Showing 195001 words to 198000 words out of 267381 words
labarin tsaffin samaruka
n Ummul. Yanzu gashi kinsa mutumin na miki wasu tambayoyi. Haba Azeema mutumin nan fah ji yake kaman Ummul ta kufce masa kenan tinda sun rabu.. Idan baki basa k’warin gwiwa ba bazaki basa dalilin rura wutan tashin hankalinsa ba.”
Azeema tai murmushin da y
afi Kama da yak’e ta dubi Haidar tace “Wann ai tsohon labari nake sanar dakai Yayanmu. Zubairu ya jima da auren ‘Yaruwarsa wacce ake so a had’asu tuntuni..” Ta shiga tura foodflaks din abincin da aka kawo masa tana fad’in “Kaci abincinka Sirkinmu. Tuwon n
an idan yai sanyi babu dad’i.”
Badia ta harareta tana girgiza Kai ta janyo Azeema suka bar wajen tana rad’a mata “Kedai wacce tai jegonki bata farse wann bakin naki ba.”
Azeema ta kuma kame bakin ta tana fad’in “Wllhi na sani… Duk yanda akai Inna Dije c
e.” Suka dara a tare Badia tana fad’in Allah ya shiryi Azeema.
*
Kafin ya tafi saida ya k’ara tuntuban Khulsum ko ta sake samun kira daga Ummul. Khulsum tace bata sake kiranta ba. Su kansu saida Haidar ya basu tausayi. K’arshe haka ya hak’ura ya bar gari
n ba don yaso ba.
**
Idanunsa na duban window yake ci gaba da fad’in “It’s been three months Hisham. Wata uku babu Khairy.. And Dareen is nowhere to be found. I feel lost, tiny and insignificant in this world..”
Hisham ya sauk’e ajiyan zuciya “I belie
ve everything happened for a reason.” Ya dan furzar da huci had’ida girgiza Kai “I have never met your wife Haidar.. Amma abinda na kula shine kana k’aunarta sosai, because ban tab’a ganinka cikin yanayi na soyayya irin haka ba..” Ya dan numfasa “Kuma kod
a ka kasance mutum da bai cika bud’e al’amransa ba jikina yana bani ba k’aramin abu bane ya shiga tsakaninku.”
Sai Haidar ya dubesa amma baice komai ba.
Hisham ya jinjina Kai kad’an “Whatever is the case Haidar, know that I’m here for you.. And you can
always count on my support.” Ya jinjina Kai alamun tabbatarwa. “Idan zakaje kaci gaba da Neman matarka ni zance naci gaba da nemar maka Dareen. Ko ba don ka hukunta Dareen ba sai dan D’anka dake cikinta. Ko ya kayi Haidar, that child she’s carrying is stil
l yours.. Kuma baida laifin komai.. Bazaka hukunta shi da laifin mahaifyarsa ba.”
Haidar ya tsaresa sosai da ido wann karon sai ya girgiza Kai yace “Are you even sure that child is mine.?” Shiru Hisham bai amsa shi ba saima tunani da ya soma cikin zuciyar
sa ‘Bastard! Zaka sheganta wann D’an kaman yanda Ubanka ya shegantani a ciki.! Kai din baka rage ma Ubanka komai ba Haidar.’
Hisham ya sinkayo muryar Haidar sanda yaci gaba “Wha if babu wani ciki. What if k’arya take, tinda iyakacin tarayyata da ita k’ary
a ne kawai.!”
Hisham ya dan furzar da huci yana mai d’aga gira sama “Bazan k’i maka ba. Kuma bazanga laifinka ba.. Because you’ve been fooled and betrayed. Amma Kai tunani Haidar.. Kayi rayuwa na Aure da Dareen koda ace rayuwar ta k’arya ce. You were once
husband and wife.. You cannot deny that. So ba abin mamaki bane idan tana d’auke da gudan jininka.. I mean, if you neglect that child zai tashi ne da tsanar koma waye mahaifinsa.. Meyasa ‘ya’ya zasu biya kuskuren da iyayensu suka aikata..? Hakan ba adal
ci bane.” Yanda yake maganar tamkar yana digging ma Haidar past d’insa ne.
Hisham yaci gaba “You can’t let that child pay the price Haidar.. You know exactly how it feels mutum ya girma babu soyayyan iyayensa. You can’t make that child a victim. You can’
t let that happen to your own child.!” Ya k’arashe cikin tsananin k’warewa tareda tono ma Haidar bayansa. Yanda ya girma da tunanin iyayensa basa sonsa duk sabida wani kuskure da mahaifyarsa ta aikata. Ya rintse idanunsa yana jin kamar dai duniyar ta dad’a
juye masa. Sann gaskiya ne abinda Hisham ke fad’i. Because shi Kansa Haidar d’in was once a victim. Bazai bari tarihi ya maimaita Kansa cikin ahalinsa ba.
Hisham ya tsaresa da ido cikin zuciyarsa cewa yake ‘Kai da ahalinka bakuda daman yin wani farin ci
ki a wann rayuwar. A lissafi Ummul ta cika watanni uku tin bayan da k’addararren Aurenku ya k’are.. Hakan na nufin ta fice daga iddarka.. Ni kuma yanzu zan tafi na gina nawa soyayyar cikin zuciyarta…All my sacrifices are finally going to pay off’ A fili k’
arasawa yai ya dafa Haidar kad’an fuska fal damuwa. Cikeda kulawa yake furta “Haidar bazan Barka ka koma irin rayuwar k’uncin da ka fuskanta a baya ba. Ka tafi ka nemo matarka yanda ta shiga ta fita.. Ni kuma zan tafi na nemo maka Dareen yanda ta shiga ta
fita ko dan wann innocent soul d’in dake cikinta.” Ya k’arashe damuwa sosai saman fuskarsa.
Haidar bai iya ce masa komai ba sai shafe fuskarsa da yai da tafukan hannayensa.
A haka Hisham ya tattari files d’in da ya shigo dasu ya fice fuskarsa d’aukeda m
ugun murmushin da ba kowa ke iya fahimta ba. Cikin zuciyarsa yaci gaba da ayyana Ummul tasa ce a halin yanzu.
Da wann farin cikin Hisham ya taho garin Bauchi zuciyarsa fari k’al da nufin ya tafi Neman Dareen a zahiri kuma wajen Ummul yazo da niyyan k’ull
a soyayyarsa.
Babu Wanda yasan da zuwan nasa. Hajja batai mamaki ba dan dama ya saba mata irin wann zuwan na bazata. Saidai ta kula wann karon da wani irin farin ciki yazo maras misaltuwa.
Suna cikin gaisawa da Hajja yake tanbayarta “Hajja nace ina U
mmul kuwa..?”
Bata kaiga basa amsa ba suka hango Ummul da fitowarta kenan daga babban parlorn da Hajja ke sana’arta na d’inki, nan suka hangota tana tafiya da kyar tana dafe garu tana kame kanta dake matuk’ar juya mata.. Kafin suyi wani aune jiri ya kus
an kaita k’asa. Hajja ta nufeta hankali tashe ta tallafota tana ambaton sunanta dan tuni idanunta sun soma juyawa.
SameenaAleeyou
📚
*AUREN WATA UKU..!*
*51*
*©
️
Sameena Aleeyou…✍
🏽
*
Bud’e ido tai sai gani tai fanka na wainawa saman kanta, t
a yunk’ura zata tashi sai taga igiyar drip daure hannunta. Nan ne ta fahimci saman gadon asibiti take. Ta waiga kad’an sai taga wani mutumi da ko shakka Babu Likita ne tsaye daga gefe hannunsa rik’eda file kansa kife kaman yana rubutu.
Hankalinsa naga ab
inda yake ta sinkayo muryarsa yana mata sannu.
Ya k’arada “Malama Ummulkhair right.?” Ta jinjina kai kad’an.
“Kina Jin wani pain..? Akwai yanda ke Miki ciwo.?” Ya k’arashe yana mai janyo kujera had’ida zama gefen gadon.
Ta d’an girgiza Kai sai ta dafa
kanta kad’an “Kaina na d’an juya min sann yana ciwo.” Sai ta dan tab’a gefen cikinta kad’an tace “Ciki na na ciwo kad’an ta gefe.”
Ya jinjina kai “It’s normal to experience such pains in early stage lokaci zuwa lokaci.”
Bata gano abinda yake nufi ba a
mma tana Jin heartbeat dinta na k’aruwa da sauri. Kaman yasan tana jiran Karin bayani ya soma jero mata wasu tambayoyin.
“Amma… Yaushe rabonki da kiga al’adarki.?” Yai tambayar fuskarsa na nuna alaman tsananin kulawa.
Sai ta kalleshi da mamaki. Ganin ir
in duban da ta masa yasa shi d’an sakin murmushi “Kinga kar ki ba ma tambayar wani manufa na kula kaman.. Baki fahimci meke damunki bane bayan kin d’ebe watanni cikin yanayin..”
Kanta ya kuma k’ullewa.. Ta d’an girgiza kai “Dr.. Meke faruwa dani..? Dan Al
lah Ka mun bayani..” Ta fad’i duk a d’an tsorace
Jinjina kansa yai yana kuma tabbatar da hunch d’insa. Sai Ya dan girgiza Kai kad’an yace “Kar ki damu ba wani abin tashin hankali bane.. Amma ki amsa min tambayata first. When last kikaga menstrual period
d’inki.?”
Sai ta soma tunani.. Ita zata iya cewa damuwa da tashin hankalin da ta tsinci kanta ciki yasa ta ma mance wani abu wai shi menstrual period. Ta girgiza kai tace “Ni.. ni … Ni ban sani ba..” Ta basa amsa tana d’an kauda fuskarta.
Dr ya rage g
irman idanunsa had’ida girgiza kai kad’an cikeda mamaki “Is it possibile.?”
Ta d’an dubesa fuska d’aukeda alamun k’osawa wann karan dan Likitan Ya fara hawa kanta da tambayoyinsa marassa kan gado.
Sai Ya dan tab’e baki kad’an yace “Ina mijinki.?”
Tamba
yar ya kuma tunzurata, ya fama mata gyambon dake cuziyarta, ta kuma jin wani k’atutun bak’in ciki ya tokare mata mak’oshi. A kufule tace “Bani dashi.!”
Sai ya kuma girgiza kai cikeda mamaki “Baki dashi kuma..? I.. thought mutumin can da ya kawoku keda mam
arki mijinki ne..”
“Na fad’a maka bani da miji.. Ni Ummulkhairi banida wani miji..!” Ta fad’a kaman zata fashe da kuka.
Likitan ya dan jada baya kad’an yace “Ok.. Ok easy..” Sai ya soma bud’e file d’in dake hannunsa yana duban file d’in yake fad’in “Amma
sakamakon gwaje gwajen da muka Miki Ya tabbatar kina d’auke da juna biyu har na tsawon watanni uku which is why kikaji Ina miki tambayoyin da nake miki.. Amma sai na fahimci wann shine karonki na farko shiyasa Har juna biyun Ya shafe tsawon wann lokacin a
jikinki tareda kin fahimta. Although pregnancy is not typically visible at 3 months, especially in a first pregnancy.. Most women begin to show in the second trimester, around 16- 20weeks.. However,…” Aya yai ma kalamansa sanda ya d’ago yana dubanta dan i
danunsa naga file din dake rik’e hannunsa yaketa wad’ann bayanan da sam babu mai saurarensa balle fahimtarsa ga dukkan alamu.
Abu d’aya zata iya cewa taji cikin kalaman nasa shine juna biyu bayan wann kalman bata sake fahimtar komai ba…
Dr ya dan girgiza
kai yana dubanta “Hello.. Are you with me..?” Ya fad’i cikin k’ok’arin dawo da ita daga duniyar da ta b’ace ciki.
Dubansa take tana girgiza kai tana jin kaman duniyar ke juya mata “Ju..juna.. biyu..!!” Ta fad’i labb’anta Har rawa suke.
Ta kuma girgiza k
ai cikin rashin fahimta “Mai.. Mai hakan.. yake.. Nufi Dr.. Ni.. Ni Ummulkhair.. Juna biyu..?” Ta k’arashe tana nuni zuwa gareta hannunta na matuk’ar rawa haka ma muryarta.
Dr ya jinjina Kai alamun tabbatarwa “Of course. You are 3months pregnant.”
Sai ta
soma girgiza kai “A’a.. A’a baku gwada daidai ba Likita… Dan Allah ka sake gwadawa.. ni banida komai..” Cikin tsananin damuwa mai gauraye da tashin hankali take maganar.
Dr ya shiga nuna mata sakamakon yana fad’in “Gwaji na jini mukayi wanda ya tabbatar
da hakan.. Ina shawartanki da ki rage stressing kanki sann ki rage shiga damuwa ko dan lafiyarki da lafiyar abinda ke cikinki… I’ll prescribe some medications for you.. Sai a kiyayesu..” Ya k’arashe yana k’ok’arin mik’ewa.
Kuka ta fashe dashi tana girgiz
a kai “A’a Dr.. A’a..Dan Allah ka cire mun cikin.. Wllhi bana so.. Dan Allah ka ceceni..”
Shima wann karon a kufule yake dubanta “Bakiyi kama da maras Kamun kai ba da nace ta wani hanyar daban kika samo.. Amma ko ta ina kika samu ki sani bama cire ciki a
nan.. Excuse me..” Ya k’arashe yana k’ok’arin ficewa yayinda Kukan Ummulkhairi Ya karu Wanda hakan yasa Hajja dake daga bakin k’ofan d’akin shigowa ba shiri.
Dr ya dubeta “Yauwa.. Akwai magunguna da zan rubuta mata dan Allah sai a kula ta sha su akan kari
..”
Hajja ta jinjina kai “Eh akwai yarona da Ya kawomu yana waje.. Zai sayo magungunan.” Bai kuma tsayawa sauraronta ba ya fice.
Hajja Tai sauri ta k’arasa ga Ummul dake cazgan kukan kamar wacce aka aiko mata sak’on mutuwa.
“Ummulkhair.. Jikin ne..?” T
a tambaya cikeda damuwa.
Shiru Ummul bata bata amsa ba sai kuka da take tana girgiza kai.
Hajja ta dubeta sai ta dubi takardan dake aje saman drawer dake gefen gadon. Nan taga pregnancy test ne kuma ya nuna positive. Ji Tai tamkar jinin jikinta Ya k’afe.
Taji kaman an d’add’aure jijiyoyin jikinta.. Ummulkhair juna biyu ke gareta.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Duk abinda ke faruwa da Ummul tono mata nata bayan yake.. Tamkar dai reputation ne na abubuwan da suka faru da ita shekarun baya.. Dama a ya
n kwanakin taso ta fahimci hakan saidai tayita kore tunanin abin dan guje ma tono nata bayan. Sabida duk abinda zaisa ta waiwayi baya guje masa take. Saidai ga dukkan alamu duk yanda kaso guje ma wani abin sai Ya tono kansa a wasu lokutan..
Hajja ta fad’
a duniyar tunanin abinda Ya faru da ita shekarun baya. Auren ta da Mahaifin Uban cikin Ummulkhair wato Aliyu Maitama kuma mahaifi ga tilon D’anta Hisham.. Sai kuka da muryar Ummul ta sinkayo tana fad’in “Dan Allah Hajja nikam bani son wann cikin.. Dan Alla
h kar ki bari na haifosa.. Dan Allah kisa likitocin nan su ciresa.. Ki taimake…” Batakai aya ba Hajja Tai k’arfin halin tattaro k’arfinta ta rufe bakin Ummul da k’arfin gaske “Kul. Ko da wasa kar na sake jin kalamai masu kama da wann daga bakinki Ummulkhai
r.. Da iliminki da karatunki.. Da addinininki..? Haba Ummul this is not like you.. Ba haka Ummul d’in da na sani take tunani ba.. Mai hak’uri a duk halinda ta tsinci kanta ciki.. Kinyi hak’uri a lokacin da kika fuskanci k’alubale na JINKIRIN Aure da fashe
fashen Aure. Kin karb’i k’addararki kuma in sha Allah kin dace da jarabawa. Toh ki sani yin Aure ba yana nufin k’alubale da jarabawa Sun k’are bane. A’a wani sabon babi na karatu da jarabawa ne rayuwa ta kuma bud’e miki.. Shi kansa zaman auren karatu ne ka
man yanda mutuwar Auren zai iya zama jarabawa a gareki. Ki sani ba akanki aka fara mutuwar Aure ba haka zalika ba akanki za’a daina ba… Kowa da yanda rayuwa take zuwa masa.. Kowa da irin k’addararsa a rayuwa. Kowa akwai abinda aka sanya masa jarabawarsa da
k’alubalen sa cikinsa.” Ta dan numfasa sai Ta kamo hannayen Ummul cikin nata wacce Har lokacin hawaye ke kwaranya mata “Duk abinda kikaga Allah Ya hukunta ma bawa, Allah yasan dalilin da Ya k’addari aukuwar hakan.. Taho nan..” Ta k’arashe tana rungumo Umm
ulkhairin daga zaune.. Sosai Hajja ta rungumeta zuciyarta fal tausayinta. Cikin zuciyar nata take fad’in ‘Ko ni da suka sheganta nawa cikin ban ciresa ba.. Dan haka Bazan tab’a bari makamanciyar tunani irin wann yayi tasiri a zuciyarki ba.’ A fili kuwa mur
mushi take tana rungume da Ummul d’in “ ‘Ya’ya rahama ne.. Kyauta ne mai girma Wanda Allah kad’ai ke bama wanda yaso cikin bayinsa.. Insha Allahu zaki haifo abinda ke cikinki lafiya kuma zai zamto mabudin alkhairi da sauyin rayuwa mai inganci a garemu baki
d’aya..”
Cak Hisham dake daga bakin k’ofa hannunsa rik’eda ledan maganin da Dr yai prescribing ma Ummul yaja Ya tsaya sakamakon kalaman da yaji na fita daga bakin mahaifiyarsa.. K’iris Ya rage ledan dake hannunsa bai sunce Ya fad’i k’asa ba… Mai hakan y
ake nufi..? Ummulkhair ciki ne da ita..? No.. No way.. Allah yasa ba Daidai yaji ba. Babu wani ciki tattare da ita.. Haidar bazai masa haka ba..! Watanni uku Sun cika ta fita daga iddan Haidar bazai yuwu ace ciki ne da ita ba.. It can’t be… It definitely c
annot be. Bai sadaukar da komai dan ya rasata daga k’arshe ba..! Jikin Hisham yaci gaba da rawa a daidai sanda ya kuma sinkayo muryar mahaifiyarsa tana tabbatar da juna biyun dake jikin Ummulkhair.. Zufa yaci gaba da karyo masa ta ko ina.. Da baya ya soma
komawa ba tareda ya iya shiga d’akin ba.
A nan cikin d’akin kuwa Hajja duk ta zak’u sai d’auki take. Bata san dalili ba amma sai ta tsinci kanta cikin matsanancin farin ciki gameda samuwar cikin. Ji take tamkar zatayi jika nata na kanta dan ‘ya ta d’auki
Ummulkhair koda a zahiri abinda ke cikin nata Ya kasance tsatso kuma jika ga mutanen da suka zamto silan durk’ushewar rayuwarta.
A b’angaren Hisham kuwa tashin hankali maras misaltuwa Ya shiga. Bayan dawowarsu gida can k’uryar d’aki Ya k’ule ya shiga dun
k’ule hannunsa yana sakin huci.. Ya bigi garu da hannun nasa yana furtawa a hankali cikin karaji “Damn you..! Damn you Haidar..! How dare you..!How could you do this to me.!” Yaci gaba da sakin huci gumi na tsartsafo masa. Ji yake da zaiga Haidar gabansa d
a Ya shak’esa da iyaka k’arfinsa. Yana nan a haka wayar Ania Ya shigo masa.. Ya dubi wayar yana ci gaba da sakin huci kaman bazai d’aga ba. Sai Ya koma ya zauna ya janyo wayar ya daga ba tareda Ya daina sakin huci ba.
Yana d’agawa daga d’aya b’angaren Ani
sa tace dashi “Ango ka sha k’amshi.. I know by now ka fayyace ma Ummulkhair irin soyayyarta dake lullub’e cikin zuciyarka.. Watak’ila Har an fara zancen saka muku rana. Toh nima dai Albishir na kira na maka dukda nasan kace ya kamata mu daina kiran juna ti
nda hak’armu na raba tsakanin Ummul da Haidar ya cimma ruwa.. Na kiraka ne na sanar dakai cewa Aunty Kwaise taje Har Kano ta d’aukoni ta dawo Dani gidanta.. Kuma kasan mai yanzu treating dina take da kyau har wani respect naga tana bani da kula na musamman
.. Yanzu bata min kallon shashasha kaman yanda take min a baya.. Na tabbata bazai jima ba zan saye zuciyarta kamar yanda Ummul ta lashe zuciyarta. In no time zata aura min d’anta dan wllhi sosai ta d’aukeni da mahimmanci wann karon.. Finally burina zai cik
a Hisham.!” Ta k’arashe tana ‘yar tsallan murna.
“Shut up.! Shut the hell up.!!” Hisham ya daka mata tsawa kafin yaci gaba cikin huci “Kina jina idona idon tsinannen Haidar d’in nan sai kashesa..!”
A d’an tsorace Anisa ta waro ido waje kaman Hisham d’in
na kallonta tace “Excuse me.. Mai kake cewa.. Kan wane dalili zaka kashe Haidar dina..?”
“Shut up Neesa..!