Showing 144001 words to 147000 words out of 267381 words

Chapter 49 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

23

farka tana d’akin hutu. Shima munada yak’inin in a couple of hours zamu turasa d’akin hutu cikin yardar Ubangiji. There’s nothing

to be worried about.”

Relief ya nuna saman fuskarsa Mommy. Ta soma jinjina kai “Da gaske Dr. Yarana are out of danger.. Zasu samu lafiya.. Ta dubi Anisa dake sakar mata murmushin nuna jin dadi “Zasu samu lafiya in sha Allah.”

Ta juyo ta dubi Likitan d

ake nan tsaye gabansu “Zamu iya ganin Ummul.”

Dr ya jinjina mata kai a hankali “Of course you can.. This way please.” Ya k’arashe yana nuna mata hanya.

Mommy ta jinjina kai tana mai shigewa Anisa na biyeda ita.

Bayan Sun shige Dr da Daddy suka keb’e a

ofishin Likitan.

Dr ya dubi Daddy yace “To be honest, I couldn’t tell your wife the real condition of your son.”

Daddy ya zuba masa ido. Sai Ya girgiza kai kad’an “Tell me his condition, Dr.”

Dr ya jinjina Kai kad’an “He’s lost a lot of blood.. But..

Zamu iya cewa he’s responding well. That’s why we moved him to the ICU… Amma..” Sai ya d’anyi shiru yana duban Daddy kafin ya girgiza Kai kad’an yaci gaba “Komai zai iya faruwa.. Because the first 24hrs is critical.. Let’s just pray he wakes up before the

n. Otherwise, we don’t know what might happen.” Ya k’arashe yana duban Daddy hadida girgiza Kai alamun hope d’in kad’an ne.

Daddy yai shiru cikin tsananin sanyin jiki tamkar Wanda yai nisa cikin duniyar tunani. Muryar Dr ya sinkayo yana fad’in “Muna buk’

akan jini da za’a k’ara masa cikin gaggawa.”

Daddy ya dubi Likitan jiki a mace sai Ya jinjina kai “Go ahead Dr.. Just do your job..”

Likita ya girgiza Kai kad’an “Unfortunately bamuda irin jininsa a nan. Mun samu shortage na jinin due its high demand. B

a don muna buk’ata cikin gaggawa ba da zamu iya jira tinda jini da baida wahalan samu. A halinda ake ciki any delay zai iya janyo matsala.”

Daddy ya furzar da huci kad’an. Dan shi dai Haidar D’ansa ne amma bai tab’a sanin lafiyarsa rashin lafiyarsa balle

wani blood type d’insa. Ya dan girgiza Kai kad’an yace “Dr.. What’s his blood type then.?”

Dr ya sanar da Daddy blood group din Haidar.

Shiru Daddy yai kaman mai tunani. Dr zai kuma magana Daddy ya dubesa had’ida katsesa cikin sauri “I have same blood

type with him.. I hope zaku iya d’iban nawa.”

Dr ya jinjina Kai yana mai sanar da Daddy su k’arasa lab dan suyi aune aune.

A can d’akin da Ummul take kaw. Shigowar Mommy yai daidai da bud’e idonta.

Ta soma k’ok’arin Ware idanunta da suka mata nauyi.

Tsaf ta sauk’esu akan Mommy dake karasowa gaban gadon nata.

“Mommy..!” Ummul ta furta cikin murya irinta marassa lafiya.

Mommy ta sakar mata murmushi ta k’araso tana dafa kanta daga nan yanda Ummul d’in ke kwance “‘Yata.. Alhamdulillah kin farka. Ya ka

rfin jikin naki..? Mai kike ji yanzu.?”

Ummul ta dubi Mommy tana k’ok’arin tuno abinda Ya faru. Take ta tuna sansa Haidar yace birkin motarsa bata aiki. Ta tuna yayita k’ok’arin ya tsaida motar bai iya ba. Ta tuna sanda motar ta bar saman kwalta Haidar Y

a mata rumfa da jikinsa cikin k’ok’arin ganin yayi saving dinta wani abu bai faru da ita ba.. Ta tuna jini da ta hango Ya wanke fuskar Haidar da ya bar saman seat d’insa yai mata rumfa cikin k’ok’arin kareta. Ga idanunsa a lumshe tamkar baya numfashi. Tind

a taga Haidar a wann yanayin bata kuma sanin ina kanta yake ba sai farfadowa da ta ta ganta a gadon asibiti. Ta soma girgiza kai hawaye na gangaro mata “Mommy Haidar.. Ina Haidar yake..? Dan Allah ku fad’a mun ya samu sauki.!” Ta soma k’ok’arin mik’ewa tan

a fad’in “Dan Allah ku kaini wajen shi.. Dan Allah ina so naga Haidar.. Please Mommy..!”

Saurin rik’eta Mommy tai itama din hawaye take. Bata bari Ummul d’in ta bar saman gadon ba take fad’in “Haidar yana can likitoci na kula dashi Ummul. Ki kwantar da h

ankalinki kinji.. Kema ba k’oshin lafiya ne dake ba. Look duba kiga ga bandage a goshinki da hannunki.”

Cikin zuban hawaye ta katse Mommy da fad’in “A’a Mommy banjin ciwon komai.. Ni Haidar kawai nake son gani dan Allah..” Ta k’arashe cikin tsananin rawar

murya irinta mai kuka.

Anisa dake gefe juya ido rai cikeda takaicin Ummul. Cikin zuciyarta take fad’in ji wani iyayin banza. Sai wani neman ganin Haidar take bata ta kanta. Yaushe ma suka San juna ita Haidar d’in. Makirar banza. Ta kuma juya ido ganin Mo

mmy ta rungume Ummul dake kuka sosai cikin k’ok’arin kwantar mata da hankali dudka Mommyn ma hawaye ke zubo mata.

A can b’angaren Daddy kaw bayan an ida d’iban jininsa an k’ara ma Haidar duban Dr Daddy yai “Doc, I want this to stay between us.. Bana so

Matata ta San ni na bama Haidar jini… Ko shi Haidar d’in idan ya farka.”

Dr ya jinjina cikin tabbatar ma Daddy baida matsala da hakan.

Daddy ya jinjina kai had’ida masa godiya kafin Ya k’ara da “Can I please, see him now..?”

Dr ya jinjina kai “Sure.. Bu

t it should be quick.”

Daddy ya jinjina kai yayinda Dr Yai masa jagora zuwa cikin ICU bayan an basa wani rigar kariya da hula harma da nurse mask kafin ya nufo yanda Haidar ke kwance na’ura ta ko ina.

Tin daga nesa jikin Daddy yai matuk’ar sanyin yanda

ya hango Haidar kwance cikin buwayar Ubangiji. Yana takowa yana tuna Haidar d’in tin haihuwarsa. Gwagwarmayar rayuwa da Ya fuskanta musamman dasu iyayensa. Ya tuna a lokutan baya sanda yake rige rigen kawo masa sakamakonsa na makaranta da kyauttukan da ak

a basa amma daidai da rana guda bai tab’a kalla ba balle Ya yabesa. Ya tuna banda hantara tsana da kyara babu abinda ke tsakaninsa da D’an nasa. Ya tuna irin k’ok’ari da yake a company kan duk wani aiki da aka d’aurasa ba dan komai ba sai dan ya tabbata ba

iyi failing mahaifinsa ba. Still nothing was enough. Ya tuna auren da Kwaise Tai masa Wanda bai saka hannunsa ba balle Ya halarta matsayinsa na tilon D’ansa dukda sanin aure wani gab’a ne mai mahimmanci a rayuwar D’an adam. Haka yaita tuna rayuwarsu na bay

a Har kawo tattaunawarsu da Alhaji Gimba da yanda Alhaji Gimba yace dashi yai tunani Ya gyara alak’arsa da iyalensa tun kafin Lokaci ya k’ure masa dan Lokaci baya jira. Saiga hawaye na kwararowa daga k’uncin Daddy. Yakai hannunsa dake tsananin rawa yana k’

ok’arin Shafa kan Haidar.

Sosai muryarsa ke rawa sanda ya soma fad’i a fili “Aliyu..!” Ya furta a hankali yana shafa kan Haidar d’in. For the very first time da ya tab’a ambaton Haidar da sunan from his heart tin bayan da aka rad’a masa sunan. Daddy yaci

gaba “My Son.!” Nan ma karo na farko da Ya ambacesa da D’ansa kai tsaye. Yaci gaba “Shin kasan a ranan da aka haifeka a lokacin da mahaifiyarka ta nuna mun kai a wann rann na samu k’arfin komawa bakin aiki.?” Ya murmusa hawaye na kuma gangaro masa “People

might think kasuwanci na da Kampanina sune abinda sukai keeping dina moving.. But the truth is that you were the one that kept me going.. You brought me back my strength koda ban nuna hakan ba.” Ya shafe fuskarsa da duka tafukan hannayensa kafin yaci gab

a “Meyasa na hukunta ka cikin laifin da ba naka ba Wanda baka da masaniy akai.?” Ya dan numfasa yana kuma shafa kan Haidar d’in “I was so angry at your Mom… That I didn't even realize I wasn't only a husband who’s been hurt and betrayed… I was also a fathe

r.. Na mance ni mahaifi ne da Allah Ya dank’a mun amana da kiwo Wanda zai tsaidani Ya tambayeni kan wann kiwon.. Nayi abubuwa cikin fushi.. Na d’auki tsangwama da kyara na d’aura akan ka just because you’re Kwaise’s Son.. Fushi yasa na mance you are also

a part me.. My soul… my flesh and blood..” Ya lumshe idonsa hawaye suka kuma gangaro masa “Bai kamata na barka ka shiga cikin matsalolinmu ba. Why are You the one who's suffering the consequences... It shouldn't be this way.. If there is one thing I regret

the most shine sake da damata da nai cikin shekarun da Allah Ya albarka ce ni da kai matsayin D’ah…. Forgive me son… Ka yafe mun D’ah na..!” Ya k’arashe kuka na neman cin k’arfinsa. Saida Yai masa addu’o’in samun sauk’i kafin ya baro d’akin duk jikinsa a

mace.

A hanyar ficewa suka had’u da Mommy. Daddy ya bita da kallo saidai batace da shi komai ba tasa kai ta shige. Jiki babu k’wari yaja k’afarsa Ya bar wajen.

A yanda Mommy taga Haidar sosai hankalinta Ya tashi. Haka ta kwantar da kanta gefensa tana ku

ka tana fad’in irin k’aunar da take masa tana fad’in kar Ya tafi ya barta. Hannun Ummul taji saman k’afadarta wacce itama ta kasa hakuri har saida likitoci suka hakura suka barta ta shigo dan taga mijinta.

Ummul na k’ok’arin bama Mommy baki amma sai ta ka

sa sai k’unshe bakinta tai dan sosai taji kuka na zuwa mata musamman yanda taga Haidar na kwance idanunsa a lumshe ga na’ura ta hanci ta baki.

A hankali kukan Mommy ke tsagaitawa, ta sa hannu tana shafan sumarsa. Murmushi da hawaye saman fuskarta take fa

d’i da Ummul “Tin lokacin da yake ciki rayuwarmu ta sauya. Na shiga matsansncin damuwa.. And maybe that’s why he was so tiny lokacin da na haife shi… Amma dukda haka he was strong, a fighter..” Ta kuma murmusawa tana hawaye “Sann Koda ya zama cikakken mut

um mai cika ido da kyaun k’ira bai huta ba.. Tin haihuwarsa baisan wani farin ciki ba.. And that’s all my fault..” Ta k’arashe tana share hawayen da suka zubo mata. Taci gaba “Meyasa nake ji kaman laifuka na yake biya..?”

Saurin girgiza mata kai Ummul ta

i “Kar kice haka Mommy.. Bawa baya wuce k’addararsa a rayuwa. Duk abinda ke faruwa muk’addari ne daga Allah. Wasu abubuwan suna faruwa ne cikin rayuwarmu domin su zamto mana darasi. Ubangijinmu zai jarancemu ta ko wata fuska. Muyi ma Haidar addu’a Allah Ya

tashi kafad’unsa Ya basa lafiya..”

Mommy ta jinjina mata kai tana mai rik’e hannun Ummul d’in cikin nata. Ummul ta kamo hannayen Mommy sosai tana fad’in “Muje ki huta Mommy. Zan tsaya a nan na kula da Haidar..”

Mommy ta jinjina mata kai a hankali tana m

ai goge hawayen da suka zubo mata. Haka Ummul ta rik’o hannunta har suka fito dikda itama ga rauni jikinta. A nan k’ofa suka had’uda Anisa. Ummul ta mik’a ma Anisa hannun Mommy tana fad’in ta kula da ita tana buk’atan hutu.

Anisa ta jinina kai tana fad’in

“Ummul is right.. You need to have some rest Mommy.. this isn’t good for your health.. Haidar bazai so ya farka yaga kema ba lafiya ba.. Muje Mommy..” Ta k’arashe tana rik’o Mommyn wacce da gani tafiyar kawai take.

Suna shigewa Ummul ta koma cikin ICU

d’in. Ta jima tana kallon Haidar dake kwance tana tuno yanda had’arin nasu Ya kasance. A hankali tasa tafin hannunta ta share hawayen da suka gangaro mata. Ta janyo kujera ta zauna nan gaban gadon nasa. Kallonsa take tana tuna yanda aurensu Ya kasance Wand

a ko sanin wanene shi balle kamanninsa batai ba farko. Ta tuna lokacin da ta shak’i poison Dr ya sanar da ita yanda Haidar Ya kula da ita. Ta tuna d’auketa da yai Ya kaita wann gidan Ya kulle.. Ta tuna yanda yai fitar da Mommy da kansa daga hannun ‘yansan

da Wanda a baya ya dage sai an kulleta a prison. Ta tuna tattaunawarsu kafin Had’arin Ya faru yanda yace mata bazai saceta ba kuma bazai sake rufeta ba sann zai sawwak’a mata tai tafiyarta shima zai tafi zai tafiya mai nisa far from everyone and everythi

ng. Ta tuna sanda hadarin ke faruwa yanda ya finciki seatbelt d’insa yai tsalle daga nasa kujeran yai mata rumfa cikin k’ok’arin kareta. Ta lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata. Bayan mahaifinta bataji akwai wani D’an adam da Ya tab’a ba ma rayuwarta m

ahimmanci irin haka. Ta bud’e lumsassun idanunta masu zuban ruwa tana kallonsa. A hankali ta soma k’ok’arin kai hannunta dake rawa ta d’aura saman nasa hannun. A hankali take furta “A lokacin da Umma ta shirya aurena da kai na shiga damuwa da tashin hankal

i na rashin sanin wanene zata aura mun.” Ta kuma goge hawayen da suka gangaro mata “Ban tsammaci farin ciki ko wani rayuwa mai inganci cikin auren ba kama daga mutanen da shafin rayuwa zata had’ani dasu Har zuwa mijin.” Ta k’ura masa ido hawaye na kuma gan

garo mata “Shin kasan kowa gudu na yake.? Ni Ummulkhairi ban tab’s tsammanin akwai wani D’anadam da zai fifita rayuwata sama da nashi ba. Koda ace akwai ban tab’a tsammani daga wajen mutum irinka ba. Wanda na tabbata ka fini a komai sau babu adadi. Sann mu

biyun duniyar mu sun banbanta. Haka ne.?” Ta kuma jinjina kai tana hawaye “Dole ce tasa na danne nawa raunin gaban Mommy dan na bata k’warin gwiwa.. Amma kasan me..? Banida wani k’warin gwiwa.. Dan Allah ka tashi kaji.. Ka tashi..!” Ta k’arashe kuka na ne

man b’alle mata da gaske. Tai k’ok’arin saita kanta kafin ta kuma dubansa murmushi da hawaye saman fuskarta “A koda yaushe kana kiran kanka Monster.. Ni kuma ina fad’a maka kai ba mugu bane.. Mugu bazai tab’a zama mai kyakkyawan zuciya wanda ke saka damuwa

r wasu sama da nasa irinka ba. Yau d’in na kuma yarda da haka bayan abinda ka mun.. Watak’ila da baka zab’i ka bani kariya ba Watak’ila da ni ce zan kasance nan a kwance ba kai ba..!” Ta share hawayen da suka ziraro mata. Ta kuma daura yatsun hannunta sama

n nasa “Ina tareda kai.. Zaka samu lafiya cikin k’udurar Ubangiji.. Allah Ya baka lafiya…SweetMonster..!” Ta k’arashe tana mai kwantar da kanta gefensa kad’an.

**

Kano…

Hilal na Ida parking Ya juyo ya dubi Umma dake zaune bayan motar. Murmushi Ya s

aki kad’an “Umma mun iso..”

Umma ta sauk’e ajiyan zuciya tana dubansa “Hilal.. Na haneka kak’i ji.. Mai zai faru idan mahaifiyarka tasan abinda ka aikata.?”

Ya d’an girgiza kai kad’an “Ammi bazata sani ba Umma. Taimako nayi niyyan yi kaman yanda kema tai

makon kikayi. Ina addu’an Allah Ya had’a mu cikin lada.”

Umma ta sauk’e ajiyan zuciya kad’an tace “Ameen Hilal d’an albarka. Mu k’arasa ko.”

Hilal Ya jinjina kai yana mai fitowa had’ida bud’e ma Umma k’ofa.

A daidai lokacin motan Ashshe dake biye dasu

ba tareda saninsu ba ta iso wajen. Ta bama driver umarni da yai parking can gefe dasu.

Sai huci take tana ayyana gidan Uban wa Suwaiba alak’ak’ai zata kai mata D’ah.? D’aga kan da zatai taga sun nufi cikin Kotu. Asshe ta zaro ido waje tana d’ora hannaye b

iyu a k’irji “Na shiga uku ni Asshe mai Hilal yake a Kotu.?!”

Batasan sanda ta finciki marfin mota ba tabi bayansu a fusace.

SameenaAleeyou

📚

*AUREN WATA UKU..!

*40*





Sameena Aleeyou…✍

🏽

*

“Ke Suwaiba dakata.!” Ta furta da k’arfin gaske d

aga nan yanda take tsaye bayansu.

Gaban Umma ya yanke ya fad’i. Ta kasa juyowa sai furtawa da Tai cikin zuciyarta ‘Asshe.!’

Shi kaw Hilal da tsananin mamaki Ya juyo yana dubanta “Ammi.!” Ya furta cikeda mamaki.

Asshe taci gaba da jinjina kai tana huci

“Baka tsammace ganina ba koh..? Nace baka tsammaci ganina ba koh..?”

Hilal Ya d’an lumshe ido kad’an ya k’araso yana k’ok’arin janye mahaifiyarsa “Ammi please don’t make a scene here.” A hankali yake maganar yana k’ok’arin janye ta.

Ta funcuke hannunta t

ana nunasa Umma da d’an yatsa “Kina jina Suwaiba kurwar zuri’ata kur..! Idan na sake ganinki kusada d’a nah.. Kinga nan.” Ta nuna mata kotu dake gaba garesu “Wllhi a nan za’a rabamu.!”

Hilal yai saurin katseta “Ammi Umma bata tilasta mun zuwa wajen nan ba

.. Nazo ne da rad’in kaina..”

“Rufe mun baki kai kuma kafin na Sallamaka da gaske kabi daji.!”

Umma ta k’araso cikin sauri tana girgiza kai “A’a Asshe dan Allah kar kice haka.. Wllhi Hilal yaron kirki ne mai biyayya.”

Da mugun mamaki take duban Umma “

Kul.! Ahir d’inki kar ki sake ki sake saka mun baki ina magana da D’ahna. Suwaiba ke har zakiyi magana akan biyayya..?!”

Umma ta sadda kai k’asa a sanyaye.

Asshe taci gaba “Kina jina idan har baki sakar mun kurwan D’ah ba wllhi sai na maidake abin kwata

nce a garin nan.! Ban haifo muku D’ah dan yaji da matsalolinku da gurguntaccen ahalinku ba ehe.!”

Ta dubi Hilal “Kai kuma idan ni ce na haifeka ka saka k’afarka a kotun nan.!” Tana ida fad’in haka tasa kai ta shige mota fuuu kaman zata tashi sama.

Hilal

Ya dubi Umma yace “Kiyi hak’uri Umma bansan Ammi na biyedamu ba..”

Umma tai saurin girgiza masa kai alamun a’a “Kar ka damu Hilal kabi umarnin mahaifiyarka. Ni zan shiga na saurari k’aran Yaya Tani. Idan bata ganni a kotun ba zatai tunanin na kuma watsar

da ita ne.. Inada yak’inin Allah zai kawo yanda za’a biya mutumin nan kudinsa Tani ta dawo gida.”

Hilal Ya jinjina Kai a hankali “Umma biyan kudin bazai zama matsala ba in sha Allah.. Na Miki alk’awarin baza’a sake zaman Kotu akan wann batun ba.”

Kaman

daga sama suka sinkayo murya “Zaman Kotu da Tani yanzu aka fara dan sai na karb’ar ma D’anuwana hakkinsa rabon gadonsa da Tani tai yana raye. Idan banci taran Tani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login