Showing 159001 words to 162000 words out of 255051 words

Chapter 54 - KARFEN KAFA complete

shigo yana fa

ɗ

i i

yakar ƙarfinsa. Hunainah ta miƙe ta fita don yin sallama da mijinta.

"Har maganar ta kai ku kasa dannewa a gaban Hunainah?"

Cikin karyewar zuciya Ramlat ta furta.

"Hum ai shikenan. Allah Ya kyauta."

Rafee'ah ta fa

ɗ

i tana mai miƙew

a ta fice daga

ɗ

akin. Sosai Zulaihat ta fuskanci ƙanwarta.

"Ya kamata ki nutsu ki yiwa kanki fa

ɗ

a Ramlat. Ke ba yarinya ba ce, kin ta

ɓ

a aure kin kuma hayayyafa, ba girmanki bane a soma ƙirgamaki aure wannan ne yasa gwara ki watsar da komai ki fuskanc

i rayuwa tun lokaci ya ƙuremaki. Da ki yi auren jeka na yi ka, gwara ki dau dogon lokaci ki auri wanda za ki zauna da shi har mutuwa ku rayu. Idan har ba ki tsaida wani kin kawo matsayin miji ba, kina ji kina gani za'a

ɗ

aura aurenki da wanda ki ke gujewa.

Na fadamaki ki nutsu ki san me kike. Ki kuma ha

ɗ

a da addu'a, za mu tayaki."

Ramlat ta gyada kai tana jin wani sassauci na ratsa zuciyarta. Zulaihat ta fita ta bar ta anan zaune. Shiru ta yi tana mai ƙurawa hannunta da ya sha lalle idanu, mutuwa mai t

onon silili. Hakan ta ayyana yayinda hawaye nta suka soma

ɗ

iga.

***

Tafe yake cikin shiga ta alfarma, a gefensa Hajiya Zeenatu ce tana zabga uban murmushi. Hannuwansu sarƙe cikin juna.

"Husseini!" Ya ji wata murya ta kwalamasa kira, kusan l

okaci guda suka juya shi da Hajiya Zeenat. A fuskar Hajiya Zeenatu, tashin hankali ne tsagwaronsa, idan ka

ɗ

auke Hussein wanda idanunsa suka ka

ɗ

a suka yi jazur. Damƙe hannunsa da Hajiya Zeenatu ta ƙara ya sanyashi dubanta a hargitse.

"Husseini kai

ne?!" Ya juya ga matar da ke tsaye tana dubansa dakyau.





I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/i7Akdw4Ovcb

🕯



*ƘARFEN ƘAFA*

🕯



_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

43)

_*Tafe yake cikin shiga ta alfarma, a gefensa Hajiya Zeenatu ce tana zabga uban murmushi. Hannuwansu sarƙe cikin juna.*_

_*"Husseini!" Ya ji wata murya ta kwalamasa kira, kusan lokaci guda suka juy

a shi da Hajiya Zeenat. A fuskar Hajiya Zeenatu, tashin hankali ne tsagwaronsa, idan ka

ɗ

auke Hussein wanda idanunsa suka ka

ɗ

a suka yi jazur. Damƙe hannunsa da Hajiya Zeenatu ta ƙara ya sanyashi dubanta a hargitse.*_

_*"Husseini kai ne?!" Ya juya ga

matar da ke tsaye tana dubansa dakyau.*_

_*"Kar ka je gareta! Zo mu tafi!"*_

_*Hajiya Zeenatu ta furta iyakar karfinta. Matar na jin haka ta taho gadan-gadan da zummar nufar Hussein kai tsaye tana fadin.*_

_*"Ni ce Husseini! Dadarka ce! Ka m

anta ni?"*_

_*Ba ta kai ga ƙarasawa ba ta ci uban tuntu

ɓ

e za ta fa

ɗ

i. Sai dai caraf aka riƙeta. Hussein ya dubi mai shi, mace ce cikin fararen kaya. Daidai sadda Hajiya Zeenatu ta soma jan hannunsa, hawaye yake fitarwa yana dubansu da wacce bai san ko

wacece ba. Caraf aka riƙe hannunsa, dole suka tsaya cak. Fuskar Ramlat ya gani na wani haske da kyalli, murmushi ta ke yi madadin kukan da Dada da kuma shi suke yi, ta

ɗ

ago hannunsa ta sanya a cikin na Dada ta matse su.*_

_*"Har abada babu wani ko w

ata da zai ƙara shiga tsakaninku."*_

_*"Ƙarya kike!" Hajiya Zeenatu ta furta tana ihu.*_



***

"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!"

Ya furta a fili yana maida numfashi kamar wanda ya yi tsere, jikinsa gumi yake fitarwa duk kuwa da sany

in da ke a

ɗ

akin. Kirjinsa bugu yake da sauri-sauri. Ya kai duba ga makwancin Hajiya Zeenatu. Bacci take ta lullu

ɓ

e har kai da bargo. A hankali ya dauki wayarsa a gefen gado ya kalli agogo, biyar saura mintuna, tabbacin Asuba ce. Don haka ya mike yana juya

yin mafarkinsa.

'Dada?' Ya maimaita a zuciyarsa yana juya sunan, yana da wata mai suna Dada? Kuma a ina? Tunani ya yi mishi yawa har ya

ɗ

aura alwala ya fito, kansa wani irin sarawa ya ke. Me mafarkinsa ke nufi? Ramlat ya gani, ihun kuma da Zeenatu ta yi

na menene?

Babu mai amsa masa, wannan tasa ya fice daga dakin zuwa falo gami da shimfida darduma ya yi nafila. Bayan idarwa ya yi addu'a. Masallaci zai fita, don haka sai ya koma dakin ya tashi Hajiya Zeenat sannan ya fita. Ta bishi da kallo har ya

fice sannan ta ja tsaki tana miƙa, ta lura da wani ustazanci da ya soma. Sallah a masallaci ya daina wuce shi, ita dai tana jin tsoron ibadar da ya soma maida hankali a kai. Ko ba komai ai ta sani wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa. Ƙarfin ikon Allah da ad

du'a ya shallake dukkan ƙarfin mai ƙarfi.

Jiki a sanyaye ta miƙe tana tunanin mafita.

'Ku bar ƙasar zuwa wata ƙasar kawai!'

Wani

ɓ

angare na zuciyarta ya shawarceta. Sai dai tana tunanin ta yanda za ta sa Hussein ya amince da wannan shawa

rar da tun ba yau ba ta ke ƙoƙari a kai.

***

Misalin shida na safe, iyalan gidan Alhaji Khalid Mu'azzam sun fito fess sun sha wanka har da yaransu idan ka dauke Ramlat da nata yaran ke gidan Muhibbat. Dalilin yaran ne Ramlat ta yi ƴan soye-soye na

snacks da zasu ci a hanya.

Ta sha adon doguwar rigar atamfa kalar ruwan toka da sirkin ja da yellow an mata dinkin Bubu. Ta

ɗ

ora ƙaramin mayafi kalar ja a samansa. Murmushi ta ke sai dai iyakarsa le

ɓɓ

anta bai kai ga shiga zuciyar ba. Tunani goma da ashi

rin take duk ita daya, rayuwar yaranta, auren Chairman, soyayyar Hussein da ta ke ji kamar Son Maso Wani ta ke yi kawai. Wannan ne yasa da safe ta tashi idanun ƙozai-ƙozai shaidar bacci bai wadaceta ba.

Bayan sun

ɗ

uru a motar da Munir yasa aka hayo m

usu ta kasuwa, tana daga can baya tare da yara sai Hunainah a

ɗ

ayan gefen. Ta bude whatsapp, ta gwada yiwa Hussein sallama sannan ta sanarmasa da tafiyar da za ta yi zuwa Daura. Daga nan ta sauka online ta kira Amrah suka ƙara sallama. Ba ta son yi mishi t

ext gudun kada ya fa

ɗ

a hannun Hajiya Zeenat.

'Koda shi ne abu na ƙarshe da zan maka, in sha Allah zan yi Hussein. Zan sulhuntaka da ƴan uwanka.'

Abu na farko da ya fa

ɗ

o ranta bayan wannan tunani, shi ne Kawunsa da aka ce yana zama a Kano. Da dab

ara za ta nemi cikakken sunansa a wurin Hafsat, sauƙinta ma unguwarsu

ɗ

aya da kakanninta (Hajja).

Ta toshe kunnuwanta da earpiece tana sauraron Suratul Maryam tana bi a hankali idanunta a lumshe. Wakokin soyayya ba ta da muradinsu a lokacin kasancewa

r ba karamin ingiza zuciyarta suke yi ba akan Hussein.

Tafiya ta yi nisa, shiru na ƴan sakanni, karatun ya tsaya, ta duba. Kira ne daga Hussein. Kirjinta ya bada dam! Ta

ɗ

aga ta yi sallama a hankali tana mai satar kallon su Hajiya, hirarsu suke yi na

dangi yayinda Hunainah ta rufe kanta da mayafi alamun bacci ya

ɗ

auketa ko zai

ɗ

auka, ba ta da tabbaci.

"Tafiya ba sallama? Ba ki fa

ɗ

amin ba sai yau?"

Daga yanda ya yi furucin za ka fahimci

ɓ

acin ransa.

Daƙyar ta iya motsa le

ɓɓ

an.

"Ka

yi hakuri."

Shiru ya biyo bayan can kuma ya sauke ajiyar zuciya.

"Naso yau na ganki."

Ta yi luum da idanu, ta kasa yarda da abinda kunnuwanta suka jiyemata.

"Uhm?" Ta nemi ba'asi.

"Hoton zan kar

ɓ

a ta ƙarfi tunda an hana ni."

Ya fa

ɗ

i a shagwa

ɓ

ance, ya sanyata murmushi tana mai sunkuyar da kai kamar yana gabanta.

"Zan turomaka."

"Promise?"

"Yes."

"Kinsan hoto

ɗ

aya rowa ce ko?"

Ta ƙara fa

ɗ

a

ɗ

a murmushinta.

"Uku fa?"

Tana jin sautin murmushins

a. Can ya amsa.

"Thanks. Allah Ya kaiku lafiya."

Bai jira amsarta ba ya katse kiran, karatun ya ci gaba. Kaso saba'in na damuwarta ya ragu, ta ji wani kwarin gwuiwa. Nan da nan ta shiga Gallery dinta ta hau kallon hotuna. Duk wanda ta ga shi ya

dace ta aika sai ta ga kamar bai kai ba. Ruwan ido, abinda ta tsana ta ke jin haushi a wurin Amrah, ita ce yau ta ke yinsa. Dakyar ta haƙura ta za

ɓ

i wasu guda uku ta aika kasancewar da network a wurin da suke nan da nan ya je, ba ta jira godiyar ba ta sany

a wayar a Airplanemode tana murmushi.

Koda suka isa yan uwan sun sha mamakin sauyawarta. Ƙofar Baaru kusa da gidan Sarkin Daura, nan ne ainahin gidan iyaye da kakannin su Abba da Hajiya yake. Gida ne babba na gandu, zaman iyaye da ƴaƴa. Sun tarar da su

Nusaiba mutan Kano duk an hallara. Hajja da abokiyar zamanta ma suna nan. Gida ya cika da ƴan uwa gwanin dadi. Sashen Ƙanin Malam Abdullahi kakanta nan ta yada zango wurin su Nusaiba sa'anninta, don ba ta kaunar zama da su Rafee'ah, zancen dai daya ne, na

Chairman. Ta fiddo miji ta gujewa aurensa.

Karshe ta watsar da duk wani tunani ta rage sutura ta shiga wanka. Bayan ta fito ta tarar su Nusaiba gaba daya na zaune ana kari da doya da kwai da shayi wanda ya ji citta da kanumfari.

"Ke kuwa Ramla

tu yaushe za mu sha naki bikin?"

Ta yi kamar ba ta ji maganar Gwaggo Hansai ba, ta ci gaba da goge ruwan jikinta. Ba ta ce uffan ba. Duka Dije kanwar Gwaggo Hansai din ta kai mata bakinta cunkushe da burodi.

"Ja'ira, ai tana jinki. Ta fi kaunar

muje ana daurin aure ta dawomana. Maimaita tarihi ko? Toh dagaske banni ƙara zuwa bikinta."

Aka yi dariya don an san zolaya ce ta Dije, ita dai Ramlat ta kara tamkewa ta mike ta kwashi kayanta, ta fasa shirin a falo, ta koma uwar

ɗ

aka.

***

Kam

ar wanda aka daskarar da jinin jikinsa haka ya yi

ɗ

if, a hankali ya sauke ƙarfen da ke hannunsa yana maida numfashi, gumi kam kamar ruwa haka yake

ɗ

iga daga cikin gashinsa, saman fuska har zuwa jikinsa. Kallon Hisham ya ke yi da wani irin fa

ɗ

uwar gaba. Hi

sham ya toshe kunnuwansa da earpiece yana gyada kai alamun waƙar da yake ji na tsumashi sai dai kacokam hankalin yana ga Hussein. Yana sane ya fesamasa batun auren Chairman da Ramlat duk kuwa da cewar yasan maganar rawa take yi ba ta tabbata ba. Amma

ɗ

an h

akin da ka raina ai shi ke tsonemaka ido. Gwara tun wuri ya yiwa abin tufka, ko ba komai zai ƙara karantar inda Amininnasa ya dosa.

Tasowar ta Hussein, da kuma fisge Earpiece din daga kunnensa duka-duka abin ya zamewa Hisham kamar kiftawar idanu. Ya

ha

ɗ

iye dariyarsa ya kara daure fuska.

"Lafiya Malam? Me ya yi zafi? Daga cewa Chairman Aliyu Dikko zai au.."

"Kar ka ƙarasa." Ya fadi a kausashe yana nunashi da yatsa idanun sun ka

ɗ

a cike da wani irin matsanancin kishin da bai san mafarinsa ba. H

isham ya cika da mamaki don bai zaci abin zai kai haka ba. A hankali Hussein ya zauna a gefensa ya yi shiru, can kuma ya dubeshi a sanyaye.

"Wasa ka ke yi, sai dai irin wannan ba maganar wasa ba ce. Please kar ka ƙara."

Hisham ya karkace yana du

bansa.

"Don me? Toh kai mene naka ciki? Me zai dameka? Menene ha

ɗ

in biri da gada?"

Ran Hussein ya yi tsananin

ɓ

aci.

"Ni ka ke kira biri? Hisham har wuyanka ya kai tsaikon da za ka ha

ɗ

ani da biri?"

Dariyar Hisham ta kasa

ɓ

oyuwa, lallai

ya ƙara yarda Hussein bai iya Hausar ba. Dariyar ta kara fusata Hussein wanda dagaske ya ji zafin birin da Hisham ya ambata. Abin ya ha

ɗ

emishi biyu don haka ya mike ya dauki jakarsa don suturta jiki. Hisham ya bishi da kallo yana mai ba shi tausayi. A yanz

u ba shi da abar kauna sai Ramlat, sai dai ya rasa dalilin abokinnasa na ƙin ba wa zuciyarsa abincinta. Ko a

ɗ

azun, kasancewar Hussein ya rigashi zuwa wurin motsa jikin, kama shi ya yi dumu-dumu da hoton Ramlat din yana kallo yana murmushi. Ganinsa ya war

tsake ya sanya wa wayar muƙulli.

Yana nan zaune ya fito, madadin gajeran wando, ya sanya dogo mai santsi fari ƙal mai ha

ɗ

e da riga. Ya sanya baƙin gilashi yanda idanun suka

ɓ

uya.

"Sai Allah Ya kaimu."

Ya furta can ƙasan maƙogwaro yana duba

n Hisham din a fisge. Hisham ya rike hannunsa.

"Haba abokina, ka yi hakuri idan

ɓ

acin ran da na jefaka ya kai girman haka. Karin magana na yi maka, haka Bahaushe ke karin maganarsa. Ba wai da gayya na ha

ɗ

aka da dabba mafi muni ba."

Hussein ya sa

hannu ya dan ja karan hancinsa ka

ɗ

an yana duban gefe.

"Wani abu na ƙara fa

ɗ

i?"

Hisham ya dubeshi dakyau.

"Ba ka fa

ɗ

a ba, amma ba haka muka saba sallama ba. Mafi yawan lokuta tare muke fita. Yau kuma ba alamar za ka jirani."

Guntun tsak

i Hussein ya ja.

"Sauri nake."

Ya furta kai tsaye har da duban agogonsa kalar silver.

"Karin maganar ce ko damuwar Ramlatu ce?"

Ya ji tambayar Hisham kamar daga sama, shiru ma mintuna kafin ya dubi Hisham ta cikin gilashin.

"Abi

nda ka fadi gaskiya ne?"

Yanda ya yi maganar a sanyaye, sai hakan ya sanyaya jikin Hisham. Shirun da ya yi, Hussein ya samu amsarsa.

"Sai da safe."

Daga fadin haka ya yi gaba. Murmushi Hisham ya dan yi. Shakka babu da Ramlatu za ta samu Hus

sein ba karamin farin ciki zai mata ba. Yana matukar son ganinsu tare sai dai kuma sanin tarihin Ramlatun kan sanyaya masa jiki. Anya Hussein zai gan ta da gashi?

***

_*Nan kusa za'a yi bikin Ramlat da Chairman Aliyu Dikko don na ji labarin zai kai

ku

ɗ

i.*_

Wannan kalaman ke yawo a kwanyarsa har ya hanashi maida hankali ga tuƙin da ya ke yi. Dole ya gangara gefen titi ya kashe wayar ya kwantar da kai bayan kujera. Runtse idanu ya yi na ƴan mintoci kafin daga bisani ya ƙara fiddo waya ya bu

ɗ

e hotu

nan Ramlat yana ƙaremusu kallo. Saura ƙiris ta zama mallakin Chairman yana nufin abubuwa da dama. Shugabanta wurin aiki, wanda ya fi shi kudi da muƙami, wannan na nuna kwa

ɗ

ayi ƙarara. Hira da ita da ma kallon hotunan har da ganinta a zahiri zai zama haram

a gareshi, wannan ma wata damuwar ce mai zaman kanta.

Ransa idan ya yi dubu to ya

ɓ

aci, kirjinsa zafi yake. Mafarkinsa na ƙara yawo a kwanyarsa, gaba daya ya hargitse lokaci guda. Ya tuna abu daya kwakkwara da ya danganci rayuwarsa ya kasa. Neman has

ke cikin duhu yake amma abin ya gagara. Koda ya tsananta tunani, kansa ya ci gaba da sarawa da ƙarfi, cikin dauriya ya kai hannu ya kunna CD na karatun Al-kur'ani da ke kan rediyon. A hankali ya soma samun nutsuwar zuci da na gangar jiki,

ɗ

if, sai ya nemi

yanayin ya rasa. Wannan kadai ya tabbatar da zargin da ya sha yiwa kansa a baya, wato ba shi da lafiya, kuma ya zamar mishi dole ya ga likita.

Ya kwashe mintuna biyar a wajen yana kallon motocin da ke safa da marwa kafin daga bisani ya ci gaba da tuƙins

a.

***

BAYAN KWANAKI UKU..

ADAMAWA

Tun fitowarta daga

ɗ

akin ta ke ƙunƙuni tana zuba abincin zuciyarta na tuƙuƙi ga wani ƙololon abu dabya tokaremata ƙahon zuciya. Tahir kallonta yake kamar ya ha

ɗ

iye, nan duniya ba ya jin akwai wacce za

i so sama da Hafsat. Aure ne yana ji a jikinsa tamkar an yi an gama.

"Kin yi kyau."

Ya fa

ɗ

i kamar mai ra

ɗ

a bayan ya ƙaremata kallo cikin riga da siket din jikinta na Atamfa. Harara ta watsamasa, ba don ta so ba ta dawo gidan don a farko tattara

wa ta yi ta koma gidam AlHassan da zama. Ya yi murmushi madadin hararar ta ƙona ransa, wannan ya ƙara ba Hafsat haushi, ta ja tsaki. Ita kuwa Dada ta ci gaba da hirarta da Tahir ranta na mata wani irin dadi. Kusan yanzun ta saba da shi sosai don kamar ba y

aron da a baya ya ke wucesu kerere babu ko gaisuwa ba. Ta kuma ƙara fahimtar

ɗ

abi'un yaron, jikinta na ba ta cewar duk wani mugayen halayensa akan wa

ɗ

anda ba ya so ya ƙare. Kuma zuga ce kawai.

"Dada anya ba nan zan dawo da zama na dindindin ba?"

Ya fadi yana mai kallon Hafsat, ta dubeshi da sauri, ya kashemata ido

ɗ

aya, ta mike sadda Dada ke ba shi goyon bayan maganarsa fuskarta a sake.

Ya yi daidai da sallamar AlHassan. Suka amsa, Tahir ya gaisheshi, ya amsa a

ɗ

an sake don yaron ya soma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login