Showing 33001 words to 36000 words out of 267381 words

Chapter 12 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

85

laifin komai akan Ummul da bak’in k’addarar da yai ma rayuwarta dabaibayi.”

Asshe tai saurin k’arisowa ta dakatar da ita.

Umma ta d’ago ta dubeta sai ta fashe da kuka “Wllhi lafiyata k’alau ina cikin h

ayyacina. Sun kasa gane banida wani buri da ya wuce naga Ummul a d’akin mijinta. Toh meyasa Tani zata d’aura alhakin ciwon Malam akaina da Ummul.?” Taci gaba da rera kuka irin na wanda damuwa ya masa dabaibayi.

Asshe ta janyo farar kujera a gefe ta zauna

tana duban Matar “Sunana Hajiya Asshe, mun bigeki da mota akan hanyarmu.”

“Yaya Tani ce tace lallai lallai sai na nemo kud’ad’en da za’ayi ma mijinmu jinya idan har ina so na sake ganinsa. Ta nad’i sautin muryata cikin waya itada Badi’a sunce ko Kotu akaj

e ya iashesu Hujja.”

Asshe ta zuba mata idanu jin yanda taketa maganganu marassa ma’ana. Labarun da yafi kama da wanda ke cikin depression. A hankali ta d’an jinjina kai ta dubi Matar “Akwai yanda yake miki ciwo ne. Kina so na kira Likita.?”

Umma ta girg

iza mata kai alamun a’a”Baiwar Allah ni fah lafiyata lau. Yaya Tani ce ta yanka ragon hauka ta d’aura mun dan kawai Ummul ta kasance ‘yata.” Sai ta d’anyi fasali ta kuma duban Asshe “Amma wacece ke.?”

Asshe ta k’ura mata idanu tana karantarta sai tace “To

h ma sha Allah. Tinda kince babu yanda yake miki ciwo.” Tai fasali dan sosai take so taji labarin Matar musamman da taji abubuwan dake fita bakinta shan cikin Matar bazai mata wahala ba “Ki kirani maganin matsalolinki.!” Ta matso had’ida d’aura hannunta sa

man na Umma “Ki yarda dani zaki iya sanar dani duk damuwarki. Ni ba muguwa bace nasan zaki fahimci haka tinda bayan bigeki da mukayi bamu k’yaleki ba saida muka tabbata mun d’aukoki mun kawoki asibiti. Kuma ban barki ke kad’ai ba har saida na ajiye wacce z

ata kula dake. A nan muka shigo da yarona kikaji yana cewa kar mu kyaleki har sai mun tabbata kin isa ga ahalinki lafiya. Wann kawai ya isheki ki yarda mu mutanen k’warai ne ba masu cutarwa ba. Kuma a yanda yanzu duniya ta koma babu yarda tinda har ni nayi

shahada na yarda dake ya kamata nima ki d’auki duk yarda ki bani. Watak’ila Allah ne ya dubeki ya had’aki da maganin matsalolonki.”

Da mamaki Umma Ke dubanta “Maganin matsalolina ni Suwaiba..?” Tai maganar tana nuni da kanta. “Baiwar Allah anya kaw kinsa

n matsalolina..? Ai inaji kaf fad’in garin Kano da kewaye babu matar da ta kaini matsaloli tinda har na kasance mahaifiya ga Ummulkhairi.!”

Asshe ta kuma gyara zama cikin son jin taji komai “Wacece Ummulkhairy.?”

Umma ta kamo bakin zaninta tana share haw

ayen dake kuma zubo mata “Ummulkhairi, ‘Yata da na mata lak’abi da Uwar alkhairi..! ‘Yata da naci mata buruna da dama.” Ta kuma duban Asshe sai ta girgiza kai wasu hawayen na kuma gangaro mata “Amma babu buri guda d’aya da ya cika. Kinsan dalili..?”

Asshe

da ko kifta idanu batayi saurin girgiza kai tai alamun a’a.

Umma taci gaba “Sabida mutane sun canfa mun ita.. Duk namijin da yazo neman aurenta guduwa yake. Kodai wani abu ya gifta a fasa Auren. Amma fah dukda wann guje mata da mazan keyi basu fah fasa n

eman aurenta ba. Kinsan meyasa..?” Tai tambayar murmushi mai ciwo saman fuskarta kafin taci gaba “Sabida Ummul d’ita tubarkallah ce san kowa k’in wanda bai samu ba.” Sai kuma ta fashe da kuka “Amma meyasa ta kasa Auruwa..? Meyasa duk masifa da nake fuskant

a a nawa gidan Auren ta dalilinta ne.? Meyasa maza ke guje mata. Meyasa k’addararta yazo a haka.” Ta k’arashe cikin gunjin kuka.

Asshe ta kamo hannayen Umma cikin nata tana k’ok’arin kwantar mata da hankali “Ki daina kuka. Shi Aure lokaci ne. Baya duba m

atsayi ko kyaun halitta. Wata da komai ta rasa miji wata ba komai Allah ya bata. Shi Aure kaman hab’o ne da zaran lokaci yayi sai kiga anyi..”

Cikin zuciyar Asshe fal mamaki. Ganin abun take kaman almara. Abinka da mai b’atacciyar zuciya sai ta kuma gask

gata aikin bokansu. Gashi tin ba’aje ko ina kaman sun had’u da makarin sihirin dake jikin Haidar a sauk’ak’e. Sai ta kuma yarda gaskiya Malaminsu ya fad’i ta mance cewa wann duk zai iya zama jarabawa daga Ubangiji mai komai ya baka abinda kake nema d’in a

kan gab’ar da kake nema. Wani shikenan sai ya kuma dulmiya cikin b’ata. (Allah kai mana tsari da shirka. Ameen)

Ta saki murmushi tana duban Umma “Ummulkhairinki zatayi Aure. Aure na bajinta. Aure irin na kece raini. Auren nuna ma duniya.!”

Umma ta dubeta

da mamaki. Sai ta girgiza kai tace “Anya kuwa Ummul d’ina nada rabon Aure a wann duniyar.?”

Asshe ta murmusa “Idan har kika aminta dani Ummul d’inki zatayi Aure..” Tai maganar cikin jaddada kalamanta.

Hilal ne yai knocking ya lek’o jin shirun yayi yawa

. Nan ya hangi mahaifiyarsa da patient d’in kaman sun jima da sanin juna. Mamaki ya cika Hilal. Ya d’an girgiza kai yana mamakin saurin yarda da juna da mata keda shi saikace ba Ammi bace ta gama cewa su tafi su kyale matar. Bai gama mamaki ba saida yaga A

mminsa sun fito tareda Matar dan dama da ya shiga tace masa bari likitan yazo ya masu sallama tinda taga isowar motarsa. Shidai Hilal haka ya tuk’a su suka nufi gida tareda Matar dasu Ammi suka bige wacce ta zamto bak’uwar Ammin tasa.

Suna isa gida Hilal

ya tareta “Ammi Wai meke faruwa ne. Meyasa kika taho da matar nan.. Ammi I thought danginta za’a nema.. Nowadays fah mutane ba abun yarda bane. This whole thing zai iya zama shiri bigeta da kukayi, kaita asibiti da duk wani maganganun da zata sanar dake. A

mmi yanzu fah har gida ake ture a sace mutane. Ammi Abba sanannen mutum ne a garin nan. Iyalansa zasu iya zama target.”

“Kai dallah rufe min baki. Duka duka yaushe ka sauk’a k’asar balle ka fad’a min abinda Ke faruwa cikinta. Nafika sanin meke faruwa. In

a zuciyar taimakon taka? Inji kai ka fara cewa we shouldn’t abandon her. Toh Shiyasa na taho da ita. Kuma ko mahaifinka yazo gidan nan ba ruwanka kar ka sanar dashi komai kaji na fad’a maka.”

D’an girgiza kai yai “Fine, yanda kikace Ammi.” Hilal yasa kai

yai shigewarsa.

Yana shigewa ta d’aga waya tai dialing wani layi. Ana d’agawa ta soma fad’in “Hello Yunusa kanajina. Zan turo maka information kan wata mata. Yanda take zama sunan mijinta da sauransu. Inaso ka gudanar min da binciken k’wak’waf kan ahalint

a da abinda Ke faruwa dasu. Bana so a d’auki lokaci. Ayi komai cikin gaggawa.”

**

A can b’angaren su Ummul kuwa hankulansu yakai matuk’a wajen tashi. Dik yanda ake tunanin za’a sami Umma anje ba’a sameta ba. Hisham kaw da shi ake aiwatar da komai tuni s

un bada cigiyan Umma.

Yai k’uri yana duban Ummulkhairy dake ci gaba da kuka da gaske wann karon. Duk k’ok’arin ganin bata d’aura alhakin iftila’in dake faruwa cikin ahalinsu akanta ba saida zuciyarta ta raya mata hakan.

Da wanne zasuji? B’acewar mahaifi

yarsu ko kuwa mahaifinsu dake kwance gadon asibiti wanda har wann lokacin bai san yanda yake ba. Ga likitoci sun tabbatar masu idan har treatment d’in da ake masa yaci gaba da failing jikinsa ya kasa amsa then he must have to undergo Cardiac surgery wanda

zaici mak’udan kud’ad’e ga had’arin dake tareda hakan.

Hisham ya d’anyi gyaran murya cikin k’ok’arin kwantar mata da hankali. Amma kaman cewa yai ta k’ara. Ringing d’in wayarsa yaja hankalinsa.

Abokin aikinsa ne kuma amininsa Haidar me kira. Ba tareda y

a bar wajen ba dan baisan barinta ita kad’ai farfajiyan asibitin suke yayinda Khulsum ke can wajensu mama sun hanata koda lek’a Abba ne.

Daga d’aya b’angaren Sautin kuka ne yai Sallama ma Haidar. Ya d’anyi still kafin yace “Wait..What’s that noise.. Whe

re exactly are you..?”

Hisham ya dubeta sanda take k’ok’arin mak’ale kukan nata bayan taji alamun yana amsa waya “You seem to forget things easily nowadays Engr. Ka mance na tafi gida ne.”

Haidar ya d’an d’aga gira yana mai jinjina kai “I hope dai lafiya

ka samu gidan. I mean lafiya ka samu Hajja..?”

Hisham yace “Yeah lafiya..” Ya k’arashe yana mai d’an jan kalamansa.

Haidar ya kuma tambaya “So who’s making that noise.?”

Ciki Zuciyar Hisham ke ayyana isa da jin kan Haidar. Wato bazai iya tanbayarsa

wacece ke kuka next to him ba shine wai hayaniyar me yake ji. D’agowa yai Ya dubi Ummul wacce ke k’ok’arin tsagaita kukan nata. Ya d’an mik’e ya matsa gefe kad’an . Ya saki murmushi mai kyau yana mai d’an rage murya “Let’s call her Someone.. Someone Very s

pecial.. Ka gane I’ll call you back.”

D’an tab’e yai “Let’s talk business.” Yace cikin katse Hisham d’in.

Hisham ya d’an kuma satan kallanta sanda Haidar ke sanar dashi sunada ganawa ta musamman gobe a Kampani. Ya zama dole ya katse hutunsa.

Hisham

ya girgiza kai kad’an “Wait what meeting Haidar.?”

“Tomorrow by 9:00am.. Design Architect Hisham.!” Abinda kawai Haidar yace kenan.

Hisham ya soma girgiza kai cikin rashin yarda “You know I can’t make it to the meeting Haidar.. I mean I’m not the only

design architect in your team...” Bai tsaya d’aukan excuse d’in Hisham ba ya katse kiran.

Furzar da huci Hisham yai yana shafan fuskarsa da tafukan hannayensa. Jiki a matuk’ar sanyaye ya dawo yanda ya baro Ummul.

Ta ya zai barta ya tafi a lokacinda take

tsananin buk’atarsa. He needs to stay.. But what about aikinshi.. Baiso wani yai taking place d’insa. Sun jima suna aiki tuk’uru kan wann project din wanda yake da tabbacin idan ya zama a successful one ba darajan Kampaninsu kawai zai d’aga ba. Zai taima

ka wajen daidaita relationship d’in Amininsa da mahaifinsa wanda a kullum yake burin faruwan hakan. Bayan haka Haidar is counting on him. Abokinsa needs him now. Amma kuma Ummul fah. Shin zai iya barinta ya tafi.? Shin waye zai kyale ciki su biyun.

Sam

eenaAleeyou

📚

*AUREN WATA UKU.!*

*13*





Sameena Aleeyou…✍

🏽

*

Akan idon su Mama Hisham yai ma Ummul sallama ya rakota har wajen Khulsum. Saidai bai sanar da ita batun tafiyarsa ba.

Mama da Azeema ko harma da Badi’a ko k’ifta idanu basuyi. Musamman da

sukaga zankad’ed’en Saurayin dake tare da Ummul. Mama tace “Toooh shi kuma wann d’in wai waye.?”

Badi’a tace “Wa ya sani masu ne Mama. Amma kaman saurayin Ummul..”

Mama ta bige bakinta “A gidan uwar waye ya zama saurayin Ummul. Wann yafi k’arfin Ummul

inaga dai yayi zaton mabaraciya ce ya taimaka mata musamman da yaga tana cikin damuwa.”

Badi’a ta harari Mama yayinda Azeema ke hararar Khulsum tana cika. Lokaci guda ta katse Mama da fad’in “Saurayinta ne mana shine yayi belin wancan k’aramar ‘yariskar a

police station bayan ta mareni.. Wllhi bazata saku ba. Ai na biya kud’in kwananta a cell amma bata kwana ba.. Toh wllhi komawa zanyi ayi duk rikicin da za’ayi. Ni da kaina na lale kud’ad’e na bawa Habibu ya biya ‘yansandan cewa su rufeta ta kwana. Wllhi k

omawa zanyi ko su biyani kudina ko su sanar dani dalilin bud’eta. Ai ko Kotu akaje akwai kud’in mari. Idan har ba biyana akayi ba wllhi rikicin nan bai k’are ba ehe. Ta k’arashe tana mik’ewa fuuu.

Mama tai k’ok’arin dakatar da ita da fad’in “Ke ke.. Ke i

na zaki Azeema..?”

Ko juyowa batai ba Azeema balle ta amsa ta. Saima dialing layin Habib da tai tana k’arawa a kunne.

Mama ta dubi Bad’ia bayan Azeema ta shige. Ta janyota suka keb’e “Yauwa Kinga d’aga waya ki kira Tasi’u yazo ayi maganar sayar da shago

n Malam da d’an sauran abinda Ke ciki. Kinga naji d’azu likitocin nan suna bayanin aikin da za’ayi ma Malam mak’udan kud’ad’e zai lak’ume wanda ko gaba d’aya Kantin da kayan dake ciki aka sayar ba isa zasuyi ba. Kinga kafin Wann shago da abinda Ke ciki tsa

utsayin jinyar Malam ya hau kansu gwara mu dafe su tunda wuri dan bazai yuwu mu zuba d’an abinda zamu samu ma jinyar Malam ba wanda su kansu likitocin k’irdado suke amma ga dukkan alamu ciwon Malam ba na tashi bane.

Bad’ia ta jinjina kai “Kuma ma Mama ai

wanda suka fi cancanta su nemo kud’in jinyar Abba wanda sukai masa sanadin ciwon ne. Ina nufin wancan annobar da uwarta.” Tai nuni da yandasu Ummul Ke zaune.

Mama ta jinjina kai “Alhamdulillahi ina jin dad’in yanda kike fahimta. Maza kirawo Tasi’un.”

T

uni Badi’a ta d’aga wa ta shiga dialing layin Tasi’u mijinta.

Khulsum ta dubi ‘yaruwarta Ummulkhairi cikeda tausayawa “Adda yau d’in fah duka baki saka komai cikinki ba. Dan Allah kiyi hak’uri ki tashi haka nan mu tafi gida yamma ta riga tayi.”

Ummul n

aci gaba da hawaye ta girgiza mata kai “A’a Khulsum bazan iya tafiya gida ba. Watak’ila Umma zata zo nan wajen Abba..!” Tai maganar cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.

Muryar Mama suka sinkayo akansu “Au har yanzu Uwar taku bata bayyana ba. Ta ta

bbata dai Angulu ta koma gidanta na tsamiya.”

Suka d’ago suna duban Mama da Badi’a tsaye kansu sai aika masu kallon wulak’anci suke.

Ummul ta girgiza kai “Mama Umma b’acewa tai bamu san yanda take ba.”

Sai Mama ta shiga tafe hannaye tana salallami “Na

shiga uku ni Tani. Ta nan Suwaiba ta b’ullo..? Ta rasa abinda da zatai sai ta guji Malam sabida jinya ya kamasa ya zama kaya. Watau Suwaiba bazata iya jinyar Malam ba dai shine ta guje ta k’yaleni da wahalar jinya.. Yanzu da zataji labarin Malam ya cika d

ik yanda take zata fito tazo amsa sunar matarsa dan ta amshi rabonta na gado.”

Sai sann Khulsum ta finciki hannunta daga rik’on da Ummul ke mata cikin k’ok’arin dakatar da ita. Sai huci take.

Badi’a ce ta janyo hannun Mama hango mijinta Tasi’u da tayi sa

i buga sauri yake ya nufosu “Muje Mama kar ma kiyi hayaniya dasu balle a ba ma masu gadi hujjar koranmu. Ganin Abba ne sai a k’iyama idan sunada rabon had’uwa a k’iyamar.

Khulsum ta kuma fincika zatabi bayansu Ummul ta kuma dakatar da ita.

Cikin kuka Kh

ulsum ke furta “Haba Adda Ummul. Haba ke kuwa.. Wai dan Allah meyasa kike dakatar dani.? Mutanen nan fah yaren da kawai suke fahimta kenan.”

Ummul ta jinjina kai tana kuma share hawayenta “Abinda suke so kenan Khulsum kiyita biyesu kuna tashin hankali. Ki

tuna Abba dake kwance cikin asibitin nan. Ki tuna halinda yake ciki. Sann ki tuna Umma da halinda take ciki. Dan Allah ki daina biyewa Mama da yaranta. Allah ya fisu Khulsum. Mu fawwala masa komai da sannu zaiyi ikonsa akan kowa. Da sannu zai ba ma Abba l

afiya ya tashi kafad’unsa kuma suna kallo. Muci gaba da yi masu add’uan shiriya har kullum domin su d’in ahalinmu ne komin lalacewarsu. Muje Khulsum, mu tafi gida mu kai kokenmu ga Rabbil izza wanda shike yaye dukkannin damuwa ya kuma kawo sauk’i da maslah

a.” Tana ida fad’in haka taji natsuwa ya sauk’a cikin zuciyarta. Jiki a sanyaye suka fice daga asibitin.

**

Tasi’u yau harda risinawa yake gaida Tani. A mutunce yau d’in ya fito masu dan batu ake na kud’i.

Mama kaw sai hura hanci take dan ba Wai ta ma

sa afuwan musguna ma ‘yarta Badia yake bane. Yanzun ma dan Badi’an ta nace ne sai an sako Tasi’un cikin hidiman, ta tabbata amfani yayi da son da Badi’a Ke masa ya saye zuciyarta da kalamai har ta aminta dashi. Dan dai ita kam har yanzu bawai ta yarda da t

ubansa bane. Tasan tuban D’anmuzuru ne. So yake a bawa Badi’a kasonta su lak’ume tare da zaran kudi sun k’are yaci gaba da mata iya shege.

Ta dubi mai sayen shagon da Tasi’u yazo dashi dan tinda Badi’a ta sanar dashi cikin waya ya taho da mai cinikinsa d

an dama tuni ya tanadi mai saye tinda aka soma batun.

Mama sai cika take tana batsewa tana ciniki da mai sayen shago. Tasi’u yana daga tsakiya a matsiyinsa na dillali sai gyaran waje yake. Mama ta narka masa harara ganin zak’ewarsa.

“Amma dai Tasi’u ka

tab’a dillanci ko..?” Cewar Mama tana dubansa a dak’ile.

Tasi’u ya Washe baki “Yo Mama banda abinki meye ba’a tab’awa ai duk abinda aka samu bugawa ake baka san ta yanda wutan zai kawo ba.” Sai faman Washe baki.

Ita kaw Hajiya Badi’a sai karkad’a k’af

afu take tana Jin kanta. Daga yanzu ta samu makamin rik’e Tasi a hannunta. Tinda zata samu kud’i abinda yafi naira dubu d’ari aiko sai yanda tai da Tasi dole ta zama itace mijin itace mai basa doka da order. Tin yanzu ma biyayya yake mata balle ta dafe kud

’ad’enta.

Aka tsaida cinikin Kantin Abba. Mai saye yace gobe suzo da takardu a saka hannu.. Nan fah Mama ta soma zare idanu dan bata San yanda ya aje ba. Tasi’u yace wann ai ba abun tada hankali bane washe gari zaije yai sabbin takardu a gama komai. Yan

da yake ladabi wa Mama da Badi’a kai ka ranste yaron gidansu ne

**

A can station Habibu mijin Azeema sun keb’e da sergeant d’in da suka tafi sukai arresting Khulsum dan dama budurwarsa ce, ta cika tayi fam sai hura hanci take “Ni fah ba matsala ta bace

dan an mari matarka. Yo a kasheta ma mana ai banida asara. Ni wllhi ba don ka min alk’awarin aure ba wllhi kaji na ranste da bazanje nai arresting kowa ba. Kuma kafi kowa sanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login