Showing 72001 words to 75000 words out of 255051 words
karatun Alkur'ani, su ne babban makaman kowane bawa da kike gani. Ki rike su ba da wasa ba."*
Ta tuna kalaman Abbanta. Zumbur ta mike ta shiga
ɗ
akinta, alwala ta
ɗ
ora ta fito ta yi nafila. Ta jima cikin Sujjud
a tana kaiwa Allah kukanta kafin ta yi sallama ta shiga karatun Alkur'ani. Tana yi tana hawaye. Komai na dawomata daki-daki, tun daga batun aurenta da Hilal har yanda ta bijirewa iyayenta akan za
ɓ
inta.
*"Ke yarinya ce Ramla, ba ki san abinda ubanki
ya hangomaki ba. Na ta
ɓ
a ganin shai
ɗ
aniyar zuciya irin taki da ba ta san Annabi ya faku ba? Wannan taurin kai irin naki Allah Ya miki magani."*
Kalaman Tsohuwa Hajja ya dawomata tiryan-tiryan. Wani sabon kukan ta kece da shi, shakka babu gaskiya Hajja
ta fa
ɗ
a. Yanzu tun ba a je ko'ina ba ta na ta fuskantar matsaloli da dama.
*"Kina shiga haƙƙin aurena, kar ki manta kema mace ce."*
Ta runtse idanu tana jin kamar a sannan take karanta saƙon da Muhibbat ta ta
ɓ
a rubutomata a baya. Wanda ba ta ma
ncewa har ƙararta ta kai ga Aliyu, ranar ta tabbatar sai da ya ci mutuncinta duk a dalilinta.
"Zunubaina masu yawa ne, Allah ina neman gafararKa."
Ta furta a hankali, a daddafe ta ci gaba da karatun sannan ta sallame ta yi addu'a mai yawa. Neman
gafara ne da kuma roƙawa mijinta shiriya da kuma tsari daga dukkan munanan ayyuka.
Ranar yanda ta ga dare haka ta ga rana, waya ta dauka ta dannawa Amrah kira sai kuma ta katse kiran. Me za ta ce? Bayan koma mene ita ce sila.
A hankali ta shiga
tuna dukkan rikicin da aka yi akan aurenta, wani rashin kunya, taurin kai, kafiya, babu irin wanda ba ta tuna ba.
'Ba zan ta
ɓ
a ganin laifinku ba.'
Ta fadi a ƙasan ranta.
*"Ba ina alfahari ba My Future, sai dai wallahi wallahi, na fi dukkan
wani namiji da ba muharraminki ba sonki. Ki dawo Ramlatun da na sani a baya, please and please ki maido Hilal cikin zuciyarki."*
Ta runtse ido gami da yin istigfari, wannan tunanin ba amfanin da zai mata, dukkan inda dai Hilal yake tana mishi fatan a
lheri a rayuwa. Aliyu wani bangare ne na jiki da zuciyarta, sonsa halitta ne da ba ta isa ta yayewa kanta ba.
***
WASHEGARI
Kishi mai tsanani cike taf zuciyarta sa'ilin da ta yi ido hudu da shi a falon, har lokacin shai
ɗ
aniyar muryar matar b
ai bar amsa kuwwa a kanta ba. Ta kauda kai kamar ba ta ganshi ba ta nufi hanyar fita zuwa makaranta ba tare da tunanin cin wani abu ba matsayinta na mai juna biyu.
Hannu ya sanya ya tare ƙofar. Ta
ɗ
ago idanunta da suka rine tsabar
ɓ
acin rai. Ba kuma
za ta ce tsana ba, don ba ta tunanin akwai
ɓ
ur
ɓ
ushinsa. Kokari take ma ta
ɗ
orawa zuciyar amma abin ya ci tura. Bata da ikon hakan.
"Malam matsa na wuce."
Ya ƙi motsi illa dai ya ƙafeta da mayatattun idanunsa dake kashemata dukkan wata ga
ɓ
a a jik
inta.
"Ki yi hakuri, ina mai ha
ɗ
aki da Allah. Wallahi ba'a hayyacina nake ba. Kafin na taho sai da na yiwa Zee dukan da ba za ta kara marmarin kallona ba balle .."
"Ban tambayeka komai ba, nidai kawai ka matsamin na wuce ina da jarrabawa. Don Al
lah ka matsa."
Ta ƙarashe wani takaici na tahomata, kuka take son yi dakyar ta iya danneshi.
Ganin dagaske ba za ta saurareshi ba sai kawai ya matsa a sanyaye, ta fice daga gidan ta kyaleshi.
Ita kanta ta yi mamakin yanda ya kwantar da kai
har yake kokarin kare kansa, Aliyun da bai fiye damuwa da kafa hujjar da mutum zai yarda da shi ba. Shi dai idan ya aiwatar to ya aiwatar. Amma a lamuranta, ba haka abin yake ba.
***
"Wai ke meke damunki ne? Ina fa lura da ke kamar ba'a hayyacinki k
ike ba. Anya kuwa kin rubuta abinda ya dace?"
Tambayar Amrah ta katse tunaninta. Ta yi murmushin yaƙe.
"Ba komai,kawai yanayin jikina ne, jiri nake ji idan ban nemi abu na sanyawa cikina ba akwai matsala."
Jin haka Amrah ta mike da sauri.
"Zama bai ganmu ba Maman Baby, tashi muje."
Ba musu ta mike suka nufi wurin siyar da abinci. Amrah na son ƙara tambayarta dalilin damuwarta sai dai ba ta san ta ya za ta fara ba.
*"Ƴar uwarki ce, ki yi hakuri da dukkan abinda ya faru tsakanink
u. Yanda ta mana laifi, kema ta yi maki. Ki dinga kokarin bata shawara a dukkanin tafiyarku. Allah Ya maki albarka keda iyayenki, Ya fiddomaki miji da zai riƙe ki bisa amana."*
Ta tuno alfarmar da Abba ya nemi ta yi mishi akan Ramlat satin da ya wuce.
Ita kuwa koda Abban bai nema ba, ta yi amannar ba ta da Aminiyar da ta fi kauna sama da Ramlat din, komai za ta
ɗ
aukeshi ba komai ba. Kuma koyaushe za ta kasance tare da ita koda ace Aliyu zai mata zagin uwa uba. Bai isa ya rabata da Ramsy ba.
"Amrah
ina cikin damuwar Aliyu."
Muryar Ramlat din ta katsemata dogon tunanin da ta fa
ɗ
a, a gaggauce ta dubeta.
"Fadamin damuwarki Ramlat. Me ya yi maki wannan karon?"
Shiru ya biyo baya har suka karasa suka nemi mazauni, Amrah ta yiwa waiter maga
na ta fadi abinda zai kawomusu sannan ta kara dubanta dakyau. Kafin ma ta kai ga magana Ramlat ta soma, kaf ta bata labarin abinda ya faru gami da fadin.
"Rabuwa da Aliyu shi ya fiyemin alheri Amrah. Sai yanzu na hango abinda ku ke hangomin. Ba zan iy
a rayuwa da shi haka ba. Amrah na yi kuskure, na yi nadamar abinda na aikata. Ya zan yi? Ya zan yi da jinin Aliyu dake tattare da ni? Yan uwan Aliyu babu mai sona, abin mamaki wacce na zaci za ta fi kowa ƙina da guduna, ita ce har da zuwa ta kawomin katin
gayyatar aurenta har ta zauna mu yi hira da dariya. Ina alhakin Muhibbat zai bar ni? Ina hakkin iyayena zai bar ni na ji dadin zaman aure? Na gaji, zan roƙi Aliyu ya sakeni na yi biyayya ga iyayena."
Wani murmushi Amrah ta yi, a ranta tasan karya ne R
amlat ta iya rabuwa da Aliyun. Ta danne tausayin da ya ke tasomata.
"Tun ran gini tun ran zane Ramsy."
Ramlat ta gyada kai tana sharce majina.
"Na yarda, hakane na yarda. Ko mene ni na jazawa kaina. Amma bansan Aliyu mashayi bane, bansan kum
a yana zina.."
"Astagfirullah, kin tabbatar ya aikata zinar? Kina da shaida? A'a Ramsy, kar ki bari shaidan ya yi wasa da hankalinki. Ba'a yankewa mutum hukunci haka, hukuncin ma na zina kai tsaye. Ke ba ki san tuggun mata ba? Ki dai kwantar da hankal
i ki ji me zai ce. Sannan sakin da kike kirawa kanki, kinsan wanda za ki ƙara aura? Kin manta da cikin jikinki? Ai wannan kadai ma ya isa duk wani mai miki kallon kin bijirewa iyaye ya yi maki uzuri. Yanzu da ace..."
Ta yi shiru har sai da aka ajiye m
usu plate din fried rice da chicken da kuma lemu da ruwa aka bar wurin sannan ta ci gaba.
"Ba wanda zai so ki haifi shege. Komai lalacewar abu gwara kin haihu ƙarƙashin inuwar aure. Ya fiyemaki sutura. Nasan ba ki ci komai ba daga yanayinki, mu ci abi
ncin ma yi maganar daga baya."
Ba musu suka yi bismillah, Amrah na satar kallonta cike da tausayi ganin yanda take kai loma, sai da ta cinye tas kafin ta dauki ruwa ta kora. Daga bisani ta soma shan lemun.
"Ko za ki ƙara?" Fadin Amrah tana duban
ta.
Girgiza kai ta yi ta harareta da wasa.
"Haba dai, kamar wata jaka?"
Ta
ɓ
e baki Amrah ta yi.
"Har kin tunamin da Smally, ci ba ƙiba."
Suka yi dariya, nan kuma aka shiga tuna rayuwar sakandire. Wasu sun yi aure wasu kuwa suna dan
ganin gilmawarsu a B.U.K musamman mazan. Wasu kuwa basu samu sun shiga ba.
Bayan sun kammala suka nufi aji, anan ne Amrah ta bata shawarwari gami da kara nunamata illar yanke hukunci cikin fushi. A hankali kuma ta ji zuciyarta ta yi fes, ta kara god
ewa Allah da samun Aminiya irin Amrah.
***
Sun kai wurin sati suna fushi da juna don tun yana ba ta hakuri yana lalla
ɓ
ata har ya watsar. Karshe kuma suka shirya don har ankon Muhibbat ya siyamata.
Allah Ya taimaketa lokacin sun kammala jarra
bawa, wannan ya bata damar shirin biki a nutse. Rana daya kawai za ta je, ranar yini. Amman hakan bai hanata fargaba ba, gani take yi kamar idan ta je habaici da zagi kawai za ta kwasa ta dawo.
Ranar yinin tun karfe daya ta shirya. Anko ta sanya an
mata
ɗ
inkin doguwar riga yanda ba za ta takura
ɗ
an cikinta ba. Ta yi kwalliya sosai abinta.
"Wannan kwalliya haka, duk murnar ce?"
Fadin Aliyu cike da zolaya, ta harareshi ya yi dariya.
"Ai ni na dauketa matsayin ƴar uwa, wallahi ko yau t
a so dawowa
ɗ
akinta, ina marhaba."
Dariya sosai ya yi sa'ilin da ya ke kokarin rufe ƙyauren ita kuma tana tsaye jikin mashin tana jiransa. Mota dama tuni ya siyar da abarsa.
"Dakyau Mrs Aliyu, amma dai ban yarda ya kai zuci ba. Irinku ai ba'a yi
maku kishiya, wataran ƙurmus za'a wayi gari kun ƙone mijin da kishiyar."
Turus ta yi tana dubansa idanunta nan da nan suka cika da kwalla.
"Bana so Aliyu, bana son irin wannan wasan. Dadin abin ma kai ne babban shai
ɗ
anin da ka yi sanadin mutuwar
aure."
Ya daure fuska tamau.
"Ni kike gayawa magana?"
Kamar ta ce an fada din, sai kuma ta ha
ɗ
iye ta kara daure fuskarta ta kauda kai.
"Wallahi sai dai ki taho ke
ɗ
aya, na fasa kai kin. Aikin banza kawai! Har wuyanki ya kai ki yi kirana
da shai
ɗ
ani? Duk shai
ɗ
ancina na kai ki? Mai sa
ɓ
awa iyaye kawai."
Cikin jin masifa da takaici ta kara magana.
"Oho dai, dadin abin dai na shirya da iyayena, kuma idan fitsari abin banza ne kaza ma..."
Wani bahagon mari ya
ɗ
auketa da shi wand
a ya yi sanadin raguwar gudun numfashinta.
"Kai! Haba Ranka Ya dade, wa ke dukan matarsa haka?"
Fa
ɗ
in wani dattijo yana mai jan kekensa ya tsaya ganin abinda ya faru. Wani banzan kallo Aliyu ya watsamasa.
"Ina ruwanka? Matarka ko tawa? Dall
ah can wuce!"
Ya fadi cike da tsawa, kafin ya haye mashin dinsa har yana tunku
ɗ
eta ya soma kokarin tashinsa yana fadin baƙa.
"Ni akwai macen da ta isa ta zageni na kyaleta? Wallahi babu don uwarta."
"Aliyu ba uwata kake zagi ba wallahi sai d
ai uwar.."
A zuciye ya sauko daga saman mashin din ya kara kai mata naushi a baki. Wani ihu ta kwarara wanda ya janyo hankalin matasan dake can gefe suna kallonsu. Da sauri suka taho, yana kokarin kai mata bugu aka rirriƙeshi. Ashar yake musu yana ki
ran su sakeshi tunda ba matarsu bace.
"Kai dallah ba ma san hauka! Matarka jakarka ce da za ka kamata da irin wannan duka? Wallahi yanzu sai mu miƙa ka hukuma!"
Fadin wani matashi cikin muryar dabanci. Aliyu ya
ɗ
an sha jinin jikinsa, ita kuwa jiki n
a rawa ta bi shawarar wani matashi da ya ce ta shige makwafta. Da gudu-gudu ta fa
ɗ
a makwaftan kuwa.
Matar na zaune tana tsifar kai sai ganin mace ta yi a kanta.
"Innalillahi, baiwar Allah daga ina?"
Ramlat ta durkusa tana kuka ga wani kuny
a da ya addabeta. Wannan ne karon farko da ta shigo gidan.
"Makwafciyarki ce, matar Aliyu. Don Allah kimin rai ki bari na zauna kafin ya tafi, wallahi kasheni zai yi, yana waje maza sun rikeshi."
Matar ta yi shiru da mamaki, ashe dai dagaske ne d
a mijinta kwanaki ya ce ya ji ihunta har ya kwankwasa Aliyu ya nemi zaginsa.
"Toh, shigo."
Ta fadi tana jan
ɗ
ankwali ta rufe gashinta, Ramlat ta bi bayanta zuwa falon. Ba laifi falon mai kyau, sai dai daga gani ba wani karfi garesu can ba.
Ruwa ta daukomata ta ajiye. Ba ta iya sha ba, sam ba ta cikin hayyacinta. Jikinta har lokacin rawa yake. Kallo
ɗ
aya matar ta gane ciki ne da ita. Tausayinta ya kamata.
"Kiyi hakuri."
Ramlat dai kuka take ta kasa cewa komai.
***
A waje kuw
a dakyar aka raba Aliyu fada wannan matashin da ya nemi zaginsa, ya buga mashin ya kara gaba.
Yaron matar da bai fi shekaru goma sha uku ba, ya shiga gidan da sallama.
Matar ta amsa.
"Ya wuce?"
Fadin Ramlat. Yaron ya gyada kai.
"Eh, yanzu ya tafi."
Zumbur ta mike ta dubi matar.
"Nagode sosai, nima tafiya zan yi."
Gyada kai kawai ta yi don ita ta kasa magana, ko sunan Ramlat din ba ta sani ba. Har Ramlat ta kai ƙofa ta biyota.
"Baiwar Allah."
Ta juyo ta ka
lleta.
Jakarta da ta bari ta miƙa mata gami da fadin .
"Sunana Jamila amma ana kirana Maman Anas. Ya sunanki?"
Ta karbi jakar.
"Ramlat."
Gyada kai Maman Anas ta yi.
"Don Allah Ramlat kar ki yanke hukunci cikin fushi, komai ya yi z
afi maganinsa Allah, kinji?"
Murmushin yaƙe ta yi ta amsa da toh gami da godiya. Tana fita ta sauya hanya saboda kunya,mutanen wurin sai nunota ake yi. Hawaye take dakyar take ganin gabanta, kai tsaye ta tari abin hawa zuwa unguwar Yakasai gidan Hajj
a.
I just published "BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/K6spRvSBkab
🕯
️
*ƘARFEN ƘAFA*
🕯
️
*_Rufaida Umar_*
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
21)
"Yanzu na dai yaji kika yi?" Hajja t
a fadi tana jin kamar ta tashi ta kara rufeta da sabon duka. Ramlat ta kalleta.
"Haba Hajja, duka fa? Duka a waje har sai da aka kwaceni. Kiyi hakuri amma nidai ba zan koma ba."
"Ku ne yaran yanzu! Babu yanda ba'a yi da ku akan ku yi hakuri ku bi
za
ɓ
in iyayenku amma sai ku tiƙe lallai sai abinda ranku ke zo. Ku lallai sai kun nunamana kun yi boko, koda dai wasunku ma ba bokon hakanan suke wannan tsiyar. Gashinan auren bai je ko'ina ba kin fara yawon dakan yaji.
Ba bakin magana dai Ramlat, mi
ƙ
ewa ta yi ta shige ƙuryar
ɗ
akin Hajja din ta yi kwanciyarta zuciyar na ra
ɗ
a
ɗ
i. Har lokacin zafin marin da Aliyu ya yi mata ba ta bar jinsa ba. Shikenan kowace mace na zaune gidan aure da daraja da ƙimarta, ita nata ya zube a idanun Aliyu? Da ace yana gan
i ai ba zai
ɗ
aga hannu ya bugeta ba. Biki kam ta fasa zuwa ko za'a mutu.
Tun tana jin sababin da Hajja ke yi har ta bar jiyowa, baccin wahala ya yi awon gaba da ita.
***
YAMMACI
Munir da iyalinsa ne suka yada zango wurin Hajja, dag
a gidan su Bilkisun suke shi ne suka ga dacewar su leƙo. Hira ta yi hira har Hajja ta gangaro kan Ramlat.
"Ramlat kuma?"
Fadin Munir cike da mamaki, Bilkisu ta ƙara bu
ɗ
e kunnuwanta da son jin abinda ke faruwa. Hajja idanu sun rufe balle Munir di
n, sun mance matsayin Bilkisu wurin Hilal balle kuma a wurinsu. Komai da ya faru ta kwararo mishi, miƙewa ya yi zumbur ya fa
ɗ
a
ɗ
akin.
Bacci take tsakaninta da Allah, ba ta yi aune ba ta ji an kai mata wawan bugu a ƙafa. A firgice ta farka gami da sal
ati.
Kallonsa take kirjinta na wani irin lugude, babu wannan ƙauna da tausayin na ƴan uwantaka a kwayar idanunnasa.
"Tashi ki bar gidannan tun ban
ɓ
a
ɓɓ
allaki ba!"
Abinda ya ce kenan. Idanunta suka cicciko da kwalla tuni hawayen suka soma zub
a.
"Yaya Munir.."
"Yimin shiru! Ni ba Yayanki bane, You have no right to call me Yaya! Kin maida mutane shashashai wadanda basu san me suke yi ba! Kin za
ɓ
i Aliyu akan uban kowa yanzu kuma kin koma yawo bin gidajen dangi kina
ɓ
atawa zuri'armu suna
. Ba ki isa ba! Wallahi Ramlatu kin yi mugun ka
ɗ
an! Wato kin ga kin kasa kashe iyayenmu da baƙin cikinki, shi ne kika taho wurin tsoffinmu ki hallakamana su. Ai ke Ramla da ƴar halal ce ta gasken, ko kasheki Aliyu zai yi ba za ki kallemu ba balle ki kawoma
na kokenki. Daga yau na miki iyaka da mu, idan su iyayennamu sun kasa fadamaki cewa ke Annoba ce a garemu, toh yau ni Muniru na fada. Ki fita hanyarmu da zuri'armu. Wallahi bama sonki mun tsaneki! Ko mayya kike ya ci ace zuwa yanzu kurwar da kika ci a dang
innan ya isheki."
Ta kasa kwakkwaran motsi, daga yanda numfashinta ke bugu ta tabbatar ba mafarki bane. Wane irin tsana Munir ya yi gareta? Bude baki ta yi amma ta kasa furta komai, a hankali ta zame ta sauko daga gadon ƙarfen Hajja ta lalubi
ɗ
ankwali
nta da mayafi da kuma jaka, jikinta har rawa yake tsabar wani irin
ɓ
acin rai.