Showing 96001 words to 99000 words out of 255051 words

Chapter 33 - KARFEN KAFA complete

matattarar yan iska, sai ya sauya da zama a masallaci tsakanin Magriba da Isha'i yana jin tafsirin Malamai. Wasu lokutan Ramlat takan farka ta ganshi durkufe cikin Sujjada y

ana kuka da addu'a. Ita kanta takan ji hawayen ya cika idanunta ta kasa komawa ta mike ta yi alwala ta yi zaman tayashi.

Abu kamar wasa, lamarin ya ci gaba da tafiya a haka. Malam har hawaye ya yi don dadi ganin sauyawar dansa, ya kuma kara yarda ce

wa bawa bai isa ya shirya dan uwansa ba idan Allah bai shirya ba.

Anan ne Aliyu ya gane cewar ashe ba shi ne ba'a so ba, halinsa aka tsana. Abulle ma ta yi kuka don murna. Akwai da yawa da suka kasa gaskata Aliyun, har lokacin basu shiga harkarsa. Dama

haka rayuwa take, ba lallai ne kowa ya so ka ba, hakanan ba ka isa ka ce ba ka da maƙiya ba.



A bangaren Aliyu da yan uwan Ramlat din ma sai godiyar Allah, ya zamana zai je har su

ɗ

an yi hira da Baba Dakta. Hajiya ma sannan ta sakar mishi sai dai a

kwai ƴar kunya tsakaninsu. Tsakaninsa da Munir kuwa ko gaisuwa bai ha

ɗ

asu. Koda ya gaidashi ba amsawa yake ba. Ƙarƙari idan ya yi sallama zai amsa yana cin magani. Wannan tasa shima ya watsar da lamarinsa.

Har Gombe ya kwashesu suka je ya sada zumun

ci da yan uwan Innarsa, sun yi mamaki sosai don ganin abin suka yi kamar mafarki. Kusan Aliyu tun Innarsa na raye rabonsa da su. Wannan ta sa sosai suka tarbesu suna tattalinsa da iyalinsa har suka dawo.

***

Ta shiga binsa daga daki zuwa falo, da y

a gaji sai ya tsaya yana kallonta. Ta turo baki kadan.

"Baby, meye wai?"

Ramlat cike da shagwa

ɓ

a ta amsa.

"Muhibbat ce fa Baban Ummi. Ta tako gidannan ya fi a ƙirga. Har ta haihu a yi suna ban je ba? Gaskiya ban kyauta ba wallahi."



Ya ta

ɓ

e baki, ta kuramishi idanu tana murmushi cike da so da kaunarsa da yanzun ta ke ji ba ka

ɗ

an ba. Ya

ɗ

an murmure hakanan ya yi haske kadan ba kamar a baya ba. Kasuwa ta dan dawomishi daidai don yanzun yana maida hankali sosai.

"Nayi zaton ma asi

biti za ki cemin za ki, ashe ba haka ba ke yawo kike son fita."

Ta daure fuska.

"Ni lafiyata kalau, na fadamaka ba ba ciki bane. Ko ka manta na yi planning?"

"Planning wane iri ne wannan da za ki dinga amai da kwadayi? Yaushe rabonki ma da

al'ada?"

Ta numfasa ba don ta wani dauki abin da muhimmanci ba don dama idan ba ta mance ba Nos ta fadamata cikin side effect din maganin har alamomin masu ciki ko daukewar jini zai iya jazamata.

"Shikenan zan je, amma daga nan zan wuce gidan M

uhibbat. Don Allah!"

Ta fadi da sauri ganin yana kokarin cewa a'a, ya yi dariya.

"Shikenan, a gaishesu. Ki dai tabbatar kin je asibitin."

Ta rungumeshi gami da yin godiya. Ya bata sumba a kunci gami da bata kudin mota da na ganin likita.

Yana fita itama ta shirya tsaf ta goya Ansar ta fice.

***

RUBUTACCEN I just published "BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/pcYjI4bZBab

🕯



*ƘARFEN ƘAFA*

🕯





*_Rufaida Umar_*



Bismil

lahir Rahmaanir Raheem.

27)

"Ke kam sai ayi magana ki yi shiru."

Maganar Muhibbat ya katsemata tunani a karo na barkatai, ta kakalo murmushi ta dubeta.

"Kai ban ji ba."

"Cewa nayi ina Ummina?"

Cike da kaunar yanda Mu

hibbat ke sonta da abinda ta haifa ta amsa.

"Tana can gidan Hajiya."

"Kai jamaa, da alama dai Hajiya ta kwacemana Ummi."

Dariya suka yi lokaci guda. Hira dai ta yi hira har hakan ya mantar da Ramlat damuwarta na cikin da ke jikinta. Duk da a

msar da Likita ya ba ta sadda ta mishi tambaya hakan bai gamsar da ita ba sai da ta ƙara tambayar Muhibbat.

"Wai nikam Sis, dama ana iya samun ciki ko anyi family planning?"

Muhibbat ta dubeta, me za ta yi ba dariya ba. Yi ta ke ba kakkautawa har

sai da Ramlat itama ta dara.

"Mene wai na dariya toh?"

"Ah ba komai fa. Sai dai na harbo jirginnaki. Ai idan Allah Ya so ikonSa, ba planning ba, ko mahaifar aka juya sai ki ga an samu ciki. Meyafaru?"

Jiki a sanyaye ta ce.

"Implant na

saka, abin mamaki wai ana yimin test aka ga ina da ciki. Wai gocewa ya yi."

Jinjina kai Muhibbat ta yi.

"Ana haka, na sha ji ana fadin haka. Wata har allura ta yi amma bai kar

ɓ

eta ba sai ga ciki. To ke me zai dameki? Ai ko ba komai Ansar ya sheka

ra."

Ajiyar zuciya ta saki, kuma fa hakane. Idan a baya munanan

ɗ

abi'un mijinta ne ta ke gudu, yanzun komai ya kau, ya zama labari da yardar Allah.

Muhibbat ta ci gaba da ba ta shawara akan kar ta damu ba komai. A karshe ta ji zuciyarta ta yi sanyi.



Sai wuraren yamma ta yi mata sallama ta bar gidan bayan ta diremata turmin atamfa cikin wadanda ta samu na barkar Ansar. Godiya sosai Muhibbat ta yi kuma ko kadan ba ta raina ba duk kuwa da cewar ta fi karfinsa. Har kofar falon ta yi mata rakiya suk

a yi sallama.

***

Juyi ya shiga yi da ita yana karawa, ita kuwa banda dariya ba abinda ta ke, hakan da ya yi ya zo mata a hagunce don ta yi mamaki. Ba ta zaci ganin irin wannan farin cikin a fuskarsa ba. Farin ciki ne da ya taho tun daga ƙahon zuc

iyarsa. Ya shiga sumbatar duk inda bakinsa ya kai a fuskarsa. Ta kauce gami da fa

ɗ

awa kan kujera tana dariya lokaci guda tana mai watsa mishi harara.

"Kai don Allah Abban Ummi. Duk rawar ƙafar don cikin ne? Ciki na uku?"

Zama ya yi a gefenta gam

i da riko hannunta.

"Bar ni na yi murna kinji ko? Kyaleni Baby. Allah Yasa ki haifarmin mace na sanyamata sunanki. Kin cancanci komai daga gareni."

Ita dai murmushi take tana kara godiya ga Allah da tarin ni'imominSa wanda ba ya yankewa. Yau Aliy

u ke

ɗ

oki da zumu

ɗ

i mai yawa haka saboda ance tana dauke da juna biyu?

Kumatunta ya ja wanda ya maidota hayyacinta. Suka yiwa juna murmushi kafin ya jawota jikinsa ya soma aika-aika

😜

. Kukan Ansar ne da ya fado daga saman kujera cikin bacci ya katsemu

su komai, kusan a tare suka isa wurinsa ya rigata daukarsa. Safa da marwa ya shiga yi yana jijjiga yaron, hakan ya bata damar tsayawa ta kurawa Aliyun idanu cikin duniyar tunani. Kwallar farin ciki suka cikamata idanu ta sharesu. Abbanta ya fa

ɗ

omata a rai,

ta tabbatar da yana raye zai fi kowa farin cikin shiryuwar Aliyunta.

Ta so ace Abba da Aliyunta sun yi rayuwa kamar na

ɗ

a da uba tun a baya, ta so ganinsu tare a zaune suna hira da dariya. Sai dai kuma Allah bai nufi hakan da faruwa ba.

***



Labarin cikinta har gidansu, ta sha dariya wajen su Zulaihat da suka hadu a gida.

"Dama za ki ka da yin Ubangiji ne? Kallonku kawai nake."

Hajiya ke wannan zancen tana gutsirar goronta wanda ya zamemata jiki.

Ramlat ta yi dariya.

"Yanzu

dole ki yaye Ansar fa ko?"

Rafee'ah ke zancen tana dubanta.

"Anya kuwa? Ni gani nake kamar ba matsala tunda ta ce likita bai hana ba."

Fadin Zulaihat.

"A'a ba zai yiwu ba, dole ma a yayeshi. Idan ya rame itama ta rame fa? Ai dukkansu a

bin ba zai zo musu dakyau ba." Hajiya ta furta cike da kulawa. Kulawar da idan Ramlat ta dubi ƴan uwannata ta ga dukkansu a cikin lamuranta suka tsoma baki sai ta ji dadi da farin ciki sun lullu

ɓ

eta.

A ranar dai haka ta koma gida ba Ansar don Hajiya

ta ce ba zai yiwu ya ci gaba da shan mama ba. Har da ƴar kwallarta na tausayin yaron, don ma dai yana da kumarinsa.

Ganinta ita daya Aliyu ya ci dariyar da ta ishe shi.

"Ai koda ba ki yayeshi ba, da hannuna zan daukeshi na miƙa wa Hajiya ko na k

aiwa Amarya shi. Ta ya za ki zauna kina ci gaba da shayarwa ga ciki? Ba zan yarda ba."

Ta turo baki ta shige wanka ta kyaleshi zaune gefen katifa.

Allah Ya taimaketa ba ta yi ciwon yaye ba sai dai sun kara ciccikowa.

Hankalinta ya kwanta t

a koma rainon cikinta da zuwa makaranta abinta.

***

BAYAN WATANNI TAKWAS..

Binsa kawai take da kwando yayinda yake aikin lodar kayan jarirai kala-kala unisex.

"Don Allah ya isa haka Sweet Aliy."

Bai ko kalleta ba balle ya saurareta

.

"A ina ka samu kudi haka?" Ta ƙara jefamasa tambaya don ita kam abin ma tsoro ya shiga bata duk kuwa da ta san yanzun Aliyun na samu fiye da baya. Ganin ta ƙi

ɗ

aga ƙafa ta bi bayansa, ya janye kwandon ya yi gaba ya kyaleta yana duba wasu turaruka n

a jarirai.

"Wannan ba Ramlatu bace?" Jin an ambaci sunanta ne yasa ta juyawa bangaren da ta ji muryar. Kallon kallo suke da juna. Kamannin Hilal sak a fuskokinsu. Tuni ta gane su waye, Anti Fareeda da sai Murja da ƙaton ciki wanda haihuwa yau ko g

obe.

Ta saki murmushi sadda suka ƙaraso gareta, Murja ko gaisuwarta ba ta amsa ba ta jefomata tambaya.

"Kema wani cikin ne da ke? Bilki ta ce haihuwarki biyu yanzu ta uku. Kin ji labarin auren Hilal ko? Kinga Allah ba azzalumin bayinSa ba ne."

"Dadina da ke Murja wataran kamar yarinya kankanuwa, ke har sai an ce miki ciki gareta? Saukinta daya ma na sunnah ne. Uhum, gwara ma da aka yi yunwa halin kowa ya fito. Da yanzun da auren Hilal za ta haifi shegu."

Kallonsu take, kamar wacce aka

ƙullewa baki ta kasa magana, kirjinta wani tafarfasa yake yi. Ta juya kawai ganin idanunta ya ciki da kwalla. Fareeda ta kara magana.

"Kinsan ma naji ance mijin ƙanjamau ne da shi. Ga duka na safe daban na rana daban."

Ta ƙara daga kafarta daida

i sadda Murja ta kara magana.

"Ai dama Allah ba azzalumin bayinSa bane, tun ka aje ko'ina yarinya ta soma ganin sakayya. Ni dama kishiya ya ƙaromata muga ta karshen soyayya."

Tuni ta yi gaba ta bi bayan mijinta kamar ba ta ji ba. Karo suka kusan

yi, da sauri ya riƙe kafarta. Kallon kallo suke da juna, ya sa hannu ya gogemata hawayen.

"Meyafaru? Keda wa? Ina can ina kokarin biyan kudi na waiga ban ganki ba. Lafiya?"

Ya ƙarashe yana daga wuya kamar zai hango abinda ya

ɓ

ata rannata, bai ga

kowa ba sai wasu mata biyu dake kallonsu.

"Ba komai fa, abu ne ya shiga idona."

Ya daure fuska, zai kara magana ta yi saurin giftawa ta gefensa ta soma tafiya gami da fadin.

"Don Allah mu je."

Bai bi ta kanta ba ya wuce zuwa bangaren m

atan yana dan dube-dubensa, so yake ya ga ko zai ga fuskar da ya sani cikin ƴan uwansa ko na Ramlat din amma babu

ɗ

aya. Zai wuce ne ya ji wata a gefensa kamar da rada tana fadin.

"Ko shi ne mijinnata?"

Ya waiga ya kara kallonsu, shi

ɗ

in suke kall

o dai, hakan ya ba shi tabbacin su ne silar hawayen Ramlatu. Ganin dai zargi ne ba shi da tabbas ya sanya shi watsamusu banzan kallo ya wuce, duk suka sha jinin jikinsu suka kauda kai.

"Kinsan fa mashayi ne, kar ya kawomana duka." Fadin Murja a tso

race bayan tafiyarsa.

"Atoh, gwara ni banda komai, ke kam naƙudar dole zai sanyaki ko ya kaiki lahira."

Suka tuntsire da dariya sai dai fa ba haka suka so ganin Ramlat din ba. Alamun jin dadi sun bayyana a fatarta da kuma jikinta, sun so ganinta

a yamushe yanda za su fi jin dadin kai labari, amma hakan ma da suka yi mata sun dandana mata wani bakin ciki. Wannan yasa hankali kwance suka ci gaba da siyayyar abinda ya rage ga Murja.

***

Tun a hanya yake masifarsa jin diramar da ta yi a shago

n da ya uwan Hilal, har suka dawo gida, ita dai ba ta iya tankawa ba banda hakuri da take ba shi. Koda suka shiga ita ya bari da baza kayan tana kallo, kallon take amma zafin kalaman su Murja ya tsayamata a ƙahon zuci.

"Mtsw. Sai ki zauna ki yi ta

kuka akan abinda ba wanda ya isa ya sauyamaki. Ko mene ya riga da ya faru, akwai dan iskan da zai hana. Don ubansu me suka ce? Da shege za ki haifa a gidan Hilal din ko? Dama hakan ce ta faru naga uban da zai hanani dauko ƴaƴana!"

Ta dubeshi a razane,

sai kuma ya shiga istigfari. Ransa sosai ya

ɓ

aci don shi a duniya ya tsani a yi mishi abu bai rama ba. Ya so ace a gabansa suka yi yanda zai zazzagamusu bala'i ya nunamusu haukartasa.

A karshe kuma ya koma lalla

ɓ

ata, ya shiga jan ta da hirar Baby ga

mi da nunamata kayayyakin su ka shiga dariya zuciyarsu ta yi sak.

***

Rayuwarsu abin sha'awa, zama na so da kauna da aminci irin wanda Ramlat ta jima tana mafarki, Allah Ya tabbatarmata da shi. Tana zuwa makaranta abinta, Amrah na nan ta ƙi kula kow

ane saurayi don ta rantse sai ta kammala karatunta.

Babu laifi suna zumunci da yan uwan Aliyu yanzun musamman wadanda suka hada uwa. Sukan zo itama ta jajjemusu tare da Aliyun.

A yanzun ba abinda ya fi burgeta sai zaman karatun da Aliyu ke da

uka duk karshen sati wurin wani Limamin unguwarsu.

Haihuwar Ramlat ya kama a watan azumin Ramadana, alokacin bai fi sati uku ya yi saura a kama azumin ba.

A sannan karatu ya dau zafi don su na aji na biyu zango na farko sakamakon yajin aikin da

aka dinga tafiya wanda hakan ya

ɗ

an kawomusu cikas a karatun.

Wataranar Asabar tana zaune a tsakar gida ta dage tana research a Google na wani project da aka bata. Aliyu na daga gefenta ya kwanta saman filo ya zubawa sararin samaniya ido yana kallo.

Shirunsa da ta ji ya yi yawa ne yasa ta dubansa. Ganin hankalinsa ma ba ya kanta ne ya sa ta mika hannu ta

ɗ

an matsa yatsun ƙafarsa suka yi ƙara. Ya juyo ya dubeta gami da

ɗ

an lumshe idanunsa ya bude.

"Lafiya? Me kake tunani?"

Murmushi ya

ɗ

an yi.

"Rayuwa nake tunani Baby. Duniyar tsoronta nake kara ji, tuna watarana zan mutu fargaba hakan ke sanyani. Idan na zauna ina lissafi sai na ga kamar ban ta

ɓ

a aikata abin kirki ba. Tun ina saurayi iyayena ke shaƙar bakin cikina, na tsoma kaina a harkar

shaye-shaye. Na dauki rayuwar da ba tawa ba, yawo da ƴaƴan masu hannu da shuni, na

ɗ

orawa kaina. Na baƙanta ran jama'a da dama, a karshe ko ban aikata zina ba, na shafa jikin matan da ba nawa ba. Idan na tuna akwai ranar da zan koma ga Allah, a binne ni c

ikin raminnan, a doramin itace a kara bina da kwali sannan a rufamin ƙasa a fuska, ina shiga matsanancin tashin hankali Baby. Daidai da

ɓ

angarenki na cutar da ke, na kasa daukar nauyinki, na kasa kula da lafiyarki, na kasa ciyar da ke a lokuta da dama kam

ar yanda sutura da shanki bai cikin damuwata a wasu lokutan. Ban tsaya anan ba na jawomaki abin gori, na kashe aurenki don na rayu da ke. A sanadina iyayenki sun zubar da hawaye a kanki, nayi amfani da karfin son da kike yimin na yaudareki. Anya duk wannan

tarin sa

ɓ

on da nayi, Allah zai dubeni Ya sanyani sahun muminan bayinSa?"

Kallonsa take tun soma maganarsa, kamar yanda take fitar da hawaye, haka shima yake fitarwa. Girgiza mishi kai ta shiga yi. Ta ture litattafan ta karasa gareshi gami da damƙe ta

fin hannunsa cikin nata.

"Kar ka kara irin wannan kalaman, Ubangiji Mai Rahma ne. Wanda ma bai tuba ba, kira Ya ke yi akan ya zo ya nemi gafararSa zai yafemishi, ballantana wanda Ya kusantoShi da neman gafara ba? Ai shi At-Tawwabu ne Mai yawan kar

ɓ

ar tuban bayinSa. Koda wasa kar ka sake zuciyarka ta jefaka cikin kokwanto Allah Ba zai gafartamaka ba. Ka yi irin tuban da Ya ke so, ka kuma nemi gafarar wadanda ka aikatawa ba daidai ba. Me ya fi wannan dadi? Abinda ya riga ya faru ba mu isa mu sauyash

i ba."

Gyada kai Aliyu ya shiga yi sai kuma ya yi shiru, Hilal, shi ya fa

ɗ

omasa a rai.

"Na nemi wata alfarma?" Ta tsinci muryarsa karo na biyu. Ta kara dubansa ta gyada kai.

"Hilal, ki nemar mini gafararsa, ki ce ya yafemin koda ace Allah b

ai ban ikon saduwa da shi ba a rayuwa."

Ji ta yi gabanta ya fadi, ta daure fuska gami da harararsa.

"Bana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login