Showing 168001 words to 171000 words out of 255051 words

Chapter 57 - KARFEN KAFA complete

don mutum idan aka ce mugu n

e komai ma zai aikata. Bari na kira Malam na fa

ɗ

amasa, shima ya tayamu da addu'a."

Daga nan Hajiya ta fita ta bar Ramlat da tarin damuwa. Dakyar ta iya mikewa ta

ɗ

auro alwala ta gabatar da sallar isha'i, zaman dirshan ta yi saman dardumar jefi-jefi ta

na sharar hawaye.

Addu'a sosai ta yi kafin ta miƙe ta nufi gefen gado ta zauna. Hayaniyar su Affan ta ishe ta don haka ta kora su waje. Waya ta

ɗ

auka ta hau kan whatsapp, babu alamar Hussein ya hau. Yau

ɗ

aya ta

ɗ

aura

ɗ

amarar kiransa. Don haka ta sauk

a ta danna masa kira. Wayar a kashe. Damuwarta madadin ta ragu sai ta ƙaru, ganin dukan na nema ya yi mata yawa, sai ta miƙe ta koma falo ta yi jugum. Ba jimawa Hisham ya kirata. Ta

ɗ

aga.

"Antinmu shiru, ina jira na ji yanda ku ka yi."

Ta ha

ɗ

iye

hawayenta da

ɓ

acin rai. Komai ba ta

ɓ

oyewa Hisham ba, ya dinga salati da salallami karshe dai ya kwantar mata da hankali.

"Kar ki sanya damuwa a ranki Ramlat, in sha Allah kamar yanda kika ce toh hakan ne, Allah Ya fi su. Mu dage da addu'a."

Ta

amsa da toh. Kamar ta tambayeshi ko sun yi waya da Hussein sai ta share.

***

Washegari haka ta shirya ta fita wurin aiki ranta a jagule. Ga wayar Hussein da ke a kashe. Ta gwada kira har cikin dare don tsautsayi amma ba ta shiga. Tuƙi ta ke kusan ba

za ta ce a cikin hayyaci ba. Don haka ba ta kawo da cewar an basu hannu ba sai da ta ji wani ru

ɗ

a

ɗɗ

en Hon daga bayanta. Hakan ya fusata ta, ta madubi ta ke duban mai shi. Ido da ido suka kalli juna, yana cin magani. Wannan karon ba Tinted glass din a mot

ar da yake. Yanda ya

ɗ

aure fuska ba alamun fara'a ya fi komai ruguza lissafinta. Asalima ba wani wawan overtaking da ya yi ya ka

ɗ

a hancin motarsa sai da ya daskarar da ita ya jazamata

ɗ

aukewar numfashi na ƴan dakiku.

"Me nayi masa?" Ta ambata a fili,

da rawar jiki ta ja motar bayan ta gaji da tsinuwa da zagin mutanen da hankalinta ba'a kansu yake ba. Koda ta gangara sai ta nemi wuri ta tsayar da motar. Hankalinta ya gushe na

ɗ

an lokaci. Tunaninta abinda ta yiwa Hussein, shi dai ta gani kamar yanda ya g

an ta amma ya kauda kai. Wannan abu ne da bai ta

ɓ

a afkuwa ba tsakaninsu. Ta

ɗ

auki wayarta da karar shigowar saƙo ya katsemata tunani, ku

ɗ

i ne har dubu

ɗ

ari aka aikomata. Ta kai duba ga lambar mai account din. Aliyu Dikkl. Hakan ta gani a rubuce. Ranta ya ƙ

ara

ɓ

aci, ga babu lambar acc balle ta mayarmasa. Ta ja tsaki. Kai tsaye ta ƙara kiran wayar Hussein, wannan karon ringing ta ke yi sai dai har ta katse bai

ɗ

aga ba. Ta kuma kira nan ma shiru, a karo na uku ma babu alamar za'a

ɗ

aga. A na hu

ɗ

u sai ji ta yi a

n kashe wayar gaba

ɗ

aya.

"Meke faruwa?" Ta ambata a fili. Kawai sai ta ji zuwa wurin aikin ma ya fita a ranta, don haka ta ba kanta mintuna kusan biyar a tsaye tana jin karatun Alkur'ani tana hawaye kafin daga bisani ta samu ƙwarin gwuiwar da za ta ta

shi motar. Gidan Amrah ta nufa, a hanya ta kira

ɗ

aya cikin abokan aikinta, Hindu. Uzurin rashin lafiya ta bayar domin dagasken ba ta jin dadin zuciya da gangar jikin.

***

Amrah ta yi mata duban tsanaki bayan gama sauraron dukkan bayanin Ramlat. Ita

kanta kwallar ce ta cicciko mata.

"Yanzu AlHassan

ɗ

in bai shigo ba?"

Ramlat da kanta ke jikin kujera sakamakon zazza

ɓ

i-zazza

ɓ

in da ta ke ji. Ta girgiza kai murya a dusashe.

"Mun yi waya da shi yanzu da zan fito, abin hawa ne ba'a kammala

gyara mishi ba, yana tunanin ma bar musu zai yi ya biyo motar kasuwa."



"Kai! Wannan lamari akwai wata sarƙaƙiya a cikinsa Ramlat. Sai dai kuma ki zauna don Allah ki yi tunani ko dai akwai abinda ki ka aikata ga Hussein har ya

ɗ

auke maki wuta haka? Ni

fa gani nake da walakin goro a miya."

Cike da damuwa ta

ɗ

ago ta zauna sosai tana duban Amrah da ciki ke ƙara girma.

"Da ace akwai abinda nake jin zan ba dukkam girma da kulawa bayan iyaye, ƴaƴa da ƴan uwa, wallahi ya biyo bayan Hussein. Kin s

an ni, kin kuma san halina Amrah. Ina son Hussein, son shi nake yi da ban san iyakarsa ba. Akan me zan ƙuntata masa? Ni duka-duka ma yaushe rabon da ko chatting nayi da shi balle ha

ɗ

uwa face to face? Ban sani ba, ban san me na yi ba. Ni dai babban burina k

oda zai zama abu na ƙarshe da zan mishi, shi ne na sada shi da ƴan uwansa da taimakon Allah."

Amrah ta jinjina kai, shakka babu Ramlatu na son Hussein, so mai yawa. Tana tsoron tarihi ya maimaita kansa idan har dangin uwa da uba suka dage mata akan a

uren Chairman. Sauƙinta ma wannan karon su Hajiya na goyon bayanta.

"Ko Hisham zan tambaya?"

Maganar Ramlat din ta maido ta hayyacinta. Gyada kai ta yi.

"Ki tambayeshi tunda amininsa ne. Ba zai rasa abinda ya sani ba."

Da haka ta da

nna wa Hisham kira. Yana

ɗ

agawa suka gaisa.

"AlHassan din ya iso kenan?"

Ya nemi sani.

"Aa, wannan tsakanina da Hussein ne."

"Ina jinki Ramlat."

Ta ba shi labarin irin sauyin da ya ke mata.

"Ko akwai wani abu da ya ce maka n

a yi mishi don Allah?"

Shiru ya biyo baya kafin Hisham ya ce.

"Ya Salam!"

Jin haka ta gyara zama tana kallon Amrah don dama a speaker ta sanya. Suka nutsu.

"Meyafaru?" Ta tambaya kirjinta na dukan uku-uku.

"Ki yi hakuri, ina g

a wannan laifina ne, yanda na

ɓ

ata kuma ni zan gyara. Kar ki damu don Allah. Zan kira ki anjima ko kuma ince zai yi kiranki da kansa. In sha Allahu."

Daga haka ya katse kiran. Suka dinga mamaki. Tunanin Ramlat me Hisham ya fa

ɗ

awa Hussein?

"Hisha

m ya san batun aurenki da Chairman?"

Amrah ta nemi sani. Maganar Ramlat ji ta yi kamar an sokamata mashi a ƙahon zuci don haka maimakon amsa sai ta harareta ta ja guntun tsakin da ya ba Amrah dariya.

"Allah Ya ba ki hakuri. Mancewa nayi fa."

Ta cije leb

ɓ

a gami da girgiza kai ba ta ce komai ba.

***

MISALIN ƘARFE SHA ƊAYA..

Rubutu yake kamar wani Mango Park ba ya ko kallonsa, Hisham ya ƙuramasa idanu da mamaki. Ya sauya kamar ba Hussein din da ya sani ba.

"Malam ya i

na magana ka kyale ni? Ba ka ji me nace ba?"

Ya

ɗ

ago ya dubeshi, ya ji, dukkan wani labari da ya ba shi, ya ji ba wai bai ji ba. Sai dai duk da hakan shi bai ga ta inda zai fara rage KISHIN Ramlat da ya ke ji ba. Ya soma yarda da abinda ya ƙaryata da

gangan, ba kuma ya son sanya ta a matsala. Wannan ne dalili sauyawar sai dai ya ji wani sanyi ka

ɗ

an a maimakon tsananin zafin da ya

ɗ

auka a farko duk akan lamarin aurenta da Chairman.

"Kunne ke ji, kuma na saurareka. Ka yi kokari."

Harara His

ham ya watsamasa yana danne tausayinsa.



"Shi ne za ka share ni? Nima fa takanas na taso don wanke laifin Ramlat amma ina da abin yi ai. Aikina na baro na zo."

Wannan ne karon farko da ya yi murmushi daga jiya zuwa yanzun, Hisham yana da raha. Ko

ya ya ka zauna da shi sai ya sanyaya ranka.

"I'm travelling to London."

"For what?!"

Yanda Hisham ya nemi sani a hargitse, hakan ya ba Hussein mamaki har ya kalleshi, ganin ya zaro ido sai ya bu

ɗ

e tafukan hannu gami da

ɗ

aga gira cikin daki

ya.

"Me akai na razanar? Tafiya ce kawai ta 3months."

"Gwara da Allah Yasa na zo." Hisham ya fa

ɗ

i a fili kuma a hankali. Da ace ba su ha

ɗ

u ba ba zai sani ba kenan. Lallai dole su yi komai cikin gaggawa.

"Me ka ce?"

Hussein ya tambaya.

Girgiza kai ya yi.

"Ba komai. Yaushe za ku wuce?"

Damuwa ƙarara a fuskar Hussein sai dai ba ƙaramin ƙoƙorin dannewa ya ke ba.

"Ba na jin za mu wuce satinnan. Ya dai danganta da samun Visa."

Ya fa

ɗ

i a sanyaye.

'Innalillahi w

a inna ilaihir raajiu'un!'

Hisham ya ambata a zuciya gami da mikewa.

"Ok ok, Allah Ya nunamana. Bari na wuce sai mun ha

ɗ

u anjima."

Hussein ya bishi da kallo har ya fita. Abinda ya kawo a rai shi ne damuwa ce tsantsa na ganin za su yi nes

a da juna. Ya dafe kai da hannu. Shi kansa damuwar ce ke cinsa, tunanin tafiya ya bar Ramlat da Chairman kan ci masa tuwo a kwarya. Sai dai ya tabbatar furta wata kalma a kanta zai zama kamar barazana ga rayuwarta. Hajiya Zeenat ta sha fa

ɗ

amasa gami da cin

alwashin kashe duk wata mace da za ta shiga rayuwarsa. Ba a bayan idanunsa ba, a gabansa ta ke fa

ɗ

i ya na kuma ji a jikinsa fiye da hakan ma za ta aikata. A hankali ya

ɗ

auki waya ya kunna Data wacce rabonsa da whatsapp tun ranar da Hajiya ta kwace wayar.

Saƙonni suka shigo har da nata. Ya shiga ya karanta. Gaisuwar safe ce ta mishi gami da tambayar ko lafiya. Ya dinga binyana karanta hirarsu da bai fi a ƙirga ba. Murmushi sosai ya ke yi san nan ya bude hotonta yana kallo. Ya kai kusan minti biyar ba'a hayy

aci ba, tashin hankalinsa ya ƙaru. A hankali ya rufe hoton ya aikamata saƙo.

-*"Ki sa ranki Hussein

ɗ

an uwanki ne. Ya na buƙatar addu'arki a duk inda zai je. Akwai wani duhu da na kasa fita, ke na gani kin fitar da ni kin sadar da ni da haske. Ina fa

tan mafarkina wataran ya tabbata. Ban ce ina sonki ba, ban kuma ce ina tsananin kishinki ba, amma ina roƙonƙi akan kar ki yi garajen aure. Nemi za

ɓ

in Allah. Ke ba yarinya ba ce. Ina miki fatan alheri koyaushe."*_



Ya aikamata ya kashe datar, dakyar ya c

i gaba da abinda ya ke ransa a jagule.

***

Kawu Modibbo tsaye a tsakar falonsa. Safa da marwa ya ke yi yana ƙarawa. Babu wani cikin iyalinsa da ya yi ƙoƙarin dosar inda ya ke, Amarya kanta haƙura ta yi da kwanan ta koma sashinta ta kwana.

*_

"Kamar wuta da ruwa, haka ta ke barazana ga ayyukanka. Na sha fa

ɗ

anaka, ba kai

ɗ

aya ke aikin ba, akwai masu yi. Naka kan rinjayesu ne wani lokacin, kamar yanda nasu kan rinjayi naka aikin. Ina tsoron shaida maka muddin ba'a kawar da yarinyarnnan ba, aikin

shekara da shekaru zai lalace. Za'a rasa dukkan wata nasara a kansa. Abubuwan da ka ke gudun afkuwarsu a rayuwarka, za su afku!"_*

Wa

ɗ

annan jawabi na Tsoho, shi ke yawo a kwanyar Kawu Modibbo suka kuma hanashi sukuni daidai da sakan. Daren jiya kasa

runtsawa ya yi balle har ya samu damar baccin. Idan komai ya lalace, hakan na nufin bayyanuwar komai.

"Lokaci ya yi da za mu ha

ɗ

a ƙarfi da ƙarfe da ke ZEENATU."

Ya furta a fili kafin ya samu wuri ya zauna kamar kayan wanki.

***

ƘARF

E BIYU...

Ta karanta saƙon Hussein sau ba adadi, sai dai ba ta fahimci komai ba. Cewar ba ya sonta ba kuma ya kishinta wannan ya haifar mata da matsananciyar damuwa. Kukan da ta yi ya jazamata tsananin ciwon kai. Hajiya na ganin haka ta tsorata, abinda y

a fa

ɗ

o a ranta kada ace wani mummunan abin ya sami Ramlatu sanadin wannan yaro, bayan ta taimaka mata ta sha magani ta shiga tofe ta da addu'a. Ummi kam su na Islamiyya ba su da labarin wainar da ake toyawa.

Wuraren ƙarfe hu

ɗ

u da mintuna ne. Wayarta

ta yi ƙara, dakyar ta iya

ɗ

agawa. AlHassan ne.

"Na shigo Kano, ina hanyar gidanku."

Ta amsa da toh, a daddafe ta miƙe, babu laifi kan ya daina sarawa. Ta shiga ta yi brush ta kama ruwa ta yi alwalar jiran la'asar. Fitowa falon ta yi bakinta du

k jikinta ya yi mata nauyi. Hajiya na zaune tana amsa waya.

"Ita Ramlatun?!"

Hakan da Hajiyar ta fa

ɗ

i ya

ɗ

au hankalinta, ba ta katse ta ba har ta kammala wayar.

"Ke da kanki ki ka ba shi Dikko damar turo ku

ɗ

i? Yaya Bello ya shaidamin ai

sun ma gama magana ya turomaki kudin aurenki ta akawun dinki da ki ka aikamasa."

Dafe kanta ta yi tana salati, kirjinta na bugu da sauri-sauri.

"Ni kuma Hajiya? Wallahi ban.."

Ɗif ta yi, sai lokacin ta tuno da ku

ɗ

in da ya turomata account

. Ranta idan ya yi dubi ya

ɓ

aci. Ta fa

ɗ

awa Hajiya gami da nunamata sannan ta ƙara da fa

ɗ

in.

"Amma wallahi ban san inda ya samu lambar account

ɗ

ina ba. Ban sani ba. Me ake nufi da ni wai?"

Ta karashe hawaye na son zubomata. A fusace Hajiya ta mi

ke tana fa

ɗ

a.

"Bari na je gidan! Ba su suka haifarmin ke ba don haka ba zan zauna rayuwarki ta ƙare haka ba Ramlatu! Idan shi Munirun ya kasa ni zan je na same su."

Daga haka Hajiya ta fa

ɗ

a

ɗ

aki ta bar Ramlatu da ru

ɗ

ewa da kuma hawaye. Waya ta

ɗ

auka ta kura Zulaihat ta sanarmata komai, itama hankali a tashe ta ce za ta je can gidan su Dada kar abin ya

ɓ

aci. Hajiya ta fito ta kama hanya ta fita.

Mintuna talatin bayan fitar ta sai ga kiran AlHassan yana shaidamata zuwansa ƙofar gidan. Ta mik

e ta shiga ciki ta gyara fuskarta da ta kumbura. Dole haka ta haƙuranta fita hakan. Tuni an gyaramasa

ɗ

akin Muniru na baya, ta yi mishi iso ya shiga yana bin ta da kallo.

"Lafiya dai ko?"

Ta yi murmushin yaƙe.

"Lafiya kalau. Sannu da zuwa.

"

Ya amsa karo na biyu, shi ba wannan ya ke da muradi ba. Labarin Hajiya Zeenatu da adireshinta ya ke da buƙata.

Abinci ta kawomishi ta kuma ce ya yi hakuri har su yi sallah tukunna. Daurewa ya yi ya amsa da toh sannan ta fice.

***

"R

ai kan ga rai?" Hajiya Zeenatu ta fa

ɗ

i tana murmushi da wani irin mamaki shimfi

ɗ

e a fuskarta tana duban Kawu Modibbo da ke zaune a ofishinta na A&Z. Ya share goshi.

I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad ht

tps://my.w.tt/rSOQW4y2Gcb

🕯



*ƘARFEN ƘAFA*

🕯



_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

46)

"Kin san dai ruwa ba ya tsami banza. Kamar yanda kin sani, na sani, komai nisan jifa ƙasa zai fa

ɗ

o. Toh idan

ba mu yi dagaske ba, asirinmu na dab da tonuwa."

Nan da nan ta ha

ɗ

e rai.

"Me kake nufi?"

Kawu Modibbo ya gyara zama yana mata kallon ƙyar.

"Wata yarinya ta zo min da zancen da ya rushe dukkan walwalata. Tana ƙoƙarin shaidamin cewar ta

san inda Husseini yake, duk da ba ta fito fili ta yi bayanin komai ba, amma daga yanda ta ambaci shi Hassan ta alaƙantashi da Husseini shakka babu akwai babban al'amarin da ta sani."

"Ya sunanta?" Hajiya Zeenatu ta nemi sani a hanzarce yayinda kirjint

a ke bugu, tana tsoron kar hasashenta ya zama gaskiya. Sai dai abinda ta guda shi ya faru, sunan da ta ke fatan kar ta ji, shi dai ta ƙara tsinkaya daga bakin Kawu Modibbo.

"Ramlatu ta ce sunanta."

Wani miƙewa da Hajiya Zeenatu ta yi sai da shi k

ansa Kawu ya ƙara tsorata. Jikinta ya shiga rawa nan da nan idanunta suka ka

ɗ

a.

"Baƙa ce, ba ta da jiki sosai kuma.."

"Abinda ya tunkaro mu, ya fi ƙarfin mu tsaya

ɓ

ata lokaci a kan suffantawa ba. Ki fa

ɗ

i kai tsaye idan kin santa."

Ya fa

ɗ

i c

ike da ƙagara. Ta ha

ɗ

iyi miyau tana goge gumin goshi.

"Tsinanniyar yarinyar da aka sha yimin garga

ɗ

i a kanta kenan! An tabbatarmin muddin ban nisanta Hussein daga duniyarta ba, to shakka babu komai zai lalace. Kenan yanzu ta gano dangin Hussein? Wanna

n mayyar ina ce?!"

"Mafita za mu nema. Kin sani, baragurbin kwai idan ya fashe, yakan shafi kowa ba mutum

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login