Showing 111001 words to 114000 words out of 267381 words

Chapter 38 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

81

ba da kuma dalilinsa. I need to investigate first.”

Dr ya jinjina masa kai “Bakada matsala Engr. If you excuse me. Zan koma bakin aiki.”

Haidar ya jinjina

masa kai kafin suka mik’e a tare suna masabaha cikin mutunta juna.

Sanda Haidar Ya fito ya iske Mommy da Anisa duk sunyi tsuru tsuru alamun suna jiran ba’asi. Babu ya Mommy. Kallo d’aya zaka mata ka fahimci a hargitse take. Ta k’araso da sauri tana tamb

ayarsa Ya jikin Ummul mai Drs suka ce.?

Haidar bai kaiga bata amsa ba dan har lokacin mamakin matar yake Wanda Ya girma ya sani matsayin mahaifiyarsa.

Wayar Mommy ne yai ruri Daddy ke kiranta nan ta matsa gefe tana amsawa dan ita Har ta mance ranan Dadd

y ke dawowa Nigeria.

Bayan ta Ida wayar ta dawo garesu tana duban Haidar Wanda ya tsareta sosai da ido kaman mai tuhumar ta.

A d’an daburce tace “That was your Dad. Gaba d’aya na mance yana hanya sabida tashin hankalin nan da muka tsinci kanmu ciki. Dr

iver yana hanya zaizo Ya tafi dani.. Yanzu yarinyar ce bansan da waye zamu barta ba.”

Anisa tai karaf tace “I’ll stay here with her.”

Ga mamakinsu muryar Haidar suka sinkayo “No, I’ll stay with her. Kuna iya tafiya Mommy. After all, abinda kike so kenan

na dawo na zauna da ita. Right.?” Ya k’arashe yana tsare Mommy da ido.

K’ak’aro murmushi Mommy tai tana jinjina masa kai alamun eh. Yayinda Anisa tai mutuwar tsaye tana kallon abun mamaki wai Haidar zai zauna a asibiti da wann bagidajiyar.? Ikon Allah. W

ai meke shirin faruwa ne.? Anya Haidar bai kamu da son bagidajiyar nan a kallon farko ba.? Sai tai saurin girgiza kai alamun a’a tana mai kwaban zuciyarta da irin wann tunani maras kan gado. Abu ne da bazai tab’a faruwa ba ko a mafarki. Haidar would never

ever fall for someone like her. Muryar Mommy taji tana fad’in suje driver yana close Daddy na gida na jira. Anisa tabi Mommy jiki duk a mace sai waigowa take tana duban Haidar da Ya tsaya kaida fata wai shi zai zauna wajen Ummul. Gaba d’aya mamaki ya kasa

sakin Anisa.

Suna isa gida ta shige d’aki tana faman safa da marwa tana tunanin kiran Leenah dan ta sanar da ita halinda ake ciki. Bata Ida tunanin ba taga wayar Haidar na shigo mata. Zuciyarta yai wani irin tsinkewa sai tana ganin kaman Haidar Ya fahimc

i cewa ita tai poisoning Ummul. Da kyar ta iya d’aga kiran zuciyarta sai harbawa yake dan tsoro.

Daga d’aya b’angaren Haidar yace “Kina jina. Kije d’akin yarinyar nan ki tattaro mun duk wani perfume dake d’akin ki kawo mun shi asibitin right this instant

. Ina jiranki..” Ya k’arada Kar ki bari Mommy ta ganki ko ta fahimci wani abu. Understood.?”

Anisa da zuciyarta bai daina tsinkewa ba a d’an daburce take jinjina kai “Oh ok.. Zanyi yanda kace.”

Jinjina kansa yai kaman tana ganinsa kafin ya k’ara tabbata

r mata da yana jiranta yanzu yanzu. Daga haka katse kiran yai Anisa kaw gijif ta zauna cikin kujera shikenan asirinta Ya tonu Dr ya sanar da Haidar guba aka saka ma Ummul cikin turare. Yanzu mai zatai..? Taje ta fasa turaren ne ko ta kai masa ne.? Amma ida

n ta kai masa ta kama kanta ne.. A fili ta furta “Oh no Neesa.. This is not happening. You screwed up again.!” Ta kuma rintse idonta tana tunanin abin yi. Cikin sauri ta d’ago wayarta . Jikinta har na wani irin kyarma ta shiga neman layin Leenah dan samun

mafita.

Leenah tana zaune taga kiran Anisa na shigo mata. Ta saki murmushi a hankali kafin ta furta “My stupid friend is calling again.” Ta kuma sakin murmushi kafin ta d’aga wayar.

A birkice Anisa ta soma fad’in “Leenah komai Ya lalace.. Our plan didn

’t succeed.. I’m afraid I messed up everything again..!”

“Girl calm down..! Just… What are you trying to tell me..?” Leenah tace cikin dakatar da Anisa.

A tak’aice Anisa ta bama Leenah labarin duk abinda ke faruwa Har kawo yanzu da Haidar Ya bata tax na

kawo masa duka turaren da suke d’akin Ummul. Anisa ta k’arada “Leenah what if he he suspects me.. What if he finds out about the truth cewa ni ce nan na zuba poison din..?”

Leenah ta rausayar da idonta “Here you are being paranoid again Neesa. Ta ya za

i zargeki idan ba kece kika basa k’ofa ba. Base on abinda kika ce. Idan har Haidar ya baki tax na kai masa turaren hakan na nufin Ya yarda dake ne.”

Anisa ta katseta “Nifa Leenah mafita na kiraki ki bani ba wai kimin narrating abinda na gama baki labari b

a. What if I destroy the perfume..?”

Murmushi Leenah tai “Idan kikai destroying turaren shine kin basa room na suspecting d’inki… You know what Neesa, You always call me a moron. But you are the one acting foolish here. Idan har kika lalata turaren nan no

doubt Haidar zai zargeki. Idan kuma ya zargeki ki tabbata sunana bai fito ba. Sabida nida kike gani inada burin aure da samun family of my own bana mafarkin karasa rayuwata a jail.” Ta numfasa “But wait.. A yanda kika bani labari Haidar yace kar ki bari m

ahaifiyarsa yasan kin kai masa turaren.”

Anisa ta jinina kai alamun eh kaman Leenah na ganinta kafin Leenah taci gaba “Then let him suspect his mother.. Incriminate her. After all, kin sanar dani turaren da kika zuba poison din ma Ummul ciki turaren da Mo

mmy ta baki ki bata ne kika canza da wani. Ya zo gidan sauk’I Anisa. Mahaifiyarsa itace ta bada wann turaren mai guba aka zuba ma matarsa ciki.!”

Dummm.! Haka k’irjin Anisa ya buga. Leenah fah cewa take tai incriminating Mommy. Mahaifiyar Haidar..?

A ha

nkali Anisa ta soma girgiza kai…

SameenaAleeyou

📚

*AUREN WATA UKU..!*

*32*





Sameena Aleeyou…✍

🏽

*

Anisa taci gaba da girgiza Kai tana duban wayan. Mommy fah.? Ta ya zata soma d’aura ma Mommy laifi.? Bayan kasancewar ta mahaifiyar Haidar ita

d’in fah ‘yaruwa take ga mahaifiyarta. Idan Abu ya lalace ba rasa Haidar kawai zatayi ba harda zumuntar iyayenta zata b’ata. Amma mai zatayi..? Ita kad’ai tana sak’awa da warwarewa ta kuma kiran Leenah dan ta gaza samun mafita.

Leenah ta rausayar da ido t

ace “Haba Neesa ya kike abu kaman wata bagidajiya.”

“Ban kiraki just for you to insult the hell out of me ba Leenah. Na fad’a Miki hujjojina if things go wrong. It will definitely be the end of me Leenah..!”

Leenah ta kuma rausayar da ido irin yanda Anis

a take kaman dai Anisa na kallon ta “Toh banda abinki Anisa. Abun nan fah a bayyane take turaren da mahaifiyarsa ta ba ma matarsa akwai poison ciki ke meye naki a ciki.? Idan akwai wacce za’a zarga bazai wuce Hajiya Kwaise Maitama ba. Unless kuma zaki b’ul

lo ta wani hanyar kisan yanda zakiyi ki kutsa cikin d’akin da Ummul take ki k’arasata amma fah wann yafi had’ari Anisa because you would easily get caught. Hanya d’aya shine ki kyale mahaifyarsa ta d’auki laifin nan because he already grows suspicious of h

er idan har zaice ki aiwatar da Abu ba tareda saninta ba. Kuma kinsan me matar nan fah mahaifyarsa ce he would forgive her, definitely. Even if she’s convicted sabida ita d’in mahaifiyarsa ce amma ke fah kika kuskura kika bari ya kamaki kashinki ya bushe N

eesa ba hannun Haidar kawai ba harda hannun uwarsa.”

Anisa ta jinjina Kai idanunta na kuma k’ek’ashewa “You are absolutely right Girl. After all, Haidar baya son wann auren tai masa. Akwai tarin tanbayoyi da ya kamata yai ma mahaifyarsa.” Ta k’arashe tan

a sakin murmushin cin nasara. Lokaci guda ta katse kiranta da Leenah ta soma shirin fita. Nan taga wayar Amminta na shigo mata.

Ta rausayar da ido kafin ta d’aga kiran mahaifiyarta “Yes Ammi. I guess labari ya isa miki.” Tace tana kuma juya ido.

Daga d’a

ya b’angaren Asshe tace “Da uban wa kiketa waya ina nemanki..?”

Anisa ta kuma juya ido “Abinda kika kirani kice kenan kawai Ammi.?”

“Ke bani son shashanci.. Wai meke faruwa ne a gidan Aunt d’inki da banji daga gareki ba. Ko kin mance na barki a can ne ma

tsayin ido na. Ki sanar Dani meke faruwa tsakanin Haidar da yarinyar can. Shin kin bata wann turaren ne da nace ki zubar.?”

Anisa ta murmusa “Of course ban bata ba Ammi..Kuma na canza turaren kaman yanda kika umarceni.. Amma saidai..”

Zuciyar Asshe yaci

gaba da tsinkewa tinda tasan kalan shashancin ‘yar tata “Amma me Anisa..? Meye kika aiwatar ba tareda sanina ba. C’mon tell me.. Meye kika aiwatar.?”

Juya ido Anisa ta kumayi a hasale ta katseta “Nayi poisoning turaren da na canza mata dashi..” Ta juya i

do tana jan tsaki “She’s like a cockroach Ammi. Duk irin tuggun da nake k’ulla mata taki mutuwa kaman dai kyankyaso.!”

K’iris ya rage Asshe bata saki wayarta ba. Baki na rawa take furta “Anisa kece kika zuba guba ma mutum..?Anisa waye ya aikeki.. Are you

that dumb.? Bance Miki ki bar min komai ba zan kula da komai..? Bance miki kar ki yanke wani hukunci on your own ba.? Anisa kanki Kalau zakiyi kisan Kai kan namijin da baisan kinayi ba.?”

Tsaki Anisa tai “There you go again Ammi. Very soon nida Haidar zam

uyi aure as soon as wann makirar is out of the picture. And please do me a favour Ammi. Duk abinda zaki ji ko ki gani naki ido.” Tana Ida fad’in haka ta katse wayan. Asshe na k’ok’arin dakatar da ita amma inaa tuni ta kashe.

Tuni Anisa tayi kaman yanda H

aidar ya umarceta. Sanda ta kawo masa turarukan asibiti sai ta dubesa da mamaki “Amma me zakayi da turare a asibiti.? Kodai Ummul d’in ce ke so.. Amma idan itace ke son a kawo mata definitely zai kasance wann ne.” Ta k’arashe tana juya kwalban turaren ciki

n hannunta ga damuwa saman fuskarta kai kace zallan tausayin Ummul din ke d’awainiya da ita.

Haidar ya tsareta sosai da ido sai ya girgiza Kai kad’an “Meyasa kikace haka.?”

“Because it’s her favourite.” Ta dan murmusa cikeda makirci tana nuni da tausayi

sann taci gaba “Mommy ce musamman ta bata turaren nan. Ummul tana son turaren sosai. Allah sarki Allah ya bata lafiya. At first bama wani jituwa amma daga baya I have become fond of her sabida tanada zuciya mai kyau. Kowa yana sonta a gidan especially Mom

my.” Ta k’arashe tana share guntun hawaye da ya gangaro mata.

Ba wai yana sauraron surutan da Anisa ke masa bane tinda yaji key points din da yake son ji ya daina gane mai take cewa sabida ta cika masa kunnuwa.

Dakatar da ita yai da fad’in “You can go n

ow. And don’t say a word to Mommy. Are we clear.?”

Anisa ta jinjina masa Kai tana mai tabbatar masa bazata sanar da Mommy komai ba. Bai kuma bi ta kanta ba yasa Kai yai shigewarsa. Anisa tabi bayansa da kallo yanda ya shige hannunsa rik’eda turarukan cik

in dan jaka.

Murmushi ta saki dan ta tabbata ko gwaji akai aka gano turare mai d’auke da guba ciki Mommy ce zata rufta. Sann ne zata b’ata sunan Ummul a wajen Mommy dan ta tabbata idan har aka d’aura ma Mommy laifi zata tsani Ummul ne taji ta fita akanta

. Zatai amfani da wann daman ta cire ma Mommy son Ummul cikin zuciyarta tinda dama ita kad’ai ke son wann jarababben aure. Zuciyarta wasai ta dauki hanyar gida.

**

Tsaye Haidar yai gaban gadon da Ummul ke kwance bayan an fito da ita daga surgery. Yai m

ata k’uri yana dubanta. Tanbayoyi da dama cikin zuciyarsa. Cikin zuciyarsa yake jero tanbayoyin da baida amsoshinsu ‘Who are you..? Maiyasa Mommy zata farauci rayuwarki.? Shin Mommy ta kawoki ne dan ki zame mata hanya mafi sauk’i wajen ganin bayan rayuwa n

a.. Kina sane da shirin Mommy akaina.? Da yarda da amincewarki ki ka zab’i ta cutar dake dan kawai ta cimma burinta akaina ko kuwa dai kema victim din Mommy ne.?’

Daidai lokacin Dr ya turo k’ofa ya shigo. Ganin Haidar tsaye ya saka Ummul gaba wacce ke kw

ance unconscious saman gado. Ya saki murmushi “Engr da alama kana ji da matar nan taka sosai. Kar ka damu in sha Allah bazata wuce kwana biyu bata bude ido ba. Alhamdulillah the surgery was successful and we can now say she’s out of danger in sha Allah.”

Har lokacin dubanta Haidar yake. A hankali ya kaikaito ya dubi Likitan “Har sai an Kama Whosoever is responsible an kuma tsaresa sann ya biya abinda ya aikata.” Daga yanda yake maganar zaka fahimci tsananin son daukan fansa cikin muryarsa. Mommy kawai yake

hangowa cikin idonsa zuciyarsa na tabbatar masa wann shine daidai lokacin da ya kamata ya d’auki fansar duk abinda matar nan ta jima tana masa. Sann lokaci yayi da zata fayyace masa komai idan ma sato shi tayi duk sai ta fad’a. Bazai barta ba sai ta fayya

ce masa komai gameda gaskiyan lamarin da ya danganci rayuwarsa.

Dr ya jinjina Kai yana duban Haidar din dan dik shi a nasa tunanin tsananin soyayyar da Haidar keyi ma matarsa yasa yaketa k’ok’arin ganin ya kamo mai laifin. Ya dan numfasa “The laborator

y test for the perfume would take less than 24hrs. Zuwa gobe da safe in sha Allah zamu tantance wane turare ne mai guba cikinsa.”

Haidar ya jinina masa Kai Dr ya k’arada “Engr.. Emm nace are you spending the night here with the patient.?” Sai ya k’ara da

“Kar ka damu if you have some matters to attend to kana iya tafiya.. You can be sure she’s in good hands.”

Ba tareda ya dube Likitan ba yace “I’ll be staying here Doc.” Ya k’arashe yana mai zama saman soft sofa dake can gefe da gadon. Gani yake kaman zata

bud’e ido ta soma amsa masa tarin tanbayoyinsa.

Dr ya murmusa kafin ya jinina Kai yai Sallama ma Haidar ya fice.

Haka Haidar yai zaune ya sakata gaba yana kallo. Yana ganin wayoyi na shigo masa amma baida lokacin daukan ko d’ayansu. Shi dai burinsa saf

iya tayi hunch d’insa ya tabbata Akan Mommy.

**

Dareen sai safa da marwa take tana kuma duba time. Bai tab’a kaiwa irin wann lokacin bai dawo gida ba. Tinda sukai aure bai tab’a kwana waje ba. Ko aiki ya rik’esa a Office komin dare sai ya dawo gida ya k

wana. Toh wai meke faruwa ne. Wane irin al’amari ne wann..? Ta kasa zaune ta kasa tsaye. Tana son sanin wani hali Haidar ke ciki. Hakan yasa ta yanke shawarin zuwa gidansu Haidar din kawai. Komai ta fanjama fanjam. Idan ma zasu hadu da iyayen Haidar for th

e first time ne ita kam gwara taje tasan meke faruwa dashi tinda gashi baya ko daga wayarsa.

Wata Zuciyar kuma ta soma raya mata toh kodai Shadow ne ya Sace Haidar to teach her a lesson tinda ga irin rabuwar da sukai a waya da Shadow d’in. What if Shadow

ya cutar da Haidar.? What if wani Abu ya samu Haidar.. No bata fata.. She wouldn’t be able to take it idan wani Abu ya samu Haidar d’inta. Jikinta na rawa ta soma kiran layin Shadow “Tell me. Do you have Haidar.. Did you kidnap him.. Ka sanar Dani mai kay

i ma Haidar..?” Ta k’arashe hankalinta duk a tashe sai rawa jikinta keyi.

Murmusawa Shadow yai cikeda k’asaita daga d’aya b’angaren “Har kin sare ne..? Da wuri haka.?”

Ta dan furzar da huci kad’an hankalinta na kuma tashi. Sai ta sassauta murya tace “Pl

ease don’t do anything to him.. Dan Allah kar ka cutar da Haidar.. Na yarda daga yanzu zanyi duk abinda kace amma dan Allah kar ka cutar min da Haidar..!” Ta k’arashe kaman mai shirin kuka.

Shadow yai wata dariya irinta basawa “Dareen Dareen.! Yanzu kin t

abbata I have both you and Haidar wrapped around my fingers. You don’t want to mess with me Dareen.”

Ta lumshe idonta a hankali tana mai sadda kai kasa kaman yana ganinta “Forgive me.! It won’t happen again.. Please don’t do anything to Haidar.. Nayi alka

wari bazan sake sab’a umarninka ba ko gaban Dodo akaje.”

Yai murmushi cikeda k’asaita “Good girl. Now that you realise your place, I want you to tell me where the hell is Haidar.?”

Mamaki ya cika Dareen. Ta girgiza kai kad’an “What do you mean.. Kana so

kace min you don’t have Haidar.?”

“I wouldn’t be asking you the same question if I have him.. Dareen wai meke damunki ne.? Shin amfanin ki Ya k’are wajen Haidar ne.? Are you that insignificant to him.? Do I need to replace you with another woman for me to

push through with my plans.?”

Saurin katsesa tai “No please.. Wllhi amfanina bai k’are ba.”

“Then what the hell is the problem..?!” Kaman kunnenta zasu fice sabida sautin maganar.

Jikinta na rawa take fad’in “Na fara zargin mahaifiyar Haidar ke yunk’

urin rabamu.. Watak’ila ta gano cewa Haidar din yayi aure a b’oye ba tareda saninsu ba. Duk wasu calls da yake da ita yake tun muna Cuba. Idan ka mun izini zan tafi gidan su Haidar yanzu mai faruwa ta faru. Let them find out about me and Haidar.”

Shadow y

a daka mata tsawa da fad’in “Don’t you dare show your face to Kwaise Maitama.! This is not part of the plan. Bazasu san dake ba har sai ahalin Ya tarwatse ya lalace. Har sai sud’in sun yak’i junansu da gaske. Idan Har kika nuna kanki yanzu fad’an zai dawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login