Showing 117001 words to 120000 words out of 255051 words
tunda ita ba ta da hankali. Ni wallahi ban yarda da ita ba ma."
Jinjina kai Hajiya ta yi.
"Ba dai ruwanki da ita, idan ta yi miki sanadin aiki ai ta gama d
a ke tunda ta san inda kike aiki."
"Da yardar Allah ba ta isa ba."
"Ai shikenan."
Fa
ɗ
in Hajiya ta ƙara da addu'ar neman tsari, Ramlat ta amsa da amin gami da lumshe ido kadan tana tuno da irin kallon da Hussein ya ke jifanta da shi, kallon
da ya nemi rikitata ta kasa abinda ta ci burin aikatawa, taimakon Allah ne ka
ɗ
ai yasa ta ƙarasa jawabinta ta bar wurin. A gefe guda tausayinsa ne ya mamaye zuciyarta, ta kuma ƙudurta taimaka mishi da addu'a don hankalinta bai kwanta da Hajiyarsa ba.
M
isalin karfe sha daya na dare, tana kwance Affan a gefenta ya yi bacci, ita kuwa tana kan whatsapp suna hira da Amrah tana bata labarin abinda ya faru yau suna dariya har Amrah ke garga
ɗ
inta akan irin wannan gangancin acewarta irin su Hajiya ba haka suka t
saya ba. Dawowar mijin Amrah ne yasa suka yi sallama ta
ɓ
ige da kallon status. Da sauri ta mike zaune tana ƙara kallon sunan Mutumin Mall kamar yanda ta yi saving lambarsa. Status ya dora na wata yarinya kyakkyawa da ba ranar ta soma ganinta ba.
"Dam
a yana whatsapp ban ta
ɓ
a lura ba?"
Ta fadi a fili kamar mai jiran amsa daga wani ko wata. Kallon hoton yarinyar ta shiga yi tana murmushi.
"Fatima." Ta furta a fili sannan ta yi screenshot. Hoto na gaba ne ya kusan zautar da tunaninta, ji ta yi
cikinta ya mur
ɗ
a, ta ajiye wayar ta fa
ɗ
a ban
ɗ
aki sannan ta fito. Gumi na tsastsafomata ta ƙara
ɗ
aukar wayar tana dawo da hoton baya ta kalla.
Su biyu ne cikin shigar ƙananun kaya iri
ɗ
aya sai bambancin kala. Ɗaya yana sanye da farin t-shirt,
ɗ
ayan k
uwa sky blue ce. Banda hakan da kuma farin gilas din da ya
ɗ
aya ya sanya a idanunsa, za ta iya rantsewa ta ƙara duk na hoton mutum
ɗ
aya ne. Kuma nan take za ta ce HUSSEIN ne. Rubutun da ya yi a ƙasan hoton ne yasa ta yin salatin da ba ta shirya ba.
"I
dan kana raye Hussein, ina riƙon Allah Ya bayyana mana kai. Ƙwaƙwalwa da zuciya ba zasu ta
ɓ
a yarda cewar ba ka tare da mu ba."
Cikin sauri ta yi screenshot na hoton sannan ta yi cropping ta yanke wurin rubutun mai kama da cigiya kafin ta yi saving, ha
nnunta har rawa yake yi. Tana so ta ce mishi ta san inda dan uwansa yake amma ta fi son ta tabbatar da zarginta. Tana son Hussein ya yi ido hudu da hoton ta ga yanayin da zai fa
ɗ
a. Anan ne za ta san yanda za ta
ɓ
ullo ta fa
ɗ
awa mutumin mall inda
ɗ
an uwansa
yake. Dama ita sam ba ta yarda da Hajiya Zeenatu ba, yanzun kuma ta ƙara tabbatar da zarginta. Ta kara komawa kan Status din, ga mamakinta ya cireshi. Sauke ajiyar zuciya ta yi, tunda dai ta yi screenshot ai shikenan.
A daren dai baccinta ragagge ne,
ita kanta ba ta san inda za ta ƙara ha
ɗ
uwa da Hussein ba balle har magana ta ha
ɗ
asu na dogon lokaci sai dai hakan bai karyamata gwuiwa ba. Ba za ta fasa abinda ta yi niyya ba.
***
Tuƙi yake amma murmushi yake yi akai-akai, daki-daki yake tuna kalama
nta da irin kallon da ta jefeshi da shi, koda ace bai kai zuciyarta ba, ba ta da masaniya akan tasirin da ya yi mishi.
Ya
ɗ
an kalli garin yanda ya yi luf luf, yammaci ne kuma babu rana dalilin damina da ke kokarin shigowa, wurare da dama a garin Kano
ya samu labarin an yi ruwa. Bai tsaya ko'ina ba sai a wurin Gym dinsu. Ya fito sanye da wandonsa three quarter sai rigarta marar hannu sai baƙar jaka da ya rataya a kafa
ɗ
arsa. Da wannan ya nufi ciki inda nan ya tarar da Hisham ya dage sai
ɗ
aga ƙarfe ya k
e. Suka yiwa juna dariya gami da cafkewa.
"Shegen sama! Ban tsammaci ganinka nan kusa ba ai. Ka biyewa aure ka soma ajiye tumbin."
Dariya Hisham ya yi yana tsane gumi da
ɗ
an ƙaramin towel.
"Ba'a magana kai kam, aure ƙarshe ne. Wallahi ba
don kai ba bazan fito ba don bani da niyya, sai gashinan ka shanyani sai yanzu."
Zama Hussein ya yi yana gyara
ɗ
aurin igiyar fararen canvas
ɗ
insa.
"Yi hakuri. Ban kyauta ba kam."
"Ina jinka, ya akai?"
Hussein ya
ɗ
an yi shiru don bai san
ta inda zai fara ba, can dai ya numfasa.
"Za ka tuna yayar Madam dinka da na kai gida?"
'Anzo wajen.' Hisham ya ayyana aransa, murmushi ya yi.
"Yes, Antinmu Ramlat."
Ya gyada kai yana shafa suma,
"Ita, sun samu matsala da Madam
ɗ
ita. Ina kuma tsoron kar ta yi mata sanadin aiki da ma abubuwa da dama. Nasan halinta da baƙin kishi."
Cikin rashin fahimta Hisham ya ce.
"Yimin dalla-dalla."
Tun farkon ganinsu da Ramlat har zuwa abinda ya faru a A&Z bai
ɓ
oyemishi ba. Hisha
m dai ya cika da mamaki, diramar ƙarshe ta ba shi dariya sosai ya kuma yi mamaki don bai zaci Ramlat din za ta aikata ba. Ɗaukar ta ya ke matsoraciya kuma shiru-shiru marar son hayaniya.
"Mamaki nake."
Hisham ya fadi yana ci gaba da dariya gami
da riko hannun Hussein da ke binsa da kallo kamar ranar ya soma ganinsa.
"Wai meye hakan?"
"Um um, amma fa duk da bansan wannan Madam din taka ba, gaskiyar magana ta
ɗ
auki hanyar da ba zai
ɓ
ullar da ita ba. Kishi ko hauka? Ba ta san yanzu kai
ya waye ba? Nikam Ramlat ta burgeni wallahi, wannan ma.."
"Nima ban ce ba ta kyauta ba, amma na fi ta sanin matata. Idan a kan kishi ne komai ma za ta aikata. So nake ka ja mata kunne don Allah, ta nesanta kanta daga inda zasu ha
ɗ
u balle har wani sa
ɓ
anin ya ƙara shiga tsakaninsu."
"Abinda ban gane ba, tausayinta kake har kake son ba ta kariya ko kuwa tsoron Madam dinka kake?"
Hussein ya yi shiru bai amsa ba can kuma ya dubeshi.
"Alaƙar da ke tsakaninta da matarka na duba, amma fa zahir
in gaskiya ba ta kyauta ba. Ko ba komai dakyar na shawo kan Madam ta fahimci dagasken ba komai tsakanina da ita. Kar ka ƙara cewa ina tsoron matata." Ya ƙarashe cike da rashin gaskiya, shi kansa ya sani yana shakkar Hajiya Zeenatu.
"Kuma dagasken ba k
omai tsakaninka da Ramlat?"
Gabansa ya fadi, ya kauda kai daga duban Hisham gami da
ɗ
an murmusawa.
"Yarinyar kallonta nake kamar irin Boss
ɗ
in nan, komai ta yi dariya yake ban, tana burgeni. Amma ban ta
ɓ
a son wata irin son da na yiwa Hajiya ba,ha
r gobe bana jin akwai wacce za ta kai Hajiya a zuciyata."
Ya ƙarashe da wani irin rauni na zuciya da gangar jiki, a karon kansa yake ji kamar ba hakan bane, amma a wani
ɓ
angaren na zuciyarsa ji yake kamar ana ƙara tabbatar mishi da cewa eh! Ba shi da
kamar Hajiya Zeenatu.
"Owk!" Abinda Hisham ya ce kenan, ya ji kuma ba don ya yarda ba. Ya hango abubuwa da dama a saman fuskar abokinnasa. Can ya ƙara karambanin watsamasa tambayar da ya ta
ɓ
a kwatanta yinsa bai ji da dadi ba.
"Kai wai yaushe za k
a kaini na gaida Mummynmu ne?"
Kamar walkiya, ya nemi annurin fuskar Hussein ya rasa, kamar wanda ya ha
ɗ
iyi garwashin wuta, haka fuskarsa ta soma wani ja-ja ga gumi da ya soma tsirfowa saman goshinsa. Miƙewa ya yi kamar wanda aka mintsila ya dauki jak
arsa. A ru
ɗ
e Hisham ya miƙe tsaye ya riƙe mishi kafa
ɗ
a ya fisge har hannunsa na bugun wani ƙarfen motsa jiki, koda da zafi, bai ji ba. Yatsa ya shiga nunawa Hisham. Ya soma magana da muryar da ta
ɗ
auki hankulan jama'ar wurin.
"Kar ka ƙara! Wannan ne
garga
ɗ
i na ƙarshe da zan maka! Bana so! Har abada banda kowa a duniyata sai Hajiya Zeenatu! She meant everything to me! Ita kadai ce dangina. Ka rike wannan ka ji?"
Ya ƙarashe a sanyaye, abin mamaki hawaye ya shiga fitarwa, a hankali ya juya ya soma t
aku ya bar Hisham tsaye a wurin baki a bude. Ga mamakin Hisham da mutanen wurin, faduwa ya yi. A guje suka yi kansa, Hisham ya tallafoshi, idanunsa a rufe sai numfashi yake fitarwa sama-sama
"Hussein, me ya yi zafi haka? Ka yi hakuri don Allah."
"Maida ni gida." Abinda ya iya fada kenan cike da wata iriyar kasala. Jama'ar na ta yi mishi sannu, wani ya riƙe jakar yayinda Hisham ya saƙalo hannun Hussein a wuyansa suka nufi motar Hussein din. Sai da ya zaunar da shi kafin ya koma da sauri shima ya d
auko tarkacensa ya zuwa a aljihu suka bar wurin. Yau ne zuwansa gidan Hussein karo na farko, dakyar yake mishi kwatance wannan karon muryarsa ta bude ba kamar
ɗ
azun ba kamar yanda idanunsa suka bude sosai. A gaggauce Maigadin ya bude ƙyaure ganin motar mai
gidan, Hisham ya tura hancin motar ya faka.
Hajiya Zeenatu na zaune a falo tana amsa waya ta ji sallamar da ba muryar mijinta ba. Turus ya yi kamar yanda itama ta yi tsaye tana dubansu.
Ganin yanayin Hussein ya sa ta ƙarasawa da sauri.
"Hab
eebee meke samunka? Kai kuma waye?"
Hussein ya zauna ya amsa.
"Hisham ne."
Ta dubi yanayin Hussein din sannan ta dubi Hisham wanda ke gaidata. Ta amsa fuska na yabo ba fallasa ganin irin duban mamakin da ke saman fuskarsa. Ya riga ya gane m
atsayinta wurin Amininsa don tun shigowarsu idonsa ya kai ga makekan enlargement din da ke dauke da fuskokinsu. Daga irin rikon da ta yiwa Hussein kadai ya ci ace duk mai hankali ya gane alaƙarsu.
'Ta
ɓ
!' Abinda ya ce kenan a ƙasan ransa. A ƙarshe ya
daure ya
ɓ
oye mamakinsa ya saki fuska. Zai ba ta bayanin abinda ya faru ne ya ji Hussein ya tareshi cikin rawar murya.
"Amm..dama kaina ne ke ciwo da jiri, ganin ba zan iya tuƙi ba yasa nace ya kawoni. Kiyi hakuri idan ganinsa ya
ɓ
atamaki rai."
Sai lokacin ta wayance gami da sakin fuska
"Haba kai kuwa, mene abin
ɓ
acin rai don abokinka ya kawoka? Wani zubin kamar yaron goye idan ka fadi wani zancen. Sannu, zauna mana bari na kawomaka ruwa."
Hisham ya girgiza kai yana dariyar yaƙe.
"A'a ba komai tafiya zan yi, nima yawa Amaryar na jirana."
Suka yi dariya, ya yi mata sallama sannan ya fice cike da tsantsar mamakin wacce ya gani matsayin matar abokinsa.
"Akwai wata a ƙasa." Abinda ya ce kenan bayan fitarsa daga gidan. Jikins
a ya ba shi akwai wata a ƙasa.
Har ya koma wurin Gym ya dauki motarsa ya yi gida, bai bar tunanin lamarin Hussein da matarsa ba. Da ma duk abinda ya faru tsakaninsu.
***
"Wai mene ne?"
A'isha ke tambayar Hisham cike da damuwa ganin yanda
yake mata Safa da marwa a tsakar falon, idan kuma an
ɗ
an jima ya ce "Ta
ɓ
!"
Ya dubeta sai ya kama hannunta suka zauna.
"Ba komai Princess, kar ki damu. Amm..please kiramin Antinmu a waya ki ban."
Cikin rashin fahimta ta ce.
"Wacce a ci
ki?"
"Ramlat."
Nan da nan tunanin A'isha ya tafi wani bigiren, murmushi ta yi don gani take fatanta ne zai tabbata tsakanin abokin mijinnata da Yayarta. Ta mike ta nufi
ɗ
akinta ta dauko wayar kai tsaye ta dannawa Ramlat kira.
Bayan ta
ɗ
aga
sun gaisa ta sanarmata saƙon Hisham sannan ta miƙa masa.
"Ranki ya dade Antinmu."
Daga daya bangaren Ramlat ta
ɗ
an yi murmushi mai sauti.
"Angon ƙanwata fatan kuna lafiya?"
"Lafiyarmu kalau, don Allah alfarma nake nema a wurinki."
"Toh wace iri?"
"Ina son idan kin samu lokaci ki zo gidana ko kuma na sameki wurin aiki wata ƴar magana zamu yi mai muhimmanci."
Shiru ya
ɗ
an biyo baya, ba wanda ya ce uffan tsakaninsu. Ga Hisham, dama ya bata ta nutsu ta bashi amsa, ga Ramlat k
uwa jinin jikinta ta sha da kuma fargabar dalilin Hisham na nemanta. Can dai ta nisa.
"Shikenan, gobe In sha Allah daga wurin aiki zan biyo."
"Yauwa Antinmu, Nagode sosai. A gaidamin ƴaƴana."
Daga nan ya miƙa wa A'isha kan wayar ya shige da
ki cike da damuwar abokinsa.
"Auta, lafiya dai ko? Ba wani laifin kika yi ba?"
Dariya A'isha ta yi jin tambayar da Ramlat ta watsomata ta cikin wayar.
"Wallahi lafiya sumul, bansan menene ba amma ina fatan alheri ne."
Ajiyar zuciya mai
karfi Ramlat ta sauke.
"Shikenan Auta, sai Allah Ya kaimu goben."
Daga nan suka ajiye wayar.
***
Ramlat ta kasa sukuni tun bayan wayar, har ta kasa hakuri sai da ta fa
ɗ
awa Hajiya. Shiru Hajiya ta yi na ƴan daƙiƙa kafin ta ce.
"Toh
ko wani laifin Auta ta yi ne yake
ɓ
oyewa?"
Girgiza kai Ramlat ta yi.
"Na tambayeta ta tabbatarmin lafiya kalau. Ko mene dai idan naje goben in sha Allah zan ji."
"Ya za ki yi da kiran da Dakta ke miki?"
Gabanta ya fadi,
ɗ
azun da yamma
a hanyarta ta dawowa daga wurin aiki ne ta amsa wayar Baba Dakta akan yana nemanta a gidansa. Tun sadda ta ji hakan ta rasa sukuni, tasan tatsuniyar gizo bai wuce na ƙoƙi.
"Kin yi shiru." Hajiya ta furta tana kallon yanda ta ke dama fura cikin nono b
a tare da ta san me take ba don inda ludayin ya ke kallo daban da abinda ta ke.
Maganar Hajiyar ya maidota cikin nutsuwarta. Sauke ajiyar zuciya ta yi.
"Nasan ba wani jimawa zan yi a gidan A'isha ba, da zarar mun kammala zan wuce gidan Baba Da
kta kafin na shigo."
Girgiza kai Hajiya ta yi tana murmushi.
"Ramlatu kenan, ba haka za'a yi ba. Ina gidannan ina gidan Baba Dakta? Ki tashi dai ki je yanzu kinga goben kin huta. Miƙomin furar na dame abata."
Ta kalli Hajiya a raunane, babu
damar ta ce a'a, ta mike jiki a sanyaye ta miƙamata.
"Mami zan bi ki!"
Ummi ta furta tana
ɗ
ago kai daga zanen da take na makaranta. Daƙuwa Hajiya ta mata.
"Gidanku, wato ma ba karatun kike ba kunnenki yana nan ko? To babu inda za ki je, id
an kuma kika bi ta babu ke ba shan fura."
Ai da sauri ta ce ta fasa. Murmushi kawai Ramlat ta yi ta nufi daki, hijabinta kawai ta zura ta dauki wayarta ta fito. A sannan ko sallar Isha'i ba'a yi ba, an dai kusa kira. Ta yi musu sallama ta fita.
***
Zuciyarta kamar ta yi tsalle ta fito sadda ta gama jin dogon jawabin da Baba Dakta ya
ɗ
auko game da batun aure. Sai da ya gama nunamata muhimmancinsa ga rayuwar ƴa mace kafin ya bita da nasiha mai ratsa jiki, daga karshe ya tafi kai tsaye ga inda ya
sa gaba.
"Lokaci ya yi da ya dace ke da kanki ki yiwa kanki fa
ɗ
a ki fiddo mijin aure Ramlatu, na kyaleki don a ganina kina da ƴancin da za ki za
ɓ
awa kanki abokin rayuwa wannan karon ba tare da waninmu ya tilasta maki ba. Ki tsaida hankalinki ki yi tu
nani mai kyau. Akwai da dama wa
ɗ
anda suka zo wurina neman aurenki kamar yanda shima kawunki Bashir ya sameni da batun maneman aurenki sun sameshi. Toh koda a baya bamu ba su damar neman yardarki ba, wannan karon ba zamu hanasu ba Ramlatu. Babban burinmu sh
i ne mu ga kema kin yi aure. Aiki ba ya hana aure idan har mijinki ya amince, idan kuwa bai amince ba sai ki zamanki a daki ki nemi wata sana'ar kamar yanda ƴar uwarki ta yi."
Yana nufin Amrah. Wato ma dai ana zuwa har can Yakasai neman aurenta? Wanna
n abu ya dauremata kai, kodayake yana daga dalilinta na dauke ƙafa a gidan Hajja, a gidan ma akwai
ɗ
an Kawunta da ke sonta sai dai mahaifiyarsa ta ce sam ba da ita ba. Wannan shine rikici ma na karshe da akai har zuwa gidan ya fice a ranta. Basu da masaniy
ar babu Kamalu a ƙoƙon ranta, ba ma shi kadai ba, kowane namiji ma ba ya gabanta. Aliyu ta so, kuma har gobe akwai kaunarsa a zuciyarta. Rana bai ta
ɓ
a fitowa ya fa
ɗ
i ba tare da ta yi mishi addu'a ba.
"Kinji ko?"
Maganar Baba Dakta ya katsemata
tunani. Gyada kai ta yi tana share kwallar da ta cikamata idanu. Cikin sallamawa ta amsa.
"Eh Baba Dakta, da yardar Allah zan yi yanda ku ke so."
Murmushi ya yi gami da gyara zaman gilashinsa.
"Allah Ya yi maki albarka. Ya za
ɓ
amaki abokin ra
yuwa wanda za ku rayu har abada cikin aminci, so da yarda."
Kunya ta sanya ta kasa amsawa sai murmushi.
"Sai abu na gaba, meyasa