Showing 237001 words to 240000 words out of 267381 words

Chapter 80 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

42

series of Aure da D’an nata yake nema a baya ana hanasa idan tak’i wann sai ya zama kaman tayi butulci ne ma Allah. Tuni ta bar ma Allah lamarin ta kuma nema zab’insa ciki. Ko wane aure yana zuwa da nasa k’alubalen. Waye zai tab’a tunanin wai ita Fann

ah D’anta zai auri d’iyar Asshe k’anwar Hajiya Kwaise.? Waye zai tab’a tunanin zata dawo gidan Aliyu Maitama suyi rayuwa mai tsafta da Hajiya Kwaise.? Lallai rayuwa cike yake da sauye shayen lamra. Allah ka sauya mana sharri zuwa alkhairi. Ameen.

Cikin k

’ank’anin lokaci aka aiwatar da komai dan tinda akazo da batun auren sai Anisa ta samu sassauci daga wajen iyayenta musamman Abbanta Wanda dama shi yaima Amminta iyaka da ita matuk’a tana tsare a police station. A cewarsa bai haifi ‘yar da zata d’aga masa

hankali ba. Ba kaman da Abban Anisar yaga D’an Aliyu Maitama ne mijin Anisar. Abun duka gida ne.. Hakan yasa babu wani dogon bincike balle jan lokaci. Balle ma shi ina ruwansa baijin ko kashi Anisa ta kawo zai fasa aura mata da dai ta zame masa masifa da t

ashin hankali cikin gidansa. Can Kano gidansu Anisa akaje ka d’auro Aure ko gida Abbanta bai bari taje ba daga cell yace a wuce da ita d’akin mijinta. Taron biki ma bai bari an masa a gida ba. Mommy ce ta had’a yar k’aramar biki can Abuja. Da kyar Abban An

isa ya bari Asshe ta halarta bikin yar nata.

Bayan biki da kwanaki biyu Daddy yace da Hisham wann karon shi zai tafi SouthAfrica dan ya kula da kasuwancinsu na can. Ya d’auki matarsa su tafi can musamman da yake an dage sauraron k’aran Anisar har sai bay

an watanni hud’u masu zuwa. Sam Hisham bai k’i tayin Daddy ba. Sati guda kawai sukai a Nigeria ba tareda Anisar ta tare da angon nata ba tinda sud’in ma tafiya ne. bayan bikin suka tattara suka nufi southAfrica. Tafiyar da zai d’auke su tsawon watanni uku.

Da wutsiyar ido yake duban Anisa sanda suka zauna saman kujerun jirgin. Ya saki wann muguwar murmushin nasa kafin ya rank’wafo kad’an cikin k’ok’arinsa na d’aura mata seatbelt “Babe, I can’t wait jirgin nan tai landing. A hannu zan sureki na fara nuna m

iki soyayyar da ban samu daman nuna miki a Nigeria ba.”

Banbarakwai haka taji abun. Ta watsa masa wani irin mugun kallo kafin tai ‘yar bazawarar murmushi na nuni da takaici “Kar mu raina ma kanmu hankali Hisham. Nida Kai munsan babu komai cikin auren nan

face k’arya. So we shouldn’t expect anything from this marriage. Dan ina mai tabbatar maka ni Anisa bazan tab’a barinka ka tab’a koda d’an yatsana ba cikin watanni uku da zamuyi tare. Kuma ka saka ma ranka.! AUREN WATA UKU shi mukayi. Ina cika watanni uku

a lokacin da muka dawo Nigeria zan rabu da k’addararren aurenka.!”

Hisham ya tsareta da ido. Sai ya murmusa yana daidaita zamansa saman seat din. Irin Wanda ya kware a shed’ana yake fad’in “A naki wauwautan Anisa kinyi zaton wasa da hankalina kike..! Kiny

i zaton kin Aureni ne dan Ki samu dama akaina ki bankado duk wasu sirrika na. Haka ne..? Kina tunanin a watanni uku da zamuyi matsayin mata da miji zaki iya samun dama akaina ki bankad’o duk wasu sirrika nawa.? Har haka kike son Haidar.? Dan na tabbata sa

bida shi kikai sadaukarwa mai girma kika amince da aurena.!” Yai maganar yana shafe hab’arsa yana mata wane irin duba. Har lokacin murmushi ne saman fuskarsa “Lallai kin tabbata sokuwa Anisa idan har kikai tunanin zaki iya outsmarting dina by marrying me.!

” Ya k’arashe yana kamo hab’arta suna fuskantar juna. Murmushin itama ta sakar masa dan bazata bari ya gane ta karaya ko abu mai Kama da haka ba.

Ya dan girgiza Kai yana dubanta “Bazaki tab’a yin hankali ba balle wayo Anisa. Idan amfani dake a karo na fa

rko ya fi min sauki a lokacin da ban Miki farar sani ba. Meyasa amfani dake a karo na biyu lokacin da na sanki kaman tafin hannuna zai min wahala.” Ya d’anyi gajeren tsaki had’ida yin ‘yar bazaurar dariya irin Wanda ake ma Wanda aka raina masa wayau kafin

yace “Ki yarda dani daga k’arshe kece zaki kasance da Haidar ba Ummul ba. Idan kika bi plan dina daga karshe Haidar zai tabbata naki.” Ya k’ank’ance idanunsa yana dubanta kaman zai sumbaceta “Mai zai faru idan na saka Miki rigar bomb. Zaki kira Haidar ki n

emi taimakonsa.. Sann shi kuma zaizo ya ceceki like a real hero.?” Murmushi yaci gaba da yi yana dubanta yayinda Anisa ke ci gaba da masa kallon mamaki tama rasa a wani aji zata aje Hisham.

Hisham yaci gaba “Zaku kasance a wann d’akin da na kulleki da rig

ar bomb ku biyu. Bomb din zai tashi daku biyun. Zaku k’one tare.. Ku biyun zaku Mutu tare kaman dai asalin masoya.. Sann ni kuma, Zan Auri matar K’anina sann na kula da bayansa ina nufin marayan D’ansa da bzawarar matarsa kaman dai D’anuwa na gari..!” Ya k

’arashe yana murmushi mai bayyana hakwara.

Matsawa ta soma k’ok’arin yi daga gefensa yai saurin rik’o hannunta ya matseta cikin jikinsa. Ya rank’wafo da bakinsa saitin kunnenta. A hankali yake furta “Kaman haka inada hanyoyi da dama da zanyi amfani dasu

dan cikan burina. So I’m warning you Anisa, do not teste my patience.!” A hankali kuma ya soma sakin hannun nata yana sakar mata murmushi. Saima ya shiga k’ok’arin gyara mata mayafinta yana fadin “Hey wifey.. Did I scare you..? Im just kidding.” Yai mata r

ad’a a kunne da fad’in “bazan kasheki ba.. Zan barki kiyi rayuwa mai tsawo da Haidar d’inki.. Happy.?” Ya k’arashe yana kashe mata ido guda da murmushi saman fuskarsa.

Anisa batace komai ba sai tsaresa da ido da tai dan dama Tabbas tasan Aurenta da Hisha

m yayi yanada shiri fiyeda Wanda yafi wann ma. Ta shirya ma aukuwar komai. Alk’awari tai bazata sake bari Hisham ya kuma samun damar cutar da Haidar da Ummul ba. Even if it will cost her her life.

**

Tin bayan tafiyan Hisham da Anisa k’asar SouthAfrica

Haidar bai kuma bi takan Ummul ba. Mommy dai ta sanar dashi idan Ummul d’in tayi Arba’in zata tare nan Abuja. Abinda Ya bama Mommy mamaki shine sam bai wani nuna d’okinsa ba balle damuwarsa. Sai bata kawo komai a ranta ba tinda tasan Watak’ila yayi d’okin

ne har ya gaji.

Sosai Ummul ta damu da halin ko in kula da Haidar yai da ita tin bayan aurensu a karo na biyu. Tanaji zaizo gidan Ya gaida su Umma yaga D’ansa Ya tafi amma ko sunanta bai ambata balle Ya buk’aci ganinta.

Ranar wata juma’a ma haka tanaji

su Azeema suna shelan zuwansa. Tana daga d’aki tana jinsa Har hira suke yana wasa ma D’ansa amma koda Azeema tace bari ayi masa kiranta sai Ya mik’e abinsa yana fadin Azeema ta shige cikin gidan Tai masa kiran ‘yan samari Wanda zasu shigo da aike.

Hanka

lin Ummul idan yayi dubu Ya tashi. Wai ita Haidar yake basarwa irin haka.. Toh mai Tai masa ne da tsanani.. Kodai Ya daina sonta ne.? Tambayar da taji ya haifar mata da fad’uwan gaba. Sai taji k’walla na yunk’urin ciko idonta.

A nan d’aki Mama Tani ta sh

igo ta isketa tana rera kuka dan dama duk idan Haidar yazo gidan sai iyayen mata su shige k’ofan Abba su bar masu filin tsakar gidan.

Mama Tani ta dubeta da mamaki “A’ah! ke kuma kukan me kike..? Ina Haidar d’in.. Wai Har ya tafi ne.?”

“Nima ban sani ba

Mama.” Ta bama Mama Tani amsa cikin kuka.

“Ban gane baki sani ba.”

Cikin kuka taci gaba “Mama Haidar ya daina sona ko yazo gidan nan wajen D’ansa kawai yake zuwa amma ko gaisawa baya tsayawa muyi.”

Maganganun ta suka so bama Mama Tani dariya amma sai t

a gimtse tace “Toh ke ba haka kike so ba. Inji a nan kike kumfan bakin ke ba don kina sonsa kika amince da komen gidansa ba. Ke bari kiji na fad’a Miki maza irin Aliyu ba’a ja musu aji dama kad’an k’adangarun nan na bariki masu d’ingilallun buje ke jira ak

ansu. Ahtoh.!”

Badia dake daga parlor ta dage labule ta lek’o tace “Ahtoh Mama fad’a mata dai. Tana nan tana wauwauta taji ana shafe Fatiha a Abuja.!”

Ummul ta kuma tunzura da kalaman Badia. Sai ta kuma fashewa da kuka.

Mama Tani ta aika ma Badia dak’uw

a “Kinci gidanku Badia. Ke bakinki bazai fad’i alkhairi ba. Kiji da naki matsalan wann gantalallen mijin naki ya gudu Ya barki ba tsuntsu balle tarko. Ke ba mai aure ba ke ba sakakkiya ba.”

“Haba Mama Aure ni da Tasi’u kuma ai ko a k’iyama.!” Cewar Badia

.

Mayafi Mama Tani da dauka tana fad’in zata dubiya layin bayansu. Badia tace da ita a dawo lafiya.

Mama Tani na tafe can k’asan babban kwalta ta hango ana ihun b’arawo sai jibgan mutumin ake ana masa ihun b’arawo mutane kaw sai tururuwa suke.

Kaman

Wanda aka ce Mama Tani ta kutsa nan ta hangi Wanda ake ma ihun b’arawo ba kowa bane face Tasi’u mijin Badia. Tasi’u dai da Ya gudu da kudin Bakauye da takardun bogi na shagon Abba ya kuma jefata a uku. Mama Tani ta dafe k’irji tana salallami “Na shiga uku

mai zan gani ni Tani.?! Tasu’u.!”

Tasi yaji muryar da Ya sani yana tunanin samun rahama daga jibgan da yake sha sai Ya soma k’ok’arin rarrafowa ga Mama Tani yana fadin “Mamana Mamana takaina kimin rai wllhi akasi aka samu ba ni ne b’arawon ba.!”

Samarin

dake wajen suka dubi Mama Tani sukace “Baaba D’anki ne.?”

Mama Tani ta zaro ido waje tana dafe k’irji “Ni Tani haramiya.! Allah shaida ban haifi b’arawo ba. Wllhi ba D’ana bane nima nan a sanadiyan wann kafuri na tafi gidan kasu bada hakki ba.! Kucimin uw

arsa da kyau amma kafin nan ku dakata.!”

Ta waiga gefe ta dubi yaran da aka tasosu daga makaranta ta amshi paper da pencil hannunsu ta mik’a ma Tasi’u tace “Rubuta.! Rubuta ma ‘yatsa rasidi dan ubanka!.”

Tasi yana haki yake girgiza kai “Mama kimin rai wl

lhi ina son Matata hasalima abinda Ya shigo dani layin nan kenan dan na maida matata kawai tsautsayi Ya hau kaina aka soma ihun b’arawo ni kuma na karyo kwana kenan na taka sawun b’arawon amma wllhi bani ne b’arawon ba.!”

Mama Tani ta jinjina kai “Sanin g

askiyanka sai Allah Tasu’u. Amma ko hakan d’in ne ba abinda zance sai Alhamdulillahi.! kaji yanda akeji. Kaman yanda ka gudu da kud’i ka barni a tsaka mai wuya banci nanin ba nanin ta cini. Ba kunya ba tsoron Allah ina Uwar matarka. Da tsufa na geme geme n

a tafi kurkuku k’anun yara suka shassahata ma wann fuska tawa Mari sabida Kai. Toh kaman haka kaima yau ka taka sawun b’arawo. Wann sai Ya zama wa’azi gareka damu baki d’aya Tasu’u.!”

Samarin sukaci gaba da girgiza kai suna fad’in “Karya yake bakinsu d’a

ya da b’arawon wllhi sai munyi ajalinsa a nan ehe.!”

Mama Tani tace ku dakata kar kuyi ajalinsa. ‘Yata ta shafe shekara da watanni tana zaman gaibu da aurensa ba tareda ansan yanda yake ba. Bazata kuma yin takabansa ba bayan tsawon lokacin da ta diba babu

sanin makomar aurensa. Tasu’u wllhi sai ka sakar min ‘ya.!” Ta k’arashe tana dangwala masa paper.

Bai rubuta ba hakan yasa samarin nan sukaci gaba da dukansa. Tasi’u da yaji bugu kaman zai Mutu sai yace su dakata su daina dukansa zai rubuta ma ‘yar Mama

Tani Badia takardan saki da sharad’in samarin zasu mik’asa ga hukuma bazasu kashesa ba. Ya gwammaci su kira ‘yansanda su mik’a shi ga ‘yansanda da dai su masa dukan kisa wajen.

Samarin sukace yaci darajan Mama Tani Ya rubuta takardan sakin su kuma zasu

basa kariya bazasu bari a illatasa da bugu ba har ‘yansanda su iso. Haka kuwa akai Tasi Ya rubuta takardan sakin Badia Wanda Ya zame masa kariya daga dukan da yake kwasa.

Mama Tani ta amshi takardan sakin tai hamdala kana tai godiya ma samarin tasa kai t

a shige tana fad’in ta gode Allah da Ya kawo k’arshen auren ‘yarta Badia da miji irin Tasi’u.

**

Kwanci tashi babu wuya wajen mai duka. A ranar da Ummul ta cika kwanaki arba’in da haihuwa Abba yace Ya cika alkawarinsa yau zata tafi ga mijinta. A zaton Um

mul Haidar zai zo amma sai taga baizo ba. Aunty Asshe ce kawai tazo sann Abba bai bari wani daga gida Ya mata rakiya zuwa Abuja ba. A Cewar Abban tinda ba sabon aure bane kome ne ba sai an Tara mutane an mata rakiya ba. Daga ita sai Aunty Asshe da jarirint

a suka nufi Abuja. Ummul taci kuka har ta gode Allah.

Tarba mai kyau suka samu daga wajen iyayen Haidar baga Mommy ba baga Hajja ba an rasa waye yafi d’okin zuwan Ummul da jaririnta. Tuni an gyare musu masauk’i a b’angaren Mommy amma sai Hajja ta rok’i a

lfarmar Ummul ta zauna a nata b’angaren ta k’arashi bik’inta dan dama Mommy tace bazata tare gidan Haidar ba sai ta cika watanni uku da haihuwa. Koda Hajja ta buk’aci Ummul da ta zauna a b’angarenta Mommy cewa Tai hakan yayi dama ‘yarta ce.

A b’angaren H

aidar kaw da mugun mamaki yake duban Aunty Asshe yana jin wani sabon turanci wai Khairy bazata tare gidansa yanzu ba.

Ya girgiza Kai kad’an still yana duban Aunty Asshe “Aunty, wai kina nufin akwai wani watanni biyu nan gaba da zan sake jira.?”

Aunty Ass

he tace “K’warai kuwa. Zancen kake so muyi Haidar. Mommy tace ‘yarta bazata tare da d’anyen jego ba sai ta cika watanni uku da haihuwa.”

Girgiza kai yake disbelievingly “Unbelievable.!” Ya furta a hankali yana jinjina kai kafin ya gyara zamansa kad’an ya

bud’e murya yace “Aunty ni kuma sai na zauna Har tsawon watannin nan ba mata.? Tsakani da Allah an min adalci kenan.? Seriously this is unfair fah.!” Yai maganar duk a gajiye.

Ya dan fito daga cikin kujerar yana dubanta “Aunty you need to talk to Mommy.

Knowing Mommy tinda tace sai Khairy sai ta cika watannin nan bazata bari ta tare d’in ba. Please Aunty do something.. Ki rarrashi sister dinki ta amince ta bani matata mu tafi. Aunty wllhi hakuri na gab yake da k’arewa.!” Ya k’arashe kaman wani maraya.

A

unty Asshe dai tausayinsa taji kai har kunya saida Haidar yasa taji. Tinda Ya iya budan baki yace mata hakurinsa ya kusa k’arewa tasan an kusa wajen. cikin zuciyarta cewa take ‘Gata ake maka Haidar dan Mommy so take a gyara maka matarka sosai kafin akai m

aka ita. Ta yanda bama zakai tunanin ta haihu ba.’ A fili kuwa cewa Tai “Kai hakurin shekara sanda bata nan balle yanzu da watanni biyu ne jal bai cika wata biyu ba tinda Anci kwanaki arba’in already.”

Girgiza kai yake yana furta “Aunty wancan lokacin dab

an. Nasan babu auren a wancan lokacin amma yanzu da aure. Thank goodness wann karon ba Mommy ce ta biya sadakin nan ba balle ta hanani Matata... Mommy Sam ta daina tausayi na Aunty. Kawai gwara na nemar ma kaina mafita.”

“Ban gane ka nemar ma kanka mafi

ta ba mai kake nufi Haidar.?” Aunty Asshe ta tambaya tana duban Haidar dake k’ok’arin mik’ewa.

“Mommy taita ajiye ‘yarta amma Aure zanyi Aunty. Ki shirya zaki had’a mun lefe ko Mommy bata sani ba.”

Ummul dake mak’ale jikin k’ofa tana sauraron su zuciya

rta yai wani irin tsinkewa taga wani irin duhu ya gifta k’wayan idonta. Wani hajijiya Ya kusan aikata k’asa. Bata san sanda ta k’unshe bakinta ba cikin kokarinta na hana kukan dake zuwa mata. Muryar Aunty Asshe ta sinkayo tana ceda Haidar.

“Dakata dakata

.. Wane irin aure kuma Haidar.? Mai yai zafi.?”

“Khairy da Mommy bakinsu d’aya Aunty.. Idan kuma kema zakiyi joining team din nasu ne fine. I’m used to fighting my battles alone.”

Ummul bata ida k’arashe sauraron hirar Haidar da Aunty Asshe ba ta janye

jiki da kyar ta fad’a kan gado tana rera kuka mai dalili. Shikenan itakam da gaske Haidar baya sonta. Badia tayi gaskiya da tace tana nan tana wauwauta zataji an shafa fatihan Aurensa a Abuja. Ashe dama aurensa yake nema Shiyasa Ya wofantar da ita bai kuma

bi takanta ba. Kuka ya kuma b’alle mata. A haka Mommy ta shigo ta isketa.

Da mamaki Mommy ke dubanta. Ta girgiza kai kad’an “Ahah.! Ummulkhair, kuka kuma.. meke faruwa.?”

Tai saurin gyara zamanta tana k’ok’arin Had’iye kukan nata.

Mommy ta zauna gef

enta tana karantar ta sai tace “Lafiya kike kuka Ummulkhair.?”

Shiru bata iya amsa Mommy ba tanata k’ok’arin danne kukanta.

Ganin haka yasa Mommy yin shiru tana nazarinta. Sai ta tuna Haidar bai jima da ficewa daga gidan ba cikin yanayi na rashin walwala

da fushi. Sann koda ta tambayesa abinda ke damunsa bai sanar da ita komai ba. Koda Mommy ta tambayesa bazai kwana nan gida ba sai ce ma Mommy yai no kawai zai tafi can gidansa Ya kwana da safe zai shigo.

Ta tsare Ummul d’in sosai da ido kafin tace “Kuny

i Sallama da Haidar d’in ne.?”

Ambato sunansa da Mommy tai yasa ta kasa danne kukan kawai sai ta fashe da sabon kuka.

Ganin haka yasa Mommy tsareta da ido tace “Fad’a min Haidar Ya Miki wani abun ne.?”

Tai saurin girgiza kai “A’a Mommy.. Kawai.. Kawai

ina kewan gida ne.”

Mommy ta d’anyi still dan tasan bata fad’a bane kawai amma kukanta nada alak’a da Haidar. sai Mommy ta soma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login