Showing 60001 words to 63000 words out of 255051 words
/>
abi'un mahaifinsu, sai dai kuma ba za ta iyaba. Ko ba komai wannan sirrinsu ne.
Dr Sadiya ga ci gaba da lalla
ɓ
ata da ba ta shawarwari har sai da A
liyu ya gaji ya dawo ofishin.
"Wai me ake yi? Ni fa zan iya barinki ki kwana anan idan ba ku kammala ba."
Ya yi maganar a fusace, Ramlat ta mike ta yiwa Dr Sadiya godiya, ita kuwa ta miƙa wa Aliyu file din suka fita. Tun a asibitin tana jinsa y
ana jan tsaki har dai suka siya magani suka fito yana mitar kudinsa sun kare.
"Wallahi injin ma na fasa kunnawa, kudin sun ƙare. Zan dai siyamaki kazar tunda na sakamaki rai."
Gyada kai ta yi kamar kadangaruwa, fuskarta duk ta kumbura saboda k
uka. Bini bini sai ta shafi cikinta. Iskar mashin na neman yi mata yawa don haka sai ta dukunkule ta kwantar da kai kadan a gadon bayansa. Hakan da ta yi dukkansu sai suka ji wani sanyi da kaunar junansu yana kara
ɗ
arsuwa a zuƙatansu.
"Ina sonka Swe
et Aliyu, ba zan iya rabuwa da kai ba."
Ta furta a hankali, kalaman sun ratsashi. Ya yi murmushi gami da
ɗ
an rage gudu.
"Baby wa ya ce miki zan iya rabuwa da ke? Ai mai rabamu sai mutuwa Baby. Don ina shaye-shaye addu'a za ki yimin har na daina,
kin ji?"
Ya ji sadda ta gyada kai a jikinsa, kusan a tare suka yi murmushi. Murmushin tana yi hawaye na zuba, zuciyarta ta kasa tsanar Aliyun. Soyayyarsa da na abinda ke cikinta suka ha
ɗ
armata. Ta kuma daura
ɗ
amarar fa
ɗ
a wa Allah matsalarta akan Ya
shiryamata mijinta.
Sai gashinan Gen din da yake cewa ba zai tayar ba, sai da ya siya mai rabin galan ya kunna suka ga haske. Ranar tattalinta ya dinga yi gami da fadamata karya da gaskiya duk don ta ji tausayinsa ta kuma yarda ba'a son ransa ya som
a shaye-shaye ba. Ya kuwa ci galabar hakan.
***
🕯
️
*ƘARFEN ƘAFA*
🕯
️
*_Rufaida Umar_*
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
_Assalamu alsikum ƴan uwana. Na gode sosai da addu'oinku. Allah Ya bar zumunci. Ameeen ameeen._
17)
Tun fitowarsu take bin bayanta, har suka bar wurin jama'a sosai. Tsayawa ta yi cak gami da juyowa a fusace.
"Wai Malama bibiyar ta menene? Me kike nufi? Kin san ni ne?"
Maganar ko kadan ba ta fusata Ramlat ba. Asalima hawaye ta soma ƙoƙarin z
ubarwa. Amrah da sauri ta kauda kai gefe, ba ta son ko kusa ta karya zuciyarta, ita kanta ta yi kewar aminiyarta sai dai kuma tunda har hakan ta za
ɓ
amusu zai fi.
"Kiyi hakuri, don Allah ki yi hakuri ki yafemin Amrah. Kowa yan guduna, idan kema kin gu
jeni wa nake da shi? Da ke kadai na saba shawara, ki yi hakuri ki yafemin kuskuren da na maki."
A
ɗ
an sace Amrah ta kalleta.
'Ta rame.' Ta ayyana a ranta. A fili kuwa ƙara tamke fuska ta yi gudun kada ta nuna rauninta a fili.
"Ai ba ki yim
in laifin da na riƙe ki da komai ba. Mutum duk abinda ya za
ɓ
arwa kansa, sai a zuba ido a bar shi da za
ɓ
insa. Ba ma miki mummunan fata ko kadan."
Ta juyo don ta san idan ta ci gaba da tsayuwar tsaf Ramlat za ta kalamance ta. Yanzun sai ta sauya dukkan
ra'ayinta.
"I am pregnant."
Ta furta a hankali bayan ta kara matsawa gaba kadan. Cak kuwa Amrah ta tsaya, ta juyo tana dubanta. Gyada kai ta shiga yi tana share fuska.
"Eh Amrah."
Har ga Allah jin cewa tana da ciki ya sanyayawa Amrah
jiki.
'To ko wannan shi ake kira rabo? Wannan auren kaddarar Ramlat ce.'
Ta yi maganar a zuciya, ganin jama'a na kallonsu ya sanya Amrah magana.
"Allah Ya raba lafiya. Na miki murna sosai. Kinga ana kallonmu, ki wuce gida kawai, gobe ma had
u a makaranta. Na yafemaki."
Ta ƙarashe da dan murmushi. Ramlat ta
ɗ
an rungume kafa
ɗ
arta tana ƴar dariya. Ko ba komai za ta maido amintarsu.
Tare suka jera suka fita waje, abin hawa ne ya rabasu. Hatta Amrah sai sannan zuciyarta ta yi sanyi.
***
Kofar falon a bude, wannan ya kara tabbatar mata da zargin maigidan na nan, tun a bakin ƙyauren ta ga motar da a yanzun ta shaida na abokinsa G Baba ne. A gajiye take lis amman murnar shirinta da Amrah ya mantar da ita hakan.
Tun kafin ta
saka ƙafa a falon, ƙaurin sigari da kuma hayaƙinsa ya baƙunci hanci da idanunta. Hira suke suna ha
ɗ
awa da ashariya. Ji ta yi zuciyarta na tashi. Ta daure ta karasa shigowa falon da sallama. Suka dubeta. Aliyu ya saki murmushi.
"Baby, kin dawo?"
Gyada kai ta yi, don takaici ko kallon G Baba ba ta tsaya yi ba balle su gaisa ta yi
ɗ
akinta. Zama ta yi bakin gado ranta na wani irin zafi. Kallon agogon bangon ta yi, shida na dab da yi. Kwafa ta yi ta rage kayan jikinta fa fa
ɗ
a wanka.
A falon ku
wa, G Baba ya zuƙi sigari ya fesar.
"Madam dinka fa ba ta yi murnar ganina ba. Hala ba ta son wannan hayaƙe-hayaƙen?"
Wani tsaki Aliyu ya ja,
ɓ
acin rai sosai Ramlat ta jazamishi.
"Don uwarta an fadamata ni ban isa da gidana bane? Ko an fa
damata shashashan miji ne? Zan je na sameta ai! Sa'arta
ɗ
aya tana dauke da Baby."
Wani mugun kwarewa G Baba ya yi, Aliyu ya tsaya cak yana kallonsa.
"Lafiya? Ka zuƙa over Malam."
Sai da G Baba ya kora ruwa sannan ya samu nutsuwa. Ya
ɗ
an dub
i kofar dakin sannan ya juyo ya kalleshi.
"Ciki? Kai murna kake Madam dinka ta haihu yanzu? Kasan irin nauyin da zai ƙara hawa kanka kuwa? Wani fita eh yane, wani hawa gajimare duk raino zai sa ka daina. Kai Zaki! Yawane wallahi! Nawa kake ma yanzu? G
askiya ku san abin yi game da cikin."
Aliyu ya daure fuska kamar bai ta
ɓ
a dariya ba.
"Malam kar ka kara yimin zancen banza! Shege ne da za ka ce kar na bari ya fito duniya? Kai ka fi kowa sanin duk iskancina bai wuce zuƙe-zuƙe da ƴar romance ba,
amma bana babbar harka balle a samu akasi. Toh don me za'a haifarmin
ɗ
an sunnah ka nemi ka kashen gwuiwa. Ba dan iskan da zai sa na zubar da cikin Baby."
Ya ƙarashe gami da watsawa G Baba harara. Shi kuwa G Baba ya kara yarda da irin son da Aliyu ke
yiwa Ramlat. Ya tabbata shi ya shafi abinda ke cikinta. Aliyu kaifi daya ne idan ya ga dama, idan har ya yi irin tsaurinnan to ba mai juyamishi ra'ayi wannan ta sanya ya ja bakinsa ya wayance da yi mishi kirari hadi da fadin.
"Ko ba komai ai ma zo mu
ƙ
arawa sama ado."
Suka cafke gami da wata irin dariya.
***
Ramlat zamanta ta yi a dakin bayan ta idar da sallar La'asar da ba ta yi kam lokaci ba. Tana jin yunwa, sai dai ba ta kaunar ganinsu. Kwantar da kai ta yi a saman hannunta jikin gado
tana daga zaune saman darduma, tunani mai zurfi ta fa
ɗ
a gami da riƙe cikinta. Har sannan tana kara jinjina lamarin, wai ciki ne da ita.
'Cikin mashayi.' Wani bangare na zuciyarta ya ayyana mata, ta jima anan zaune har wahalallen baccin da ba ta samu
yinsa da safe ba ya soma fisgarta sai dai cikinta na ta ƙara saboda yunwa.
A hankali ta ji hannu saman fatar cikinta. Firgigit ta bude idanu, Aliyu ne durkushe ya daga rigar yana shafa cikin. Suka hada ido, murmushi ya sakarmata. Ita kuwa warin siga
ri ke tayarmata da zuciya don haka ta mike da sauri ya riko hannunta gami da miƙewar shima.
"Baby lafiya?"
Ta rufe baki da hancinta da hannu ta shiga tureshi tana girgiza kai.
"Don Allah ka fita, warin taba, zan yi amai wal..."
Yunkurin
aman ya katseta, da sauri ta fa
ɗ
a ban
ɗ
aki shi kuwa ya fita daga dakin. Ba wani abin kirki ta amayar ba, ta wanke baki ta fito, ganin baya dakin yasa ta daukar turare mai sanyin kamshi a bakin madubi ta
ɗ
an fesa a jikin wani dan handkerchief ta toshe hanci
n sannan ta bude winduna dakin.
Kiraye kirayen sallar Magriba ne ya sa ta mike ta zura hijabinta. Sai da ta yi sallah sannan ta mike ta nufi falon don Aliyun ya shigo har sau biyu kafin ta idar. Maimakon ƙamshin sigari, sai ta ji ƙamshin turaren wut
a. Ba kowa a falon hakan ya bata tabbacin Aliyun ne ya kunna. Ta saba duk sadda ya gama busa hayaƙinsa za ta yi azamar daukar kaskonta ta kunna gawayi ta saka turare. Sai ta ji hakan da ya yi ya burgeta, kaso hamsin na damuwarta ya yaye. Sai a sannan ta ci
dora abinci mai saukin dahuwa ta ci, ta shiga karatu.
***
Washegari da
ɗ
okinta ta fita daga gidan. Aliyu ne ya kai ta saman mashin dinsa.
Koda ta shiga Malami ya shigo basu sami damar gaisawa da Amrah ba sai dai wannan karon sun samu zama wuri
guda. Ana tashi, kowa ya fice daga ajin suka yi zamansu.
"Mai ciki ba za ki ci komai ba? Rana fa ta yi." Fadin Amrah cikin murmushi. Harararta ta yi sannan ta ja guntun tsaki.
"Ni har tsoron haihuwar ma nake."
"A gidan Aliyun ko kuwa me?"
Tasan Amrah da biyu ta yi tambayar, ba kuma ta so ta bada kofa yanzu Amrah ta san sirrin gidanta. Ta fi kaunar Amrah ta dawo da tausayi da kaunarta a zuciya kamar dai a baya.
"A'a, kada na mutu wurin haihuwa."
Dariya Amrah ta yi.
"Sai kum
a aka fadamaki haihuwar ƙarar kwana ce? Addu'a za ki yi, In sha Allah za ki haihu lafiya. Af, ga saƙon Umma ma. Ta cemin ki dinga shan kayan marmari da abinci lafiyayye. Kar kuma ki yawaita daukar abu mai nauyi. Kuma wai ko nan gaba za ta aikomaki mene? Oh
o na manta. Ta ce dai na miki albishir tana nan zuwa."
Dadi, farin ciki da annashuwa suka cika zuciya da fuskar Ramlat. Daga washe haƙora tana dariya sai ga hawaye na fita. Hawayen tana da wata uwa da ba ita ta haifeta ba, amman ta tuna da ita. Tana k
okarin ba ta kulawa irin ta uwa.
"Meye abin kukan?"
Fadin Amrah da ke jin zuciyarta itama na neman karyewa. Ta daure ta tattaro dauriyar wuri guda, ta shiga zolayarta.
"Oh, wa ya ga Ramsy da
ɗ
a? Naga yanda za ki yi raino. Wai har ki shayar.
"
Ta ƙarashe gami da sanya dariya, itama ba ta san sadda ta dara ba ta hau share fuskarta.
"Kema ai kamar yau ne."
Ta
ɓ
e baki Ramlat ta yi.
"Ni da aure sai na kammala karatu in Sha Allah."
Murmushi Ramlat ta yi kafin su ta
ɓ
a hira,
so take Amrah ta jefomata tambayar da ta shafi gidanta ko dangin mijinta, sai dai ta lura kokarin kaucewa hakan ma Amrah ke yi. Don haka itama sai ta kara rufe cikinta ba ta kaunar su sami wata matsalar.
***
Bayan sati biyu hankalin Ramlat a kwa
nce, za ta yi waya da Abbanta da kuma Hajiya wacce a sannan ta
ɗ
an sassauta kadan. Umman Amrah kuwa kiranta take sosai su yi hira ta yi ta kwantar mata da hankali. Ta dauketa kamar ƴar da ta haifa a cikinta. Bangaren Aliyu, ya rage zuwa ya yi mata shaye-sh
aye a gida kamar yanda ya daina shigomata a buge. Hakan ya kara kwantar da hankalinta ba ka
ɗ
an ba. Abinda ke yawan bata mamaki ya daure mata kai, banda Abulle babu wani ko wata a dangin Aliyu dake zuwa gidanta, zargin ba sa kaunarta ya kara tabbata a kansu
. Don haka ta ja jikinta ta kama kanta. Hakan bai hana ta kira mahaifin Aliyun ta gaidashi, shi kam lafiya sumul yake amsamata.
A yammacin juma'a ta fito falon bayan ta yi wanka ta shirya cikin riga da wando Pakistan. Tashinta daga bacci kenan bay
an ta dawo daga makaranta. Kicin ta shiga ta hau kiciniyar yin tuwon semo da miyar kuka kasancewar hakanan ta ji tana sha'awarsa. Sai dai me? Babu gas.
"Ya Salam." Ta furta a fili. Jiki a sanyaye ta fito falon tana jan tsaki, waya ta dauka ta lalubo
lambar Aliyu ta kira.
"Kamar ya babu gas? Har gas din gidan ya ƙare?"
Shi ne tambayar da ya jefomata bayan ya saurari bayaninta. Ta ciji le
ɓɓ
anta ta kasa cewa komai. Sai kuma ta ji ya ja tsaki kafin ya ce.
"Nidai wallahi banda kudi, kema
kin sani kuma. Yanzu haka ganinan wani banza dan gin..."
Kiit, ta katse kiran, a duniya ta tsani ta ji yana ashariya. Abin na ƙona ranta.
"Allah Ka shirya." Ta firta a fili, ita kam yunwa ta ke ji don haka ta mike. Ta tuna da lemun da ta gani Ali
yu ya ajiye a fridge da safiyarnan, sadda aka kawo wuta. Ta soma shiga kicin ta dauko ragowar bireda ta fiddo lemun. Tun kafin ta ƙaraso ta bude ta shiga kwankwada. Sosai ya yi mata dadi. Tana zama ta hau tauna biredin, idanunta na kan wayarta dake ƙara ku
ma sanin Aliyun ne ta ƙi
ɗ
agawa. A hankali kuma ganinta ya soma zama dishi-dishi. A kokarinta na ajiye robar lemun saman Centretable sai ya zube a ƙasa.
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Mene haka?"
Ta fadi cike da karfin hali. Ita ta san m
e take ji. Jirin na kwasarta, yana kokarin fitar da ita daga hayyacinta. A hankali ta kai hannu ta dauki wayar ta danna. Cikin muryar ƴan maye ta soma magana.
"Aaaaaliiii."
Ba ta ji me yake cewa ba ta wurgar da wayar, ta mike ta na tafe tana ran
gaji da zagaye falon, ba ta yi aune ba ta ci uban tuntu
ɓ
e da takalminta ta bugi gefen mararta da tv stand ta zube anan. Duk da ba'a hayyacinta take ba sai da ta saki ƙara.
***
A hargitse ya banko kofar falon ya shigo. Kallo
ɗ
aya ya yiwa robar lemun
ya san abinda ke faruwa. Jijjigata ya soma.
"Baby! Baby! Ramlat!"
Ya rasa na kira, cak ya
ɗ
agata ya fita. Ba kuma zai yiwu ya sanyata a mashin ba, dole ya dawo da ita ya fita ya taro
ɗ
an sahu suka bar gidan zuwa asibiti.
***
"Ka yi hakuri,
cikinta ya riga da ya zube."
Bayanin Dr Lamin kenan bayan ya gama fa
ɗ
awa Aliyu cewa a jininta da aka auna an samu tabbacin ta sha kwaya mai ƙarfi, ya kuma yi fa
ɗ
an meyasa ya bar ta yin shaye-shaye duk kuwa da sanin da ya yi tana da ciki. Ga mamakin
shi kansa Aliyu ya kasa cewa komai, har Likitan ya yi fa
ɗ
a ya kammala. Batun zubewar cikin ya fi komai
ɗ
agamishi hankali. Idanunsa suka ka
ɗ
a.
'Ko mene laifinka ne ai! Da ba ka ajiye a gidan ba, ta ina za ta gani ta dauka tunda ba halinta ba ne!'
Fa
ɗ
in wani sashi na zuciyarsa.
***
Awanni ka
ɗ
an bayan farfa
ɗ
owarta ya shiga. Ta
ɗ
ago idanu ta dubeshi sai ta soma hawaye.
"Kaga abinda halinka ya jazamana ko?"
Ya zaune gami da riko hannunta.
"Laifinki ne, meyasa ba ki
ɗ
aga wayata ba ina t
a kira? Tunawa nayi na ajiye a fridge shiyasa na so na garga
ɗ
eki."
Ta kauda kanta kawai, cike da bakin ciki. Abin kunya sanadin shaye-shayen mijinta, cikinta ya zube.
"Kaicona." Ta furta a fili, sai kuka. Kewa, kewar iyayenta take. Don haka ta
juyo ya dubeshi.
"Bani wayarka."
"Ki yi me?"
"Abbana zan kira."
Ya daure fuska.
"Ki ce mishi kin sha abin maye cikinki ya zube? Asirinmu za ki tona? Dama ya lafiyar giwa ballantana an jefeshi da kashi? Toh ki je ki gwada tona asi
rin namu. Naki ne zai fi wari, ni dama ba ganina suke da gashi ba."
Daga haka ya mike ya sa kai ya fice a zuciye. Ta bishi da kallo, wani malolon abu ta ji ya tsayamata a maƙogwaro. Tana jin haushin irin kalaman da Aliyu ke yi akan iyayenta. Ko ba kom
ai iyayenta kuma su suka haifeta. Dole ta takawa abin burki.
'Kin manta ke kika bada ƙofa.' Cewar wani bangare na zuciyarta, hakan sai ya karyarmata da gwuiwa. Ta yi shiru ta soma hawaye. Tana jin haushi da tsanar kanta akan duk abinda ya faru tsakani
nta da yan uwanta, a gefe guda kuma don Aliyu ya zama kamar bugun numfashinta wanda ba ta jin za ta iya rayuwa babu shi. Sai dai kuma hakan ba zai hana ta janyo ƴan uwanta jiki ba, ta dinga ziyartarsu koda ba su zo mata ba. Ta kudurta sauya takunta tun kan
abu ya yi nisa.
***
Sai da ta yi kwanaki uku aka sallameta daga asibiti. Shi ne lokaci na farko da ta ga matan mahaifin