Showing 192001 words to 195000 words out of 267381 words
it will never be. Mahaifyarka sai tafi shiga tashin hankalin idan har hakan yai destroying d’inka. You are a man, and you supposed to act like one.. Be brave enough to face your problems..Kar ka guje ma matsalolinka dan idan ka guje masu zasu
bibiyeka ne har k’arshen rayuwarka.” Ya dan numfasa “I’ll ask you this question again, do you love your wife.?”
Dubansa kurum Haidar keyi, ya shiga jinjina Kai ba tareda ya iya furta koda kalma ba.
Alhaji Gimba ya jinjina Kai “Then what are you waiting
for, go and reconcile with your wife. Kaje ka dawo da iyalinka.”
Sai Haidar ya d’anyi shiru yana tunanin irin k’iyayyar da ya hango a kwayar idanun Ummul. Ya sani a halin yanzu Babu abinda tafi tsana Watak’ila sama dashi.
Jin yayi shiru yasa Alhaji Gimb
a murmusawa yace “Bansan Aliyu da rashin k’warin gwiwa ba dukda ance rauni na cikin soyayya.” Ya k’arashe cikeda barkwanci.
Sai Haidar ya d’an k’ak’aro murmushi yana jinjina Kansa “In sha Allah Uncle, zan dawo da ita. Kuma bazan tab’a sarewa ba. Na gode
k’warai.. Allah ya saka da alkhairi ya k’ara girma.”
Alhaji Gimba ya murmusa “Yanzu naji Zaki na magana. Allah ya maka albarka ya mana jagora.”
Haidar ya amsa da Ameen had’ida k’ara godiya ma Alhaji Gimba.
Alhaji Gimba ya mik’e suka jera zuwa motan Hai
dar a tare tamkar yana ma Haidar d’in rakiya.
Haidar bai tab’a tsammanin rana irin wann zata zo ba. Mutumin da a baya yake masa kallon tarayyarsa da mahaifinsa babu wani alfanu. Mutumin da yai masa mummunar fahimta a baya. Sai gashi yau wann mutumin ya z
amto tamkar mutumin da ya jefa masa igiya cikin rijiya mai duhuwa yace ya kama ya fito. Tabbas zaka k’i wani abu wann abun alkhairi ne a gareka, zaka so wani abu wann abun sharri ne a gareka.
Fatan alkhairi Alhaji Gimba ya kuma yi ma Haidar d’in. Ya ku
ma ce a duk lokacin da wani abu ya shige masa duhu ko yake nema shawari his door is always open yazo ya samesa matsayin Uba a wajensa. Godiya Haidar ya kuma masa cikeda girmamawa kafin ya wuce.
Tinda ya fito daga gidan Alhaji Gimba yake ji kaman ya k’ara
masa k’warin gwiwa ne.. Yayi alk’awarin zai jira Ummul Har tayi healing koda zai d’aukesa tsawon shekaru ne.. Amma yau da Alhaji Gimba ya nusar dashi zai iya wasa da damarsa sai yaji bazai iya jira ba. Zai tafi yayi yak’in dawo da Ummul cikin rayuwarsa da
taimakon Allah.
Washe gari sassafe yai shiri da zummar d’aukan hanya garin Kano. Ya shigo ya gaida iyayensa sann ya k’arada “Daddy, Mommy.. Ina so zan tafi garin Kano yanzu.. Zanje na dawo da Khairy.”
Farin cikin Mommy ya gaza b’uya. Duk a ‘yan kwanaki
n ta kula ko zancen Haidar baiso a masa sai gashi yau yace zaije ya dawo da matarsa. Suka saka masa albarka tareda fatan alkhairi.
Daddy ya dakatar dashi.
Mommy ta dubesa da mamaki. Sai Daddy yace da Haidar ya jirasa a mota yana nan fitowa.
Mommy tace
“Engr. Ya naga ka tsayar dashi..?”
Ya murmus “With your permission Rankidad’e, I’m going with him.. I want to be a father to my son..”
Har k’walla saida suka ciko idon Mommy. Ta tuna farkon Auren Haidar da Ummul d’in Daddy cewa yai ba hannunsa ba ruwansa
tayi yanda take so da rayuwar D’anta. Yau sai gashi ya saka kansa tsamo tsamo a al’amarin Haidar d’in.
Ta murmusa tace “Toh kodai nima nayo muku rakiyar ne.?”
Daddy ya girgiza Kai yana d’aura wristwatch d’insa “A’a wann tafiya ce tamu ta maza. Daga bay
a sai kiyi naki.”
Murmushi kawai Mommy tai ta musu fatan sauk’a lafiya baida dacewa.
**
Koda suka isa garin Kano sun samu an kaisu Har k’ofar gidan Malam Isubu mai Manja kaman yanda aka fi saninsa.
A farfajiyan gidan aka saka masu tabarma daga nan k’o
fan su Ummul d’in dan Tani bata bari ‘yanuwan Mahaifin Ummul da suke uba d’aya Wanda suka amshe kudi hannun Asshe farkon Auren Ummul d’in sun shiga cikin maganar ba, sanin abinda ka iya zuwa yazo. Dukda maganan na maza ne amma kamawa take Shiyasa tazo waje
n tinda tasan da cewa akan kudi ba abinda su d’in bazasuyi ba. Sann basu san da mutuwar Auren Ummul d’in ba. Bayan sun gaisa Nan take sanar dasu Daddy har kawo wann ranan basu saka Ummulkhairi a idonsu ba. Sun bincika duk yanda ya kamata amma babu labarint
a.
Haidar ya dubeta cikin shock “Khairy bata nan..? Toh ina take.?”
Tani ta sauk’e ajiyan zuciya “Duk yanda ya kamata mu bincika gidan ‘yanuwa da zuri’a mun bincika amma Babu labarinta. Tin a lokacin naso mu koma mu sanar daku halinda ake ciki amma mahai
fiyarta tak’i hakan. Ta d’auki duk laifin ta aza ma kanta..A cewarta wann hukuncinta ne take karb’a.. Sannan har rana mai kaman wann Mahaifin Ummulkhairi dake cikin jinya baisan Aurenta ya mutu ba.. An dai sanar dashi tayi Aure a haka yana jinyar amma bais
an da wann labarin ba dan jinyar tashi abu ne da ya danganci zuciya. Likitoci suna bada shawarin ba komai za’a sanar dashi kai tsaye ba duba da irin yanayin jinyar. Sann baisan da cewa mu kanmu bamu san yanda Ummulkhairi take ba.”
Haidar yaci gaba da girg
iza kai yana duban Daddy “This is all my fault Daddy.. Duka laifina ne.. Daddy idan na rasa Khairy.. Bansan ya zanyi ba..” Ya k’arashe cikin tsananin nuna damuwa.
Daddy bai kaiga furta kalma ba Azeema ta fito da murmushi saman fuskarta. Kai tsaye ta furt
a “Bazaka rasa ‘Yaruwata ba Sirkinmu Dangayu. Domin kudin kuna son junanku.. Naga haka a k’wayan idonku.. ‘Yaruwata..” Bata kai aya ba Khulsum ta fito da sauri dan dama tin baya dawowar su Umma daga Abuja suka d’auko Khulsum da Abba daga gidan Inna Dije. T
ani ta kuma d’inke bakin Inna Dije da fad’in idan taji fit wani abu ya fita daga bakinta ya karad’e dangi gameda Auren Ummul toh ta tabbata itama nata Auren ya Mutu kenan sann itada D’anuwanta Malam Isubu har abada.
Khulsum ta girgiza kai tana duban Azee
ma “Kiyi shiru Azeema..”
Duk sai suka maida dubansu ga Khulsum da Azeema.
Azeema tace “Khulsum ki k’yaleni na sanar dasu.. Baki gani ne Yayanmu naso ya maida matarsa.. Meyasa bazaki bari a sanar dasu ba..”
Khulsum na huci tace “Sabida ‘Yaruwata tace bat
a so a sanar dashi.. Sabida ita d’in bazata tab’a komawa gareshi ba.” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata.
Haidar da baisan tuni ya mik’e tsaye ba ya isa gaban Khulsum yana girgiza kai “Kinsan yanda Khairy take..? Tell me, where is she.. Where can I find h
er.?”
Ta dubesa sai ta kauda fuskarta gefe tana share hawaye.
Haidar ya kuma jefo mata tambaya “Please tell me, kinsan yanda take..? Ina take.. Dan Allah ki sanar dani..”
Azeema tace “Bazata sanar dakai ba. Dan nima bata sanar Dani ba.. Kaf gidan nan ba
bu Wanda ta sanar dashi. Nima abinda yasa naji tana waya ne na lab’e na saurara nan naji da Addarmu Ummulkhairi take waya.”
Mama Tani ta mik’e tana duban Khulsum “Ke Khulsumu meke faruwa..? Yanzu dik irin d’aga hankalin nan da kikaga munyi munata neman Um
mulkhairi dama kinsan yanda take.. Shine kika kyalemu cikin duhu.. Muna nan muna tunanin Har yanzu fushi kike da ita Shiyasa baki tada hankali wajen neman ina take ba Ashe kina sane..”
Kuka Khulsum take tana girgiza kai “ ‘Yaruwata bata sanar Dani yanda t
ake ba.. Amma nayi waya da ita kuma ta sanar dani cewa tana nan lafiya kar na damu ta kuma tambayeni jikin Abba.. Sann tace na kula da Umma kuma na nemar mata yafiyar Umma.. Sann..” Sai ta dubi Haidar da yai mutuwar tsaye yana dubanta, taci gaba “Sann tace
ko ka zo nemanta kar na sanar dakai cewa munyi waya.. Dan har abada bataso ta sake ganin ko mai kamanninka..” Ta k’arashe tana mai fashewa da kuka.
Cikin wane irin yanayi Haidar ke furta “No please.. Don’t do this.. Please tell me.. Tell me idan ta sanar
dake yanda take.. Ko kuma.. Ina layin da ta kiraki dashi..” Duk a daburce yake.
Khulsum ta girgiza kai “Ta rufe lamban bai fito ba..”
Ya lumshe idanunsa yana dafe kai “No.. There has to be something.. Just think please.. Or maybe we can try to retrieve
all the calls from your line.. And see if we can track the number..”
Ganin duk ya daburce yana neman ficewa hayyacinsa yasa Daddy d’an yin gyaran murya yace “Haidar, taho nan ka zauna.. Abi komai a sannu..” Ya dubi Khulsum yace “ ‘Yanmata jeki abinki ko.
” Khulsum ta risina ta tana mai jinjina kanta kafin ta shige tana share ragowar hawayen da suka zubo mata. Azeema na take mata baya.
Tani ma ta dawo mazauninta ta zauna.
Daddy ya dubi Haidar yai gyaran murya “Haidar ina so ka natsu ka kuma natsa zuciya
rka. Yanada kyau mubi komai cikin lumana dan tada hankali bazai tab’a kawo mana maslaha ba. Idan har Ummulkhair tana cikin k’oshin lafiya wann ma abun mu gode ma Allah ne. Kuskure ne an riga anyi shi dama kuma shi gyara sai a hankali.”
Tani ta jinjina kai
“Wann gaskiya ne.”
Daddy ya kuma jinjina kai kafin yace “Amma yaya jikin Maigidan..? Yana asibiti ne Har yanzu kokuwa..? Mai likitoci suka ce gameda rashin lafiyar nasa.?”
Tani ta dan gyara mayafinta “Toh jiki Alhamdulillah zamu ce. Sann asibiti kuma sa
i jikin ya d’anyi tsanani ake zuwa.. Yana nan a gida. Saidai maganar ne ba sosai ba.. Amma yakan fahimci wasu abubuwan.. Rahotannin asibitin nasa duk yana wajen d’iyarsa Khulsumu dan kusan tareda ita akai jinyar nasa gaba d’aya. Ba abinda zamuce ma yarinya
r saidai Allah shi mata albarka.”
Daddy ya jinjina Kai yana fatan lafiya ga Abban kana ya mik’e yace “Ko zamu iya ganin shi.?”
Tani ta jinjina kai “Eh yana d’aki yana kwance. Mu k’arasa. Bismillanku..” Tai gaba Daddy da Haidar na biye da ita suka nufi wa
ta ‘Yar k’aramar k’ofa da zai sadaka da d’akin Abba.
Suka d’an tsaya daga waje kafin Tani ta shiga ta tadda Umma ciki nan take sanar da Umma su Haidar da mahaifinsa zasu shigo su gaida Abba dama tuni Tani d’in ta sanar da ita zuwansu.
Umma ta gyara zama
nta ta dan gyara Abba ma kafin ta rufe kanta da mayafi, Har rabin fuskarta saida ta rufe sabida surkunta.
Tani Tai masu iso. Daddy ya soma d’an rage tsawonsa ya shige d’akin Haidar na biye dashi.
Suka gaisa da Umma suka tambayi mai jiki kafin Tani ta d
’an matso kusan Abba tana sanar dashi ga Surkin Ummul da mai gidanta zasu gaishe shi.
Allah sarki Abba sai ya soma k’ok’arin mik’ewa jin an ambaci Maigidan Ummul d’insa da surkinta. Daddy yai saurin taimaka masa yana masa sannu da jiki dukda muryar Abban
ba wani sosai yake fita ba.
Bayan sun gaisa da Daddy sai ya fice amsa wayarsa dake ruri.
Cikin muryarsa da bai fita sosai irinta majinyaci mai Jin jiki Abba yace “Ina Maigidan Ummulkhairina.?”
Haidar ya k’araso cikeda risinawa yana gaida Abba zuciyars
a ya kuma cika da tausayin Khairy da ahalinta. Sai Abba ya soma k’ok’arin d’ago hannu yana mik’a ma Haidar alamun yana so suyi masabaha. Haidar yai saurin tallafo hannun Abban ya rik’e cikin nasa suka gaisa. Sai yaji Abba ya rik’e hannunsa gam yana fad’i d
a kyar “Kaine Aliyu mijin Ummulkhairi na..?”
Sai Haidar ya jinjina kai a hankali “Eh.. Eh Abba ni ne..”
Abba yaci gaba “Ina matuk’ar son ‘Yata Ummulkhairi, tanada zuciya mai kyau.. Ka rik’e mun.. Ita da amana kaji koh..”
Dukda tausayin Abba had’ida wan
i abu mai kama da rauni da Haidar keji yana taso masa tin daga can k’asar zuciyarsa bai hanasa jinjina Kai cikin sauri, ya soma furtawa cikeda k’warin gwiwa “In sha Allah Abba.. Zan rik’eta… Zan rik’e Khairy amana.. Na maka alk’awari.!”
Abba ya murmusa
had’ida jinjina kai sai kuma yace “Ina Ummulkhairi.. Maiyasa bata biyoka ba..? Na jima ban ganta ba. Ina kewar.. ‘Yata sosai.”
A nan ne kuma jikkunansu gaba d’aya yayi sanyi. Babu ya Haidar Wanda ya gama d’aukar ma majinyacin mutumin alk’awarin kular masa
da ‘yarsa wacce baisan ina take ba.
Sai Tani Tai karaf tace “Ai.. ai laulayi take… K’aramin juna gareta shiyasa bata samu zuwa ba.” Ita kanta Tani da tai maganar saida taji banbarak’wai. Yayinda Umma tai saurin dubanta da idanunta masu cikeda rauni. Shi
kaw Haidar sai ya sadda kansa kad’an.
A haka dai Har suka fito zasu tafi. Baffanin Ummul guda biyu da suka amshi kud’ad’e hannun Asshe suka bada Auren Ummul d’in nan suka jeru suna jiran fitowar su Haidar ganin hamshak’iyar motar da ke k’ofar gidan nasu
. Sai jinjina lamarin suke suna fad’in albarkacin bakinsu gameda mijin Ummulkhairi da mahaifinsa Wanda Tani ta hana su gana dasu a cewarsu.
Ai ko suna ganin fitowar su Haidar suka k’arasa kaman zasu kwanta suna mik’o ma Daddy hannu alamun musabaha. Daddy
da Haidar suka tsaya suna gaisawa da mutanen cikeda girmamawa. Nan sukai introducing kawunansu matsayin K’annen Mahaifin Ummulkhairi kuma Wanda suka bada Auren ita Ummulkhairin. Nan suka sake sabon gaisuwa na musamman suka kuma cikasu da goma na arziki da
ga Daddy har Haidar din babu wanda aka bari baya. Kowa kokari yake yayi alkhairi daga aljihunsa. Alkhairin da ya bar su Baffah Ado cikin tsananin al’ajabi. An masu kyautan ban girma sai kawai suka fara wasa Ummulkhairi cikin gidan suna cewa ta kawo alkhair
i. Wacce a baya suka kyamaceta da k’addararta Har cewa suke tana bata sunan zuri’a da muguwar bak’ar k’addararta yau sai gasu nan suna rigen kiranta jininsu. Rabon da su shiga sashen su Ummul su duba D’anuwansu tinda Abba da Khulsum suka dawo daga Jigawa c
an gidan Inna Dije. Yau sai gasu nan tsamo tsamo suna kiran Abba Yayansu. Tani kaw ta masu d’add’aya tana fad’in maza aci arziki. Ummulkhair da suke ambato da Ummulsharri a baya yau sai gashi suna k’aryata harsunansu dan cewa suke ta amsa sunanta Uwar alkh
airi.
**
Bayan Haidar ya kai Daddy masauk’i nan suke tattaunawa da Daddyn gameda ciwon Abba. Daddy yace “Inaga ko zakaje Asibitin ku tattauna da Likitocinsa na nan. Sai a duba hospital report din nashi kaji shawarwarinsu.. Idan yaso ko can Abuja ko dan t
a kama a fitar dashi abroad ne sai su sanar dakai.”
Haidar ya jinjina Kai “Ina da wann plan din Daddy.. Hospital din da na kwanta lokacin da na samu had’arin mota is a prestigious hospital, sunada likitoci k’wararru daga k’asashe da dama sunada advanced t
echnology.. In fact is a foreign hospital.. Because a yanda naga jikinsa ba Lallai Likitoci su bamu shawarin a fita dashi kai tsaye matuk’a akwai solution a nan.. Duba da process din da za’a bi. Dan Ga dukkan alamu yana jin jiki sosai. Amma zan tuntub’i Li
kitocin nasa kaman yanda kace.”
Daddy ya jinjina kai “Good.. Yayi kyau.. Toh ai inaga ni zan bi jirgin yamma na koma. Zan turo Sadis (Daya daga cikin trustees d’in Daddy ne a wajen aiki) sai ya tayaka ku kula da al’amran.”
Haidar ya dan murmusa yana ris
inawa “A’a Daddy da ka barshi. Zan kula da komai by myself.. Financially da dik wani abinda ya kamata.”
Murmusawa Daddy ya d’anyi yana jin dad’in yanda D’an nasa ya zama responsible. Sai yace “Even so, Sadis zaizo ya tayaka da wani abin. Jirgin yamma nake
son bi.” Ya k’ara maimaita ma Haidar d’in.
Sai Haidar yai saurin jinjina kai “I’ll call the airport right away” Ya fad’i yana mai ficewa. Daddy ya jinjina masa kai.
Haidar bai bar garin ba saida ya tabbata an shirya duk wani abinda ya kamata gameda taf
iyan Abba zuwa prestigious hospital din da za’ai treating d’insa. Umma tace fir saidai Mama Tani ta tafi tareda Abba ita zata zauna da yaran. Haidar ya musu goma na arziki dukda cewa da Umma take ya daina d’awainiyar nan musamman idan ta tuna abinda ke far
uwa na rashin Ummul. A cikin zuciyar Haidar kaw cewa yake baiyi rabin abinda Khairy ta musu shida ahalinsa ba. Cikin zuciyarsa yana kewarta sosai.. A koda Yaushe k’aunarta k’aruwa masa yake.
Kafin ya bar garin da yamma yana zaune saman tabarma a haraban
gidan dan tuni ya zama D’an gida. Azeema sai zuba masa surutu take ta d’auko wani tsohon album d’in Abba tana nuna masa hotunan Ummulkhairi harda Wanda take sanye da uniform na makaranta. Ya jima yana kallon hoton. Sihirtaccen murmushi saman fuskarsa.
Az
eema taci gaba da basa labarin k’uruciyarsu Har ta gangaro kan samarukan Ummul da ake saka musu rana a fasa. Har kan Zubairu da su Alhaji Kamilu da yanda kowa ya zata Zubairu zata aura sabida yanda Zubair d’in yaso Ummul. A nan ne fah sukaga Haidar ya had
’e rai tamau. Badia sai mintsilin Azeema take tana fad’in Tai shiru haka nan amma inaa Azeema sai zuba take yawa kurna.
Mama Tani ta kawo masa abinci tana fad’in su Azeema su kyalesa haka nan yaci abinci.
Azeema ta dubeta ta dubi tuwon. Tuwon gero ne da
miyar yauk’i.
“Haba Mama ya zaki bashi irin wann abincin. Na tabbata bai ma tab’a gani ba.”
Haidar kam ma iya cewa baima abindake faruwa ba. Dan tinda Azeema tai mentioning Zubair tsohon saurayin Ummul ya rasa sukuni.. Sai ya dan dubi Azeema ya girgiza
Kai kad’an yace “Amma ina Zubair yanzu.. Yayi Aure.?”
Azeema ta saka ma bakinta sakata tana Zare ido. Badia ta rankwafo had’ida rankwashin Azeemar kad’an ta rad’a mata “Kin gani koh. Ke baki san kishi irin na maza bane kinzo kina