Showing 189001 words to 192000 words out of 267381 words

Chapter 64 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

46

kawo kiyi Dikda naji wani babban kwafsi.. Ki sani k

oda ace cikin jikinki na Haidar ne bakida wajen zama cikin rayuwarsa. Haidar nawa ne ni kad’ai.!”

Dareen ta juyo tana wani irin duba na cin amana ma Hisham dan batasan da zancen wata Anisa ba sai kawo wann lokacin. Ta soma girgiza kai tana jada baya “Lall

ai ka cika shed’ani Hisham.! Ka cika babban mayaudari.. You are a Demon.! Na kasa yarda na Barka kayi amfani dani dan cimma bak’in burinka akan Haidar a karo na biyu..! Amma ka sani wann shine zai zama na k’arshe.. Zan tafi yanzu.. Zan sanar da Haidar koma

i duk wani mugun k’ullinka akansa ko dan D’ansa dake cikina.. Bazan tab’a bari ka sake cutar da Haidar ba.. Zan sanar dashi komai koda zan rasa shi..!” Tana ida fad’in haka ta fice a guje.

Hisham Ya soma k’ok’arin binta a guje yana kiran sunanta yana fad’

in ta dakata.. Anisa tuni ta take masa baya.

Koda suka fito Sun tadda Dareen Har ta bud’e gate ta fice.. Anisa ta shige mota tace da Hisham maza Ya shige su bi bayanta. Hisham Ya shige suka soma bin bayan Dareen dake gudu a k’afa tana saka hannu tana nem

an abun hawa. Saidai akai rashin sa’a babu alamun mutane a layin balle abun hawa. Dareen taci gaba da gudu a galabaice tana k’ok’arin tsere musu..

SameenaAleeyou

📚

*AUREN WATA UKU..!*

*50*





Sameena Aleeyou…✍

🏽

*

Wasa wasa an shafe sati uku d

a mutuwar Auren Ummul da kuma Haidar. A wann lokacin Daddy ya shafe a k’alla sati guda da dawo daga SouthAfrica, kuma labarin scandal din da yai erupting wajen bikin tariyar Haidar d’in Ya cimmasa. Hankalin Mommy duk ba’a kwance yake ba sanin mijinta mutum

ne da ko kad’an baiso wani abu ya shafi Kasuwancinsa. Yanda rayuwar ahalinta Ya soma daidaita bata fatan abinda zai kawo musu wani mishkila ko sab’ani. Ga mamakinta sai Daddy ya tari abun bisa lumana ba kaman yanda Ya saba a baya ba. Dan ko zancen bai bat

a k’ofan ta masa ba dikda taso yi masa. Bai canza ko kad’an daga irin kulan da yake bata ba tin bayan da suka daidaita tsakaninsu. Hasalima k’ara janta jiki yai yana fad’in irin kewarta da yai. Ta d’an dubesa a sanyaye tana so suyi zancen sai Ya kuma janyo

hannayenta yace “Kwaise na gaji da tafiye tafiyen nan. Inaga lokaci yayi da zan mik’a ma yaron nan ragamar kasuwancin.. Koda wani portion ne. We are not getting any younger.. Shekaru k’aruwa suke..”

Mommy ta jinjina kai duk jikinta a sanyaye. Alamun shig

owar mota sukaji. Daddy ya lek’a window sai Ya murmusa yace “Ina tunanin Yaronnan ne … Na kira shi yana company.. Na sanar dashi Ya bar aikin da yake yazo gida magana zamuyi.”

K’irjinta ya bada dam.! Dan tuni jikinta Ya bata ba magana mai k’aramin mahimma

nci bane zaisa ya kirawo Haidar ya bar aikinsa yazo gida dan kawai suyi magana.

“Let’s go downstairs..” Ta sinkayo muryar Daddy yana k’ok’arin nufan k’ofa.

Jikinta babu wani k’wari tabi bayansa.

A parlor suka iske Haidar Har ya k’araso yana jiran sauk

’owa mahaifin nasa.

Haidar ya risina ya gaida iyayensa. Duk suka amsa masa da sakin fuska saidai kallo guda zakai ma Mommy ka fahimci tana cikin damuwa.

Daddy ya dubi Haidar cikeda kulawa “Aliyu.” Ya kirasa da asalin sunansa.

Haidar ya amsa cikeda gir

mamawa.

Daddy yaci gaba “Na dawo na taradda abubuwa marassa dad’in gani da kuma sauraro. Garin yaya al’amra suka lalace har haka.?”

Haidar ya jinjina Kansa a hankali sai yace “Daddy Kai hak’uri.. Ban.. san abubuwa zasu zama haka ba.. Amma tuni nasa jam’i

an bincike su binciko yanda Dareen take.. Kai hak’uri Daddy.. Idan duka wann ya saka Kasuwancinka cikin had’ari..”

Daddy ya sauk’e ajiyan zuciya kad’an sai ya girgiza kai yace “Ba wann nake son ji ba.”

Mommy ta dubesa da mamaki. Sai Daddy yaci gaba “Ba

batun Kasuwancina da abinda zai shafesa nake son ji ba.. A’a naka batun nake son ji.. Al’amarinka da iyalinka. Because you matters to me more than any business.”

Haidar yaji wani abu can k’asar zuciyarsa. Yau Daddy ya zab’i ya fifita al’amarinsa sama da K

asuwancinsa da a baya yake d’aukakawa.

Jikin Mommy yai sanyi musamman da taga Haidar yayi shiru. Duka laifin nata ne. Gwara ta sanar da Daddy yanda al’amarin ya kasance.

Jiki a sanyaye Mommy tace “Dama..” Haidar bai bari takai aya ba yai karaf yace “Dad

dy scandal din da ya faru ya.. janyo sab’ani tsakanina da Ummulkhair.. Kuma har ta kaiga na mata saki.. d’aya.”

Sai Mommy ta dubi Haidar cikeda tausayawa.. Ta fahimci yasan duk abinda tai amma ya zab’i ya rufa asirinta. Bazai bari mahaifinsa yaji ga abin

da ta aikata ba gameda AUREN WATA UKU. Allah sarki D’a da uwa. Sai taji girma , k’ima da soyayyan d’an nata ya k’aru a kwayan idonta. Fatan ta Allah ya albarkaci rayuwarsa Ya daidaita al’amarinsa da iyalinsa.

Daddy ya dan numfasa sai ya dubi Mommy yace “

Rankidad’e, can I have a moment with my son.?” Ya k’arashe yana dan mata alama da ido.

Mommy tace “Badai cireni akai daga cikin ahalin ba.”

Ya dan murmusa kad’an “Waye ya isa ya cire ran gida cikin ahalinta. Magana ce tamu. Men talk.”

Ta d’an murmusa “

Kace dai kawai wariya. Toh bara na baku waje dama inada abinyi.” Ta k’arashe tana mik’ewa.

Daddy yai gyaran murya kad’an yace “Haidar banji dad’in abinda kai ba dukda sanin saki a musulunci ba haramun bane amma sai idan Ya zama dole akeyi. Idan akace dag

a samu sab’ani za’a dinga saki da ko mu nan iyayenka bamu kawo har wann lokacin muna tare ba. Kai shaida ne.. Kaga k’alubale da iftila’i na rayuwa da mukaita fuskanta. Amma dukda haka muka jajirce. Har hakuri ta kawo mu yanda muke yau. All marriages have u

ps and downs but this decision should not arrive easily.” Sai Daddy ya mik’e tsaye kaman Wanda ya tuna wani abu “Kaga tashi muje.. Akwai yanda nake so ka rakani.”

Haidar ya jinjina Kai yana amsawa. Suka jera suna tafe shida mahaifinsa. Ta window Mommy ta

hangesu sun jera Sun fice. A ranta tace ko ina D’a da mahaifin suka nufa sai Allah. Ta murmusa tana jin dad’in yanda sabo ya fara shiga tsakaninsu.

Koda suka fito Haidar ya tambayi Daddy ko Yai masa kiran driver d’insa amma sai Daddy yace a’a shi Haidar

d’in zai tuk’a motar. Nan ma cikeda girmamawa Haidar ya amsa masa. Daddy ya shige mazaunin mai zaman banza yayinda Haidar ya shige wajen driver. Suna tafe Daddy yace dashi gidan Alhaji Gimba suka nufa. Kai tsaye Haidar ya d’auki hanyar gidan aminin mahaif

in nasa.

Koda suka isa Daddy yace da Haidar yai parking daga waje. Nan ma yabi umarnin mahaifinsa. Suka fito Daddy na d’an gaba kad’an yayinda Haidar ke take masa baya. Sai Haidar yaga Daddy ya nufi masallacin k’ofan gidan Alhaji Gimba. Suka gaggaisa da

mutane ya tambayesu Ya Sheikh bai fito ba. D’aya daga cikin mutanen yace “Ai zai wahala Ya Sheikh ya fito yau sabida tun jiya yake cewa bai gane jikin ba.” Daddy yai masa fatan samun lafiya. Ya kuma yi ma mutanen Sallama Wanda kusan dukansu Dattijai ne kam

an sa da ma Wanda suka fisa. Da alama duk sun saba dashi dan tare suke d’aukan karatu a nan masallacin tsakanin sallar magrib da isha wajen Imam ya Sheikh.

Sun fito tareda Haidar kenan saiga Alhaji Gimba. Nan suka tsaya suna gaisawa. Haidar ya dan matsa

gefe ya basu waje.

Alhaji Gimba ya dubi Daddy ya dan girgiza kai “Lafiya dai naga ka taho tareda Haidar..?”

Daddy ya dan sauk’e ajiyan zuciya yace “Lafiyan zance ba lafiya ba tinda kanada masaniyar abinda ya faru lokacin bikin tariyarsa da iyalinsa.. T

inda Har business competitors dinmu sun so suyi amfani da wann su sokemu.”

Alhaji Gimba ya jinina Kai “Haka ne.”

Daddy yaci gaba “Toh Wato abinda ke faruwa shine.. Wann abu da ya faru har ya haifar da matsala tsakanin shi Haidar d’in da iyalinsa.. Kuma

kaga abu da yara tashi d’aya yayi saki.. Kasan da yawan samarin nan ba’a zama a fahimtar dasu menene ma Auren kansa kafin su shigesa which is wrong.. As a parent musamman ma Uba inaga yanada kyau idan D’anka yakai munzanin Aure ya kuma zo maka da batu na A

ure idan Har zaka nemar masa Auren ‘yar wani. Ko dai kai ka zaunar dashi ka fahimtar dashi menene Auren kokuma ka kaisa yanda za’a zaunar dashi a sanar dashi Auren tareda hakkokinta da hukunce hukuncenta.. Dan nima har yau ina nadaman wasu kurakuren da na

yi a baya kuma bana fata irin haka ya faru da D’a na. Idan ka duba da yawa yanzu Shiyasa zakaga mace macen Aure yayi yawa dan shiga cikin Auren kawai ake ba karatun sanin hukunce hukuncenta.. Shine kaga na kawo shi nan dan Sheikh Imam ya fahimtar dashi was

u abubuwa. Sai kuma akai rashin sa’a Sheikh yau bai fito majalisi ba.”

Alhaji Gimba ya jinjina Kai “Wann gaskiya ne Abokina. Ina ma iyaye da yawa zasuyi yanda kayi da an rage wasu mace macen Auren da babu gaira babu dalili. Amma tinda yanzu Sheikh baya na

n ni zan zaunar dashi mu d’an yi magana ta fahimta.. Kasan kai zai iya jin nauyinka a wasu abubuwan.. Sann idan son samu shima kasa ya dinga zuwa d’aukan karatu ko ba lokacin da muke ba.. Akwai lokacin da aka Ware dan samari kaman shi. Lallai yanzu Babu ma

i zama da jahiltan addini sai Wanda yaso.”

Daddy ya jinjina Kai “Wann haka ne.. Toh zan bar maka shi. Zan kira driver yazo ni ya d’aukeni.”

Alhaji Gimba yace “Akwai driver na ai sai ya kaika.” Nan sukai sallama Daddy ya sanar da Haidar shi zai tafi

A d’

an wani hut dake haraban gidan suka zauna yayinda Alhaji Gimba ya soma jan Haidar d’in da hiran Kasuwanci kafin ya d’anyi gyaran murya yace “Haidar, ni aminin mahaifinka ne nasan kasan da wann.”

Haidar ya jinjina Kansa a hankali. Alhaji Gimba yaci gaba “K

aman yanda musulunci yace abokan iyayen mu iyayen mu ne. Idan sunga munyi wani abu ba daidai ba zasu iya kiranmu su mana gyara.. Idan ma ta kama su tsawatar mana duk zasuyi.. Haka ne.” Nan ma jinjina kai Haidar yai. Alhaji Gimba yace “Ma sha Allah. wato Ha

idar, mahaifinka ya sanar Dani abinda ke faruwa, ba wai dan ya bud’e min sirrinka ba sai dan so da yake a samo maslaha.”

Haidar yai shiru yana sauraronsa.

Alhaji Gimba yaci gaba “Wato shi Aure wani abu ne da yakeda mahimmanci Haidar a rayuwar Al’umma g

aba d’aya. Dalilai da dama suna sawa ayi aure haka dalilai da dama Suna sawa Aure ya mutu Wanda ba’a so. Daga cikin dalilan mun sani Aure ibadah ne bautan Allah ne kuma d’abbaka sunnnar Ma’aiki (SAW) sann duk Wanda ya d’auki aure matsayin ibada bautan Alla

h zai samu dacewa da tsira harma da farin ciki a cikinta. Hakan nan Aure yana sa kamewa daga fad’awa tarkon zinace zinace. Kaman yanda yazo a hadisin Abdullahi Dan Umar Allah ya kara yarda a garesu. Yanda Manzo (SAW) yace yaku taron samari ga Wanda ya samu

iko daga cikinku yayi aure. Shi aure yana tsare gani sann yana kame al’aura. Har yake cewa ga Wanda bai samu hali ba toh yayi azumi. Shi azumi garkuwa ne.. Sann dalili na gaba samun nagartacciyar Al’umma. Ta hanyar Aure ake haihuwa a samu Al’umma nagartac

ciya. Bazamu fad’ad’a ba amma kaga ko wad’ann muka d’auka Sun ishemu dalili. Haka zalika shi Auren nan ba’a barmu kara zube ba saida aka koyar damu yanda zamu zauna cikinta ta fuskar shari’a da koyarwar addini. Ta yanda d’aya bazai zalunci d’aya ba a cikin

zamantakewar. Domin kuwa addinin musulunci addini ne mai kyau da tsari da kuma adalci. Haka zalika idan rabuwar Aure ta kama dole, Wanda ba’a fata toh nan ma saida aka koyar damu yanda zamu rabu bisa kyautatawa da mutuntawa.” Ya dan gyara zamansa kafin ya

ci gaba “In Islam, it is believed that married life should be filled with mercy, compassion and tranquility. Sann Zaman aure zo mu zauna ne zo mu sab’a.. Ko harshe da hakori watarana ana samun mishkila.. Toh idan an samu sab’ani ba haka kawai ake saki ba s

abida girman al’amarin.. Akwai hikima da musulunci ya saka saki hannun namiji. Dan idan mace ne zakuyi fad’a sau d’aya amma tana iya cewa ka saketa sau dubu. Kaga tunaninta da naka ba d’aya bane.. Hangen nesanka da nata ba d’aya bane.. Kai ko a halitta ta

fuskar k’iran jiki kaida ita ba d’aya bane. Ita haka Allah ya halicceta mai rauni kai kuma mai jurewa. So idan al’amara irin wann suka taso endurance dinka da tolerance d’inka ya kamata yafi nata. Idan an samu rashin fahimta ko matsala a zamantakewa a tsak

anin. Kuyi k’ok’arin samo maslaha tsakaninku ba sai third party ya shigo ba, idan kukai trying a tsakaninku still ba’a samu maslaha ba sai a saka manya ciki dan amfani manyan kenan. Bama a fata har takaiga zuwa gaban manya toh amma idan ya zama ba mafita s

ai a mik’a matsalar gaban magabata. Idan ya gagara a mik’a matsalar gaban jagororin Al’umma wato malamai. Idan shima baiyi working ba toh fah ka sani duk yanda ake son wani Auren rabuwan shi yafi alkhairi. Sann idan Allah ya k’addari ba sauran zama dole za

’a rabu.. Toh sai a rabu cikin mutuntawa da kyautatawa..” Ya dan gyara zamansa “Shin ya ma ake sakin.? Saki yana nufin furtawa. Intention na saki ba saki bane. Idan kace ma matarka zan sakeki, wann ba saki bane.. I intend to divorce you, this is not a divo

rce. I think we should get separated, this is not a divorce either.. It has to be a statement or a verb. In the sense that Na sakeki, .. Or you are divorced. Shikenan ta saku. Shi da yayi sakin yanada chances na kome guda biyu, idan yayi na uku babu kome H

ar sai ta auri wani mijin bashi ba. Idan miji ya saki matarsa sau d’aya, meaning one down two to go. Sann Anfi so matar ta zauna gidan mijin tayi iddarta. Akwai hikima da musulunci yace ayi hakan. Dan a wann zaman zai iya maida matarsa kuma ta maidu ba sai

anje ana biko da sauransu ba. Menene Iddah.? Shine waiting period after the divorce. Ga macen da batada juna biyu iddah period dinta shine 3 monthly cycles.. If she’s too old like If she’s in her menopause ma’ana wacce ta daina Al’ada ko kuma yarinya k’ar

ama wacce bata fara ba their iddah period is 3 months.. Idan mata mai juna biyu ce kuma iddarta shine ta haihu.. And this may be 2 months, 3months, 7months.. Depending on her pregnancy.” Sai ya dan gyara zamansa “Now, it is prohibited for a man to divorce

his wife a lokacin da take al’ada, or when she’s in the state of purity yet he had intercourse with her in that state of purity. An hana saki a wad’an nan lokutan. Wann shine saki na bidi’a. Innovated divorce. Mafi rinjaye Sun tafi akan it is sinful but v

alid. Ma’ana kuskure ne hakan amma matar ta saku. Idan mutum zai saki matarsa. God forbid, yet they had intimacy few days, few weeks ago. Musulunci yace he waits until she gets her menses. Idan tai tsarki ba’a samu intimacy ba sann sai ya saketa. Kaga zai

wahala ma yayi sakin idan har zai jira wann lokacin. Amma da yawa hakan baya faruwa sabida mafiya yawan sake sake cikin b’acin rai akeyi. Akwai hikima cikin duk abinda musulunci yayi umarni ko yayi hani..”

Yaci gaba da bayani kan hukunce hukunce da hakko

ki Haidar na saurarensa.. Har ya fara tuna nashi sakin da matarsa Wanda sun samu intimacy kafin ya saketa. Ya lumshe idonsa kad’an yana karanto istigfari. Har saida ya sinkayo muryar Alhaji Gimba yana tambayarsa “Be open with me Haidar. Shin kana son matar

ka.?”

Haidar ya jinjina masa kai “I love her with my life Uncle… But..”

“There’s no but if you truly love her..”

Jiki a sanyaye Haidar ya girgiza Kai yace “I choose to be the problem Uncle.. I choose to carry the burden..” Ya dan girgiza kai a hankali “

Mahaifiyata ta wahala sosai.. Tanada kurakurenta, but.. I can’t let her carry it all alone.. Bazan iya barinta ita kad’ai ta fuskanci matsalar ba sabida ita din ta fahimci kuskuren ta kuma ta tuba.” Yaci gaba da jinjina Kai “I choose to be her shield in th

is.. Idan hakan na nufin sitirta kuskurenta, even if it would destroy me.!” Ya k’arashe cikin yanayi mai ban tausayi.

Alhaji Gimba ya dubesa cikeda tausayawa. Yanada masaniya gameda family issue da ahalin Aminin nasa suka fuskanta. Yau Haidar ne yake sa

crificing farin cikinsa sabida mahaifyarsa lallai rayuwa ta sauya kuma Haidar ya cika D’an da za’ayi alfahari dashi. Sai yaci gaba da jinjina Kai a hankali murmushin saman fuskarsa yake duban Haidar d’in.

“Idan na fahimceka Haidar, kayi komai ne sabida m

ahaifiyarka. Kuma duk d’a nagari irin haka zaiyi.. Ba ina nufin sakin ba.” Ya d’anyi gyaran murya “Ka zab’i ka sadaukar da farin cikinka sabida mahaifyarka.. Amma rabuwa da iyalinka bazai zama mafita ba. Bansan menene wann kuskure na mahaifyarka da Kake so

n sitirtawa ba, ka sani duk Wanda Ya rufa asirin wani musulmi Allah zai rufa nasa ranar gobe balle Mahaifiya. Saidai akwai hanyoyi da dama da ake bi dan shawo kan matsala. You can’t let yourself be destroyed in the process.. Because Destruction is not the

solution and

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login