Showing 39001 words to 42000 words out of 267381 words

Chapter 14 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

70

wace kasuwa tana k’ark’ashin local government d’in da take ne.”

Ya dubi Mama “Yauwa Mama nan wajen shine wajen saka hannun magada watau masu sayarwa kenan. Nan kuma wajen saka hannun mai saye ne. Nan kuma wajen saka hannun shaidu.”

Badi’a ta katsesa “Amma shi mai sayen baizo da shaidu ba.”

Tasi’u ya Washe baki “Wani aiki sai Badidi ta. Banda abinki meye amfani na. Ai duk dai a rubuce ne kawai ake abin ni duk zan iya saka hannu na zame maku shaidu.. Eh ai duk abun a rubutu ne kawai.”



Ya dubi mai saye yace “Mutumi na ai sai ka saka hannu ko..” Mutumi Ya amshi takarda Ya saka hannu.

Tasi’u Ya kuma Washe baki yace “Ai shikenan ka mallaki shago a garin Kano.. Burinka Ya cika.. Allah yasa ma kasuwa Albarka.” Sai Washe baki yake dan dama

mutumin k’auye ne irin Wanda ko cirani basa fita cikin kauye suke kasuwancinsu burinsa Ya mallaki nasa shagon cikin garin Kano nan yai gamo da Tasi’u.

Tasi’u ya dubi su Mama “Yauwa Mama ga wajen da zaki saka hannu.”

Mama ta dubesa a dak’ile “Banida ha

nkali ne zan saka hannu banga kud’ad’e ba.”

Tasi’u yace “Banda abinki Mama Tani waye yake yawo da kudade masu yawa irin haka. Ai sai b’arayi su bi mu. Haba shi fah kud’i d’an sirri ne.”

Mutumin Kauyen yace “Wann gaskiya ne. Daga nan zamuje tareda shi su

rkin naki Ya amsa kud’in.”

Tasi’u yace “Ahtoh tare zamu tafi takardu suna hannuna bani damk’a masa takardun Har sai ya dank’a min kud’ad’en. Ko nima baki yarda dani bane. Na tabbata da baki yarda dani ba da baki bani ‘yarki Badi’a ba.”

Mama ta jinina kai

“Shikenan..” Ta dubi Badi’atu tace ta nuna mata yanda zata saka hannun. Tasi’u kaman zai kamo hannayenta yake nuna mata. Yace Badi’a ma ta saka duk suka saka.

Tasi’u yace su koma asibiti wajen Abba shi zai k’arisa ji da komai. Zuciyar Mama ba wai ya kwa

nta ba suka nufi cikin asibiti. Sam rawar k’afan da Tasi’u yake ba wai ta yarda dashi bane. Sai ta soma tunanin anya batayi gangancin barin Tasi’u su tafi su biyu da mutumin amsar kud’ad’en ba. Koda yake ya Santa ya san halinta ita ba Badi’a bace tsaf kwab

o yai ciwon kai sai ta tatse. Da wann tunanin suka shige cikin asibiti.

(Rayuwar Duniya kenan. A wann babi munji yanda Matan Abba Wanda ke kwance gadon asibiti sukai cinikin dukiyarsa da kuma ‘yarsa. Mama dai tayi cinikin dukiyarsa yayinda Umma tayi c

inikin ‘yarsa. Fad’in Manzon Allah S.A.W cikin hadisin Abdullahi ibn Amr . ‘Duniya jin dad’i ne kuma mafi alkhairin jin dad’inta shine samun mace ta gari.’ Sahih Muslim 1467. Tabbas babban rahama ne Allah ya baka Matar kirki wacce zata tsare maka mutuncin

kanta iyalanka da kuma dukiyarka Wanda suke amana a hannunta. Allah kasa mufi k’arfin zukatanmu. Ameen).

SameenaAleeyou

📚

*AUREN WATA UKU.!*

*15*





Sameena Aleeyou…✍

🏽

*

Mama dai ta gaza zaune ta gaza tsaye tin bayan tafiyar Tasi’u da mai say

en shagon Abba. Ta dubi Badi’a dake shafen shafen waya tace “Ke kira min Tasu’u shirun nan nashi yayi yawa.. Karb’an kud’i saikace karb’an bashi.. Maza kirasa naji ina ya makara ne wai.”

Badi’a ta d’an girgiza kai “Haba Mama ko fah awa d’aya baiyi da tafi

ya amma kin d’aga hankali a kirasa. Nasan halin Tasi barsa da shaye shayensa amma banda sata.”

Zuciyar Mama yai wani irin bugawa. Ta dubi Badi’a a zabure tace “Badi’atu ina hankali na da tunani suka tafi Har na mance Tasu’u Ya tab’a shaye shaye.. Yo ina a

ke dank’a amanan kud’i hannun d’an wiwi Bad’ia..!”

“Mama mijin nawa ne d’an wiwi..? Ya tuba fah.”

“Idan ba d’an wiwi ba d’an uwarki ne..!” Mama tace tana danna mata dak’uwa.. Zufa ya shiga keto mata ta ko ina “Na shiga uku.. Na kashe kaina ni Tani. Wani

b’atan basira ne ya d’ebeni na dank’a amanan dukiyar nan hannun Tasu’u.”

Badi’a tai tsaki “Yo tsaban kina sauri mana a kauda shago kar ya shiga jinyar Abba ko Umman su Ummul ta dawo amsan hakkinta da na yaranta..”

Mama taci gaba da safa da Marwa “A’a Ta

su’u bazai tab’a min wann gangancin ba. Wllhi akan kud’in nan sai na cajesa daga hula har takalmi ba abinda ya shalleni ehe. Bayani d’aya na sani na kud’ad’ena..” Ta kuma duban Badi’a “Ki sake kiransa nace.. Ungo kirasa da nawa wayan..!”

Badi’a taja dogon

tsaki tana mitan Mama ta isheta.

Wasu nurses suka fito suka tambayan iyalan Malam Isubu. Mama ko takansu batabi ba ita dai damuwarta kud’inta. D’aya nurse d’in da ya ganesu Ya k’araso yana fad’in “Hajiya ashe kuna nan. Muna can munata nemanku a ward.”

Mama wacce gaba d’aya take a daburce ta dubesa a harzik’e tace “Toh gashi ka ganmu ai me akayi..?”

Nurse d’in ya d’an tab’e baki ganin yanda ta hayayyak’osa “Dama wasu magani da drip za’a saya shine akace a sanar daku..”

Bai kai aya ba Mama ta katsesa “D

a uwar me za’a sayi maganin inyi.. Kai kaga mun maka kalan masu bada kud’i.? kuje ku masa abinda zaku iya mu nan bamu maganin k’wandala ehe..!”

Ta dawo kan Badi’a tana fad’in ko batir d’in wayar mutuwa zai kar ta fasa kiran Tasu’u.

Nurse d’in Ya kuma b

ud’e murya yace “Ku fah muke jira Dr zai iya shigowa round..”

“Kai bana son fi’ili wai bakaga tashin hankalin da muke ciki bane?”

Nurse yace “Wann matsalar ku bari idan Kun bar nan sai ku warwareta dan Allah. Yanzu dai ku sayi abinda aka ce ku saya dan

a samu a ceci rayuwar majinyacin.”

Muryar Badi’a yaja hankalin Mama alamun ta samu Tasi a waya. Badi’a ta juyo tana duban Mama da murmushi saman fuskarta “Ki kwantar da hankalinki Mama barin saka miki shi a speaker kiji.”

Daga d’aya b’angaren Tasi’u Wand

a daga jin yanda yake kana iya sauraran k’aran ababen hawa alamun yana bisa kwalta kenan. Fad’i yake cikin d’aga murya irin na Wanda ke bisa abin hawa musamman babur “Mama ina bisa hanya ne shiyasa bani iya d’aga kiran. Gasu na karb’o su.. Go slow ne ya ta

re mu kinsan ana fashe fashe sabida k’ara manyan titi.. Eh gani na ma kusa k’arasowa kenan.”

Mama saida ta silale ta zauna dirshan a k’asa tana dafe k’irji “Yauwa yanzu naji batu” Ta marairaice murya tunanin yanzu kud’inta na hannun Tasi’u dole ta bisa a

sannu kafin ta dafesu “Ayya ayya Tasu’u na.. Sannu da k’ok’ari kaji d’an albarka.. Muna nan muna jiranka.. Allah iso da kai lafiya.”

Nurse da ya zuba ma sarautar Allah ido ganin Ya zo masu da muhimmin batu amma hankulansu na kan wani abu daban yace “Amma

Hajiya kun saurari abinda na fad’a kuwa.?”

“Mun saurara mana. Meye.? Ko so kake mu maimaita maka ka tabbatar mu ba kurame bane.”

Ya d’an girgiza kai “Hajiya gaskiya ina ganin girmanki kuma ni aikina nake k’ok’arin yi a nan. Ya kamata ki dinga tantance ka

lamanki.”

Mama ta tab’e baki dan a halin yanzu hankalinta ya kwanta taji labarin kud’ad’enta “Kaga k’aramin likita wllhi fah saidai ku k’yalesa mai aukuwa Ya auku dan nan da kake gani bamuda abinda zamu bada.”

Nurse d’in yace “Ban gane mai aukuwa Ya auku

ba. Ya kukeso ayi yanzu.? Kunsan cewa kud’in kwanakin da aka biya masa ma sun kusa cika. Kwanan nan za’a buk’aci k’arin kud’i musamman duba da irin jinyar da majinyacin ke fama dashi. Jinya ne babba kuma mai cin kud’i..”

Mama ta dubesa galala “Au dama b

a gwamnati bane Ke biyan kud’in jinyar nasa.?” Dan ita a nata zaton alfarmar gwamnati Abba ke ci tinda dai tasan tin zuwansu kwabo ba’a amsa wajensu ba.

Nurse ya girgiza kai cikin rashin yarda gajeriyar dariya na neman kufce masa “Mama kenan, a K’asar mu

ta gado kike fah ko kin mance ne na tuna miki. Nothing is free in this country.”

Mama ta tab’e baki “Kai kasan me kace. Ni dai na fad’a maka gaskiya bamu maganin fici ehe.”

Nurse yace “Amma ina wann mutumin da yai settling bills d’inku yake.. Ina nufin

ina mutumin da ya biya kud’ad’en..?”

Mama ta dubesa da mamaki “Wane mutumi kenan..?”

“Wanda na ganshi nan ya rako wasu ‘yanmata biyu.. Ina tsammanin ‘ya’yan majinyacin ne..”

Mama tace “Toooh..” K’irjinta na bugawa “Kar dai ace wai su Ummul kake nufi. Ub

an wa ya biya kud’in toh..?”

Badi’a ta katseta “Wann mutumin mana da suke tare wanda har Azeema tace Miki saurayin Ummul ne kuma shine yaje yayi belin Khulsumu a police station. Ta tabbata dai saurayin Ummul ne.”

Mama ta dafe k’irji cikeda mamaki. idan

har Wanda aka ambata da saurayin Ummul ya biya tulin kud’ad’en nan watau mai kud’i kenan wann karon Ummul ta samo. Toh wllhi bazata saku ba wai bindiga a ruwa. Yanda sauran batun auren suka lalace shima wann haka zai lalace yabi iska. Bari ta gama da batun

kud’ad’enta ta tabbata sun shiga lalitarta. Ya zama dole ta bincika tasan waye shi daga ina yazo dan tasan yanda zata b’ullo ma al’amarin amma bazata zuba ido Ummul ta k’are a gidan maik’o ba dukda wann canfi da aka mata.

Nurse yace “Ku nake sauraro.”

Mama tace “Yo ina kaw zaku gansa. Dama yaran karuwai ne yaje yayi abinda zaiyi dasu ne shine ya biya ladan jinyar ubansu. Sai ku jira su zo su baku dan nasan yanda Uwarsu ta tafi nata yawon suma ba zama zasuyi ba qila sun had’e a bayan gari. Ku jira Zasu

zo so su kuma biyanku wasu kud’ad’en. Idan Har kuma basu samu ba sai Malam ya jira har ta Allah ta cimmasa. Idan kuma lokacinsa baiyi ba har wa’adin kwanciyar sa saman gadon asibitin ya cika sai a maidasa can gida saman katifarsa ya cika a can.”

Badi’a

tace “Ahtoh magana kenan..”

Mamaki ya cika nurse d’in. Wai dama a duniya akwai mutane irin haka. Shikam yasha cin karo da mutane daban daban a aikinsa na asibiti amma bai tab’a cin karo da mutane irin wad’ann ba. Girgiza kai kurum yai yasa kai ya shige zu

ciyarsa fal tausayin Malam Isubu.

**

Abuja.

A fusace Daddy Ke dubanta “Wai meyasa kike son b’ata mun rai ne Kwaise. How many times do I have to tell you this.. Duk abinda ya danganci wann D’an naki bai shafeni ba..”

Mommy ta soma girgiza kai “Why.? Me

yasa..? Aliyu D’anka ne Engr.. He’s your flesh and blood.. Meyasa kake masa irin wann k’iyayyar haka..? Su waye suka shiga tsakaninka dashi har haka..?!”

Cikin tsawatarwa Daddy ya katseta “Har sai kin tambaya waye ya shiga tsakani na dashi Kwaise.. Meyasa

a kullum kike son tuna mun baya.! Kinfi kowa sanin wann D’an naki only reminds me of my sin. He reminds me nothing but my past Kwaise. Kuskure mafi muni da na tafka a baya… All because of you and your selfishness..!”

Mommy na hawaye take girgiza kai gani

n hannun mijin nata Har na rawa yake nunata. Cikin kuka take furta “Ni ce na maka laifi ba Haidar ba. Amma ka daina hukunta Haidar kan laifin da baida masaniya akai..” Muryarta yaci gaba da rawa “Haidar Ya taso cikin k’unci da tsangwama. A baya Nayi zaton

izuwa wann lokacin zaka k’aunace sa kuma ka mance komai sann ka zama mahaifi a gareshi kaman yanda ko wani uba yake. He’s your only son our only son…”

Katse ta yai ta hanyar d’aga mata hannu “This family can never be like a normal family Kwaise.. Kinfi ko

wa sanin haka. Farin ciki bazai tab’a wanzuwa cikin wann ahalin ba..”

Cikin rawar murya tace “Nayi zaton ka yafe mun.?”

Ya jinjina mata kai “Na yafe miki amma idan Har zanga d’anki sai na tuna Kwaise!”

Mommy ta girgiza kai hawaye na kuma zubo mata. Tabb

as an shiga tsakanin D’anta da mahaifinsa. Dan idan ba aikin asiri ba ba yanda za’ayi Ya d’auki laifinta Ya d’aura kan d’anta Wanda baida masaniyar laifin har yai masa irin wann k’iyayyar.

Ta kuma share hawayenta “Meyasa kake zaune damu ni da Haidar.. T

o build your image a duniyar kasuwancinka.?” Taci gaba da huci “Fine.. Mun cika maka wann burin.. Kanada iyali da duniya zata d’aga ido ta kalla ta kirasu da ahalinka. Amma babu komai cikin ahalin face k’arya da k’unci.. Nothing is real here..!”

“Kwaise.

!!!” Ya ambaci sunanta cikin d’aga murya.

Mommy na hawaye taci gaba “Eh kasuwancinka shine kawai gaskiyarka.. But your family..”

“You are right… I only care about my business because it’s the only thing that keeps me moving bayan tarwatsani da kikayi yea

rs back..!”

Ta lumshe idanunta hawaye na kuma gangaro mata. Sai kuma ta sassauta murya “I endured everything.. I even lost my own son without even realizing it. Thinking maybe wataran zaka k’aunacesa.. But than… I failed..! I failed as a mother and I fail

ed as a wife..!” Kuka yaci k’arfinta sanda ta duk’a k’asa tana mai isarta.

Ta d’an d’auki lokaci a haka kafin taji hannun Daddy saman kafad’unta. A hankali ya d’agota. Kaman wacce akace ta k’ara kuka.

Ya d’an shafi fuskarsa ganin yanda take kuka sosai t

ana fad’in ta gaza ta ko wani b’angare. Ta gaza protecting ahalin. Rungumeta yai ta b’angaren jikinsa kad’an yana fad’in Ya isa ta daina kuka. A haka yai masu masauk’i suka zauna saman kujera.

Saida suka d’ibi lokaci a haka kafin ta soma fad’in “Bazan til

asta maka ka so Haidar ba. But please just this once.. Alfarma nake nema.. Be a father to him..”

Ya d’an dubeta sai kuma ya kauda kansa kad’an “Ban tab’a cewa ni ba mahaifinsa bane Kwaise. D’anki shi ya zab’i ya cire kansa daga cikin ahalin nan.”

Ta d’an

sauk’e ajiyan zuciya kafin ta mik’e sosai tana gyara zamanta “Aure nake so a masa..”

Daddy ya dubeta da mamaki “Aure.? Cikin yaran Business partners dina kike so na nemar masa matan.?”

Ta girgiza kai alamun a’a “Na riga na samar masa mata a garin Kano.

‘Yar gidan mutunci wacce bata da bud’ewan ido da wayewa da yawa balle a samu matsala along the way. Ba babban Aure nake so ba, ba auren da za’a wallafa a mujalla ko a gayyato manyan mutane ba. No aure nake so ayi a sauk’ak’e. Kawu na dake can Maiduguri zai

iya wakiltanka dan shi na wakilta akan komai. Ga Asshe ma a can Kanon. So dik wani necessary bincike da Ya kamata a gudanar an gudanar..”

Dakatar da ita yai ta hanyar d’aga hannu “Idan keda ‘yanuwanki kun gudanar da duk abinda ta kamata kuyi so meye nawa

kuma. Ni dai kin sani bazan tab’a karb’ar ma D’anki Aure ba Kwaise. Kuma abinda ya shafi rayuwarsa ba damuwata bane. The only alak’a dake tsakanina dashi shine abinda ya shafi Kasuwancina. Kampanina da ci gabanta.”

Mommy ta rintse idanunta tana jin wani

zafi na ratsa cikin k’irjinta. Tasan za’a Rina haka tinda dai ta jima da sanin duk wani abinda ya danganci Haidar wofi ma ya fisa mutunci a idon mahaifinsa. Ya zama dole ta tabbata anyi auren nan at all cost. Tinda tasan wann ba komai bane face sharrin mu

gun asirin da aka jefesu dashi. Ta tabbata tinda Malaminsu ya sanar dasu da zaran anyi auren matsalan dake cikin ahalin zaizo k’arshe gwara tayi komai domin ta tabbata auren ya yuwu.

Ta numfasa kad’an “Auren bazai yuwu ba saida yarda da amincewarku.. Ina

nufin kaida Haidar..”

Ya kuma dubanta da mamaki “What exactly do you mean.?”

“Ina nufin Yarda da amincewarka shine kawai zai karkato Haidar Ya amince da wann Auren. Kasan halinsa za’a iya masa auren mu daina ganinsa har abada, bazai yarda ya zauna da ma

tar ba. Yanzu haka ma Gaba yake damu tinda gashi ya daina zama gidan nan.”

“Wanda yafi k’arfin zaman gidan iyayensa ne zai zauna ma Auren da zaki masa.? Ke kanki kinsan D’an naki baida mutunci bai ganin kowa da mutunci daga ni har Ke.”

“Amma yana mutu

nta aikinsa.!” Mommy ta dakatar dashi da fad’in haka.

Daddy ya tsareta da ido.

Taci gaba da jinjina kai “Musamman project d’in nan da yaketa kai komo akai. Naga yanda ya dage yake matuk’ar so Ya jagoranci aikin.. Idan har muna so ya amince da auren zamu

iya amfani da wann damar. Ina nufin zaka amince ya jagoranci aikin matuk’a zai amince da Auren. Daga baya na tabbata zai so Yarinyar kuma zasu gina family tare. Zai tara hankalinsa waje guda. A yanda matsalar..”

Bata kai aya ba ya katseta “A’a dakata daka

ta Kwaise amma ba dani Aliyu Maitama za’ayi wann shiriritar ba..”

“Engr dan Allah ka min wann alfarmar a rayuwa.. Just this once..”

Ya gyara zama sosai yana dubanta cikin rashin yarda “Seriously.. Wann ai hauka ne.. Kwaise a ina kika tab’a jin anyi abu m

akamancin wann..? Are you asking me to put my company at risk here.?”

Mommy ta silalo daga saman kujera ta duk’a gaban Daddy saman gwiwoyinta. Ta shirya sadaukar da komai domin ta ceto ahalinta.

Cikin muryar kuka take furta “Zanyi ko menene Engr.. Zan d

uk’a a gabanka na rok’eka sabida inada yak’inin Auren nan zai zama silan shiriyar Haidar da kuma kwanciyar hankalin ahalin nan cikin yardar Ubangiji..”

Saurin d’agota yai yana fad’in “You don’t need to do this Kwaise.”

“A’a ka kyaleni na duka gabanka ida

n har hakan zaisa ka amince da buk’ata ta.”

Daddy ya soma girgiza kai “Kwaise, babu abinda zakiyi da zaisa na damu da d’anki ko na damu da al’amarin shi.. Kaman yanda ban d’auke shi da mahimmanci ba haka ban d’auki wann auren da kika dage sai kin masa da

mahimmanci ba. Amma idan har haka kika zab’a ki sani I won’t

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login