Showing 135001 words to 138000 words out of 255051 words

Chapter 46 - KARFEN KAFA complete

kiranta sau tari a wayarsa, bai yi saving lambar ba, amma ita tana da lambar a wayarta. Allah Ya hana bincike, shiyasa ba ta zurfafa ba. Sai kuma sanin da ta yiwa Modibbo

na bala'in son kansa da kuma ƴaƴansa, wannan ne waekness dinsa. Duk abinda yaransa ke so koda ba ya son abin, zai yi yanda zai yi ya nemamusu farin ciki. Wannan ya yi sanadin lalacewar wasu a yarannasa.

"Ke za ki biyewa wannan shashasha har ki wani

tsaya zurfafa tunani? Kin yarda da abinda ta ce kenan?"

Dariya Kausar ta yi tana girgiza kai.

"Ko kadan." Suka

ɗ

an dara, Hafsat ta turo baki.

"Toh nidai gaskiya Dada ba zamu yarda da wannan aikin da kike fita ba, idan kika ci gaba zan kira

Hamma."

Dada ta yi murmushi cikin harshen fulatanci ta amsa.

"Dayake shi ya haifeni ko? Banda abinki Hafsatu, ni da gida

ɗ

an uwana? Wa ya fadamaki abinda na yi fa

ɗ

uwa ce? Babu, zumunci na sadar kuma Allah zai duba."

Ita dai Hafsat ta ja ha

nnun Fatima suka fice zuwa falon Amarya. Banda Dada ta tilastamata kuma tana son zuwa gurin Rasheeda, ba abinda zai sa ta tako ƙafarta Kanon, a yanzun ma ji take da ace akwai wasu ƴan uwannasu can za ta yi tafiyarta.



Da yammacin ranar AlHassan ya

iso ƙofar gidan Modibbo, waya kawai ya yi ya ba Hafsat umarni fitowa tare da Fatima su yawata. Da wani irin

ɗ

oki Hafsat ta mike ta shirya Fati suka fice ba su ko tsaya sallama da kowa ba banda Adda Kausar da suka fa

ɗ

awa ta sanar Dada.

Fuska ta dau

re ganin yanda Taheer

ɗ

a ga Hajja Fatuma ya tsuramata idanu yana kallo. Bafulatanin usuli wanda daga ka ganshi ka ga jinin Mamman Gidado.

Dagasken gaske tana lura da yanda yake wani safa da marwa a sashin Amarya wanda hatta da Rasheeda sai da ta nuna mam

akinta a fili, acewarta abu ne mai wahala ka ganshi a sashin nasu.

Har ta isa ta bu

ɗ

ewa Fatima gaban mota ta shiga itama ta bude gidan baya ta fa

ɗ

a babu walwala. Alhassan ya dubeta yana murmushi sadda ya ja motar.

"Ke kuma ke da wa?"

Turo b

aki ta yi.

"Bakomai."

Ya ta

ɓ

e baki. Ko me ya faru ai su suka sani, shi dai kam dama bai nunamusu yana son zuwan ba.

"Daddy ina zamu je?"

Cewar Fatima a

ɗ

okance. Ya ja kumatunta da murmushi.

"Surprise ne."

Ya yi ta biyemata s

u na surutu har suka iso tafkeken shagon na A&Z.

Hafsat sai a lokacin ta saki ranta, suka fito suka jera ciki. Da ka gansu ka san jini

ɗ

aya ne.

Kai tsaye suka hau sama, ma'aikatan sai kallon AlHassan suke yi kusan a mamakance. Duk a zatonsu M

ijin Madam ne, ganinsa da budurwa ya ba kowa mamaki, har da samari da ƴanmatan da suka mayar da wurin wajen zuwansu. Shi kuwa Alhassan wayar da aka kirashi ce ta sanya shi ba Hafsat kudade tare da ba ta umarnin ta suyamusu duk abinda ya dace, yana jiranta

a waje.

Sauri yake sosai yana son barin hayaniyar cool music da ke tashi a wurin ganin Director

ɗ

insa na wurin aiki ke kiran. Magana ce za su yi mai muhimmanci. Karo ya ci da ita sadda ta sanyo kai nan take wayarsa ta fa

ɗ

i, ya

ɗ

ago ita kuwa ta matsa baya

gami da fadin.

"Yi hakuri fa."

Ɗ

agowar da zai yi sai da ta ji hantar cikinta ya ka

ɗ

a. Ba don ace tare suke tafe da mijinta Hussein ba, kuma yana cikin mota sanye da kananan kaya, madadin wannan da ke sanye da shadda blue, za ta rantse shi ne ts

aye. Murmushi ya yi mata da nunamata ba komai kafin ya yi gaba. Har tana tuntu

ɓ

e haka ta juya ga mararta da ta cika taf da fitsari, haka ta karasa ga Hussein wanda ya juyamusu baya yana kokarin rufe motar. Ganinta a gigice yasa shi dubanta da mamaki.

"Lafiya?"

Dafashi ta yi gami da riƙe kai.

"Lafiya, a'a ba lafiya, muje don Allah. Jiri nake ji shiga mu tafi."

Hussein dai abin ya dauremishi kai, zai yi musu abin mamaki Hajiya ke roƙonsa ya bar kowace magana a gefe su wuce su koma gida. B

a ta da lafiya. Dole ya shiga motar bisa umarninta itama ta shige. Ba ta samu nutsuwa ba sai da ya doshi gate, sai dai kafin ya kai ga fita jikinsa kawai ya yi wani irin la'asar yayinda ya ji kirjinsa na dukan uku-uku, ya kalli bayansa ta mirror. Bai ga ko

wa ba face wani matashin da ba zai fi shi a shekaru ba, tsaye jikin mota ya juyamusu baya yana amsa waya.

"Ya kake tafiya kamar ba ka so? Ka yi sauri don Allah."

Maganar Hajiya ta dawo da shi nutsuwarsa, ya

ɗ

an ƙara ƙarfin gudun.

"Wai meke

faruwa? Naga lafiya muka shigo wajennan."

Girgiza kai ta yi tana share gumi.

"Nima dai ban sani ba. Watakila plantain da kwai da na ci ne ya

ɗ

an juyamin ciki."

"Kuma kika ce jiri?"

Ta ja guntun tsaki ganin zai ƙureta, ita dai yanzu ta f

i kaunar a kyaleta tayi tunani mai kyau. Wannan ya nuna twin brother din Hussein ya zo Kano kenan? Lallai dole ne ta hana Hussein zirga-zirga. A farin farko dai za ta bincika ta ji dalilin zuwansa, idan har zama ne na dindindin, barin Kano na har abada ya

gansu ita da mijinta koda ba ya so. Haka ta yi ta tufka da warwara, Allah-Allah take su isa yanda za ta samu damar yin tunani mai kyau.

Shi kuwa AlHassan koda ya gaji da gaisuwar da wasu daidaikun ma'aikatan masu wucewa suke mishi sai kawai ya shig

e cikin motarsa ya zauna ya ci gaba da wayar. Har su Hafsat suka fito

ɗ

auke da ledoji yana waya. Hayaniya kwakkwara hanasu ya yi, kusan har ya soma tuƙi suka yi tafiyar mintoci yana waya. Can dai ya katse ya ajiye, da murmushi ya dubesu.

"Sorry, ban k

yauta muku ba ko?"

Fatima ta turo baki ta gya

ɗ

a kai. Dariya ta basu.

***

"Hajiya Ramlatu, ina son ganinki."

Shi ne abinda ya ce kenan bayan ta saka wayar a kunne. Ramlat ta ajiye kan wayar ranta na zafi, tsabar raunin hankalin Chairman ya

soma isarta, tana kallon abin kamar da biyu yake yi.

Ta mike ta gyara zaman na

ɗ

in laffayarta ta tabbatar ko'ina na jikinta ya ƙara rufuwa ruf sannan ta ƙarasa ciki.

Kallon haramun dai bai fasa ba don haka ta daure fuska.

"Gani Yalla

ɓ

ai

."

Ta fa

ɗ

i a ladabce cikin basarwa don yanzu ta bar ganin ƙima da mutuncinsa.

"Amm..yanzu a kan aiki muke don haka ba zan ce komai ba. Sai dai idan ba damuwa ko za'a yimin iznin zuwa gida?"

'Anzo wurin.' Ta fadi a ƙasan ranta. Girgiza kai

ta yi.

"Ka yi hakuri Yalla

ɓ

ai..."

"A'a kinga Ramlat, ba batun nayi hakuri bane. Tsakani da Allah ba zan iya ba. Na fadamaki yanzun muna bakin aiki ne, magana ce kuma zan zo muyi ta fahimta."

Shiru kawai ta yi, ganin ta ƙi ce mishi uffan

ne ya sa shi magana.

"Zan ba ki daga nan zuwa Monday, please ki yi tunani mai kyau. Ki sani, koda ace a baya sharri ne a zuciyata, yanzun babu

ɗ

igon wannan Ramlatu. Wallahi babu."

Yanda yake magana kamar wani yaro sai ma ya so ba to dariya, ita

dai ba ta ce komai ba.

"Shikenan kina iya tafiya."

Ta juya ta fice ba ta ce mishi uffan ba, Chairman ya bita da kallo kafin ya lumshe idanunsa ya sauke ajiyar zuciya. Sanin gidansu Ramlat abu ne mai sauƙi a wurinsa, sai dai ya fi kaunar bi ta

hanyarta ko don ya goge wannan kallon girma ya fa

ɗ

in da ta ke yawan jifansa da shi. Ko ba komai dai da gaskiyarta. Da niyyar cuta ya zo sai soyayyarta na gasken ya sauya komai.

***



I just published "BABI NA TALATIN DA BAKWAI" of my story "Ƙ

arfen Ƙafa". https://my.w.tt/4aFXFyDdjbb

🕯



*ƘARFEN ƘAFA*

🕯



*_Rufaida Umar_*

Bismillahir Rahmaanir Raheem.

37)

LAMIƊO CRESCENT

"Ki soma fa

ɗ

amin wannan ƙullen da kike yimin na mene wai? Ina da aikin yi, kin hana n

i fita."

Hussein ke maganar a tausashe da

ɓ

acin rai saman fuskarsa. Zeenatu dubansa take yi don ta rasa ma hanyar

ɓ

ullo mishi. Ba ta son fitarsa, jinta take kamar wata zararriya, gaba daya babu aikinta

ɗ

aya da ya tafi daidai. A baya ta rantse ba za ta

bar garin Kano ba amma kam a yanzun a shirya ta ke da yin nesa da duk abinda zai sa Hussein ya su

ɓ

ucemata.

"Tafiya zamu yi, Kano nake son mu bari."

Kallonta kawai yake yi cike da tunanin meke damunta har haka. Dariya ta so kwacemasa don shi kan

sa yana mamakin irin ƙwarin gwuiwar da ya ke samu na yi mata jayayya akan duk abinda ya zartar a yanzun.

"Kinsan me kika ce kuwa?" Ya fadi kansa tsaye yana kallonta har sai da ta ji ƙirjinta ya bada dam! Dakyar ta ha

ɗ

iyi yawu.

"Me kake son ka ce

? Jayayya za ka yi da ni? Ba za ki bi ra'ayina ba?"

Ya yi shiru kawai yana kallonta da wani mamaki, wani tsana yake ji kamar yana son tasomishi sai wata soyayya da bai san mafarinta ba ta zo ta danne wannan tsanar. Kauda kai ya yi gami da miƙewa daga

saman gadon.

"Kiyi hakuri, abu ne da ba zan iyaba."

Daga haka ya fa

ɗ

a ban

ɗ

aki. A gigice Hajiya Zeenat ta miƙe ta fice zuwa

ɗ

akinta. Wanka ta yi a gurguje ta shirya. Kamar yanda ta zata hakan ce, ya shirya da zummar zuwa ofis. Bai yi mamakin shiri

n da ta yi ba illa murmushi da ya yi, abin kam ya ba shi dariya. Wannan bibiyar bai san kuma ta mece ce ba duk da a bayan ma tana yi mishi don wani sa'in kamar daga sama haka yake ganinta a ma'aikatarsu.

Ya shirya suka fita tare, ita ke tuƙi don a

cewarta za ta fita daga nan duba Hajiya Batool ba lafiya, bai damu da gasken take ko a'a ba. Ya dai amsa zuciyarsa a

ɓ

ace.

***

Tuƙinta cikin nutsuwa take yi, yau gaba daya ta makara a dalilin zazza

ɓ

in da ya kama Ansar sai da ta kai shi asibiti tuku

nna ta maida shi gida. Ta so ta ƙi zuwa sai dai hakanan ta daure tunawa da aikin duba wasu files na Tax.

A harabar wurin parking ta ajiye motar ta ƙarasa ciki. Ko zama ba ta kai ga yi ba wayar dake saman tebur ta

ɗ

au ƙara, tsuke fuska ta yi gami da ja

n tsaki ciki-ciki. Tun sadda suka yi haka da Chairman ta ƙi jinin abinda zai sa ta ha

ɗ

u da shi sai dai ba yana ta iya. Wayar ta

ɗ

aga da sallama, ya amsa gami da ba ta umarnin ta je. Dire wayar ta yi ta ajiye jakarta ta fita bayan ta gyara zaman hijabinta.

Yana zaune da manyan kaya har da babbar riga, idanunsa sanye da gilashi yana danna laptop. Shigowarta yasa shi kallonta.

'Ban yafe ba.' Ta furta a ƙasan ranta. A fili kuwa gaidashi ta yi a ladabce, ya amsa yana wani washe haƙora. Bayan gama jin

dalilin da yasa ba ta shigo da wuri ba ya gangara kan abinda ke cin ransa. Chairman ke kiran yana sonta, dama tuni ta riga ta gane.

"Ke ba yarinya ce karama ba, nasan kinsan me nake nufi kike kaucemin. Wallahi na gaji, bani da burin da ya wuce na aure

nki a yanzu Ramlat. Don Allah kar ki ce za ki ƙi. Na miki alƙawarin gidanki daban, ba zan ha

ɗ

aki da matana ba."

Ya kammala surutansa tana sauraro, ƙarshe ta soma da ba shi hakuri.

"Inada wanda zan aura don har anyi magana."

Wata dariya ya k

ece da ita, hatta ita Ramlat sai ta ji maganar nata banbarakwai, ta kara hade fuska.

"Haba Hajiya Ramlatu, yanzu fa na gama fadamaki ke ba yarinya ba ce. Wane sokon ne zai yi gangancin tsallake sati biyu ba'a

ɗ

auka muku aure ba? A'a ban yarda ba gaski

ya. Nidai ki kar

ɓ

i ƙoƙon barata ki ba address da kanki a ganina zai fi mana mutunci."

Ta yi shiru, ya ci gaba da magiya kamar ba Chairman mai cin magani a gaban staffs ba, haka ba don ranta ya so ba ta mishi kwatance. Ranar kowa ya kalleshi yasan yana

cikin farin ciki marar misaltuwa.

Koda aka tashi, kai tsaye tsohon department din da take ta ziyarta. Ta kuwa ci sa'a duk suna ciki, aka gaisa ba ta ko bi ta kan Halima mai amsa gaisuwar ciki-ciki ba.

"Yanzun nake shirin shiga wurinki. Ƴar hal

ak kin ƙi ambato."

Ta kai duba ga Naja'atu Azare mai wannan batu, suka yi dariya. Takardar gayyatar biki ta fiddo daga jakarta ta miƙa mata. Murmushi sosai Ramlat ke yi har fararen haƙoranta na bayyana.

"Kai na ji dadi sosai wallahi, ki ce abun

ya zo. Allah Ya nunamana, Yasa muna raye." Aka amsa da Amin.

Hira ta tsaya yi a karshe suka dunguma gaba daya matan suka fita, Halima har lokacin fuskarnan ba fara'a.

"Wai ke me akai miki kike ta cin magani?"

Saudat ke tambayar tana duban

ta.

"Ba komai, sai Allah Ya kaimu."

Daga nan ta yi gaba ta bar su.

"Wai nikam Ramlat kamar dai akwai wata a ƙasa tsakaninku da Halima, na lura duk sadda kike wuri ba ta fiye kaunar hakan ba." Samira ke wannan maganar tana duban Ramlat. Ita

kam murmushi kawai ta yi, tana ji suna fa

ɗ

in rashin kyautatawar Halima a lokuta da dama ita dai ta musu sallama ta nufi inda ta yi parking. Idan da sabo ya ci ace dama ta saba da halinta. Murmushi ta yi da wani bahagon tunanin da saƙe-saƙen zuciya ke jefaw

a

ɗ

an adam ya ziyarceta, wato ace ta yarda da auren Chairman, Allah Kadai Yasan irin kiyayyar da za ta fuskanta daga Halima. Ba ma daga gareta kawai ba, har da yawa cikin matan wajen.

***

Zaune gaban Boka Gora, Hajiya Zeenatu ce da Hajiya Batool ko

wannensu rai a

ɓ

ace.

"Shekaru sama da goma muna tare da kai, kar ka yi mana haka. Ka taimakemu ka kula da damuwarmu. Bamu da wanda muke da shi da zai share hawayenmu face kai." (Wa'i'yazubillah)

Gora ya yi wata dariya ta shai

ɗ

anun da suka riƙa k

afin ya

ɗ

aure fuska tamau. Ya kwalalo musu manyan idanuwansa da suka sha kwalli.

"Kar ku rainamin hankali! Wa ya fadamaku zan kasa sanin kun yi doguwar tafiya har wata ƙasa don a yi muku asiri? Cin amanar da zai biyo bayan dukkan taimakon da na yi muk

u a baya kenan! Yanzun da ku ka zo me kuke so nayi bayan komai ya warware! Komai ya lalace! Ke Zeenatu! Ki fara tattara kayanki ki bar ƙasarnan don asirinki ba zai je ko'ina ba sai tonu! Ita dai yarinyar da na garga

ɗ

eki a kanta, ita ce silar rushewar dukka

n ayyukanki! Ke kuma Batulu! Nan ba da jimawa ba,

ɗ

anki zai zo da batun ƙarin aure! Auren da zai rushe duk wani asiri da kika yi tsakaninsa da matarsa! Anan ne duk abinda kika binne zai fito fili muraran!"

"Ƙarya kake! Wallahi ƙarya kake! Dama na fa

ɗ

a

maki kar mu zo wurinsa!"

Hajiya Batool ke maganar jikinta har yana

ɓ

ari, fuskarnan wacce man bleaching ya maida jawur, sai ƙara kyalli take. Ita kuwa Hajiya Zeenatu idanun kamar an watsa barkono. Ba ta san hawaye ke fita daga idanunta ba sai da ta ji

suna kokarin shigewa bakinta. Shi kuwa Gora banda wata shegiyar dariya ba abinda yake yi don ko ka

ɗ

an kalaman bai

ɓ

atamasa ba, ya saba ganin irin wannan hauka da jahilcin na mata.

Tsawa Hajiya Zeenatu ta dakawa aminiyarta ganin gaba

ɗ

aya ma ta ƙi m

aida hankali ta nutsu su nemi mafita. Ita da take da tashin hankalin rasa miji irin Hussein ba ta yi gigitar da Hajiya Batool ta yi ba. Ta sa mayafi ta sharce gumi idanunta a kansa.

"Mun tuba, wallahi mun tuba ba zamu ƙara sa

ɓ

awa umarninka ba. Ka taim

akemu Gora, a wannan ga

ɓ

ar idan ka ce za ka bar mu, ba wanda zai tsira."

Ya ci gaba da kallon ƙasar da ke shimfi

ɗ

e gabansa yana ƴar dariya gami da gyara hannun babbar rigarsa.

"Akwai tsada..."

Bai ma kai ga ƙarasawa ba duk suka tari numfash

insa.

"Zamu biya ko nawa ne, wallahi ko duka abinda muka mallaka ne."

Ya jinjina kai, kaf ba wacce bai san halinta ba a cikinsu. Yana da karatun kowaccensu don tun ana damawa da su a siyasa da bariki yake tare da su. Maida hankali kan ƙasa ya yi

can kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login