Showing 183001 words to 186000 words out of 267381 words
su fice za’a k’arisa
shirya Ummul.
Azeema ta kuma harararta Tai k’wafa.
Ummul ta kamo hannayen ‘yanuwanta tana sanar dasu kar su koma masauk’i su jirata nan parlor tana fitowa.
Koda suka fito parlor Azeema dai bata zauna ba sai zagawa take tana bama idonta abinci a cewa
rta.
A haka Anisa ta k’araso daidai sanda Azeema take tab’a wani k’aton flower vase. Anisa ta rausayar da ido tana fad’i a fili “Dealing with Ummul is already giving me a headache. Now I had to deal with these local champions.?” Ta rausayar da ido tana f
urzar da huci.
“Excuse me.!” Ta darara ma Azeema tsawa.
Azeema ta juyo da mamaki tana dubanta.
Anisa taci gaba da nunata a wulak’ance “That flower vase worth your entire family.. Tell me, idan kika fasa zaki iya biya ne.?”
Badia ta d’anyi k’asa da mur
ya taceda Azeema tazo ta zauna su jira fitowar Ummul. Ta dubi Anisa tace “Kiyi hak’uri bazata fasa ba.
Hararsu take daga sama zuwa k’asa kafin taja dogon tsaki ta shige tana toshe hanci.
Azeema ta yunk’ura zata bi bayanta Badia Tai saurin rik’ota.
“Ki k
’yaleni na shayar da wann mai k’irar zabon mamaki Badia.”
Badia ta girgiza kai “A’a Azeema yau ranar farin cikin Ummul ne bazaki b’ata mata da wani abu ba. Musamman fad’a da dangin mijinta.. Ki kyaleta kawai karma ki kulata.”
Azeema Tai k’wafa “Wllhi dar
ajar Ummul taci da nayi wasan kura da ita dan dama hannuna k’aik’ayi yake kwana biyu. Ban saba da wann salihancin ba.”
Badia tace “Naji dai bazakiyi ba..” Ta k’arada inata so na tambayi Ummul ina surkin namu mu gaisa.”
Daga can Azeema ta hango Haidar na
tahowa dukda bata sanshi ba amma kallo d’aya ta masa ta gane shine angon. Sai ta shiga tab’a Badia tana fad’i a hankali “Ke wllhi gashin can yana zuwa.. Shine ango. Shine surkinmu.. Na shiga uku Badia kiga irin mijin da Ummul ta samu bayan duk k’alubalen
da ta fuskanta saikace tauraron fina finan Hindiyan nan. Ummul ta had’a komai Badia kawai ta nemi lahira. Gaskiya na yarda da karin maganar nan da ake cewa Wani JINKIRIN alkhairi ne. JINKIRIN Ummul ya zama Alkhairi Badia. Wllhi ta amsa sunanta Ummulkhairi.
”
Jin Azeema duk ta zauce yasa Badia take mata k’afa kad’an dan ya kusa k’arasowa yanda suke. A hankali take furta “Ke meye haka wai. Ni dan Allah ki natsu saikace wacce kikai gamo sai sunbatu kike. Ki mata fatan alkhairi kawai.. Kinga gashi nan ya iso da
alama d’akin da Ummul take zai shige.”
Kafin Badia ta rufe baki Azeema ta mik’e ta hau d’aga masa hannu “Sirkinmu.!”
Haidar ya juyo da mamaki sai ya shiga ‘yan waige waige yana tunanin kodai ba dashi ake ba.
Azeema ta kuma nunasa da yatsa “kaidai sirk
inmu.” Ta k’araso yanda yake bata daina washe baki ba “Mu ‘yanuwan Ummul ne.. Ni k’anwarta ce.. Waccan kuma dake zaune Yayarta ce Babanmu d’aya ai da Ummul..”
Badia dake zaune daga saman sofa takaici ne ko kunyar abinda Azeema take ta ma rasa wanne ne d’
aya take.
Sai sukaga Haidar Ya murmusa ya fasa shigewa d’akin Ya nufo yanda suke. Anisa da k’arasowarta wajen kenan mamaki kaman ya kasheta ganin da gaske Haidar Maitama kema kucakan nan sannu da zuwa kuma fah ransa a sake. Wai anya ba’a canza shi ba kuwa
. Tana tsaka da tunaninta ta sinkayo muryar Azeema tana fad’in “Sunana Azeema. Ni ce ta hud’u wajen Abbanmu ai.. Daga Ummul sai ni ke biye mata..”
Haidar Ya jinjina kai har lokacin da murmushi saman fuskarsa. Ya nuna Badia yace “And.. you are..?”
Sai B
adia da Azeema suka dubi juna. Azeema ta k’araso da sauri tana rad’a ma ‘yaruwarta “Adda Badia, kinsan dai mudai boko rakiya mukayi dan na tabbata Har yau ko shakeki za’ai da kyar ki iya rubuta sunanki. Su Ummul da Khulsum ne masu kwakwalwar ganewa. Turanc
i fah yake miki.. Tambayarki yake Ya kike.. Kice masa you are fine. Haka nakeji ake fad’a. Kar ki masa shiru zaki disga Ummul.”
Badia tace “You fine.”
Sai Ya d’an murmusa kawai yace “I’ll check on.. Khairy.. Sannunku da zuwa once again.”
Azeema taci g
aba da waving d’insa har ya shige. Badia ta fuzgota tana fad’in “Ke dan Allah wai meye haka ne.? ki kama kanki mana.”
“Mutanen da muke gani a tv mun gansu a zahiri Har gaisar damu yake kice na kama kaina.. Ke Nifa yanzu ko unguwarmu na koma wllhi ba ma k
owa zanke magana ba ehe… Kiji wani sunan yan gayu da yake kiran Ummul dashi.. Kai wllhi na Miki murna ‘yaruwa Kekam taki addu’ar ta amsu.”
Badia ta girgiza kai “Allah Ya baki lafiya Azeema.”
Azeema ta kyalkyale da dariya tana amsawa da Ameen.
Anisa d
a takaici Ya cikata furzar da huci Tai tana barin wajen. Dik yanda zatai bazata bari sunan wad’annan Almajiran ya shiga guest list ba tin daga waje zata sa securities suyi watsi dasu.
Ana shirin fita wajen event Anisa tai kicibis da Azeema a dan wani lob
by. Sai kawai ta k’ara wayarta a kunne alamun tana amsa kira “I need to double-check the guest list because ba ko wasu shara bane za’a barsu su shiga. You know is a high class event.” Ta k’arashe tana aika ma Azeema harara.
Zata wuce Azeema ta cakumo wuy
arta ta dawo da ita baya “Toh ya ne.! nace ko kinada abin cewa ne.?” Ta k’arashe tana tunkud’a drink din dake hannun Anisar ai kaw ya zube ma Anisa a jiki ya b’ata mata expensive gown dinta.
Mamaki ya hana Anisa rufe baki ganin bata ko tanka Azeema ba amm
a tai mata wann d’ibar albarka.
Girgiza Kai Anisa take tana fad’in “No this is not happening.. Not my dress..!” Ta dubi Azeema dake nad’e hannu riga Kai kace zata d’aga wani abin ne tace “You ask for it.!” Tai maganar tana sakin huci tana k’ok’arin Kai ma
Azeema Mari amma sai caraf Azeema ta rik’e nata hannun ta kuma d’auketa da maruka har biyu masu kyau.
Anisa ta kuma zaro ido cikin mamaki. Saima Azeema ta soma bata tsoro ta fara tunanin jada baya zata gudu Azeema ta kuma jawota tana fad’in “Ashe k’aryar
tashanci kike k’aramar maras kunya ba yanda zakije.”
Anisa taji rik’on manyan yan dambe ta soma kokawan k’wace kanta tana fad’in “Let go.. let me go.. What are you doing you witch.. I said let me go.”
Wani d’aki mai kaman store Azeema ta turata ta janyo
k’ofar da k’arfin gaske Wanda taga har wani d’an haske ya kawo daga wajen rik’ewar mai d’aukeda alamun wajen danna yatsa, sann harda wasu lambobi jiki. Bata tab’a ganin irin k’ofar ba. Sai ta d’an matsa da baya ganin k’ofan na haske.
Anisa ta fara girgi
za Kai tana bugun k’ofan tana fad’in ta bud’eta. K’ara Anisa ta saki tana Kama Kai sanin cewa da tai k’ofan Smartdoor ne. A fili take fad’in a taimaketa tana buga k’ofan.
Azeema kuwa shek’ewa da dariya tai jin Anisa tanata ihu daga cikin d’akin sann ta
kasa fitowa. Sauri sauri Azeema ta bar wajen tana kyalkyale dariya ga wayar Anisar da ya fad’i nan wajen sanda take k’ok’arin turata d’akin. Tasa k’afa ta kuma cilla wayar a gefe tai wucewarta abinta. Sai nishad’i takeji tayi maganin zabuwar can.
Anisa
taci gaba da bugun k’ofa tana neman d’auki ga wayarta can a gefe Hisham sai kira yake no response.
SameenaAleeyou
📚
*AUREN WATA UKU..!*
*47*
*©
️
Sameena Aleeyou…✍
🏽
*
Da kyar Anisa ta samu d’aya daga cikin ma’aikatan gidan wacce k’ofan ke amfani
da fingerprint dinta tazo ta budeta. Duk ta galabaita kwalliyar ma duk yaji jiki a fuskarta. Ba’a maganar daurin kai da tuni ta kwance. Haka ta fito a firgice tana neman wayarta. Can ta tsinceta gefen madubin console daga k’asa. Sauri sauri ta fice ma’aik
atan na mata a dawo lafiya ko ta kansu bata kuma bi ba.
Tana driving take dialing layin Hisham duk a d’imauce take.
Hisham yana d’agawa Anisa ta soma jero masa tambayoyi a gigice “Hish.. Hisham.. Tell me I didn’t screw up like always.. Tell me I’m not
late.. Tell me, we can still execute our plans…I.. I’m just few minutes away from the venue.!”
Ga mamakinta muguwar murmushin nan taji Hisham yayi. Yaci gaba da fad’in “Do you think I’d let your stupidity ruin my plans.? I always have plan B for every sit
uation Neesa.” Ya kuma murmusawa kafin yaci gaba “Too bad idan bakiyi sauri ba zaki iya rasa kallon show d’in.. The fall of Maitama’s.. The biggest scandal of their lives is just about to erupt.!” Ya k’arashe yana shekewa da dariya.
Anisa ta girgiza kai
cikin rashin fahimta “Mai kake nufi.?”
Ya kuma murmusawa “You wouldn’t want to miss the show.!” Yana ida fad’in haka ya datse wayarsa yana dariya.
**
A can filin taro kuwa Haidar matsawa gefe kad’an yai sakamakon kiran Amininsa Hisham da ya shigo masa.
Cikin nuna tsananin damuwa tamkar gaske Hisham ke fad’in “Banida wani zab’i ne Haidar dole na bar duk abinda nake na tafi gida na duba jikin Hajja.. Jikin nata ya d’anyi nauyi ne Haidar. Dan Allah Kai hakuri. Nasan ya kamata ace ina tareda kai a rana mai
matuk’ar mahimmanci irin haka a wajenka.”
Haidar ya girgiza Kai “Amma ka saurari kanka.? Maiyasa zaka bani hak’uri.. What’s more important than lafiyar Hajja.. Iyaye first kafin kowa Hisham.”
Mamaki ya kusa kashe Hisham jin yau wai Haidar ke d’aukan al’
amarin iyaye da mahimmanci. Lallai ya yarda rayuwar Haidar ta fara d’aukan saiti bazai tab’a bari wann ahalin su dunk’ule waje d’aya ba. Sai ya dan jinjina Kai yace “Haka ne Haidar.. A gaishe mun da amarya ace mata ina nan zuwa gaisuwa da cin girki in sha
Allah. Allah sa ta iya abincin gargajiya kasan nan nafi wayo ni, dan mijinta dai bature ne..!
Gajeren tsaki Haidar ya d’anyi “Kai komai sai ka saka wasa ciki. Ka gaisar mun da Hajja sosai. Idan tana iya amsa waya ka had’amu mu gaisa.. In sha Allah zan sam
u time nazo na dubata.”
Katse kiran yai bayan Sun gama kafin ya nufo wajen motar yanda Ummul take. Amarya da ango na k’arisowa media suka masu chaa suna nema ji ta bakinsu. Saidai securities basu wani basu chance ba balle su samu daman magana dasu.. Sann
tuni Mommy ta hana wani d’an jarida shiga wajen taron Wanda hakan ba k’aramin tada hankalin Asshe yai ba. Shirinsu na barazanar rugujewa.
Hannunta rik’e cikin nasa suke tafe. Haidar kaw tin sauk’owarsu a mota yake karantarta.
Tafiya take tana ganin kam
an duniyar na juya mata, ji take kaman dai wani babban al’amari ke shirin faruwa da ita. Gani take kaman duk illahirin jama’an dake wajen ita suke kallo. Jiri ya d’an d’ebe Haidar yai saurin tarota ta fad’o jikinsa. Cikeda kulawa ya rik’eta sosai “Are yo
u.. ok..?”
Sai ta d’an jinjina masa Kai.
Har lokacin rik’e yake da ita. Cikin rashin gamsuwa ya dan girgiza kai “But.. You almost fell..”
Ganin yanda ya rik’eta ga idon mutane akansu duk sai taji kunya ya cikata. Tai saurin girgiza Kai tana yin k’asa da
kanta shi kaw na dad’a rank’wafo da Kansa dan ya saurari abinda take cewa.
“Kar ka damu k’alau nake.. Inaga takalmin ne kawai da ban.. Ban saba tafiya da irinsa ba.” Ta fad’i duk a dan daburce cikin k’ok’arinta na ganin ya k’yaleta.
Maimakon ya sakarta
saima sake rik’eta da yai, ya kuma girgiza Kai yana kallonta sosai “You look pale.. You sure you’re fine.?”
Jinjina masa kai kurum tai ba tareda ta iya amsa sa ba.
Sai Ya k’arada “Have you had lunch.?.”
Shiru batace dashi komai ba saima yan waige waige
da ta soma kanta a k’asa dan gani take kaf mutanen dake wajen su kawai suke kallo. Muryarsa ta kuma sinkayowa “Wait.. Have you been skipping your meals..?”
Sai tai k’arfin halin girgiza masa kai. Ganin dai idan bata amsa sa ba bazai daina jefo mata tanba
yoyi baz Da kyar ta iya furtawa a hankali “Lafiya nake… Naci abinci… Kawai kar ka damu.. Ina so na zauna.”
Bai kuma cewa komai ba sai d’an jinjina Kansa da yai ba wai dan ya gamsu ba. Ya sakalo hannunta suka k’arasa wajen da aka tanadar domin su.
Bayan
an sanar da zuwan amarya da ango, manyan bak’i da sauransu.. Nan aka soma gudanar da shagalin biki.. Asshe ta fito da niyyan gabatarwa kwatsam taji microphone baya aiki. Ta kalli microphone da mamaki tana kuma jijjigasa domin kuwa da kamar wuya abu irin ha
ka Ya faru wajen taron da ya amsa sunansa ya kuma samu halartar manyan bak’i na musamman. Bata ida juya speaker ba taji sautin tafi ta bayanta. Juyawan da zatai da tsanani mamaki sai gani Tai k’atoton screen d’in dake bayanta wata budurwa ta bayyana.
Yay
inda hankalin kowa yayi wajen. Dareen taci gaba da tafi cikin screen tana takawa. Lokaci guda take fad’in “Surprise.! Surprise.!! Ga Wanda basu sanni ba sunana Dareen.. Kuma Mata ga Haidar Maitama wacce mahaifiyarsa ta k’uduri niyyan raba Aurenmu.”
Wann
ya kalli wann wancan Ya kalli wann.
Dareen taci gaba “Wann taron bikin da ake, an ginasa ne bisa cin amana, yaudara da kuma zallan k’arya.. An ginasa ne dan tarwatsa wani Auren. An ginasa ne dan a kashe nawa Auren da Haidar.. Haka ne Hajiya Kwaise Maita
ma.?”
Mamaki Ya hana Mommy motsi sai kallon screen din da take, yayinda Dareen taci gaba “Saidai abinda baki sani ba Hajiya Kwaise wann Auren da kikayi ma Haidar dan ki raba namu Auren bazai dore ba bazai je ko ina ba domin kuwa an gina auren ne bisa zalu
nci.. Dan kawai a raba masoya guda biyu. Ina nufin ni da masoyi na Haidar..” Taci gaba da murmushi “And now more than ever Aurenmu da Haidar bazai tab’a mutuwa ba Kinsan dalili Mommy.?”
Zukata sukaci gaba da bugawa. Mamaki da al’ajabi yaci gaba da bayyan
a tsakanin fuskoki. Yayinda video d’in Dareen yaci gaba “I am pregnant.! I am three months pregnant.. I am carrying your grandchild Hajiya Kwaise.. Your son’s child. Ina d’aukeda juna biyun Haidar har na tsawon Watanni uku.!”
Ba Haidar da yai mutuwar zaun
e yana duban Screen din ba, ba Ummul wacce ta koma tamkar mutum mutumi tana kallon abinda ke faruwa tamkar ba zahiri ba baga Mommy da ta koma tamkar hoto a wajen.. Baga su Tani da suka maida kawunansu k’anun alhaki ba sakamakon ganin abinda ke wanzuwa kan
idonsu. Kai duk wani mahaluk’i dake wajen Daskarewa yai yana kallon ikon Allah..
Dareen taci gaba da murmushi cikin video d’in “Haidar my love.. I am carrying your child.. Our child.. The fruit of our love.. You are going to be a father my love.. Zamu za
ma iyaye.. Ba haka naso na sanar dakai ba sai dan naga an shiga tsakaninmu da yawa.. Na sani this is going to affect your family business somehow.. But believe me, I didn’t mean to jeopardize your business.. Please forgive me my love.” D’iff screen din ya
d’auke.
A daidai lokacin Anisa ta k’araso ta tadda wann babban shiri da Hisham yai. Cak Anisa ta tsaya tana sakin murmushi tareda jinjina ma shed’anancin Hisham.
Asshe ta mik’e a firgice ta nufi yanda MC da sauran masu kula da event suke tana fad’in “Wh
at’s this.. What’s the meaning of this.. Who’s in charge of the event.. Wai meke faruwa ne.. Ya akai haka ta kasance..?”
Kowa yace bai san Ya akai aka sabotaging event din ba. Baga securities ba baga MC’s da sauransu ba.
Anisa ta saki murmushi sanda ta
hangi Azeema. Ta shiga shafa b’arin fuskarta yanda shatin yatsun Azeema suka bayyana sakamakon marin da ta mata. A zuciyarta tace ‘Baki mari banza ba. Zan nuna miki barikin gaske.. Anisa nake, I always get what I want.’ Ta kuma murmusawa. Lallai dole tayi
amfani da wann damar. Sai ta k’araso tana kuka tana rik’e Mommy tana fad’in “Mommy ni ce wacce ta kamata tai coordinating komai a wajen nan kaman yanda kika amince mun, amma wancan munafukar ta kulleni a gida sai yanzu na samu na k’araso.. Ma’aikatan dake
cen gida sune shaiduna.. Mommy I’m sure bakinta d’aya da duk Wanda sukai sabotaging event din nan.. Ita ta taimaka musu ta rufeni a d’aki dan su samu saukin executing plan dinsu. Mommy ki yarda dani da shirinsu suka taho wajen nan.” Tai maganar tana nun
i da Azeema.
Duk jijjiga Mommy da Anisa take Mommy bata iya cewa komai ta koma tamkar hoto, ko motsi k’akk’wara bata kuma yi ba tin bayan da Dareen ta bayyana cikin wann faifayin. Sai kawai AnisaTa tafi aguje zata shak’o Azeema tana fad’in she’s working w
ith the people that sabotage the event. Ta shiga kiran securities tana fad’in su kama Azeema ita zata fad’i wad’anda take ma aiki wad’anda suka sakata ta kulleta a d’aki sabida kar ta samu damar halarta wajen event din.
Haba nan fah Azeema ta shiga kurur
wa tana fad’in ita wllhi bata san komai ba bata san kowa, sann bata aiki ma kowa. Mama Tani ganin securities sunyo kan ‘yarta ta nufesu cikin k’ok’arin k’watan ‘yarta tana fad’in su rufa mata asiri kar su kulle mata ‘ya ta d’and’ani zaman gidan yari bazata
so wani nata ya kuma d’and’ana ba. Gaba d’aya taro ya yamutse ya hargitse ya rikice.
Kasa komai Haidar yai har lokacin idonsa na kan screen d’in dikda ya d’auke. Har lokacin Dareen yake hangowa cikin screen d’in. Wacce rabonsa da ita tin ranar da suka