Showing 213001 words to 216000 words out of 255051 words

Chapter 72 - KARFEN KAFA complete

so naga yanda waccan bakar munafukar za ta yi idan ta ji labarin aurennan."

"Ni kuma kinga tsoron ranar da za ta sani

nake yi. Sai kuma mamakin dalilin Hussein na ƙin

ɗ

aukar mataki a kanta. Idan na yi tunanin ko yana sonta dagaske, ba ki san ya nake ji ba."

"Gaskiya da mamaki ace yana sonta, nidai jikina sai ya bani kamar so yake sai ya nunamata ita din ba komai ba c

e kafin ya dauki mataki. Ai ko don yanda ta dinga kai maki hari, ya cancanta dama Hussein ya aureki mu ga ta tsiya."

Ramlat dai dariya kawai ta yi.

"Kin sanar da Muhibbat?"

"Eh na fadamata, ta ce za ta shigo ranar daurin auren tunda dai wun

in ma duk rana daya ce."

"Allah Ya nunamana."

Ramlat ta amsa da amin gami da lumshe ido.

A daren bayan ta yo wa Amrah rakiya kofar gida don Dahiru ya zo daukarta, sai ganin Hussein ta yi. Suka dubi juna da Amrah da mamaki. Amrah ta murmusa

.

"Kinga

ɗ

an halak, ashe dai yana tafe."

Ita dai Ramlat mamaki ma ya hanata cewa uffan. Suka karasa daidai sadda ya fito daga mota suna gaisawa da Dahiru, daga nan ya amsa gaisuwar Amrah har da kar

ɓ

ar Baby ya yi mata wasa sannan ya yi musu sallam

a ya shige ciki ko inda Mutuniyartasa ta ke bai kalla ba. Ita ma ta dauke kai ba ta damu ta gaidashi ba.

"Wai ke ba Angonnamu kenan ba? Shi ne ko gaisuwa."

Dahiru ya fadi cike da zolaya. Ta harareshi don dama sun saba.

"Ban ga damar gaidash

i din ba."

Ya daga kafada.

"Ai shikenan. Mu dai maza ba'a ja mana aji."

"Ko?" Cewar Amrah cikin son a tuna baya. Ya yi dariya kawai ya bude motarsa ya shiga.

"Allah Ya bamu alheri Amarsu. Sai da safe kafin wannan Madam din ta

ɓ

allomin r

uwa."

Dariyar suka yi kawai, ta bude gidan baya ta ajiyewa Amrah ledarta. Ba ta juya ba har sai da ta ga sun ja mota, ta koma ciki tana son ganin yanda za su kwashe da Gogannata.

A hankali ta ke takawa tamkar mai tafiya akan ƙaya, murmushi kawai

ta ke zabgawa tana duban sararin samaniya wanda taurari da kuma watan na Rajab da bai fi kwanaki shida da bayyana ba. Hakan na nunk da kusantowar da wata azumin Ramadan ke ƙara yi. A hankali kuma ta maida kanta ƙasa ta ci gaba da tafiya har ta kusa barand

ar da za ta sada ta da falonnasu. Yanda ta ganshi a tsaye hakan ya dauremata kai, ta yi zaton yana ciki su na gaisawa da Hajiya, ko kuwa dai ya shiga ne ya fito? Oho. Ba ta da tabbaci, ganin kallonta kawai ya ke yi sai ta sunkui wa kai, koda ta karasa har

za ta gifta sai kuma ta ga rashin kyautuwar hakan, don haka sai ta tsaya ta gaishe shi.

Maimakon ya amsa kawai sai ya kuramata idanu, idan ya ce ba ta sauyamasa ba, to ya yi karya. Ta wani cicciko ta yi haske, kamshi ke tashi kawai a jikinta. Ramlat

ta ji shirun ya yi yawa don haka ta

ɗ

an

ɗ

ago kai. Nan da nan ya daure fuska ya hadiye murmushin da ya yi niyyar su

ɓ

ucemasa. Ya wayance da

ɗ

an jan karan hancinsa da jan hancin kamar mai mura.

"Am...Meyasa ki ke giftawa cikin maza da uban ƙamshinnan? Ko

da ace babu maganar auren wani a kanki, kina sane da cewa haramun ne ko?"

Kanta a kasa ta yi murmushi a kasan ranta ta ce.

'Ka ji da masifaffen kishinka.'

"Ni ko fita ba na yi yanzu."

"Ko? Meyasa na ganki a waje? Idan mijin Amrah ne, mi

jinki ne?"

Ta

ɗ

ago ta dubeshi sai ma ya ba ta ƴar dariya. Maimakon ta ba shi haushi sai ta burgeshi, kawai sai ya jingina kai jikin gini yana kallonta. Ganin haka ta hadiye dariyar.

"Allah Ya huci zuciyarka."

Lumshe ido kawai ya yi ya bude.

"Matso, magana za mu yi."

Ba musu ta dawo ta tsaya daga gefensa. Kamar ta ce masa su nemi wurin zama amma kawai sai ta share.

"Kamar yanda na san cewa kin sani, yana da kyau na kara fa

ɗ

amaki da bakina. Bayan aurenmu Adamawa zan kaiki. Kano

sai dai mu zo ziyara. Abu na biyu babu batun aiki, ko a Kanon ko a Adamawa. Ba zan jure ganin ina fita nema, matata na fita ba. Kar ki ce za ki ha

ɗ

a kanki da Zeenatu, wannan daban take hakanan tsarin rayuwarta daban da taki. Ina fatan kin fahimta?"

Ramlat da ta kasa ha

ɗ

iye kishin Hajiya Zeenatu, ta gyada kai, ciki-ciki ta amsa.

"Na ji."

Jin yanayin sauyawar muryarta ya sanya shi

ɗ

an matso da kai ka

ɗ

an yana murmushi, cikin rada-rada ya ce.

"Mece ce damuwarki? Hajiya Zeenatu ko kuma maga

nar aiki?"

Ta juyo da zummar harararsa, sai dai ganin irin kusancin ya kai har fuskarsu na dab da ha

ɗ

ewa yasa ta saurin ja baya tana maida numfashi. Shi kansa sai da ya ji wani yarr tun daga yatsar ƙafafunsa zuwa kwakwalwa. Ya sauke ajiyar zuciya.

"Ina iya tafiya?" Ta nemi sani a gaggauce.

"Kin gaji da ganina? Sati nawa ba ki ganni ba?"

Baki sake ta dubeshi. To ma duka-duka yaushe suka hadu a titi ya cashe mata? Sai kuma ta juya kanta kawai tana duban yatsun kafafunta.

"Shikenan,

zan kiraki a waya. Kina iya tafiya."

Ta amsa da toh sannan ta nufi ciki.

"Ba ki ji ba."

Ya katse ta, ta ciji lebban bakinta don ita kam ba ta son kallonnasa, ta daure ta juya. Murmushi kawai ya yi mata. Sai aikin kallo, ta gaji da rashin mag

anar ta juya abinta zuwa ciki.

Yau kam duk juyinta tunanin Mijinnata ne, ta yi mamakin sauyinsa amma ta fi kyautata zaton kawai kewarta da ya yi ne ya chanja shi. Koda ta kammala shirin kwanciya, ta ji bai kira ba sai ta yi zaton ya yi bacci. Da A

suba bayan ta idar da sallah, ta zare wayar a chaji. Ga mamakinta missedcalls har biyar duk na Hussein sai saƙon da ya turo. Ta bude.

_*Kin kyauta kenan?*_

Ta yi murmushi, Hussein rigima kenan. Ita shaf ba ta tsammaci zai kira ba tunda har goma

ta wuce ga kuma bacci na cin idanunta don kwanakinnan ba ta fiye samun yi sakamakon sammakon zuwa wurin gyaran jiki da ta ke yi. Madadin ta ba shi amsa sai kawai ta share ta jefa wayar gefen gado sannan ta fita gaida Hajiya. Koda ta dawo, biyawa ta yi ta t

ashi Ummi da Ansar su yi sallah. Ba ta ci wuya ba suka tashi domin sun riga sun saba. Kamar yanda ta yiwa Hajiyar, hakanan su ma suka shiga suka gaisheta.

Ƙ

arfe takwas a gidan Hajiya Bingel Sudan ta yi mata, ta yarda sosai da gyaran matar don ta san

ta kan gyara. Duka-duka ba a sani jima da farawa ba amma gaba daya ta sauya, sai dai ba laifi Yayyunnata mata sun kashe kudi.

Koda ta koma gida ta iske kaya jibgi a falo, ashe kasuwa su Maman twins suka je. Tarkacen kayan kicin ne kala-kala da Munir

ya bada a siya. Babu laifi kullum kudinsa da

ɗ

a albarka ya ke yi. A bakin Rafee'ah ta ke jin zancen furnitures, wai Baba Dakta ya ce komai da ya danganci wannan a barshi a hannunsa. Ta kara jinjina riƙon zumunci da kuma abota na Baba Dakta wanda bai ta

ɓ

a ba

ri sun koka da rashin Abba ba.

"Kai wannan Jug din ya yi kyau. Ga azumi ya taho, har na hango bakin Hussein yana kwankwa

ɗ

ar lemu."

Rafee'ah ke maganar tana dariya, gaba daya suka sa dariyar har Ramlatu.

"Ke dai Rafee'ah ban san sadda za ki

girma ba. Yara uku amma har yanzu da sauranki."

Rafee'ah na dariyar furucin Hajiya, Maman Twins ta ce.

"Ai da alama sai Baban Abba ya ranga

ɗ

omata kishiya."

"Shi ya isa? Ta

ɓ

di! Ai shiyasa ko magana ya dauko nake katseshi da cewa ko gidanmu da

ya tal na tashi na gani. Soyayya tun na yarinta har girma don haka kada ma ya fara."

Daƙuwa Hajiya ta mata.

"Ungo nan! Kin isa ki ja da ikon Allah? Yau Isma'il ya so aure ai kuwa baki isa ki hana ba. Ba gwara kishiyar ciki ba da a yi maki ta waje

ba?"

Nan fa aka shiga hirar kishiya, Maman Twins na fadin ita kam tana ma ji a jikinta Baban Twins aure yake son yi tunda ginin da ya fara na bangare biyu ne. Ita dai Ramlatu ta yi shiru kawai tana duba kaya, idan abin ya ba ta dariya ta dara. Can ku

ma maganar ta dawo kanta.

"Kedai me kishiya irin Zeenaru take ko wa? Wallahi sai kin tashi tsaye da addu'a. Azkar safe da yamma kar ki bari ya wuceki. Ni na ji dadi ma tunda ba wuri daya zai ha

ɗ

aku ba."

Ta dubi Maman Twins.

"A ina kika ji?"

"Ni ya fadawa. Na fi zaton akwai dai abinda ya ke nufi a kan matar, amma bari mu zubawa sarautar Allah ido. Ke dai kamar yanda Uwanin ta fada, ki zage damtse da addu'a. Ya sanar da ni ma zuwan matar Hassan da wasu cikin yan uwansu, amma ba gidansa za

su sauka, masauki zai kama musu. Ba yanda ban yi ba da shi akan ya bari su zo nan yace babu komai."

Hajiya ke zancen ita dai ba ta da labari ma sai lokacin. Sai kuma suka koma batun rakiyar Adamawa, su na tantance wadanda ya kamata su je.

"Bilki

su fa? Ke an fadamaki Bilkisu za ta shiga sabgar Ramlat?"

Rafee'ah ta tambaya da mamaki jin Maman twins na batun Bilkisu.

"Toh aikuwa za ki sha mamaki tunda Munirun da kansa ya sanarmin cewa za ta je. Kuma ita ta amsa da hakan."

Hajiya ta f

adi. Nan dai Maman twins aka hau rantsuwar gulma ce kawai za ta kai ta. Haka suka yi ta tattaunawarsu abin gwanin sha'awa. Aisha ciki ya soma nauyi ba kasafai ta ke fitowa ba.

***

WASHEGARI...

"Ki soma shirya kayanki. Tafiya

ta zo."

Hajiya Zeenatu ta dubi mijinnata gabanta ya fadi.

"London ko ina?"

Ba tare da ya dubeta ba ya ce.

"Adamawa kafin London. Ai na fa

ɗ

amaki zamu je yan uwana su ganki ko?"

Ta dan yi shiru tana tuna wayar da suka yi jiya da dadd

are da Kawu Modibbo. Gargadi ya yi mata a kan zuwa Adamawa don a cewarsa ya zo garin, bai kuma ga wata alama da ke nuni da cewar ta samu kar

ɓ

uwa ba, asalima labarin da ake shi ne, asiri ta yi ta rabashi da mahaifarsa.

"Kin yi shiru."

Hussein ya

furta gami da

ɗ

an riƙo yatsun hannunta yana murmushin yaudara. Ta bishi da na yaƙe.

"Hum, kana ganin ba ni da matsala da su? Za su kar

ɓ

e ni da hannu bibbiyu?"

Hussein ya ci gaba da bin ta da kallo, abinda ya ke zargi ya kara tabbata. Jiya ya ji t

ana waya kuma tsaf ya ji me tace. Sai dai bai gama fahintar waye ke tare da ita a danginsa ba, ko ma waye dai ya lura sun jima su na tare. Zai bi ta sannu har wayarta ta fado hannunsa ya dauki lamba.

"Kamar kowane dangi, akwai masu murna da ci gaban

mutum da ma wadanda ba su yin farin ciki. Ba zan rantse maki cewa duka dangina su na sonki ba Zeenat, musamman abinda ya faru tsakaninmu wasu su na daukar alhakin ki cewa ke ce silar komai. Amma bangaren yan uwana kuma shaƙiƙaina, ba ki da wata matsala. D

on haka ki kwantar da hankalinki. Ban ta

ɓ

a fadamaki ba saboda bana son sanyaki cikin wani hali. Amma yanzu ya zama dolena na fa

ɗ

a don kar ki ga wani abu a wajen wasu ki ji ba dadi. Ba zaman kowa kike ba face ni."

Wani dadi ya lullu

ɓ

eta, ta ji a du

niyar nan ta kara son Mijinnata. Ba ta sadda ta rungumeshi, ya runtse ido yana ji kamar wuta ta

ɗ

osana a fatar jikinsa.

"I love you."

Ta furta a hankali. Ramlat ce ta fado a ransa kafin ya ce.

"I love you too."

Da wannan ya shawo kanta

ta mike har da batun za ta shiga kasuwa ta soma siyan tsaraba. Ya fiddo kudi zai karamata ta girgiza kai da binsa da hararar wasa.

"Ah haba, yan uwanmu ne fa. Rike abinka, da kudina zan musu tsaraba."

Ya yi murmushi kawai. Yana binta da kallo, y

a lura kwana biyunnan kurajen nata da sauki sun fara mutuwa, ta dai ce na gargajiya ta soma kar

ɓ

a ta gaji da zirga-zirgar asibiti. Shi dai ba abinda ya shafeshi. Kusantarta ne tuni ya bari.

***

*RANA BA TA ƘARYA!*



I just published

"BABI NA HAMSIN DA TAKWAS" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1019046229?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=4ocpUEJVa%2B0bXSp4wxbK3lhNgthMCA7

nB5QC2dclyyGJkYlECeIGKhiQUzgNGFlkVbskOsJU12vwNQbJIqJ2Pbn6%2F7TbXN1B%2BYmSMvxcC1P2DtDikL9OR4lEi83T5hqO

🕯



*ƘARFEN ƘAFA*

🕯



_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

58)

Ana gobe

ɗ

aurin aure

tun da safe, suka bi jirgi zuwa Yola. Awa biyu da mintoci ta kaisu. Kamar yanda Hussein ya shirya, Kausar da AlHassan ne masu zuwa tarba. Kausar tun da ta ga Hajiya Zeenatu ranta ke zafi dakyar ta iya tankwara zuciyarta.

'Allah Ya isa.' Ta fadi a kas

an ranta, Hajiya Zeenatu kuwa wani dadi ta ji ganin irin tarbar da ta samu a wurin Kausar duk da shekarun da ta ba ta. Suka dunguma a motar AlHassan zuwa gida. Bai yi gangancin sauketa a gidan Dada ba don ya tabbata Dada za ta iya kasa hakuri don ba ta iya



ɓ

oye abinda ke ranta ba wasu lokutan sai dai ya san akwai ta da hakuri.

"Anan za ki zauna sai zuwa gobe idan an huta sai a leka dangi. Hakan ma ina ce ya yi miki?"

Hajiya Zeenatu dake karewa dakin da aka ba su kallo ta juyo tana dubansa fuskart

a cike da damuwa.

"Yanzu dagasken a yau za ka juya? Gaskiya idan hakane zan jira a gidannan zuwa sadda za ka shigo garin sai mu leka dangin tare. Wallahi haka kawai na ke jin fargaba."

'Me akai da maza Zeenatu?' Ya furta a ƙasan zuciyarsa a fili

kuwa murmushi ya yi kamar gaske ya shafi gefen fuskarta.

"Shikenan, yanda ki ka ce hakan za'a yi. Nima kin riga da kinsan dalilin komawar, ban larasa handling komai a wurin aikinmu ba ne, gobe juma'a in sha Allah da zarar na kammala, Asabar da safe za

n taho."

Ta gyada kai.

"Babu wata damuwa. Allah Ya kaimu."

"Amin. Amma toh ko bikin ba za ki leƙa ba? Na fadamaki Cousin Sister ce a wurina."

Ta tuno da hakan don Kawu Modibbo ya fadamata zancen bikin don shi ne silar zuwansa garin shim

a. Sai dai ya gargadeta da shiga dangin gudun samun matsala don haka ta girgiza kai. Shima Hussein kawai fada ya yi don ya gwadata, amma tuni ya ji tana batun ba bikin da za ta leka da wanda suka yi waya kwanaki.

"Ka yi hakuri dai, ka ga ba'a san ni

ba. Zan jira har ka dawo ka gabatar da ni a wurinsu."

Ya jinjina kai.

"Ba damuwa."

Daga haka ya rage kayan jikinsa ya shiga bandaki, can ya fito, wanka ya yi. Ya sauya kaya ya feshe jikinsa da turare. Hajiya Zeenatu ta ƙuramasa idanu, kanan

un kaya ya sanya. Rigar da ya sanya milk mai gajeran hannu sai blue jeans. Tsayawa suffanta kyawun da ya yi mata ta sani

ɓ

ata baki ne, mijinta kara kyau ya ke koyaushe da kuma ƙuruciya musamman gashinsa baƙi si

ɗ

ik da ya kwanta a sumar kansa irin na Bafulat

anin Yola wanda ke kara fiddo da zahirin waye Hussein. Ta shagala a kallonsa da jin wani irin tashin hankali da kishin zuwan da za su dinga yi Yolan yanzu, tana da tabbacin idan matan Kano ba su yi nasarar raba ta da shi ba, to wadannan kyawawan matan na f

ulanin Yola za su iya rinjayar zuciyarsa. Hakan tunaninta ke ba ta. Har ya kammala ya

ɗ

aura agogo ta shagala a tunani.

"Muje mu ci abinci, su na jiranmu." Ya fadi ba tare da ya kalleta ba, jin shirun sai ya

ɗ

aga kai yana dubanta. Ta shagala a tunani,

sai da ya

ɗ

an yi tafi kusa da ita sannan ta yi firgigit.

"Um, am..me ka ce?"

"Tunanin me kike? Nace mu je mu ci abinci daga can zan biya wurin Dada sai na wuce Airport."

Ta yamutse fuska.

"Sai zuwa anjima zan ci, yanzu bacci nake ji."

Ya

ɗ

an

ɗ

aga kafa

ɗ

a.

"Ok. Bari naje, idan kin yi nisa a baccin ba sai na tasheki ba. Zan wuce."

"Allah Ya kiyaye hanya."

Ya fice yana mai amsawa da wani irin nishadi a ƙasan ransa.

A falon ya yada zango, yana cin abinci su na hira

da AlHassan da Kausar duk akan tsarin bikin.

"Yanzu kenan ita kadai za ta zauna a gidan? Yaushe Amaryar za ta zo nan? Don naji ana cewa tare duka za su shiga dakunansu."

Kausar ke neman sani.

"Asabar za su zo. Ke dama ai yanzu ba zancen zu

wanki Kano saboda matarnan. Su Hafsat dai da saura sai su je."

AlHassan ke maganar.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login