Showing 213001 words to 216000 words out of 267381 words

Chapter 72 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

22

kunnensa na hagu "Yes Sadis, ka shigo asibitin.? Don't let him escape.! Ka tabbata bai kufce maka ba Sadis."

Daga d'aya b'angaren Sadis ya kaste

Haidar da fad'in "Ga plate number dinsa ina gani..Positive. I can see his car clearly yana fitowa daga asibitin.. It's him."

Haidar yaci gaba da jinjina Kai yana jijjiga yaron dake cikin hannunsa “Good Sadis.! Make sure that Bastard doesn’t escape. I’ll

call the cops now.” Daga haka katse kiran yai.

Daidai lokacin Ummul ta fara motsa jikinta alamun tana yunk’urin farkawa. Still idanunta a lumshe suke.. Cikin wane irin kasaltacciyar murya take furta “Umm.. Umma.. Umma na.. Umma na..!”

Haidar ya k’ura m

ata ido ba tareda ya furta komai ba. Ga jaririn rungume cikin hannunsa.

A hankali ta soma bud’e idonta da suka matuk’ar nauyi har ta sauk’e su tar akan Haidar. Sosai ta razana da ganinsa, alamun tsoro Ya nuna saman fuskarta.. Bata ma kula da jaririn dake

rik’e cikin hannunsa ba. Ta soma k’ok’arin matsawa baya daga nan yanda take kwance saman gadon tana fad’in “Mai.. Mai kake a nan..? Ya akai kasan ina nan..?”

Idanunsa suna kuma rinewa zuwa ja yaci ga a da takowa zuwa gaban gadon nata “How could you..? H

ow could you have done this Khairy..? How could you have kept something so serious like this..? Ta ya zaki b’oye mun abu mai girma irin wann.? What kind of punishment is this..?” Ya numfasa zuciyarsa na kuma masa zogi. Sai ya sassauta murya kad’an still ya

na iya sauraran tsananin b’acin rai cikin muryar nasa “Khairy.. How could you have trusted that imbecile..? Ki fad’a mun saceki yayi..?! Answer me now.!” Ya k’arashe cikin dacin rai Har hawaye na gangaro masa.

Kuka ta fashe dashi itama. Ta soma k’ok’arin

saukowa daga saman gado. Ta nufi k’ofa tana kuka dukda tangadi da take. Haidar yai sauri ya tare k’ofan.

Ta d’ago ta dubeshi cikin kuka. Da kyar ta iya furta “Ni Ka.. Ka k’yaleni na wuce.. Na tsaneka bani son ganinka.. Ka..!” Sai ta duk’a a wajen tana kuk

a sosai.

Shima duk’awan yai gabanta sirirn hawaye na gangaro mishi ga yaron na kuka cikin hannunsa. Cikin rawar murya mai cikeda sanyi wann karon yake furta “No Khairy.. I can’t… I won’t let you go..! How.. Can I let you go when you are so close to me..

? I went insane looking for you, you know.! Ta ya zan bari ki sake guje mun.. Just how Khairy..?!”

Haidar na hawaye Ummu na kuka haka ma jaririnsu kuka yake.

Ta dubeshi ta dubi jaririn ba tareda ta daina kukan ba. Saima sadda idonta k’asa da Tai tana ma

i ci gaba da kukan.

Har cikin bargo da tsokarsa yake jin rad’ad’in kukan nata. Ji yake kaman Ya janyota cikin jikinsa Ya lallasheta amma baida wann ikon a halin yanzu.. Ya tuna months back batada masauk’i sai cikin jikinsa. He couldn’t believe shi da Kans

a ya furta ma Khairy kalman saki. Kalman da gashi Ya haifar masu da barrier tsakaninsu. Ya lumshe idonsa yana jin zuciyarsa na masa ciwo… A hankali Ya Ware idonsa sanda yaji kukanta na k’aruwa “Please don’t cry… Ki daina kukan nan haka..!” Yaci gaba da dub

anta yana jinjina kai “I’ll kill for every tear..”

Batace da shi komai ba sann bata dubesa ba bata kuma fasa zubda hawaye ba saima abinda Ya k’aru.. A daidai nan yaron Ya kuma calla k’ara daga nan cikin hannun Haidar. Ya mik’e tsaye yaci gaba da jijjiga

yaron yana fad’in “See.. You are making him cry as well..” Yaci gaba da jijjiga yaron yana fad’in “Oh c’mon champ.. hush now.. Don’t cry..” Yaci gaba da jijjiga yaron yana lallashinsa a haka Ummul ke satan kallonsu. Har yaron yai shiru.. Wayar Haidar ta so

ma ruri.. Yai saurin cirowa daga aljihunsa. mommy ce mai kira.

Ya d’aga kiran cikin sauri yana ci gaba da jijjiga yaron da d’aya hannun.

Ummul tana jinsa yana waya da Mommy yana sanar da ita tayi jika cikin tsananin farin ciki maras misaltuwa.

Haidar

yaci gaba “You have a grandson Mommy.. A beautiful Grandson.”

Daga d’aya b’angaren Mommy sai ta fashe da kukan farin ciki. Fad’i take gata nan zata shigo jirgi ta taho Bauchi. Haidar yace ta bari idan Allah yakai rai da safe sai su taho gaba d’aya da Dad

dy.

Mommy taci gaba da girgiza Kai tana fad’in “No Haidar.. I can’t wait till morning.. I can’t wait to see my grandson..” Cikin muryar kuka mai gauraye da joy take maganan.

Shid’inma dauriya kawai yake amma ji yake kaman yayi kukan musamman da Mommy tac

e “Na kasa yarda rana irin wann zaizo Haidar… Zanga D’anka.. Ma sha Allah. TabarakAllah…! Alhamdulillah is all I can say..” Ta d’anyi still kafin taci gaba “What about Ummul..? How is she.. How is my daughter Haidar..?”

Sai sann Haidar Ya dan waiga ya dub

i Ummul wacce ke kwance ta basa baya hawaye naci gaba da gangaro mata.

“She’s fine Mommy.. I mean.. She will be fine..”

Mommy tace “What do you mean she will be fine.. Ina take..? Can I talk to her.. please put her through.. I want hear her voice.. I wa

nt to know how she’s doing.?”

Haidar ya dan furzar da huci lokacin da jaririn Ya fara yan k’anan kuka. mommy ta sinkayo sautin yaron daga cikin waya. Annurinta ya ninku, yayinda k’walla ta kuma ciko idonta “Is that my grandson.. Is that his voice..?”

Hai

dar ma murmushin yake yana duban yaron “Yes Mommy.. It’s your grandson.. He wants to hear your voice I guess. I’m putting you on speaker.”

Yasa Mommy a speaker yana yana duban yaron yake fad’in “Guess who’s on the line Son.? It’s Grandma. Say hi to gran

ny.!” Cikeda farin ciki yake maganan gwanin ban sha’awa.

Mommy tace “Hello my cutie.. Is that you..? Is that your tiny voice.? How’s my little love doing..? Oh c’mon don’t cry.. Is the little one hungry..?” Cikeda farin ciki da ya gaza b’uya take maganga

nun. Haidar sai murmushi yake yayinda Ummul ke saurarensu daga nan yanda take kwance har lokacin hawaye ke gangaro mata musamman da ta sinkayo muryar Mommy tana magana ma jaririn.

Mommy tace da Haidar Ya bata Ummul. Sai Haidar Ya d’an waigo kadan yana du

ban Ummul da ta basu baya. Kuka take maras sauti. Ya d’anyi gyaran murya yace “She’s.. still asleep Mommy..”

Mommy ta jinjina kai “Kyaleta tana buk’atan hutun.” Ta k’ara da “Haidar, nace ya batun aurenku.. Mecece makomar aurenku da Ummul.?” Jikinta duk a

sanyaye Tai tambayar cikeda shakkun amsar da zata samu daga gare shi.

Lumshe idonsa yai kad’an had’ida furzar da huci daidai lokacin wata mata mai sanye da kayan nurses ta dan manyanta matar ta shigo. Ta dubi Haidar dake rik’eda jariri ta kuma dubi Ummul

. Kallon na mamaki ko tuhuma take ma Haidar ganin bataga mutanen da suka taho da Ummul ba. Kafin tai magana Haidar yai saurin furta “I’m the father.” Sai ta saki murmushi matar tace “Ba shakka naga kama.. Congratulations to you.” Ya jinjina mata kai had’id

a mata godiya kafin ya sumbaci yaron Ya mik’a mata. Ta amshi yaron tana nufan Ummul.

Ficewa waje Haidar yai yana amsa kiran Mommy. Mommy ta sake nanata masa tambayar da Tai masa.

Furzar da huci Ya kuma yi yana shafa kansa kad’an “All that I’m sure Mommy.

. Shi ne I won’t give up my wife.. I’ll never give up Khairy.. I won’t give up my little family.. I will do everything I could to make sure ahalina bai tarwatse ba.” Ya dan numfasa kafin yaci gaba “If Khairy is the architect of our love Mommy.. Then I’ll b

e the Engr.. If she’s the one that designed our love.. Then I’d make sure it is well built.. I will be the protector of that love.. I know it won’t be easy.. It will be difficult.. But then, I won’t give up.. Never..!”

Mommy ta goge hawayen da suka ganga

ro mata. Murmushi ne saman fuskarta amma can k’asan zuciyarta zallan tausayin D’an nata ne. Ta shiga jinjina kai tana fad’in “May Allah be with you Son… Ina rok’on Allah ya had’e maka ahalinka kaman yanda Ya had’e mun nawa.”

Haidar Ya amsa da Ameen Mommy

. Yai mata godiya Tai masa fatan alkhairi da nufin washe gari idan Allah yakai rai jirgin sassafe zasu biyo itada mahaifinsa.

**

A can waje kuwa Sadis bai fasa bin bayan motan Hisham ba har saida ya cimmasa. A dole Hisham yai birki yai parking.

Hajja ta

soma karanto salati tana waige waige ganin Mota ta sha gabansu ba shiri.

“Hisham meke faruwa.. Waye wann meyasa yake bibiyanmu.?”

Hisham da k’irjinsa bai daina bugawa ba girgiza kai yake yama kasa ficewa daga cikin motan. Fad’i yake cikin rawar murya “I

.. Ya.. Yaron Ogana ne a wajen aiki.. Ogana da nake aiki k’ark’ashin Kampanin sa.. Engr Aliyu Maitama mahaifin Abokina Haidar.!”

Cikin wane irin shock Hajja ta d’ago tana duban Hisham fiyeda Wanda ta shiga lokacin da taga Haidar.

“A..Aliyu Maitama.. K’ar

k’ashin sa kake aiki..?!” Ta fad’i cikin birkicewa.

Hisham Ya jinjina kai “Eh Hajja k’ark’ashinsa nake aiki kuma na tabbata shi Ya turo a kamani a tunaninsu ni macuci ne kaman yanda Haidar yai zato.. Hajja abun is complicated amma na tabbata komai zai fit

o fili idan suka tabbatar banida laifi kuma ni taimakon Abokina kawai nake.”

Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un shine abinda take nanatawa cikin zuciyarta. Bata sake fahimtar komai ba sai tsintar kanta da Tai a station dan tuni an kama Hisham anyi dashi

ofishin yansanda.

Hisham Ya kamo hannayen Hajja cikin nasa daga nan yanda yake rufe cikin cell. Ya kwantar da murya sosai “Hajja I’m innocent.. Ban sace Ummul ba.. Ban kuma raba Haidar da Ummul ba.. Hasalima ban tab’a sanin Ummul abokina Haidar take aure

ba har sai bayan da suka rabu.. Sann a wann lokacin na san ‘yaruwarsa Anisa tana neman rayuwar Ummul da abinda ke cikinta kaman yanda tayi ajalin rayuwar tsohuwar matar Haidar da abinda ke cikinta..!”

Hajja bata fahimtar komai sai hawaye dake gangaro mata

tana duban D’an nata cikeda tausayawa. Ta ya fara aiki k’ark’ashin kampanin mahaifinsa ba tareda saninsa ba.? Ta ya D’anuwansa ya zama abokinsa ba tareda saninsa ba.? Ta ya D’anta ya fad’a gidan da taita k’ok’arin nisanta shi dashi ya fad’a cikinsa tsamo

tsamo..? Ta ya duka wad’annan abubuwan suka faru. This a too much of a coincidence.

Muryar Hisham ta sinkayo yana fad’in “Hajja ki daina kuka.. Banida laifin komai Hajja ta.. Your son is innocent.. I’m sure Haidar would understand so as his father. Su d

’in mutane ne masu nagarta.”

Hajja ta kuma lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata. Silalewa Tai nan wajen tana kuka sosai. Kuka mai tab’a zuciya.

**

Washe gari jirgin safe su Mommy suka biyo zuwa Bauchi. Haidar kuwa asubahin fari Ya baro masaukinsa Y

a nufo asibitin dan dama bai yarda ya bar asibitin ba saida ya samar ma Ummul da jaririnsu room nurse da zata kula dasu dan ko nawa zai kashe a kular masa dasu tinda shi dai bazai yuwu Ya kwana dasu ba.

Cikin tsananin damuwa mai tattareda tashin hankali

Ummul ta kuma tambayar nurse din “Ina Hajja.. ina Hisham meyasa ban sake ganinsu ba tin jiya..? Ki fad’a mun.. Haidar ne yace ki rufe ni a nan Ki hanani fita..? Dan Allah Ki sanar Dani.. Ina Hajja da Hisham..?”

“Suna yanda Ya kamata ace nan suke.!” Haida

r da shigowarsa kenan da kaya nik’i nik’i na jaririn da na mahaifiyar jaririn Ya fad’i haka.

Nurse din ta sauk’e ajiyan zuciya tana ma Haidar sannu da zuwa. K’ok’ari taketayi Ummul ta saka ruwan tea a cikinta ko jariri zai samu ruwan nono amma tak’i sai

tambayarta take ina Hajja da Hisham.

Nurse din Suka gaisa kafin Haidar Ya shiga aje kayayyakin dake hannunsa matar tana sanar dashi Sun sha fama da ‘yar rigimarsa daren jiya dan cewa Tai saidai a barta ta fice. Ta dubi Ummul murmushi saman fuskarta ta ku

ma dubi kofin tea dake aje gefe sai ta dubi Haidar tace “Kuma tak’i ta saka komai cikinta balle wann babban mutum din ya samu isasshen abinci.” Ta mik’a mata mug din “Ya kamata ki shanye wann.. Mu a Likitance ruwan nono shine farkon rigakafi ko wane jariri

ke buk’ata.”

Ummul ta galla mata harara. Dariya taso bama nurse din amma ta gimtse tace “Daure dai ki shanye wann.. Ni kinga ma tafiyata.” Ta mik’e tana ma Haidar Sallama.

Bayan ficewarta Haidar ya maidoda da dubansa ga Ummul wacce ta nannad’e jikint

a cikin mayafi. Ya dan furzar da huci kad’an kafin yace “Kiyi hak’uri ki sha.. Take one more sip.. Please.!”

Kauda fuskarta gefe ba tareda ta dubi yanda yake ba. Ga jaririn tuni ya soma mutsu mutsu yana cilla k’afafu sai tsotsan hannunsa yake alamun yunwa

.

Haidar ya kuma furzar da huci yana shafe fuskarsa “Look Khairy.! Idan baki sha ba zan tako har wajen na baki da kaina kuma kinsan zan aikata..!”

Ta dube shi a dak’ile “Ni kuma sai na tsaya wani k’ato ya bani abinci a baki.. Allah ya sawak’e mun. Idan

ka mance ne dai na sake tuna maka.. Ni Ummulkhair ba matarka bace. AUREN WATA UKU mukayi kuma ya k’are.!”

Haidar ya shafi fuskarsa da tafukan hannayensa had’ida furzar da huci. Yasan dole zai sha fama ba kad’an ba. Yakai dubansa ga yaron da tuni ya b’ige

da kukan yunwa ga Ummul ta had’e rai sosai ta kauda fuska gefe. Dik yanda take son ta d’auki D’anta ta basa abincinsa ta lallashesa yai shiru ta kasa sabida tsananin k’iyayyar mahaifinsa dake kuma tunzurata. Sosai kukan jaririn ke mata zafi amma ta kasa k

oda motsawa sabida Haidar dake wajen.

K’arasowa yai ya d’auki yaron ya shiga jijjigasa yana lallashinsa. Sai ya saka ma yaron lip d’insa na k’asa aiko tuni ya capke ya soma tsotsa kaman ya samu abinci. Ummul ta saci kallonsu yanda Haidar ya saka bakinsa m

a yaron sai jijjigasa yake. Hawaye suka gangaro mata.

Daidai nan sukaji Sallama a k’ofa. Haidar ya bada izinin shigowa.

Wa zata gani.? Mama Tani ce da ‘yanuwanta guda biyu Azeema da Badia. Suka tafi a guje suka rungume Ummul suna kuka. Yayinda Haidar k

e gaisawa da Mama Tani ya mik’a mata jaririn yana musu sannu da hanya. Dan dama Tun a daren jiya ya tura Sadis ya tafi Kano d’aukosu. Asuba Sun kamo hanya shisa sukayi isowan safiya.

Haidar ya fice wajen Sadis ya basu waje.

Sosai Ummul ke kuka tana tam

bayan sauran ahalinta. Ta dubi Azeema tace “Ina Khulsum..? Maiyasa bata biyoku ba..? Itama tana fushi dani ko.? Umma da Abba duk fushi suke dani ko.?” Hawaye suka ci gaba da gangaro mata tana girgiza kai take fad’in “Bazan iya dubansu cikin ido ba.” Cikin

tsananin rawar murya take maganar.

Azeema ta murmusa tana share ma Ummul d’in hawayen da suka gangaro mata “Dukanmu muna fushi dake ‘yaruwa.. Shin wak’e gudun danginsa a lokaci mai mahimmanci irin wann…? Amma Kar ki damu zamu iya yafe Miki ko dan zuwan S

abon D’anmu.!” Ta k’arada “Kinga d’ago ki gani.. D’ago kiga da wa muke tare.” Ta k’arashe da murmushi saman fuskarta.

D’agowar da Ummul zatai sukai ido hud’u da Khulsum. Rabon su da su saka juna a ido Tun lokacin Auren Ummul d’in a gidan Hajiya Asshe ra

nan da mahaifiyarsu tai ma ‘yanuwan Farrak’u a k’ok’arinta na ganin Auren Ummul Ya tabbata.

Hawaye suka ci gaba da kwaranya musu.. Khulsum tana k’arasowa gaban Ummul kukan Ummul d’in Ya k’aru sosai. Murya na rawa Khulsum ta furta “Adda Ummul..!” Sai suka

i bursting cikin kuka sosai su duka biyun. Suka rungume juna suna yin mai isansu. Har saida Mama Tani tace zasu tasa mata sabon maigida da kukan da suke dan tuni bacci ya d’auke jaririn cikin hannunta.

Ana haka su Mommy harma da Daddy sukai sallama tared

a jagorancin Haidar.

Gaishe gaishe aka soma kan Ummul na kife k’asa tin shigowar Mommy da Daddy. Mama Tani ta mik’a ma Mommy yaron tana fad’in ta rigata ganin angon nasu. Sukaita ‘yar bankwanci a tsakani Mommy tana fad’in ma sha Allah ta sumbaci goshin y

aron. Sak Haidar dinta sanda yake jariri. Su Azeema kaw ficewa sukai bayan Sun gaisar da iyayen Haidar.

Mommy ta mik’a ma Daddy dake zaune saman farar kujera yaron. Ya amsa yaron kyakkyawan murmushi bisa fuskar Daddy. Haidar yana gani Daddy na ma yaron a

ddu’a ya tofa masa. Ya mik’a ma Mommy yaron bayan ya jero ma jaririn da mahaifyarsa add’u’o’i. Har kawo wann lokacin Ummul bata iya d’ago fuskarta ba.

Daddy ya dubi Haidar yace suje daga waje. Ba musu Haidar yabi bayan mahaifinsa.

Bayan ficewar su Mama T

ani ma ta zame jiki ta fice tana ce da Mommy bari ta barta ta gana da sabon Angonta dan gashi da alama har ya kori Daddy.

Mommy ta murmusa tana jinjina barkwancin Mama Tani.

Mik’ewa Mommy tai rungume da yaron cikin hannunta ta dawo kusan Ummul wacce t

inda Mommy ta nufota k’irjinta ya tsananta bugu. Ta kasa koda motsawa balle ta dubi Mommy tin bayan gaisuwa Wanda shima da kyar ta iya. Ta sani tana fara magana kuka ne zai biyo baya.

Mommy ta kwantar da jaririn cikin baby crib d’insa dake gefe. Ta kuma

matsowa sosai kusan Ummul. Sai Mommy ta d’aura hannayenta saman na Ummul. Ummul na ganin hannun Mommy saman nata hawaye suka shiga gangaro mata.

Mommy ma kuka ne taji na zuwa mata. Sai kawai ta rungumo Ummul cikin jikinta tana fad’in “Taho nan ‘Yata..!”

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login