Showing 75001 words to 78000 words out of 255051 words
Ita kuwa dagaske ko Aliyu zai dinga yanka namanta gunduwa-gunduwa ba za ta kara zuwa ta kai ƙararsa ba. Ba ta son koda kallon Munir don ganinsa take kamar wani bare a wurinta yan
da yake dubanta a yanzun. A gaggauce ba ta ko tsaya sallah ba ta fito falon ya biyo bayanta.
"Ke ina za ki je? Muniru korarmin ita ka yi? Ina kuma kake son ta fa
ɗ
a?"
Fadin Hajja tana miƙewa tsaye a rikice, Bilkisu ta
ɗ
ora ƙafa
ɗ
aya kan
ɗ
aya wani
azababben dadi yana yawo daga kai har kafafunta tana ji kamar ta yi tsalle ta rungume mijinta. Burinta ta ga Ramlat a wulaƙance fiye da yanda ta yiwa
ɗ
an uwanta.
'Ka
ɗ
an ma kenan!'
Ta fa
ɗ
i a ƙasan ranta, Ramlat kuwa ba ta ko lura da ita ba, ba ta
tsaya amsa kiran da Hajja ke faman kwalamata ba, ta zura takalminta ta bar gidan.
A hanya har tuntu
ɓ
e take yi tsabar sauri da tunani har ba ta kula da abinda ke gabanta. Haka har ta iso titi tunanin kalaman Munir ke mata yawo a kwanya.
Wani wa
wan burki da aka ci, gami da salatin da jama'a suka
ɗ
auka ya ankarar da ita dalilinta ne. Ta hau titi ba ta sani ba, ta hau ba'a hayyaci ba har mota na shirin
ɗ
auke ta. Ta tsaya cak, mai motar wani dattijo, ya fito ya dinga surfamata ruwan masifa. Abu daya
ta dauka a ciki, kalmar da ya yi amfani da ita.
"Ba ki da hankali!" Wannan ka
ɗ
ai ya tsaya a kwakwalwarta. Tana hawaye ta gyada kai.
"Eh ban da hankali. Ka yi hakuri, ka yi hakuri." Abinda ta iya fa
ɗ
i kenan kafin kuma ta tsinci kanta da ƙarasawa
wurinsa ta durkusa.
"Don Allah Baba ka yi hakuri. Wallahi banda hankali ka taimaka ka kaini asibiti."
Kowa kuma sai ya tsaya kallonta, kallon ta
ɓ
a
ɓɓ
iya, ita kuwa kuka take, kukan da take jin har ta mutu ba za ta daina ba. Kukan dana sani, kukan nadam
a.
'Bijirewa iyayenki ne ya jawomaki.'
Wani bangare na zuciyarta ke mata tuni.
"Ke mene haka? Tashi ki tafi na yafemaki. Allah Ya kiyaye gaba."
Dattijon ya samu kansa da fa
ɗ
a don abin kuma mamaki ya koma ba shi. Ta miƙe cikin bin umarn
insa har da godiya ta ja gefen titi ta tsaya. So take ta tari abin hawa da zai maidata inda ta fito, gidan Aliyu. Gidan da a yanzu Muniru ya tabbatar mata nan ka
ɗ
ai ne gatanta. Dakyar ta iya
ɗ
aga yatsa ta tsaida napep har sannan idanun wadanda aka yi abin
gabansu suna kanta. Ta fadi sunan unguwa ta hau ba ta ko tsaya ciniki ba.
Ɗ
an sahun har da saita madubi yana kallonta, kuka take yi babu makari (hannu ko gefen mayafi), ba ta damu a ganta ba. Ba ta da za
ɓ
i akan ko
ɗ
aya. Nadama ce tsantsa da dana sani.
"Bansan zai jawomin baƙin jini har haka ba, a lokacin giyar soyayya ce ta kwasheni. Ban san haka zan koma ba. Ramlat nada gata ta kowane bangare, iyayena ba su rageni da komai ba. Amma na kasa yi musu biyayya akan abinda bai taka kara ya karya ba, wann
an wane irin sakamako ne? Ni na dawo haka?"
A fili take zancen, ko kuma zantuka. Mai adaidaita sahu tun yana tsoro da yi mata kallon ta
ɓ
a
ɓɓ
iya har ya gane kamar damuwa ce da
ɓ
acin rai ya jawomata komai. Tausayinta ya kamashi, kamar ya ce dama duk wand
a bai bi iyayensa ba, rayuwa za ta zo mishi a baibai, sai kuma ya ja bakinsa ya yi shiru.
Dakyar ya samu ta mishi kwatancen inda za ta sauka, ta ciro dari biyar ta mikamasa babu batun kar
ɓ
ar chanji. A farko ta yi niyyar shiga gidan Maman Anas, sai ku
ma kalaman Munir suka tunzurata ta bude gidan Aliyu ta shiga.
Mashin dinsa yana nan kuma inji a kunne shaidar ya dawo, tana shiga falon hayakin sigari da ƙamshin shisha ya kara
ɗ
e hancinta, ko mutum dakyar kake iya hangowa a falon. Ba ta yi mishi maga
na ba, shima bai mata ba sai ido da ya bi ta da shi har ta shige
ɗ
aki.
Bai ta
ɓ
a zaton dawowarta a ranar ba, wannan ya
ɗ
an kashemasa jiki. Yana son Ramlatu, abinda ya sanyawa ransa shine ba ta iya magana ba. Shi kuma ba ya son raini, idan shi ya fadam
ata, ya isa ne. Ita kuwa ba ta isa ta fadamasa ya kyale ba.
***
Sallolin da suke kanta ta biya, zama ta yi tana lazimi har aka kira Magriba ta
ɗ
ora da shi. A hankali yunwa ta addabeta, ta fito falon. Hayaƙin ya tafi sosai, sai ta kula da labulayen d
a ya
ɗ
aga, gami da ware fanka. Kai tsaye kicin ta shiga, Allah Ya taimaka tana da miya don haka taliya fara kawai ta dafa ta dumama miyar. Nan ma koda ta fito ba ya falon,
ɗ
akinta ta wuce, ta dawo ta dauki ruwa ta koma ta kulle da muƙulli.
Tana cik
a cikinta ta jawo wayarta da zummar kashewa. Karo ta ci da sunan Muhibbat na yawo saman screen din da alamar message. Budewa ta yi ta soma karantawa.
*Assalamu alaikum matar yayana. Naji shiru ba ki zo ba, Yaya ya cemin ba ki jin dadi. Ba haka na so
ba dai, amman ba komai. Allah Ya saukeki lafiya. Nagode sosai."*
Wasu hawaye suka zubomata saman ƙuncinta, Muhibbat su ne irin matan da ake kira ƴan aljanna. Mace ce da ba ta da riƙo, ba ta da fushi. Idan ma ta yi, ba ta da wuyar sauka. Ta sani, laif
ukan da ta yi mata ba zasu ƙirgu ba. Ta tsinci kanta da rubutamata saƙo kamar haka.
*Kyawawan halaye su ne linzami a kowane tafiya. Su ne nagartar kowane
ɗ
an adam da cikar kamala. Ki godewa Allah, kin dace da samun haka. Ina mai jin kunyarki a koyau
she. Ki yafemin, ni mai tarin laifuka ce gareki. Ki yafemin domin Allah.*
Tana kaiwa nan ta aikamata, wayar ta ajiye ta mike ta soma kokarin rage kayan jikinta. Ruwa ma dakyar ta ke ta
ɓ
awa ta yi alwala tsabar sanyin gari. Wayarta ce ta dauki ƙara, ta
yi azamar dubawa. Hajiya ce.
"Salamun alaikum, Ramlatu kina lafiya?"
Wani rauni ta ji da na zuciya da gangar jiki.
"Waalaikumussalam. Hajiya ina wuni?"
Ta amsa kafin ta kara tambayar tana ina?
"Ina gidana."
Shiru ya dan biyo
baya kafin Hajiya ta ce.
"Toh Alhamdulillah. Bari na bar ki haka dare ya yi. Da safe ma yi magana."
Daga haka Hajiya ta katse kiran ta bar Ramlat da bin waya da kallo. Sai kuma jikinta ya bata watakila sun yi magana da Hajja.
Hakan bai mat
a dadi ba, kenan zargin Munir na jefa iyayensu cikin damuwa ya tabbata a kanta.
***
Ita kuwa Hajiya tun bayan Magriba Hajja ta kirata ta fadamata komai. A farko ma ta dauka Ramlatun gidan ta je.
Hajiya ranta ba ƙaramin
ɓ
aci ya yi ba, ta k
ira Munir ta yi mishi tas ta kara da fadin.
"Don ka wulaƙanta ƴar uwarka a gaban Bilki me yake yi? Idanunka sun rufe ka mance wacece Bilki a wurin Hilal! Ko bayan ranmu kai ba mai rufe sirrin Ramlatu bane? Wato ka gwammace Ramlatu ta shiga duniya a ba
yan babu mu, akan ta zauna cikin sutura a gidanka? Wallahi Muniru koda wasa na ji ka ƙara sanya baki cikin lamarin Ramlatu sai na sa
ɓ
amaka tunda ba alheri ne ke kai ka ba!"
Daga haka ta katse kiran tana hucin
ɓ
acin rai.
"Me ya yi?"
Muryar
Abba ya sanya kirjinta dokawa tara-tara. A falonsa take wayar duk a zatonta wanka ya shiga. Ya ƙaraso yana dubanta.
"Me ya faru ga Ramlatun?"
Ta rasa me za ta ce, dole ta fadamasa. Ransa ya
ɓ
aci, shima wayar ya cira ya kira Muniru. Ranar dai Muni
r sai da ya yi dana sanin zuwa gidan Hajja har ta kai shi da ganin abinda zai jawomasa
ɓ
acin ran iyaye.
Bayan kammala wayar, Abba da kansa ya umarci Hajiya ta kira Ramlatun ta ji inda take.
Hankalinsu bai kwanta ba sai da suka tabbatar tana gida
.
"Goben ba kiranta za ki yi ba, da kanki za ki taka ki je gidanta."
Abinda Abban ya fadi kenan bayan kammala wayar Hajiya da Ramlatun. Hajiya ta jinjina kai, Abban har ya mance da alwashin da ya ci na cewa ba dai su taka gidan Ramlatun ba idan
ta auri Aliyu. Murmushi kawai ta
ɗ
an yi. Ɗa da mahaifi kam sai Allah.
***
"Sau nawa zan ce ka rabu da ni? Na gaji da tuban muzurunka!"
Ta fadi a fusace bayan ta yarfe hannunta daga nashi. Aliyu ya kara marairaicewa.
"Ki yi hakuri Baby,
kema kin sani ina sonki. Ban san meyasa kika kasa gane cewa raini kawai na tsana ba. Wannan ka
ɗ
ai ne dalilina na kai maki hannu. Amma wallahi matukar kin kiyaye ba zan ƙara ba. Ki yi hakuri don Allah."
Ta yi shiru kawai ta kyaleshi ta ci gaba da ninke
kayan wankinta. Kwanaki biyunnan kayanta na wanki sun taru, ba ta iya wankin saboda kasala da kuma zirga-zirgar makaranta.
"Yauwa ki ha
ɗ
a kayan wankinki wuri guda, yau zan kai maki wurin mai wanki da guga. Naga ma zannuwan gadonki suma sun yi dau
ɗ
a.
"
Ranta ya
ɗ
an yi sanyi amma ta waske ba ta nuna ba. Duk daurewarta da rashin sakin fuska sai da Aliyu ya rinjayeta suka shirya. Karshe ma har ya ja ta dakinsa ya biya bukatarsa. Sai gasunan suna hira da dariya abinsu. Shi ya taimaka mata da komai na
gidan suna dariya. Wayarta ta yi kara suna falo a zaune suna hira. Ganin sunan Hajiya ta dauka da sauri, wannan karon muryarta a sake ba kamar jiyan ba.
"Gamunan a kofar gidan naki. Allah Yasa dai shi dinne, nan dai Rafee'ah ta kwatantawa Malam Tanko
."
Ta dauka mafarki take don haka ta kaiwa cinyarta duka, aikuwa sai ta mike har da doka tsallen murna, Aliyu na kallonta kawai.
"Toh Hajiya bari na leƙo na gani."
Ta katse kiran a gaggauce ta dauki
ɗ
ankwalinta ta daura.
"Ya dai?"
"Hajiyata ce ta zo Sweet Aliy, ka tayani murna."
Ba ta ma saurareshi ba ta fita da sauri. Aliyu ya bita da kallo yana tunanin anya kare bai lashewa Ramlatu zuciya ba. Tsohuwarnan ba ta ta
ɓ
a takowa gidansu ba sai yau. Amma ya zama dole ya danne
ɓ
aci
n ransa, ko ba komai yana saka ran ba hannu Rabbana za ta zo gidan ba. Ya mike ya shige dakinsa don sanya sutura ta kamala madadin singelet da gajeran wando dake jikinsa.
Hajiya ta shigo bisa jagorancin Ramlat ta zauna. Jikin Ramlatu har rawa yake do
n ta ma rasa irin tarbar da za ta yi mata.
"Hajiya ki ƙaraso dakina."
"A'a bar ni anan dai."
Fadin Hajiya tana ƙarewa falon kallo, ba laifi ya yi kyau. Aliyu ya fito da sallamarsa.
Nutsuwar da ya yi da kuma kalar gaisuwar da ya yi ga H
ajiya ba karamin burge Ramlat ya yi ba har mamaki ya kusan kasheta a zaune. Hajiya ta amsa fuska a
ɗ
an sake, kafin kuma ya mike yana amsa gaisuwar A'isha ya fice daga gidan.
Ba wani jimawa Hajiyar ta yi ba amman Ramlat ta ji dadi ba ka
ɗ
an ba. Ta so H
ajiyar ta ci abinci ta ce sam. Dakyar ta samu Hajiyar ta karasa
ɗ
akinta ta gani da kuma kicin.
"Gida ya yi kyau, Allah Ya yi albarka." Ta furta sadda take karewa kicin din kallo. Da zumu
ɗ
i Ramlat ta amsa.
Har kofa ta yi musu rakiya tana jin kam
ar kada su tafi, farin cikinta ma har da saƙon da Abbanta ya aikomata na kudi. So yake ta rage tambayar Aliyu komai musamman na dawainiyar makaranta, burinsa ta zauna lafiya ba tare da ta miƙa hannu da yawan bani-bani ga miji ba.
***
BAYAN WATANNI
TAKWAS
Dubansa ta ke ranta a
ɓ
ace, shi kuwa tsayawa ya yi yana karemata kallo.
"Ba don tulelen cikinnan ba Baby, wallahi da sai na kifar da ke na bi ta kan gadon bayanki na fice."
Ta gyada kai.
"Za ka iya ai! Wannan kadan ne daga aikin
ka. Aliyu ina aka ta
ɓ
a haka? Tun yaushe nake maka batun kayan Baby kana yimin kwana-kwana. So kake na je asibiti a zageni? Kai kullum zancenka ba zai gagara ba! Kullum zancenka kenan! Ni na fadamaka lallai i lalla sai ka yimin abin kece raini? Naji na yard
a ko nawa ka kashe ka siyi irin wanda kake da muradi wannan kai ta shafa, amma wannan na amfani urgent bai kamata ka yi wasa da shi ba."
Ta fadi kamar ta yi kuka. Ta gaji da gafara Sa ba ta ga ƙaho ba. Haihuwa ta matso kullum cikin
ɓ
oye laifin Aliyu t
ake tana cewa ya siya kayan haihuwa don ta gaji da abin maganarsa. Auren da duka-duka ko shekara biyu ba su rufa ba ta kai ƙararsa ya fi a ƙirga, ciki ne kadai ke sanyawa ba ya kai mata bugu yanzun, amma fa bai fasa dukkan wani rashin mutunci ba, sai abind
a ya ƙaru. Ga sauyin rayuwa da ta ƙara lullu
ɓ
esu, komai sai a hankali. Ta lura ba shi da niyyar yin ko yaya ne.
"Kin gama?"
Ya fadi yana hade gira. Ta kalleshi a kaikace, duk shan sigari da shaye-shaye ya ƙara motsar da shi, koyaushe ci yake am
ma a bushe. Le
ɓɓ
ansa kuwa baƙin da suka yi ko sha'awa basu ba ta.
"Nace kin gama?"
Shiru ta kara yi mishi.
"Ke bari ki ji, ya dace ace kin gama sanina amma kamar bokon kike zuwa kawai ba don ki amfana da iliminki ba Baby. Ni Aliyu ba ki i
sa ki sauya ra'ayina ba, abinda nayi niyya shi zan aikata. Ko yau kika haihu washegari zan siyo duk abinda ya kamata, na fadamaki akwai kudadena a wurin Shamsu Case, wannan satin zai ban, a kanki da Babynmu zai ƙare. Ke wai ba daga gidanmu za'a kawo kayan
ba ma? To ki samamin lafiya."
Zai gifta ta kara tare hanyar, shi dariya ma ta ba shi. Gaba daya hancin ya bude ga uban rama da ta yi. Wuyanta wani baƙi da ya ƙara ba'a magana, hakanan fuskarta.
"Naji, naji za'a kai daga gidanku, amma don Allah
ka yimin wannan alfarmar ka fidda kanka da kuma ni kunya a asibiti, haba Aliyu, ta yaya zan je banda ko zanin rufe yaro? Na gama cika baki a ko'ina ka yimin dukkan siyayyar da ta dace, haihuwa fa ba'a saka mata rana, ko yaushe za ta iya kama mutum."
Tsaki ya ja.
"Shikenan, ba dai rigar jariri ba ce da famfas? Zan tahomaki da su."
"Ba su kadai ba ne, ko ka manta da list din da na ba ka na asibiti?"
Ya ta
ɓ
e baki gami da sanya hannu ya kauda nata hannun jikin ƙofa.
"Ki turomin ta
text."
Daga haka ta kauce din ya fice, ranta fatan ya kasance gaskiya take. Alokacin kuwa ta fiddo takardar ta shiga rubuta dukkan muhimman abubuwan ta aikamasa.
Fatanta Allah Yasa ya siyo din, zuwa yanzu ta gama sanin Aliyun ba shi da tabb
as ko kadan. Zai yi wuya ya daukarmata alkawari ya cika. Rayuwa yanzun ta kara juyamusu baya, kasuwa ta ja wa Aliyu baya sosai, hakan kuma har da rashin maida hankalinsa ga abinda ya dace. Babban bakin cikinta yanda ba damar ya ganta da ƴan chanji sai ya s
an yanda ya yi ya dauke. Ta sha zuwa ta ganshi cikin sif dinta yana mata bincike. Wannan abu ya fi komai ci mata tuwo a kwarya. Idan ma ya dauka ta riga ta san a mashaya yake ƙarar da su. Akan hakan har yaji ta yi zuwa gidansu, ta share dukkan gargadin Mun
ir ta watsar. Sai da ta yi kwanaki goma cif sannan Aliyu ya kasheta da dadin baki ta shirya ya zo suka tafi. Iyayen kawai kallonta suka yi. Kusan a yanzun ma basu kaunar shiga fa
ɗ
anta da Aliyu don a karshe kunya take ba su.
***
"Please kar ki damen
i, sata kike so nayi na kawomaki wai? Ban samu kudi ba, iyakar abinda zan iya yi kenan. Mtsw."
Ta bishi da idanu kafin ta maido duba ga kayan da ya siyomata. Gwanjo ne, gwanjon ma ba masu kyau ba. Rigunan jarirai ne, biri da wando kala uku sai karama
ta ciki shima kala uku sai wani tsohon showel fari wanda ya tashi daga farin ya koma ruwan madara. Sai kuwa famfas leda guda. A gefe kuwa Pad din mata ce karamar leda guda sai man goya da reza.
"Shi kadai za ka iya siya Aliyu? Wannan su ya dace da
haihuwarka ta farko? Ɗan farko fa Ali..."
"Dillah Malama ki yimin shiru mana!"
Abinda ya ce kenan a tsawance wanda bai ko girgizata ba, idan da sabo ai ya ci ace ta sabI think you'd