Showing 15001 words to 18000 words out of 267381 words

Chapter 6 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

39

fah.. zai k’one..”

“Yaya ki rik’e min ni nayi nan..!” Ta fad’i takalma a hannu ta nufi waje kaman zata tashi sama.

Tana ficewa Mama ta kece da wata irin muguwar dariya. Har ga Allah shashancin Suwaiba na saka ta nishad’i. W

ai Malam ya rasa da wa zai had’ata su goga a kishi saida wann shashasha ballagaza lamba d’aya wacce sam wayau da hankali basu isheta ba. Indai kishiya irin Suwaiba ne a kawo mata gomansu ma. Ta kuma kecewa da dariya tana kwaikwayon gudun Umma takalma a han

nu. Ta bud’e murya tana fad’in “Kiyi a hankali dai kar ki fad’i ayi haihuwar guzuma uwa kwance ‘ya kwance.”

**

Abuja.

Hisham ya kuma girgiza kansa a karo na biyu yana duban Haidar dake zaune calmly kaman babu abinda Ke faruwa saima d’an tapping tab

le din dake gaba garesu da yake da yatsarsa guda fuskarsa na duban wani b’angaren.

“Haidar kamata yai muyi suing news outlet da sukai publishing labarin nan for defamation of name..”

Kaikaitowa yai yana duban Hisham, ya d’anyi still kafin ya girgiza ka

i “Seriously Hisham..Are we going to waste our time going against the media..?” Ya d’an girgiza kai “Don’t you think we should focus on finding the traitor that leaked the video..?”

Hisham ya d’anyi Shiru kaman mai nazari. Sai kuma ya jinina kai “Yeah yo

u are right.. Gaskiyanka ne fad’a da media ba riba.. Wann b’eran na cikin company zamu kama sai ya sanar damu wanene uban gidansa. And I’m pretty sure shine wanda ya fitar mana da bayanan sirri na company.” Rufe bakin Hisham keda wuya wayarsa ta soma ruri.

Daga Company ake kiransa.

Hisham ya d’aga suna gaisa nan ya fahimci aminin mahaifin Haidar ne Alhaji Gimba mai kiran. Bayan sun gaisa ya tambayesa ko suna tareda Haidar.

Saida ya dubi Haidar d’in wanda hankalinsa ya koma kan wayar salular salulansa kafi

n ya d’an matsa gefe ya sanar dashi eh suna tare. Magana suka d’anyi na lokaci kafin daga bisani sukai sallama.

Hisham ya dawo wajen zamansa ya zauna yana tunanin ta yanda zai soma sanar da Haidar abinda Alhaji Gimba ya sanar dashi.

“That was Alhaji Gi

mba. One of the board of directors.. Aminin Dad..”

Haidar ya murmusa da gefen bakinsa kad’an jin yanda Hisham Ke masa bayanin mutumin da ya masa farin sani “What’s with the introduction..?” Yai maganar yana tsare Hisham da idanu.

Hisham ya gyara zamans

a cikin kujeran “He called to say ya shirya maka interview with the media tomorrow by 10am at the company.”

Haidar ya kuma murmursawa da gefen bakinsa irin na Wanda takaici ya gama cikasa yana mai girgiza kai “Unbelievable.!” Ya furta a hankali. Yanzu b

a Daddy kawai ba even his friends suna intruding cikin rayuwarsa.

“Kan wani dalili zai shirya mun interview ba da sani ba..?”

Ya mik’e tsaye yana nuna Hisham d’in “Look, you call that man right this instant and tell him I’m not attending.!”

Hisham ya

girgiza kai had’ida furzar da huci kad’an yasan halin abokin nasa yasan kayansa hakan dama zai kasance. Shima d’in mik’ewa tsaye yai “Of course you are attending..”

Haida ya dubesa da mamaki “Amma kaji yanda kake min magana..?”

Hisham ya kuma furzar da

huci “Haidar he’s only trying to help here.”

“Did I ask for his help..?!” Ya katse Hisham a fusace.

“But..”

“Bana buk’atar taimakon kowa.. And Much less from him.!” Ya k’arashe yana mai buga table d’in da hannunsa. Lokaci guda yasa kai zai shige.

Hi

sham yai saurin dakatar dashi “Haidar this is the only way to save…”

“The Company’s image, right.?” Haidar ya katsesa da fad’in haka.

“No.. I mean to fix this.. Ina nufin ya shafi sunan mahaifinka Haidar.. Harma da ahalinka.”

“Oh c’mon.! What family..

Wani ahali kake magana..? Kafi kowa sanin banida wani ahali.”

Hisham ya d’anyi still “Haidar kullum ina fad’a maka ba’a fad’a da iyaye a zauna lafiya..”

“Oh shut up.!” Ya fad’i yana mai nufan motarsa.

Hisham ya furzar da huci kad’an yana mai take masa b

aya yake ci gaba da fad’in “Haidar kai kad’ai kafi cancanta ka jagoranci project d’in nan.. You work so hard to get to where you are now.. Bazaka bari all your efforts and hardworking su tafi a banza ba.. I know you so well, you don’t surrender. You just n

eed a minute to cool off..”

Kaman dai badashi yake maganar ba haka yaba ma banza ajiyarsa ya isa ga motarsa cikin sassarfa.

Daidai sanda Haidar ke tada motar Hisham ya bud’e murya yana fad’in “10am tomorrow at the company.” Yai maganar cikin d’aga mur

ya dan tuni Haidar yaja motarsa ya bar wajen.

Hisham ya girgiza kai kad’an dafe da kunkuminsa yabi bayan motar Haidar d’in da kallo. Yasan ba lallai Haidar ya halarci wann interview d’in sanin wanene abokin nasa.

Yana tafe cikin mota yana kuma nazarin a

bun. Wai Alhaji Gimba ya shirya masa tattaunawa da ‘Yan jarida. How could he..! Ta yaya zai yanke babban hukunci haka ba tareda ya tuntub’e shi ba. Akan me za’a sakashi magana da media ba tareda amincewa da yardarsa ba. Duk ma ba wann ba since day one bai

k’aunar mutumin sabida k’ok’arin shiga rayuwarsa musamman tsakaninsa da mahaifinsa da yake. Ya tsani a shiga rayuwarsa without an invitation. Idan bai gayyaceka cikin rayuwarsa ba kawai kar ka shiga. Ya furzar da huci a hankali yana so ya gano wani abun.

**

Kano.

Banda sautin keken d’inki dake tashi cikin zauren baka iya sauraron komai. Ko wacce ta bada hankali da himma wajen ganin ta zama k’wararriya a sana’ar da suke koyo. Kaman daga sama suka soma jiyo kururuwa na nufosu.

Gaban Ummulkhairi ya yanke

ya fad’i. Cak ta dakata da abinda take tana mai furtawa a hankali “Umma..!”

SameenaAleeyou

📚

*AUREN WATA UKU..!*

*07*





Sameena Aleeyou…✍

🏽

*

Ta yanda take shiga ba ta nan take fita ba “Sai kinyi ajalina da bak’in ciki kiji dad’i. A sau n

awa zan miki iyaka da wann gidan amma kin rantse sai kin tona min asiri Ummul. Me kike nema ki zama ne wai.!” Ta karashe tana fashewa da kuka.

Hajja Fannah wacce tun shigowar Umma ta sallami sauran ‘yan ajinta dakatar da Umma tai fad’in “Haba Umman Ummul

ya kike kausasa harahenki akan ‘yarki. Shin baki san fushinki mai tasiri ne akanta koda baki nuna ba. Ke fah uwa ce kuma za’a tsai dake a tambayeki gameda kiwon da aka baki. Kaman yanda kikeda hakki akan yaranki haka suma sukeda hakki akanki.. Addini bai b

armu kara zube ba face saida ya tsara mana yanda zamu tafiyar da rayuwarmu.. Yanzu islamiya har na matan aure sun yawaita.. Duk wanda kikaga ya zauna da duhun kai shi yaso.”

“Malama dalla ki min shiru ba wa’azi nazo kimin ba… Yo idan ma zan d’auki wa’azi

sai na d’auka daga bakin ballagazar mace irinki mai zaman kanta wacce ta kasa zaman aure. Sann da kike maganar a koma makaranta yanzu kai waye kije garinmu kaf ki tambaya waye mahaifina.. D’iyar malamai nike jikan sha rubutu. Ubana Malami ne mai tak’ama d

a Zauren karatu, na girma ina kwankwad’an ruwan alk’alami da tawada.. Ni har an isa amin gorin ilimi nida na gajeta. Sauk’a uku nayi da k’ananan shekaru kafin a rufani akaini d’akin miji..!” Taci gaba da jijjiga tana nuna Hajja Fannah “Kuma bari kiji na fa

d’a miki idan ma kece kike ziga Ummul kike burin ki hanata aure

kaman yanda ke kika kasa zaman aure toh Allah bazai baki nasara ba. Ummul tun tana ciki aka nema mata tsari da shed’anu irinku. Ko ana ha maza ko ana ha mata Ummul d’ina zatayi aure kaman yand

a ko wacce mace mai mutunci keyi ehe..! Ke kuma shige muje kafin na kwashe miki albarka..!” Ta k’arashe tana tasa k’eyar Ummulkhairi wacce da alama ta gama saduda da sha’anin Umma.

Mamaki bai saki Hajja Fannah har suka fice. Gaba d’aya ta gaza katab’us. I

ta a halin yanzu ta fara tantama idan Mahaifiyar Ummul na cikin hayyacinta. Girgiza kai tai cikeda tausayin Ummul tana mai ayyanawa lallai tana cikin jarabawa.

**

Khulsum da dawowarta kenan daga makaranta taji k’urin miya na k’una kan wuta duk ya cika gi

dan. Ga hayak’i na fitowa daga kitchen. Da sauri sauri ta shigo a tunaninta babu kowa ne amma sai ta hangi Mama zaune tsakar gidan tana gyaran k’umbarta.

Bata ce komai tasa kai zata shige muryar Mama ya dakatar da ita “Toh shafaffiya maras kunya. Kin shi

go kina kallo na dan rashin mutunci ko sannun fatar baki ta gagareki. Toh ai sai ki shige ki aje jakarki kije ki gaida tukunyar miyan dake k’auri kan wuta idan ba haka ba tuwon dare ya haramceku. Ahtoh dan a banza azumin da ba lada zai hau kanku daga ku ha

r uwarku dan nikam raina guda inada gidajen ‘ya’ya ‘yan albarka da suke kame gidan mazajensu da zasu bani tuwo. Saima gidan da na zab’a naci. Banda asara har yaushe za’a ce manyan budare da suka rik’a suka rik’e a gida ana saka masu kwanon tuwo gidan mahai

finsu. Yo sadaka kuke ci sa’anninku masu mutunci dai suna d’aunansu suna aikin lada suna girka ma mazajensu tuwo.” Ta mik’e tana buge zaninta “Idan Kinga dama kar ki duba miyan girkin uwarki Suwaiba ne dan nikam na gama girka ma k’artai irinku tuwo a gidan

nan. Dan dai cikina d’aya da Malam bazai gagara ba. Amma bazai yuwu da girmana a ganni ina zama bakin murhu ina girka ma gandama gandaman ‘yanmata irinku tuwo ba. Daga me yawo da sunan karatu sai mai yawo da sunan koyon san’a..” Tasa kai ta nufi d’aki “Ta

ni ta daina girka ma k’artai tuwo wacce duk tai zuciya cikinku ta tafi nata d’akin mijin ta girka.” Ta k’arashe tana rangad’a gud’a da shewa.

Khulsum ta girgiza kai kurum kafin ta aje jakar makarantarta nan tsakar gidan ta cire hijab ta nufi kitchen d’in

. Shigarta keda wuya ta soma jiyo muryar Umma ta yanda take shiga ba ta nan take fita ba.

“Ko labari na sakeji kinje gidan matar can da sunan koyon San’a Ummul saidai ki nemi wata mahaifiyar amma bani Suwaiba ba. Banda salo da fitina ke da ake gab da sak

a miki rana yo wacce sana’a zaki koya ya wuce zaman aure dake gabanki.”

Da mugun mamaki Khulsum ke duban mahaifiyarsu “Umma.. Yanzu d’an koyon sana’ar ma hanata kikayi. Umma itafa sana’a dogaro da kai ne…”

“Ki rufe mun baki Khulsum, aure shine babban sa

na’ar dake gaba gareta.. Shine daraja da cikan mutuncin ‘ya mace.”

Khulsum ta saki baki da mamaki “ Umma a wann zamanin da akasarin wasu mazan basu sauk’e nauyin d’awainiyar matansu da Allah ya hukunta masu wann san’ar ba ita zata rufa masu asiri ba. Umm

a ko za’a baka Shi fah abu naka dad’i ne dashi.”

“Idan bakiyi shiru ba Khulsum zanzo wajen naci miki mutunci.. Hanshak’iya ana fad’a kina fad’a.”

Muryar Mama da fitowarta daga d’aki waya manne kunnenta ya katse Umma. Cikin d’aga murya Mama Ke ci gaba da

fad’in “Hellaww ina jinki Badidi na Badi’atu ‘yar albarka.. Wai shi Tasi’un ya kawo miki Kaji kika soye mun.. Kaji D’an albark. lallai Tasi’u ya cika Surki na k’warai.. Allah dai ya maku albarka ya k’ara zaunar daku lafiya a gidajenku ya rabamu da sharrin

mahassada masu san ganinmu a rana.”

Kuka ya kuma zuwa ma Umma bata iya sauraron wayar da Mama keyi ba ta shige d’aki.

Ita kuwa Mama tana ganin Umma da yaranta sun shige d’aki ta sauk’e nannauyan ajiyan Zuciya tana datse wayan Badi’a wacce ita kanta Badi

’an ta rasa gane wasu surkulle mahaifiyarta Ke mata cikin waya. Ita da take sana’ar da

ita irin uk’ubar da Tasi’u Ke bata a ‘yan kwanakin wanda ta gaza jurewa tana ce mata ita ta gaji da auren gida zata dawo sai taji tana mata wasu sunbatu wai Tasi’u ya ka

wo Kaji a gyare mata.

Mama ta koma d’aki ta kuma danna kiran Badi’a. Kaman jira Badi’a take ta d’aga kiran “Mama wani irin abu ne inace miki Tasi’u ya dawo da hallayansa na baya yau bugun tsiya ya min saida mak’ota suka k’waceni kina kira mun wasu kaji.”

Mama ta yarfe gumi “Ke Badi’a saurareni. Idan Tasi’u tsire naman jikinki yake haka zakiyi hak’uri ki zauna.. Zanzo gidan na sameki nasan yanda zamu b’ullo masa amma koda wasa kar kiyi tunanin dawowa gida.” Daga haka bata kuma tsayawa sauraron Badi’a da tu

ni ta fashe mata da kuka tana fad’in ita dai ta gaji.

Mama kaw ta mik’e tana tunanin yanda zasu b’ullowa al’amarin Tasu’u mijin Badi’a.

**

Abuja.

Maitama Builders (MB).

Zauren tattaunawar ta cika da ‘yan jarida abinda ya shafi b’angaren kasuwanc

i. Kowa shirye yake da tambayoyin da zai Engr AA. Maitama yake. Hisham ya shafi goshinsa dan interview d’in zai kasance live ne sakamakon yanda kowa ya k’agu yaji gaskiyar al’amarin bayan video da yai trending a manyan shafuka musamman shafukan watsa labar

ai na kasuwanci.

Hisham sai kai komo yake yana duba lokaci yana add’uan Allah sa kar Haidar ya badasu. Wann shine kad’ai damarsu ta k’arshe da zata d’aga darajan Kampanin ta kuma wanketa daga daud’an da aka shafa masu.

Masu gabatar da interview sun cir

e rai da zuwan Haidar. Sun mik’e da zummar tafiya Hisham yai saurin dakatar dasu yana sanar dasu Lallai Haidar zai zo shi.

A can gidan Daddy kuwa suna zaune shida Alhaji Gimba a parlor suna duban live event d’in yanda Daddy Ke girgiza kai. Ko janye idan

unsa daga screen bayayi “I told you he’s not capable of anything good..”

Alhaji Gimba ya girgiza kai “Inada yak’ini akanshi, Zai bayyana, kuma zai abinda ya dace.. Na tabbata bazai bamu kunya ba.”

Daddy ya soma k’ok’arin mik’ewa da zummar haurawa sama y

ana furta “This is a complete waste of time Gimba. Ni zan shige ciki..”

Alhaji Gimba yai saurin dakatar dashi “A’a Abokina.. D’an Dakata, kalli nan..!” Yai masa nuni da screen yanda aka hasko Haidar yana k’arasowa cikin hall d’in. Yayi kyau cikin shiga ir

inta cikakkun ‘yan kasuwa masu huld’a ciki da wajen k’asa. K’warjininsa ya cika wajen.

Bakin Alhaji Gimba ya gaza rufuwa sabida farin ciki.

Daddy ya jinjina Kai “I hope it doesn’t turn out to be another scandal.” Ya fad’i idanunsa akan Haidar da ake has

kowa.

A can Company Hisham ya murmusa yana duban abokin nasa harda d’aga masa yatsa guda alamun jinjina. Wani duba Haidar ya aika masa kafin ya wuce yanda aka tanadar masa domin zama.

Yana k’arasawa mai gabatarwan ya mik’e had’ida mik’a masa hannu suka

i misabiha kafin Haidar ya gyara zaman suit d’insa ya Zauna attentively.

Nan da nan aka soma gudanar da interview d’in. Yana jefo ma Haidar tambaya yana amsa sa daki daki cikeda k’warewa da sanin aikinsa nan ya jefa floor ma audiences wani ya d’aga hann

u ya soma jefo ma Haidar nasa

tambayar “Yallab’ai, munga wani hoto na yawo a kafafen sadarwa har wani gidan jarida ya wallafa wani labari cewa fad’a ya kaure tsakaninka da mahaifinka sabida gazawarka da kuma banbancin ra’ayi da kuke dashi. Shin menene gas

kiyan al’amarin..?”.

Haidar ya kafesa da idanu kafin yai clearing throat d’insa.

“A ko wace ma’aikata I believe ana samun sauye sauye da banbancin ra’ayi tsakanin shugaba da ma’aikatansa. Which is what makes the company stand firm on its feet..”

Babu w

anda zaice bai zama impressed da yanda Haidar ke amsa tambayoyin da ake masa with so much courage and determination.

Mutumin ya jinjina kai “So does that mean da gaske ne kenan kaida Mahaifinka baku samun jituwa har a wajen aiki..?”

Haidar yai masa k’ur

i dan ya gane turosa akai yai masa tambayoyin da zasu tunzurashi. Tafukan hannayensa ya d’an had’e waje guda “I’m not here to tell a story about my personal life. But Being the son of the president of this company doesn’t make me different from others. If

I don’t receive any VIP treatment it’s because that’s the company’s policy. And I believe this is why the company remains on track despite all the challenges.”

Ya kuma jinjina kai. “One more question Engr. “Is it true that your company is going bankrup

t.. And the economy is at the state of crisis.?”

Haidar ya d’an rage girman idanunsa kad’an yana duban mutumin, lokeci guda ya d’an gyara zaman suit d’insa “Let’s call this a business perspective. Some times failures lead to future successes. I can assur

e you, MB (Maitama Builders) does not… and will never fear challenges..” Ya k’arashe yana mai mik’ewa lokaci guda mai gabatarwan ma ya mik’e yana mai mik’awa Haidar d’in hannu alamun musabiha “Mun gode da bamu lokacinka da kai Rankayadade.

Alhaji Gimba

ya dubi Daddy “Look, duba kaga yanda yake amsa tambayoyin with so much focus and determination. He has all the potentials and skills to take this company to a greater heights. I’m super optimistic about him.”

Daddy dai baice komai saima mik’ewa da yake k

’ok’arinyi.

Alhaji Gimba ya rakashi da kallo yana mamakin Allah yai baiwa wa mutum da samun d’a irin Haidar Wanda yake d’aya tamkar ga dubu amma ya kasa gani ya kuma kasa appreciating. Sosai lamarin abokin nasa ke d’aure masa kai yanaji inama nasa d’an y

a kasance kaman Haidar.

**

Hisham ya kuma duban Haidar had’ida girgiza kai “Ban fahimceka ba Haidar.”

“Meye baka fahimta ba..?” Haidar yace yana duban Hisham d’in.

D’an gyara tsayuwarsa Hisham yai “Kanaso kace min gadar zare yaso k’ulla maka da ya shir

ya wann interview d’in..? Kanaso kace min

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login