Showing 54001 words to 57000 words out of 255051 words
Abulle kuwa har ranta ta ji tana son Ramlatun, ta dage akan sai ta ci abinci, a dole ta tsakuri tuwo miyar agushin da ta diremata. Daga nan suka fice sashin mutan gidan. Jikin Ramlat ya yi sanyi matuka da irin tarb
ar da ta samu a gurinsu, ta dauka zasu kaunaceta kamar yanda Abulle ta nuna, sai dai abin ba haka ba.
Bangaren karshe da suka shiga, bangaren Justice. Aliyu ya nufi falon Justice yayinda ya ce ta shiga ciki. Shi kam banda ma dole da Abulle ta yi mish
i da ba zai shiga ba. Hajiya Maryam ta kalleta ta watsar, tun kan su shigo labari ya zo mata daga bakin Autar Kawu AbdulRashid, Hannatu.
Sanye cikin hijabi ta fito daga dakinsu don amsa kiran Mamarta. Ta ci karo da Ramlat zaune ƙasan kujera ga Mamar
ta kurawa talabijin idanu abinta.
"Muhibbat, ga matar Aliyu ta zo a gaisa."
Kusan lokaci guda suka kalli juna, kowannensu kallon ƙurillah yake yiwa
ɗ
an uwansa. Kowacce so ta ke ta gano abinda ta fi ƴar uwarta.
Bangaren Ramlat, kammanin Aliyu t
ake gani a fuskar Muhibbat. Shakka babu ba ta hango abinda za ta gwada mata ba.
Hakanan Muhibbat, sai dai ta ce da Ramlat din baƙar fata a kanta, banda wannan ba za ta ce ga abinda za ta gwada mata ba itama.
Murmushi suka saki a tare, murmush
in da ya fi zama na yaƙe. Kowanne na kokarin danne abinda ya ke ji game da
ɗ
an uwannasa.
Suka gaisa a mutunce sannan Muhibbat ta koma
ɗ
akinta. Rufe kofa ta yi ta sauke ajiyar zuciya. Ya dace ta shafe komi a yanzu itama ta ci gaba da gudanar da rayuwa
rta.
A bangaren Ramlat, sai ta hango wani sanyi da taushin zuciya a wurin Muhibbat din, ba ta ta
ɓ
a zaton ma za ta jure ganinta koda da sakan daya bane. Sai ta kasance mutan gidan ga dukkan alamu su ke tayata kishin. Tana nan zaune har Aliyu ya turo
a kirata, ya dubi kwayar idanunta yanda ya sauya. Cikin sauri ya tallafi fuskarta.
"Baby meke faruwa? An fadamaki wata maganar ne?"
Ganin hanyar baranda ce ta shiga falon Justice, sannan hanya ce ta jama'a yasa ta kauda fuskarta tana murmushi.
"Ba komai. Mu tafi."
Sauke ajiyar zuciya ya yi.
"Na dauka wani abin suka fadamaki yanzun na shiga na nunamusu ainahina."
Mamakin kalaman ya sanya ta dubansa, sai dai tuni ya soma tafiya yana bata umarnin ta biyoshi.
'Kin manta sun
ansa Aliyu? Gadanga ƙusar yaƙi. Ba dai zuciya ba.'
Fa
ɗ
in wani bangare na zuciyarta. Ta samu tarba mai kyau kamar yanda ta zata, don dukkan dattawan sun kar
ɓ
eta hannu bibbiyu da salama. Banda mata da sauran yan uwan Aliyu, wasu ƴan mata ma tana jin sad
da suka saki wata shewa da gu
ɗ
a, ta kuma san da ita ake.
A mota shi ke ta zuba hira banda ita, ta karanci abubuwa da dama a gidansu Aliyu.
Amman kuma suna isa gida ta bar zancen a gefe guda a ƙasan ranta saboda soyayyar da Aliyu ya shiga nunama
ta mai kashe duka lakan jiki.
***
Tsakaninta da iyayenta sai waya, za ta kira su dauka a gaisa. Yaya Munir kuwa ta tabbatar blocking dinta ya I daga kiransa don a farko sai ta jira ya yi ta ringing ba zai
ɗ
aga ba, yanzun kuwa gaba daya ma ta bar sa
munsa. Amrah kuwa ƙarara ta fito ta yi mata kaca-kaca akan ba ta son kiranta. Itama karshe ta nunamata tana da zuciya, ta tattara ta watsata a kwandon shara.
Sakamakon jarrabawarsu ta fito, Aliyu da kansa ya shiga fafutukar nemarmata Admission a B.U.
K.
_"Kai Baaba, kar ka yarda matarka ta fi ka Degree idan kuwa ba haka ba kana cikin kwale-kwale."_
Sa'ad ke ba shi wannan shawarar sadda ya shiga jami'ar Bayero wurinsu. Shi kam bai jin wannan a dalilin da zai tauye farin cikin Ramlat. Ko ba k
omai shi ma DAN ADAM ne, yana da zuciya, ya kuma yarda da cewar ta mishi halacci.
_"Bar
ɗ
an iska! Wato kai za ka yi jidalin kudin karatun ma?"_
G Baba ya furta hakan. Aliyu ya toshe kunnensa ya kuma zagesu tas. Karshe suka zuba ido su ga gudun r
uwansa.
***
*WASA FARIN GIRKI*
Tsalle ta shiga yi har da juyi kafin ta kara wani tsallen ta fa
ɗ
a jikin Aliyu, ya kuwa yi mata kyakkyawar runguma suna
dariya. Murnar ba ta komai ba ce illa ta samun Admission a jami'ar Bayero.
"Wash! Baby k
aryamin wuya za ki yi wai?"
Ta sakeshi suka yi dariya.
"Ban isa ba Sweet Aliy. Nagode sosai sosai. I love You so much."
Ya ja hannunta ta fa
ɗ
a jikinsa.
"Muje ki nunamin a zahiri."
Daga nan ya shiga yi mata ra
ɗ
a a kunne. Ta ka
uce suna dariya.
Sai da komai ya kammala sannan ta yi mishi rakiya har wurin motarsa, kamar kar su rabu haka ya ja ya fice Kasuwa.
Wayarta ta dauka da zummar kiran Hajiyarta su gaisa, sai dai abin takaici ba kudi a ciki. Nan take ta tuna kati
n da Aliyun ya siyamata a darenjiya da suka fita shan ice cream, yana tsokanarta akan ba zai bata ba sai ta ce tana sonsa sau cikin carbi, ita kuwa dariya kawai ta yi. Daga nan ya zura a aljihu ta mance ba ta kar
ɓ
a ba.
"Alhamdulillah." Ta furta a ba
yyane cike da nishadi, ta nufi dakinsa. Kai tsaye wandon da ya cire jiya ta fiddo a kwandon zuba kayan wanki. Zura hannunta keda wuya, ta ji kwali da wani abu. Ba
ɓ
ata lokaci ta ciro duka. Kirjinta ya bata dam!
"Kwalin taba da lighter?"
Ta fa
ɗ
i
a mamakince, zama ta yi gefen gado jiki ba ƙwari, ta kasa yarda Aliyu mashayin taba ne. Ganin komai ta ke kamar a mafarki.
'Ba ki ganin yanda le
ɓɓ
ansa keda duhu?'
Fa
ɗ
in wani sashi na zuciyarta. To ta ya za ta yanke hukunci da hakan bayan cewa a
kwai masu irin halittar? (Baƙin le
ɓ
e)
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Allah Yasa tunanina ba gaskiya bane."
Ta fadi a fili. Kamar ta maida inda ta ganshi, sai ta barshi a saman gadon don kawai ta ji me zai ce. Jiki ba kwari ta shiga laluba
daya bangaren, anan ta ci karo da katin wayar ta ciro, ta maida wandon kayan wanki ta fita.
Murnar da take duk ta dusashe don haka koda ta gama shigar da katin a waya, sai ta
ɓ
ige da rubutawa Abba text tana mai sanarmishi da cewa ta samu Admission a
B.u.k.
***
Abba na zaune sun karyawa a falo, da iyalinsa. Wayarsa ta yi ƙarar shigowar saƙo. Ya kai duba sa'ilin da yake kokarin kur
ɓ
ar shayin citta da kanumfarin Hajiya. Ganin sunan Ramlatu na yawo a saman wayar yasa shi ajiye kofin a gaggauce ya
bude sakon. Murmushi ya
ɗ
an yi.
"Madallah."
Ya furta cike da dakiya. Hajiya ta dubeshi tana murmushin itama. Suka hada ido.
"Ƴarki ta samu gurbin karatu a jami'ar Bayero. Sai ki bita da addu'a."
Idan ya ce ƴarki, ta gane wacce yake
nufi, don haka ta kauda kai ciki-ciki ta ce.
"Allah Ya bada saa."
Abba ya amsa da Amin gami da godiya. Ita mamakin Abban ma take yanda yake nuna halin ko'inkula da abinda Ramlat ta yi musu. Mutum mai tsauri idan aka ta
ɓ
osbi, shi ne ya sauko har
haka. Tana mamaki kam. A wajenta abu ne da bai da saukin wucewa, ba kuma ta jin kafafunta za ta taka gidan Ramlat har abada.
***
Ɗaure fuska ya yi.
"Binciken kuma na menene kike yimin?"
Ta bude baki gami da tattara fatar gira tana kallo
nsa.
"Bincike? Ni ba bincike na je ba, katin da ka siyamin na je
ɗ
auka. Sweet Aliy don Allah ka fadamin gaskiya. Hankalina ya kasa kwanciya wallahi, sigari ka ke sha?"
"Idan ina sha sai me? Please Baby Ina roƙonki ki kyaleni. Haba, na shigo gi
da ba ki kai ga ban abinci ba za ki ƙara min yunwa? Tunda nake da MUHIBBAT ba ta ta
ɓ
a yimin irin haka ba. Bana so please ki bari idan kina so a zauna lafiya."
Yana kaiwa nan ya shige bandaki gami da rufo ƙofar. Da ace tasan asarorin da suka hau kansa
a Kasuwa, da ba za ta tareshi da batun wani banzan sigari ba. A dalilin ya burgeta, ya yi amfani da maƙudan kudadensa na saro kaya ya ha
ɗ
a lefe, bai tsaya anan ba sai da ya ha
ɗ
a da cin bashi. Yanzun kwanciyar hankalinsa daya, ya samu Abulle ta shigemasa ga
ba wurin Justice ko zai ga haske.
Ta kasa kwakkwarar motsi, kamar dai kunnuwanta ne basu ji daidai ba. Ta fi tunanin mafarki ne, za kuma ta farka.
*Wannan zahiri ne, mai dogon zango!*
I think you'd like this story
: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/Cxvlk7xM09
🕯
️
*ƘARFEN ƘAFA*
🕯
️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
_Littafin Ƙarfen ƙafa dungurugum sadaukarwa ce gareki yar uwa kuma mai bani k
yawawan shawarwari a dukkan tafiyata. Barr Firdausi Kabir.
🤩🤩🤩👏🏿
Allah Ya bar zumunci. Baki ba zai iya misalta godiyata gareki ba. Allah Ya bar kauna fisabilillah. Ameeen.
💞💞
Madallah da yar uwa kuma ƙawa ta gari._
🤲🏿💃🏿💃🏿
16)
Ju
yi kawai take amman baccin ya ƙi zuwa. Tunanin Aliyu na shan sigari ya fi komai dagula lissafinta. Kishin yabon Muhibbat da ya yi a gabanta ya fi komai ci mata tuwo a kwarya. Ga kewarsa da take ji, tun zuwanta gidan basu ta
ɓ
a raba makwanci ba. Wannan na da
ga dalilan da ta kasa bacci ba tare da shi a kusa ba.
Kamar yanda ba ta yi bacci ba, haka shima. Karfe kusan ukun dare ta fito falon da zummar daukar ruwa. Ji ta yi an rungumeta ta baya, za ta yi ihu ya rufe bakin.
"Baby ni ne fa." Sauke ajiyar
zuciya ta yi, sai kuma ta shiga kokarin tureshi.
"Ka rabu da ni."
Ba ta yi aune ba ta ji ya
ɗ
auketa cak zuwa dakinsa, duk yanda ta so ta kwace abin ya ci tura, sai da ya ajiyeta saman gado kafin ya yi saurin ƙarasawa ya datse kofar yana nishi.
"Baby kin soma nauyi wallahi. Wai! Kin ji hannuna?"
Ta kara murtuƙe fuska sai hawaye.
"Ni ka budemin na fita, ƙishin ruwa nake ji."
Ruwan ya miƙomata na roba, ta kar
ɓ
a ta sha. Zama ya yi gefenta gami da narkar da murya. Gaba daya ya koma
kalar tausayi.
"Baby na tuba. Ba zan ƙara ba. Zan yi kokari na daina idan hakan zai sa ki farin ciki."
Ta
ɗ
an soma jin sanyi, ya sa hannu ya shiga sharemata ruwan hawayen. Yana kara kashe jikinta da kalamai masu dadi, duk inda ta
ɓ
ullo sai ya tos
he. Har dai ya ci nasarar shawo kanta.
***
"Kai Zakina, kana da hankali kuwa? Duka-duka yaushe Alƙali ya ba ka gudunmuwar biki? Yanzu don rashin ta ido ka ke so ya karamaka jari? Kar fa ka manta ba haifarka ya yi ba."
Kalaman Abulle sun matuka
r
ɓ
atamasa rai.
"Eh ki gorantamin! Dama kema nasan ba sona kike ba, kowa ma a gidannan ya tsaneni ya tsani ci gabana. Toh ai shikenan, duk abinda zai faru ya faru. Idan aka soma bi da ni ofishin ƴan sanda kwa fidda kudi wurin belina."
Yana kaiwa
nan ya sa kai zai fita, Abulle tuni ta yunkura ta rike gefen rigarsa.
"Haba Zakina, Gadanga ƙusar yaƙi. Me ya yi zafi shi ba wuta ba da za ka dinga batun ƴan sanda, da yardar Allah ba za ka ta
ɓ
a tozarta haka ba har abada. Jari ko? Ka kwantar da hanka
linka ai ni na haifi Alƙali ba shi ya haifeni ba, don haka dolensa ya yi yanda nake so. Sha kuruminka anyi an gama. Haba
ɗ
an marayana? Yi dariyar mana."
Yanda ta yi din sai ya sanya shi murmusawa.
"Yauwa ko kefa Kakus, ke fa kika haifesu, ba wand
a ya isa ya ketare umarninki. Idan ma sun gwada ki yi musu kuka da barazanar tsinuwa ki ga idan za su ƙi."
Ya ƙarashe murya ƙasa-ƙasa, bai damu da duk ma abinda za ta ce ko ta aikata ba, shi dai ya tsira a wajen Alhaji Yusha'u, ya biyashi kudadensa ya
kuma farfa
ɗ
o da kayan shagonsa.
"A'a, bai kai ga nan ba. Ai idan an tafi ga hakan ban ma isa ba, shi a wa? Kai dai ka kwantar da hankalinka kawai. Da kaina zan kiraka na damƙa maka."
Sai sannan ya saki dariyar farin ciki, wannan ya kwantar da h
ankalin Abulle. Kauna da tausayin Aliyu na kara ratsa ta. Kusan dagaske babu mai sonsa a gidan, ta kuma sani halinsa aka tsana, toh hannunka kuma ai ba zai ru
ɓ
e ka yanke ka yarr ba.
"Yanzu ka sa ranka a inuwa dai. Wannan bushewar taka ne ban san ta m
enene ba Zakina. Kodai kishiyartawa ce ba ta kiwatamin Kai yanda ya dace?"
Ya sanya harshe ya lashi busassun le
ɓ
ɓ
ansa yana murmushi.
"Babyna tana kiwata fiye da zatonki. Har ta fi diyarku kula da ni."
Ta
ɓ
e baki Abulle ta yi.
"Mu gani
a ƙasa, wai an ce da kare ana biki a gidansu. To Allah na tuba ko sadda kake auren Muhibbat ka fi haka kyau da sheki."
Miƙewa ya yi gami da jan tsaki.
"Kinga Kakus na tafi, ba zai yiwu na tsaya sauraronki kina zagarmin mata ba. Sai anjima."
Bai bari ta kara tankawa ba ya yi wuf ya fice a
ɗ
akin ya bar ta ta dogon salati.
Shi kansa ya sani yanzun sigari da kayan maye na kara hudashi yana shiga cikin jikinsa. Ƴan dabarun da yake yi ma a baya don kar gano komai zuwa lokacin ya gani ya da
ina. Shikenan kuma ba zai huta da rayuwarsa ba? Zai
ɓ
ata lokaci da tsoron mutan duniya. A'a. Ya gaji. Ba ruwan Ramlat a ciki, shaye-shayensa ne.
Ya ayyana hakan a ransa.
***
"Saboda bishiyar kudi ce da ni?" Ya furta ransa na wani zafi, zafin
ba na komai bane sai irin yadda Mahaifiyartasu ke biyewa son ran Aliyun kamar shi kadai ne jikanta.
"Kai AbdulRazaƙi, ni kake fa
ɗ
awa haka? Na shiga uku ni Abulle, dama akwai ranar da zan yi magana ka nunamin iyakata? Oh duniya ina za ki da mu? Allah
Ya jiƙan Malam, Allah Ya kawo nawa ajalin na mutu ku huta."
Justice ransa ƙara
ɓ
aci, ya yi maimakon ya lalla
ɓ
ata kamar yanda suke yi idan ta soma irin wadannan zantukan, sai ya hau fa
ɗ
a, ta inda yake shiga ba ta nan ya ke fita ba.
"Nan kika
ɗ
aur
ewa yaronnan gindi ya je ya ha
ɗ
a lefen burga, ba yanda ba muyi don a tsawatar ba kika hau yi mana barazana da tsinuwa muka kama bakunanmu. Shi yaron bai an muna da details na dukkan abinda yake shukawa ba a gari? Ko an fadamasa don mun ba shi jari ba ma sa
nya idanu? Sai ki yi ta zama kina biyewa yaro yana ƙara lalacewa? Sisina ba zai ƙara shiga hannun Aliyu ba da sunan wai jari."
Yanda ya dage yana surfa ruwan fa
ɗ
a sai Abulle ta yi lakwas ta kuma kasa kata
ɓ
us. Ko irin rikon da Aliyu ya yi ga ƴarsa bai
sa ya
ɗ
auki zafi irin na yau ba. Duk cikin yarannata ta fi su sanya da kuma yanke hukunci cikin sanyin zuciya ba da hargagi ba, ta san Alƙali magana daya yake, idan kuwa ya yi to fa shikenan ta zauna. Yana da wahala ya yi ja in ka da ita, yau kam ko daga
yanayin fuskarsa za ka fuskanci ransa dagaske a
ɓ
acen yake don har wani ja-ja yake yi.
"To ai shikenan, zan aika kauye wurin Shehu,(mijin mai tayata aiki Ladidi da ta damƙa mishi amanar kiwo) ko bijimina ne sai a siyar na ba shi. Amma ka yi hakuri ka
tambayeshi wanda ke binsa bashi ka biyamishi. Ka yimin wannan alfarmar domin Allah da Annabi s.a.w. Yaronnan maraya ne, babansa bai da karfi. Ni ce komai nashi, hannunka ai ba zai ru
ɓ
e ka yanke ka yar ba."
Ta yi maganar cikin karaya har da sharar kwa
lla, yasan har yanzu dai ana jika. Abulle ba za ta ta
ɓ
a bari Aliyu ya san zafin nema ba da kansa, kowane gata burinta ta yi mishi. Ganin hawayenta ya sa shi saurin magana.
"Shikenan, bashi ko? Zan biyamishi, zan tura da kaina wurin Alhaji Yusha'un da
ya ce yana binsa. Na san mutumin a yanzu shi ne shugaban ƴan kasuwar kwarin, da kaina zan biya. Wannan ya miki?"
Sai ta hau dariya da sanya albarka. Haka ya fita yana kara jinjina kaunar jika da kaka dake tsakanin bayin Allahn.
***
*Bayan Wat
anni Biyu*
Allah Madaukakin Sarki Mai sauya dukkan lamura, Shi ke da ikon mayar da talaka Sarki, ya kuma maida Sarki talaka. Kamar haka, Ya kawo