Showing 87001 words to 90000 words out of 255051 words

Chapter 30 - KARFEN KAFA complete

tuni dama Ramlat ta rigashi dawowa. Sosai kuma likita ya gargadeshi akan shaye-shaye da illolinta.

Kwanakin da suka biyo baya suna faruwa ne sama-sama ga muta

nen gidan. Duk kokarinsa na shawo ka Ramlat abin ya ci tura, ya kasance ba ya fita yawon dare, idan ya shigo gida da yamma shikenan sai dai ko masallaci da yanzun ya soma zuwa sallah. A baya zuwan bai dameshi ba, ya gwammace ya yi sallarsa a daki. Ta yi f

a

ɗ

an har ta gaji ta bari.

Wataranar Asabar ta tashi tana son ziyartar yayyunta, gidan Munir ne ba ta jin za ta iya takawa tunda ya nuna ba zai iya yafemata ba. Ta tabbatar idan ta je duk abinda ya yi mata ita ta kai kanta.

Tun safe ta lura ba

shi da niyyar fita, wuraren karfe goma ta cimmasa a daki. Kwance yake yana juyi, kwanakinnan tana lura da shi a fisge. Yana cikin damuwa, girki ma idan ta yi bai fiye ci ba. Ga yawan shan Panadol da ya shiga yi kusan kullum ciwon kai.

Kallonta yake t

un shigowarta dakin sai kuma ya ja guntun tsaki ya kauda kai.

"Ina kwana." Bai amsa ba, bai kuma kalleta ba. Ta ha

ɗ

iye ta kara gaidashi.

"Ba zan amsa ba! Ki rabu da ni idan ma mutuwar ce na mutu Baby! Ya ku ke so mutum ya yi? Me kuke so ya zama

?! Ance Aliyu dan iska ne kuma mashayi! Yanzun kuma da Allah Ya taimaka ya soma kokarin gyara rayuwarsa, nan ma bai burge ba! Kin juyamin baya ba kya shigowa inda nake sai dai ki yi girki ki dankwafarmin ki shige daki saboda mayunwaci ne ni! Ke haka Allah

Ya ce ki yimin? Haka Ya ce ki yiwa Mijinki?!"

Ya na kaiwa nan ya mike zaune gami da jan tsaki kafin ya riƙe kansa da bai bar sarawa ba.

Ta yi mishi ƙurr da idanu tana kallonsa kafin ta nisa.

"Ka saka a ranka ba don mu kawai za ka gyara ba

, saboda karan kanka da kuma Ubangijinka. Ba mu da wuta ba mu da aljanna. Nayi kuskure, ka yi hakuri."

Ganin ta sauko yasa shima ya sauko ya lalla

ɓ

a don dama neman shirin yake, ya gaji da zaman gabar. Sai da ya biya bukatarsa kafin ya bata umarnin t

a shirya da kansa ma zai sauketa gidan Zulaihat din. Wannan ya kara tabbatarmata dagaske Aliyun ya soma kimtsuwa.

Ta shirya cikin wata atamfarta da ta ware cikin sabbin da za ta dinga fita unguwa, ta shirya Ummi cikin riga da wando ƴan kanti

ɗ

aya d

aga cikin kayan da Abba ya siyamata. Ta yiwa gashinta ado da ribbons kala-kala ya yi mata kyau.

Duk wanda ya gansu yasan suna cikin farin ciki. Har kofar gidan Zulaihat ya kai ta, suka yi da shi za ta je gidan Rafee'ah a can zai isketa ya

ɗ

auketa. H

akan ya sa ya bata

ɗ

ari uku ya riƙe dari biyunsa, a cewarsa ita kenan a aljihun, dari biyar.

***

Kallonta Zulaihat take har Ramlat ta gaji ta yi magana.

"Wai Maman Khalifa lafiya?"

"Kin rame ne, kuma kamar dai kina da ciki."

Ta k

auda kai a kunyace ta dai daure ta amsa da eh.

"Ciki dai Ramlat? Yanzu ba ki ji shawararmu kin yi family planning ba?"

Zulaihat ta furta don takaici bai sa ta iya ja bakin ta yi shiru ba. Ramlat ta kasa magana ta yi shiru kawai sai hawaye.

"Tab, Allah Ya kyauta to. Ya raba lafiya."

Nan ma kasa maganar ta yi.

Ganin kamar Ramlat din batun cikin na tada hankalinta yasa Zulaihat ta barshi suka shiga hirar bikin da ya taso na su Naja'atu da su Maryam jikokin Hajja. Su biyar cif za'

a aurar nan da wata biyu.

"Ki dai samu ya yi maki koda anko ne koda bai bada ma gudunmuwa ba, ke sai ki duba idan kina da hali ki yi. Sannan don Allah ki dinga cin abinci sosai ko za ki

ɗ

an maido jikinki kar a yi ta yawo da ke a cikin taro."

Ta

gyada kai.



Sai wuraren karfe hudu ta nufi gidan Rafee'ah. Ita kanta ta yi mamakin ganin Ramlat da ciki sai dai banda Allah Ya raba lafiya ba abinda ta ce don ba ta son shiga sabgarta da Aliyu.

Aliyu bai zo daukarta ba sai wuraren takwas na da

re. Sun gaisa da Rafee'ah da mijinta sannan suka bar gidan.

***

BAYAN WATA DAYA..

Tsumma ne a ƙasan ƙafarta tana goge inda mai ruwa ya

ɓ

atamata a falon tana tsaki. Sati biyu kenan da dawowarsu sabuwar unguwa kuma sabon gidan da ko ruwan famfo

babu sai dai a siya.

Aliyu ya fadamata ƙudurinsa na siyar da gidan don ya samu na jari, ba tare da ta san inda zasu koma ba ta amince. A cewar ta da ta zo ta ga yanda ginin yake da ba ta amince ba sannan ga dukkan alamu idan damina ta zo dakunan za

su yi warin ruma da kuma alamun danshi a jikin bangon. Ciki da falo ne a gidan sai fyallen daki guda daya, sai kicin hade da store. Ba daki daya a tsakar gida.

Babban damuwarta bai wuce ganewar da ta yi yanzun Aliyu tuban muzuru ya yi, ta kamashi

ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba yana shan sigari a

ɓ

oye. Ta yi kukan ta yi fa

ɗ

an amma a banza, wannan ta sa ta zubamasa ido ta maida hankali ga kaiwa Allah kukanta.



Shigowarsa falon ne ya bata damar dauke tsummar ta amsa sallamarsa a ciki.

"Baby wani wari kamar na gardi nake ji."

A kufule ta amsa.

"Mai ruwan da ka turo ne."

Ya ja tsaki.

"Kai rashin ruwan nan ya soma damuna. Ga cacar kashe kudi. Mtsw."



A ranta ta ce kai ka sani, ta shige kicin abinta.

***

"Biki ko na dangina fa bana anko ke kin sani. Yanzu ma da muke ta kai, wa ke ta kaya?"

Wannan na daga cikin dalilin da ba ta son tambayarsa wata bukata. Kusan ma yana daga abinda Abbansu ya gargadesu, tambayar miji wata buƙata kar ya kawo ma

ka raini. Wani abin ne ba za ka iya shiru ba.

"Aliyu ban ta

ɓ

a neman ka yimin wata sutura ba sai yanzun, abu ne na fita kunya. Cikin dangi da yan uwana zan shiga. Don Allah ka taimaka dai ka yimin."

Ya

ɗ

an yi shiru yana wani cin magani, can kum

a ya ce.

"Shikenan kiyi addu'a a samu kudi. Sannan batun sutura har yau ai kina morar suturorin da na miki, ko ba komai na kashe sama da miliyan daya a lefenki."

"Ba sai ka gorantamin ba."

Ta fadi ranta a

ɓ

ace. Bai ce uffan ba don yanzun

bai fiye bari su yi dogon sa'insa ba, a cewarsa juna biyu ne da ita. Hakanan yana kokarin ganin ya kiyaye kai hannu jikinta da sunan bugu.

Ta shige daki a fusace ta kyaleshi anan tare da ƴarsa.

***

Allah Ya taimaketa dai ta samu ya kawomata

atamfar ankon amma ba kudin

ɗ

inki. Hakanan ta yi godiya ta ƙuƙuta ta bada

ɗ

inkin, zuwa yanzu takan leƙa makwafta saboda halin rayuwa da son kiyaye shari'ah.

Ta ciko ba laifi sai dai ga duk wanda ya ganta da ciki sai ya tanka. Har ta gaji ta fice daga

cikin masu auren ta koma bangaren Amaren cikin ƴan mata ta zauna.

Kallon kowaccensu take cike da burgewa. Amrah ta saje a cikinsu ta ci ado har ta gaji sai hira da shewa ake. Ta tuno da nata ƴanmatancin, kauda kai ta yi gami da mirza idanunta gudun

saukar ruwan hawayen da ya tahomata. Ita da ƴan uwanta amma a karan kanta kunyar kanta take ji na abubuwan da suka afku wanda har abada tarihinta ba zai goge a zuƙatansu ba. Ko ba komai ta bar baya da ƙura.



Amrah na hankalce da ita hakan yasa ta mi

ƙ

ewa ta kar

ɓ

i Ummi a hannunta ta zauna ta shiga jan ta da hira har ta saki jiki.

***

Aka kammala biki lafiya aka kai yan matan dakunansu, ba ta samu zuwa kai su ba don ta gaji da habaice-habaicen da wasu a dangi ke mata game da aurenta. Zamanta ta

yi a gida abinta.

Kamar koyaushe bayan kammala girkin dare ta yiwa

ɗ

iyarta wanka ta shafe jikinta da hoda yanda za ta ji sauƙin zafin da ake a gari, ga ba wuta a unguwa don sai a fi sati biyu ma ko wata babu kyallinta kamar yanda ta soma shaidawa k

uma ta ji daga bakin makwafciyarta. Shigowar Aliyu gidan ya bata mamaki, koda dai yanzun bai kaiwa dare sosai a waje, amma ta yi mamakin ganinsa wuraren bakwai da mintuna. Zama ya yi gefen gadonta yana dan yamutse-yamutsen fuska.

"Lafiya?" Ta nemi b

a'asi.

Dan guntun tsaki ya ja yana mai

ɗ

an sosa kirjinsa.

"Kamar dai banda lafiyar Baby, zuciyata sai ta dinga tashi ga gudawa da nake tun safe haka nake zaryar ban

ɗ

aki a kasuwa."

"Allah Ya sauwake, Ya baka lafiya. Ya kamata ko chemist ka

leka."

Ya jinjina kai yana mai sa hannu ya dauki Ummi dake faman mikomasa hannu tana

ɓ

angala dariya.

***

ABU KAMARI just published "BABI NA ASHIRIN DA BIYAR" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/ZRLvPBGxyab

🕯



*ƘARFEN Ƙ

AFA*

🕯



_*Rufaida Umar*_

Bismillahir Rahmaanir Rahmanir Raheem.

25)

Abu kamar wasa, ƙaramar magana ta zama babba. Cutar amai da gudawa ta yiwa Aliyu kamun kazar kurkuku. Chemist ya je aka ha

ɗ

a mishi magunguna.

Koyaushe yana

gida, hankalin Ramlat ya tashi.

Abu ya wuce kwanaki ya koma sati, Aliyu ya bi ya ƙara ramewa ya yi duhu. Abin ya zamewa Ramlat goma da ashirin, ga ciki ga raino kuma ga kula da miji. Ganin abin ya ci tura ta tursasa mishi da taimakon Baban Nusaiba m

akwafcinsu, aka kaishi asibiti da motar Baban Nusaibar. Ta bar Ummi a makwafta.

"Madam, ba ka ji bane?"

Ta

ɗ

an dawo hayyacinta ta kara duban inyamurin Likitan.

"Ka dauka ka je ka biya a yi."

Gyada kai kawai ta yi ta mike ta fito zuciya

rta cike da tunani ga faduwar gaba. Tsoronta kar ta je Aliyu wani cutar ya shafo mai rikitarwa. Likita ya tabbatar gudawarsa bai da alaƙa da abinda yake tunani ke damun Aliyun, wannan ta sa har scanning sai da ya ce a yi.

"Ya ake ciki Maman Ummi?" Fa

din Baban Nusaiba. Ta dubeshi idanunta duk sun fa

ɗ

a sun yi ciki, ita kanta ta rame sai ƙaton ciki wanda sai ka rantse ya kai watanni takwas.

"Ba komai, bari na karasa na biya."

Ya gyada kai gami da amsawa da toh. Allah Ya taimaka ta taho da At

mcard dinta, ganin kudin hannunta ba zai isa bane ya sa ta fita ta zaro ku

ɗ

in. Komai ta biya aka yiwa Aliyu duk abinda ya dace. A nan ne Baban Nusaiba ya yi mata sallama kan zai koma. Godiya sosai ta yi mishi har ya fita sannan ta maido dubanta ga Aliyu wa

nda ya samu bacci.

Hawaye ta ji sun zubomata sakamakon tunanin da ya yi mata tsinke. Yanzu idan ya mutu me zai koma ya cewa UbangijinSa da Ya ba shi aron rai da kuma lafiya a rayuwa ya kasa tsayuwa ya kyautata rayuwarsa kuma ya godewa wannan ni'ima

? Ba wannan ba ma, wace cuta ce da Aliyu? Idan wannan tambayar ta fa

ɗ

omata a rai, numfashinta har tsayuwa yake cak tsabar firgici.

Tana wannan tunanin ta soma hamma kafin itama ta soma gyangya

ɗ

i saman kujera don

ɗ

akin ba su ka

ɗ

ai bane, akwai majiny

ata har uku a bayansu.

Ƙ

arar wayarta ce ta katsemata baccin, ta yi firgigit ta

ɗ

auka. Amrah ce. Miƙewa ta yi ta fita daga waje.

"Na ji shiru ba ki shigo makaranta ba, kuma nayi niyyar zuwa gidannaki ban san kwatance ba."

Ta ha

ɗ

iyi miyau ma

i zafi.

"Muna asibiti, an kwantar da Baban Ummi bai da lafiya."

"Ya Rabb, meke damunsa?"

Ta gano rudewar da Amrah ta yi, ta kuma fahimci dalilin. Hakan ya ƙaramata rashin nutsuwa da tsoro.

"Wallahi ban dai sani ba Amrah, an mishi test.

"

"Toh Allah Ya sauwaƙe, Ya ba shi lafiya. Zan shigo ko zuwa gobe ne tunda yanzu kam na kama hanyar gida akwai tazara."

Nan suka yi sallama ta mata godiya.

Ganin dacewar ta kira ta sanar a gidan su Aliyu yasa ta dannawa Malam kira. Bayan sun

gaisa ta fadamishi Aliyu ba lafiya suna Akth. Nan da nan ya ce gashinan zuwa suka yi sallama.

***

Bayan awanni biyu, tana zaune gefen Aliyu wanda ke shan kunun gya

ɗ

a da Abulle ta kawomishi sai dai hankalinta ba ya tare da su, yana ga Malam da ƙan

in Aliyu, Mudan. Suna wurin likita kai sakamakon Aliyun. Kirjinta dukan tara-tara yake yi. Fargaba kan ba'a magana.

"Ya kamata ki je gida ki huta."

Ta kalli Aliyu mai wannan batun cikin karfin hali. Girgiza kai ta yi.

"Um um."

"Nima a

binda zan ce kenan, ki tafi gida tunda shi Mudan ne zai kwana, gobe kya shigo. Ai da gajiya, ke dai sannu Allah Ya saukeki lafiya."

Fadin Abulle cike da kulawa, kaunar Ramlatu sosai ke ratsata, tana lura da yanda take ba Zakinnata kulawa.

Shigowa

r Malam ne ya sanya hankalinsu komawa garesu, fuskar Malam ba za ka iya tantance yanayinta ba.

"Kun dawo? Me likitan ya ce?" Abulle ta nemi sani. Malam ya samu wuri ya zauna.

"Babu komai, sai dai likita ya tabbatar ciwon zuciya na barazanar kama

yaron, ya kuma ce lallai ya bar shan duk abinda zai gusar da hankalinsa ko ya shaƙi iska marar dadi, idan kuwa ya ƙi komai ma zai iya faruwa. Shi gudawar sanadin me ma..?"

Ya maida akalar tambayar ga Mudan don shi ya mance ma tsabar damuwa.

Mud

an ya dora.

"Bacterial infection ne wanda shan sigari ya haddasa masa, shi ya kawomasa gudawa. Amma ya ce in Sha Allah wannan mai sauki ne. Ya dai ce dole ya kula ya bar shaye-shaye saboda cutar dake masa barazana."

Salati kawai Abulle ke yi ta

shiga yiwa Aliyu fa

ɗ

an ya taimaka mata ya bari, tun tana yi har ta shiga kuka. Aliyu idanunsa suka ka

ɗ

a, ya kasa kallon kowa musamman ganin jama'ar

ɗ

akin sun zubamusu idanu gami da baza kunne.

Cak ta mike tsaye.

"Zan wuce gida."

Abinda ta c

e kenan. Suka dubeta.

"Toh Ramlatu, ki je da Mudan ya taho da kayan shi Alin. Ba sai kin yo girki ba, daga can gida sai a kawo. Allah Ya baki lafiya kema. Sai hakuri kin ji?"

Malam ke wannan jawabin cikin nutsuwa. Ta gyada kai, har lokacin danne

hawayenta take yi, ba ta ko kara kallon Aliyun ba suka fice tare da Mudan. A hanya ma ba ta ce uffan ba duk kuwa da irin korafin da Mudan ke yi akan Aliyun da takaicin abin, suna isa ta ha

ɗ

amasa abinda za'a buƙata, tare suka fito. Ita ta nufi makwafta ta

dauko Ummi shi kuma ya miƙa titi.

Sai da ta zauna a falon tana duban Ummi dake wasanta, ta kara kai duba ga cikinta, kafin wasu zafafan hawaye su soma wanke mata fuska.

"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!" Ita ce kalmar da ta shiga ambata tan

a kara nanata wa.

Daga wannan sai wannan, komai na zuwarmata a daki-daki. Rayuwa kenan, kalar rayuwar da ta ke hangowa zasu yi da Aliyu a baya, ba irinta ta samu ba. Ta shanye dukkanin komai ta hakura, yanzu kuma ga wata sabuwa. Kukan ta shiga yi sos

ai, wayarta ta dauki ƙara ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba wurin

ɗ

auka ba tare da ta duba ko waye ba.

"Assalamu alaikum."

Ta fadi cikin muryar kuka.

"Waalaikumussalam. Ramlatu? Meke faruwa ne? Kukan me kike?"

Ta yi firgigit ta dawo nutsuwa d

a hayyacinta, ABBA ne. Da sauri ta saita kanta ta shiga ƴar dariyar yaƙe.

"Lah Abba ina wuni? Ba kuka nake ba, mura ce ta ke neman yimin kamu."

Shiru ya dan biyo baya can kuma Abba ya yi magana

"Kin tabbata Ramlatu?"

Ta gyada kai tana

jin sabon kuka na tahomata.

"Eh Abba."

"Shikenan. Ya karatu? Ina fatan dai komai lafiya? Kar ki ga ina ta tambaya, mafarkinki nayi cikin wani irin yanayi shiyasa na damu."

So da kaunar Abbannata ya kara mamayeta. Ta shiga murmushi har cik

in zuciyarta.

"Abba lafiyata kalau. Abba na gode na gode. Abba ka yafemin don Allah. Na yi maku laifuka masu tarin yawa, na so kaina.."

"Zancennan ba ya wucewa ne Ramlatu? Ban hanaki tayarwa ba? Sau nawa za'a ce maki ya wuce?"

"To na daina.

Ya jikinka?"

Ya yi murmushi mai sauti.

"Jiki da sauki Ramlatu, ba abinda ke damuna yanzun."

Ta tsinci zuciyarta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login