bai yi bincike ba? Har da gwal a sarkokin."

"Hajja ina zuwa zan kiraki."

Hajiya na fadin hakan

ta katse kiran. Ba wai don abin bai tayarmata da hankali ba, sosai hankalinta ya tashi. Yaron da aka ce a kasuwar ma ba wani mayar da hankalin a zo a gani yake ba. Ba ta son tunkarar mijinta da wannan batun, don ta lura yana cikin damuwar auren Ramlatun h

ar lokacin. Wannan ta sa ta kira Munir. Kafin ma ta yi nisa ya katse zancen.

"Hajiya ke mahaifiyata ce. Don girman Allah kiyi hakuri ki bar min zancen Ramlat. Hajiya ki zubamata ido tunda kun mata abinda take so. Ku yi hakuri ku bi ta da addu'a idan d

a bukatar hakan. Ba ita kadai ku ka haifa ba, muna raye zamu share kukanku. Ki yi hakuri, ki sanya a ranki hakan ya zama alheri ba sharri ba."

Da wannan ya samu ya zame kansa daga abinda Hajiyar ta kawomishi, na bincike akan harkar Aliyu.

'Wane

bincike bayan mai afkuwa ta afku? Komai ta fanjama fanjam!'

Ya fadi a kasan ransa.

***

"Ai yanzu kin girma, kin mallaki hankalin kanki, ba kya bukatar nasiha daga gareni. Duk abinda kika aikata ga rayuwarki daidai ne."

Kalaman Hajiya suk

a shigeta sosai, ta cikin laffayar da Zulaihat ta na

ɗ

eta a ciki, kuka take. Ba ta san sadda ta bude lullu

ɓ

in ba ta karasa ta dafa cinyar Hajiyarta.

"Don son Annabin Rahma s.a.w Hajiya ki yafemin. Ki yafemin ko zan ga haske a rayuwata. Na yi miki laif

i, ki yafemin don Allah."

Zuciyar uwa mai rauni, ta cika da tausayinta. Tausayi na abinda take hangomata wanda ita ba ta hanga ba. Shaye-shayen da Abba ya ce Aliyu na yi ya tsayamata a ƙahon zuciya. Ta daure ta mike bayan ta zame jikinta.

"Ku wuc

e Uwani, dare yana yi. Allah Ya bada zaman lafiya."

Ba tare da ta ƙara magana ba ta shige ban

ɗ

aki, Zulaihat wacce ko a jikinta ta amsa da Amin kafin ta

ɗ

ago Ramlat.

"Mrs Aliyu mu karasa ga Abba ko?"

Ta riga ta

ɗ

an kusan da biyu Zulaihat ke

kiranta da hakan, suka shiga Abban na zaune saman darduma yana karanta Alkur'ani mai girma. Ya

ɗ

ago ya dubesu, tunda ya dora idanu akan Ramlat bai kifta ba.

"Ramlatu an fito?"

Yanda ya furta cikin taushi ya sanya zuciyarta kara narkewa. Ya yi ƴa

r dariya.

"To mene abin kuka? Yanzu kin zama matar aure. Komai ki ka yi, ko za ki yi ki sani cewa Allah Yana kallonki. Ki ji tsoronSa wajen gudanar da lamuranki. Ramlatu duniya da kike gani tana da fa

ɗ

i, sai dai zuƙatanmu sun fi ta fa

ɗ

in. Idan mun yar

da da hakan, mun cikata da alhairai masu yawa, mun yi irin aikin da Allah Zai farin ciki da mu. Mu zama cikin ceto AnnabinSa s.a.w. Duk isa da taƙamar mace, ba komai ba ce a wurin mijinta. Ki rike wannan, ki bi mijinki sau da kafa. Kar ki sake ki zama mai

tona asirinsa."

Abba ya ci gaba da koro jawabai, ba Ramlat kadai ke kukan ba, hatta da Zulaihat kukan take. Kukan tausayin wannan uba mai matukar don

ɗ

iyarsa da alheri, mai mafarkin ya ga ta yi aure a inda ba za ta ta

ɓ

a wulakanta ba. Sai dai kash, bu

rinsa bai cika ba.

"Nagode Abba, Abba kaima ka yafemin. Hajiya ta ƙi yafemin. Abba ka tayani roƙonta."

Nan take ya umarci Zulaihat ta kira Hajiya. Ta bi umarninsa sai gasunan tare.

"Na yafemata idan don haka ka kirani."

Ta tari hanzar

insa don tasan kafiya irin ta Ramlat da naci.

Murmushi ya yi.

"Mun gode Hajiyarmu. Ban riƙe ki ba a rai kinji Ramlatu? Tashi ki tafi dakin mijinki. Allah Ya yi muku albarka. Ya dauwamar da ku a dakunan da'iman."

Daga nan suka mike zasu fita

, dakatar da su ya yi. Da kansa ya taso ya lalubo hannun Ramlat wacce lallenta na tun bikinta da Hilal shi ne a hannun, har baƙin ya soma gogewa. Alkur'ani mai girma ya sanyamata a ciki.

"Babu wani hasken da ya wuce haskenSa. Babu magani da kuma warak

a face ta hanyar karantashi da kuma addu'a. Kar ki yi wasa da tilawarsa."

Wani kukan ta kara kecewa da shi, maimakon Abban ya koma mazauninsa, sai ya kama kafa

ɗ

arta ya yi mata rakiya har cikin motar da Aliyu ya turo. Iyayen Aliyu su na kallo, sannan y

a koma cikin gidan zuciyarsa a karye.

***

_*MRS ALIYU*_



Ya kara jawota jikinsa ya rungume, kuka take sosai. Duk kuwa da cewar ta tsarkake jikinta ba ta bar jin radadi-radadi ba.

"Haba Baby, damuwa kike son na shiga ne? Sai kuka kike, ya z

an yi miki ki daina?"

Ta soma ƙoƙarin tureshi daga jikinta.

"Ni ka rabu da ni."

Ya yi murmushi gami da kara kankameta.

"Ni ba zan iya rabuwa da ke ba Baby. Ki yimin duk abinda kika san zai sa ki huce. Kinji?"

Ta turo baki, ya sa h

annu ya shiga sharemata hawaye.

"Fadamin me kike son na yi miki a rayuwa kwatankwacin wannan farin cikin da kika ban, kinsan an ce yaba kyauta tukuici."

Ta tsinci zuciyarta da jin dadin kalamansa. Ba ta san sadda ta yi murmushi ba. Damarta kenan

, ya kuma kamata ta yi amfani da shi kar ya wuce.

"Karatu nake son ka bar ni na ci gaba."

Ya rungumeta yana ƴar dariya.

"Wannan mai sauki ne Baby. Ki ajiye a ranki kin yi karatu kin gama, wannan ya zamemin kamar farilla, fadi wata bukatar."

Ta yi shiru, jin saukar dumin hawaye saman fatar kirjinsa ya sanya shi

ɗ

ago ha

ɓ

arta yana dubanta.

"Baby, meyasa?" Ya yi maganar kamar mai ra

ɗ

a. Ta sauke kwayar idanunta daga kallonsa.

"Sanadinka na shiga tarin matsaloli. Na jure dukkan wu

ya, na karya dukkan alƙawura, don Allah ka rikeni amana, ka bani kulawar da iyayena da dangina zasu aminta da za

ɓ

ina. Ina son mu ba marar

ɗ

a kunya."

Ya yi murmushi.

"Kina shakku a kaina ne? Ko kina kokwanto akan son da nake miki? To ki daina, ha

r mai

ɗ

a sai mun ba kunya a zamantakewarmu. Ki kwantar da hankalinki."

Ta yi murmushi, so da kaunarsa na ninkuwa cikin ranta. Nan kuma labarin ya sauya.

***

Soyayya ce tsantsa ke gudana a gidan masoyan, Aliyu dakyar yake iya fita kasuwa ya ga

yanda yaransa ke tafiyar da lamura. Iya soyayya da shagwa

ɓ

ar Ramlat har mamaki yake ba shi. Hakan ke kara susutar da shi. A wannan lokacin yana takatsantsan da shan dukkan wani abun maye a gaban Ramlat.

Sai da suka cika sati biyu da aure sannan

suka shirya zuwa gaida iyayensa. Ta ha

ɗ

e cikin leshinta maroon ta yafa farin mayafi sai takalmi da jakarta suma farare. Ta yi ado daidai gwargwado, ta ciko kadan, ramarta ta ragu sosai. Hakan ya ƙaramata kyau.

"Babyna kin yi kyau kamar mu fasa fita

r."

Ya fadi yana rungumo ƙugunta. Ta watsamishi kallon soyayya ya kama saitin kirjin gami da lumshe idanu yana murmushi.

"Ahh, kasheni za ki yi ko?"

Dariya sosai ta shiga yi ta kwace jikinta.

"Muje don Allah."

Ya kamma hannunta

suka nufi motarsa. Tafiya suke suna jinsu kamar a gajimare. Wakar Nazifi Asnanic mai taken Jamila da Jamilu shi ke tashi a motar, hannunsa na dama cikin tafin hannunta. Ji take kamar ba ta da wata matsala da ta yi saura a duniya, kamar wata sarauniya haka

take ji musamman yanda Aliyun ke rera wakar yana dubanta jefi-jefi. Har suka iso wakokin soyayya daga Asnanic da Nagudu kawai suke ji.

"Mun iso Madam."

Ta

ɗ

an harareshi da wasa sannan ta yunkura da zummar maida takalminta da ta cire a zaman mota

r. Kafafunta suka taka wani dunkulallen abu kamar takarda. Ta sa hannu ta dauka sa'ilin da ta zura takalmin. Daidai sadda Aliyu ya bude mata murfi ta fito. Kirjinta ne ya buga, ko ba ta shan sigari, ta san wannan dai karan sigari ne.

"Mene wannan?" T

a tsinci kanta da watsa tambayar duk don ta samu tabbaci. Yatsuntsa ta ji ya sa ya karba gami da yin cilli da shi yana tsaki.

"Wannan banzan ne, G Baba ya sha min a mota."

Ta ji hankalinta ya kwanta, ta sauke ajiyar zuciya.

"Muje Baby, yau

Kakus za ta ganki."

Ya karasa zancen da riko hannunta su soma tafiya cikin son basarwa. Har ga Allah ta yarda da zancensa.

***

"Masha Allah, ashe kishiyartawa itama ba baya ba kamar wata balarabiyar Sudan."

Dariya Aliyu ya yi, itama Raml

at murmushi ta yi gami da ƙara sunne kai.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login