Showing 120001 words to 123000 words out of 267381 words

Chapter 41 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

75

ever wanted is a quite and happy life. Away from all this chaos. Yana maganar Mommy tana dubansa hawaye na gangaro mata. Ta rasa tausayin waye take ji cikinsu gaba daya.

Haidar yaci gaba “Amma Idan wann shine Abu na k’arshe da zanyi a rayuwata

zanyi. Na ranste sai na isa k’arshen komai. Mark my words.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice daga room d’in.

Mommy ta dubi Daddy “Engr we need to stop him. Da gaske yaron nan ba cikin hayyacinsa yake ba.”

“Ki min shiru Kwaise. This is all your fa

ult you know. I’ve warned you.. Na Miki gargadi amma bakiji ba. I knew nothing good would come out of this marriage da kika dage sai kinyi ma d’anki. Ga abinda nake Miki gargadi akai amma bakiji ba.”

Mommy ta girgiza Kai “Ka yarda dani Engr wllhi ban saka

guba ma yarinyar ba.”

“Just shut up Kwaise.! Meke tsakaninki da wann yarinyar is absolutely none of my business..” Ya kuma matsowa yana nunata da yatsa yana sakin huci “Na gargadeki cewa idan har wann watsattsen auren da kikai ma wann D’an naki ya shafi

Kasuwanci na ki kuka da naki auren.!”

“Har yanzu barazana kake mun da Aurena.” Mommy ta katsesa. Taci gaba da jinjina Kai tana hawaye “Shin meye matsalar.? Auren da nai ma Haidar ne matsalar kokuwa dai har yanzu akan Fannah ne da abinda ke cikinta.!”

Ca

k Daddy ya tsaya ya dago yana dubanta yana jinina kai “You are right Kwaise. You are absolutely right. You should be grateful ban miki korar kare ba bayan abinda kika mun.!”

Mommy taci gaba da hawaye tana duban mijinta nata yanda yaci gaba “Bayan abinda

kika min nayi hakuri na zauna dake da abinda kika haifa tsawon shekarun nan.!”

“Nasan albarkacin Haidar naci kake zaune Dani kawo wann lokacin.!”

“Will stop with your guilt tripping Kwaise.! Idan kinsan da haka kar ki bari na tuna Miki abinda kika aikat

a mun a baya.!”

Mommy na hawaye taci gaba “Meyasa baka barmu munyi tafiyarmu ba nida Haidar idan har zaka rik’esa ka kasa accepting dinsa tsawon shekarun nan.?!” Taci gaba da hawaye “Na sani nayi kurakurai da dama a baya. Kuma babban kuskuren da na kasa y

afe ma kaina shine k’iyayyar da na nuna ma Haidar a lokacin da na haifosa ka k’i accepting dinsa.”

Daddy Yaci gaba da jinina kai yana huci yayinda Mommy taci gaba da hawaye.

“How do you expect me to accept your child bayan kinsa na sheganta D’an wata.?

Ta ya kike zaton zan rayu da naki D’an na bude ido na ganshi yana girma bayan akwai wani D’an nawa can Wanda na sheganta sa da bakina. A kullum na bude ido naga D’anki Kwaise ba komai yake tuna mun ba face mummunan kuskuren da na tapka. Kuskuren da na zart

ar da hukunci akansa ba tareda bincike ba.!” Ya jinjina kai kafin yaci gaba “Dik randa naga Haidar sai na tuna akwai D’anuwansa can wanda naki accepting d’inshi tun yana ciki. Ta ya kike zaton naki D’an zai girma da soyayya na.? Ki gode ma Allah da na bama

D’anki sunana.”

Cikin kuka Mommy tace “Haidar D’anka ne dole ya amsa sunan ka.”

“Amma kin haramta ma wani D’an nawa Ya amsa sunana Kwaise.!” Ya katseta da fad’in haka jikinsa Har rawa yake.

Hawaye yaci gaba da gangaro ma Daddy “Na tuna miki zaluncin d

a kika mun ne.?! Kwaise kin kawo wani k’ato yayi fyade wa Matana a cikin gidana.. Da aurena akanta da cikina a jikinta Wanda kika sa na Sheganta shi tin yana ciki baizo duniya ba. Kinsa na rabu da matata a WATA UKU na farkon aurenmu. Kinsa na tura Fannah g

idan Yari ta raini cikinta a can ta kuma haifesa a can. A gidan Yari ta haifi D’ah na da na sheganta sabida son zuciya irin naki Kwaise.!”

Mommy tai bursting cikin kuka tana girgiza kai take fad’in “Wllhi Allah shine shaida na ban basa umarnin ya aikata m

a Fannah wani abu ba. Sharri kawai nace Ya mata. Allah shine shaida na babu fyad’e a plan d’in.”

“Just shut up already.! Kar ki sake ambatan sunan Fannah da wann bakin naki.!” Daddy ya katseta.

Haidar Ya banko k’ofar Ya shigo cikin wane irin yanayi yak

e duban iyayen nasa “Wacece Fannah..?!”

SameenaAleeyou

📚

*AUREN WATA UKU..!*

*34*





Sameena Aleeyou…✍

🏽

*

Kallo daya Daddy yaima Haidar ya watsar. Kaman dai baiji tambayan da yai ba. sai kuma ya kalli Mommy “Kina iya sanar da D’anki zunub

anki idan kinso. I’ll send our lawyer to handle your case. As you know, I have a reputation to protect bazan bari ke ko D’anki ku min sanadi ba .” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice.

Haidar yabi bayan mahaifinsa da kallo kafin ya maidoda dubansa ga ma

haifiyarsa. Ya dauki lokaci kadan yana tsaye wajen yana dubanta kafin daga bisani ya soma janyo k’afafunsa ya zauna saman kujera mai fuskantar nata “Tell me Mommy. Wacece Fannah.?”

Mommy ta dago idonta masu zuban ruwa tana duban D’an nata kafin ta jinina

Kai “She… She was your Dad’s wife.. Matar mahaifinka ce kafin su rabu.”

Haidar ya jinina Kai a hankali “So Daddy yanada wata matar a baya.?”

Mommy ta jinina Kai a hankali.

“What happened then, mai ya faru da ita..? Ina take yanzu.?”

Mommy ta girgiza Ka

i a hankali “I have no idea Son. Bansan yanda take ba a halin yanzu.. Kuma na nemeta shekara da shekaru ban sameta ba.”

“Meyasa kika nemeta.?” Ya kuma jefo ma Mommy tambaya.

Ta d’ago tana dubansa “Dan na nemi yafiyarta.”

Ya kuma jinjina Kai “So tell me

Mommy. Mai kika aikata mata.?”

Mommy tasa hannayenta biyu ta share hawayen da suka zubo mata. A hankali take jinina Kai “Zan sanar dakai komai Haidar. Abinda ya faru a wancan lokacin… Watak’ila ka samu gurbi cikin zuciyarka ka yafe min D’ah na.” Ta k’aras

he cikin tsananin rawar murya yayinda Haidar ya zuba mata ido.

Waiwaye…

Years back..!

Borno State, Maiduguri.

Hajiya Kwaise zaune saman kujera a madaidaicin parlorn ta Wanda ya tsaru iyaka tsaruwa a wancan lokacin. Kuka take sharshar da hawaye a lokac

in da taji sautin wayar landline na gidan na kururuwa. Ta mik’e da kyar ta isa ta daga wayar. Daga d’aya b’angaren muryar Aliyu Maitama ta sinkayo “Kwaise an d’aura auren.. An daura auren.. An daura aurena da Fannah..” Yanda yake maganar zaka fahimci kaman

Wanda aka saka shi dole haka yake maganar. Bata k’arasa sauraro ba ta saki wayar ya fad’i kasa tana mai kuma rushewa da kuka. A haka Asshe ta k’araso ta sameta. Asshe k’anwarta da tin bayan da Kwaise tai aure rik’on Asshe ta dawo hannunta dama ba wani gir

me mata sosai tai ba kuma su biyu iyayensu suka Haifa.

Mommy ta dago tana duban Asshe cikin rawar murya “Asshe Aliyu yayi aure.. Aliyu ya auri d’iyar leburan dake aiki k’arkashinsa Wanda block na gini ya fado ya fasa masa Kai ya rasa ransa dalilin haka.

Asshe Aliyu na ya aure ‘yar wann mutumin..!” Ta kuma rushewa da kuka.

Asshe ta dubeta cikeda tausayawa “Aunty Kwaise mijinki loves you. Wllhi koda ace yayi aure bazai daina sonki ba. Ni fah ban taba ganin wacce mijinta ke mata irin Son da Uncle Engr ke Mi

ki ba. He loves you dearly. Zai komai dan farin cikin ki Aunty Kwaise. Keda kanki kin fada Aurensa da wann yarinyar Fannah k’addara ce kawai batada kowa bayan mahaifinta da ya Mutu ta dalilin aiki k’ark’ashin ma’aikatan mijinki da yake. Wllhi na tabbata da

n ya taimaketa ya aureta. Ba wai dan yana So ba ko dan ya daina sonki. Idan ba so da mijinki ke Miki ba. Mutum kaman Engr Aliyu matashi mai tashen kud’i ga k’uruciya ga dama na rayuwa da ya samu ai da tuni ya cika gidan nan da mata sai yanzu da k’addarar h

akan tazo. Dan Allah kar ki saka wani Abu a ranki.”

Mommy ta dago tana share hawaye “Asshe bazaki taba ganewa ba. Namiji Akan mace sunansa namiji bazakiyi shaidarsa ba. Nidai bazan iya sharing Mijina da wata ba balle wann bagidajiyar ‘yar lebura.”

Asshe

ta furzar da huci “Toh ya kike so ai yanzu.?”

Mommy bata iya bata amsa ba sai mik’ewa da tai ta shige k’uryar daki wani sabon kuka na taso mata.

Haka ta yini a daki bata aikin komai sai kuka. Asshe ke Lek’ata lokaci zuwa lokaci. Ko abinci Mommy ta kasa c

i ranan.

Can dare taji shigowar motar mijinta. Nan ta Mike da sauri tana lek’en window. Hangosa tai tareda Amaryar sa tana biye dashi kanta a k’asa. A haka suka shigo har parlorn gidan.

Koda Daddy ya shigo ya tadda Mommy juya masa baya tai. Ya k’araso

jikinsa duk a mace “Kwaise. My love..” Sai ya kasa ci gaba da magana yayinda kukan Mommy ya karu.

A hankali ya isa ya rungumeta ta baya. Su duka biyun hawaye na gangaro masu. Cikin kwantar da hankali yake furta “Wann shine k’addarar mu Kwaise. Allah ya k

’addari Fannah zata shigo cikin rayuwarmu. Yarinyar abun tausayi ce bata da kowa sai mahaifinta da ya rasu sakamakon aikin da yake k’ark’ashina.

Mommy na hawaye take girgiza Kai “Ba hurumi na bane na tuhumeka dan ka k’ara aure Aliyu. Addini ya halatta mak

a auren mata d’ai d’ai har hudu idan kanada hali. Kawai alfarmar da zan rok’a daga gareka shine Kai Adalci tsakaninmu.”

Ya murmusa yana dubanta. Ya saka hannunsa ya share hawayen da suka gangaro mata “I love you Kwaise.. So much..! Ban tab’a son wata mace

sama dake a rayuwata ba. Ki tayani addu’a Allah ya bani ikon yin Adalci tsakaninku because.. I’m not sure idan son da nake Miki zai barni na kamanta adalci.. Kwaise ba kece cikin tashin hankali ba. Ni ne cikin tashin hankali.. Because son da nake miki bai

da match da ko wace mace. When it comes to you wayona baida yawa Kwaise.”

Mommy ta tsaresa da ido kafin ta k’ak’aro murmushi ta riko hannayensa “You can do this in sha Allah mijina. I’m here for you.. Tashi na shiryaka amarya tana jira.”

Kaman rak’umi

da akala haka Daddy ya Mike Mommy ta shiryawa tsaf harda su fesa turare kaman ba ita ce ta yini kuka a daki ba.

Koda suka fito suka tadda amarya ma Mommy bata nuna komai ba. Asshe taita mamakin canzawan ‘Yaruwar tata. A haka rayuwa ke tafiya masu Mommy

bata nuna komai ga Daddy ya saki jiki ganin hankalin Kwaise ya kwanta. Ya maida hankali kan bunk’asa k’aramin kampaninsa a nan birnin Maiduguri da Kewaye.

Watan Fannah biyu a gidan ta fara nuna alamun masu juna biyu. Kwaise da kanta ta dauketa ta kaita a

sibiti akai mata gwaji aka tabbata tana d’aukeda karamin ciki na tsawon watanni biyu. Sosai Mommy ta nuna marnanta har kaman tafi Fannah murna. Lokacin Daddy na cuku cukun Kai Kasuwancinsa tsakanin Abuja da wasu jihohi Mommy da kanta tai masa Albishir na

cikin da amaryarsa ke dashi sanda sukai waya tinda shi a wann lokacin ya rage zaman Maiduguri. Farin ciki wajen Aliyu Maitama baya misaltuwa. A wann lokacin yai ma matan nasa kyauta ta sabuwar mota dal ‘yar yayi a wancan lokacin. Ya kuma d’ebesu gaba daya

suka tafi Umra suka gode ma Allah da kyautar da yai masu dan a lokacin aurensa da Kwaise kusan shekaru biyar kenan babu rabo saida Fannah ta shigo sai gashi ta samu daga shigowarta.

Bayan dawowar su daga Umra Daddy ya tafiya ta kasuwanci da zai d’aukesa

kusan wata guda.

Asshe ta dubi Mommy wacce keta faman sakin murmushi tana gustiran Apple. Ta d’an girgiza Kai tace “Kenan kin yarda ta rigaki Haifa masa Magaji Aunty Kwaise.? Ni fah kirkikin da kike ma matar nan tai yawa. Ke kaman bakijin kishi irin na m

ata da ake fad’a.”

Murmusawa Mommy tai “Asshe kenan. Sarai nasan abinda nake kuma lokaci yayi da zan executing plan dina. Trust me.”

Asshe ta girgiza Kai “Toh amma Aunty Kwaise mai zakiyi yanzu.?”

“Wann cikin da Aliyu Maitama ke rawar k’afa akansa da Ka

nsa zai sheganta sa tin a ciki kafin a haifosa. Zai ma Fannah korar wulak’anci. Wann cikin kuma Engr Aliyu Maitama bazai taba accepting dinsa ba.”

Asshe ta girgiza Kai “Amma ta ya zakiyi hakan.?”

Mommy ta kuma gyara zama “Uban Fannah labourer ne a kampa

nin Maitama. Bincikena ya tabbatar min akwai wani lebura matashi kuma abokin aikin mahaifinta dake mutuwan sonta. Hasalima saurayinta ne kafin iftila’ain da ya samu mahaifinta ya samesa. Zuwa Kai ma mahaifinta abinci da take site a can Saurayin nata ya gan

ta ya fara sonta. Da uban ya Mutu mijina bai san da labarin tanada wani saurayi da suke soyayya ba Wanda shima yake aiki k’ark’ashin sa. danginta sukai wuf suka nuna masa batada kowa saidai ya aureta sabida tinanin zasu sami kudi. Ance sadaki suka yanka m

asa kaman dai mai biyan diya. Saida masa ita sukai. Fannah batada say ga danginta Wanda bayan rasa mahaifinta da tai ba rike ta zasuyi ba dole suka tilasta mata auren mijina dukda tanada Wanda take so. Dashi zanyi amfani na fitar da Fannah daga gidana dan

ance har gobe yana mutuwan sonta.”

Asshe ta sauk’e ajiyan zuciya “Toh ya abin zai kasance.?”

Mommy ta kuma murmusawa “Abin shine kece zaki taimaka min har komai ya kankama K’anwata.”

Asshe ta girgiza Kai cikin rashin fahimta “Kaman ya kenan Anty Kwaise.

? Ki sanar Dani wane irin taimako zanyi dan nafi kowa burin matar nan ta fice daga gidan nan.”

Mommy ta jinjina Kai suka tsara yanda zasu aiwatar da komai cewa Asshe ta tafi ta samu wann Saurayin suyi ciniki dashi da Mommy yazo gidan a ranan da Engr Aliyu

Maitama zai dawo gari ya kamasa a d’akin matarsa zai hau kan dik abinda ya gani ya zauna tinda su biyun tsaffin masoya ne.” Ta k’arashe tana sakin murmushi.

Da taimakon Asshe Mommy ta tsara komai har shigowa gidan da Auwalu tsohon Saurayin Fannah yai ba

tareda kowa ya gansa ba.

Fannah da fitowarta kenan daga band’aki tayi wanka cikin murnan mijinta na hanya zai dawo ya dubasu itada abin cikinta mai watanni uku a lokacin. Nan ta tadda Auwalu tsohon saurayinta kwance saman gadon ta daga shi sai singlet d

a gajeren wando. Jikinta ya d’auki kyarma ta soma salati tana karanto Innalillahi. Kafin tai wani aune Auwalu yai tsalle ya capkota had’ida toshe bakinta da k’arfin gaske. Fannah tana kuka tana k’ok’arin kururuwa amma inaa ya toshe bakinta.

Daddy ya daw

o cikeda d’oki da murnan ganin matarsa mai juna biyu. Ko sashensa bai nufa ba ya fara nufan b’angaren ta d’aukeda tarin tsaraba irin Wanda mata masu juna biyu ke so. Nan ya tadda Kayan tashin hankali maras misaltuwa k’ato rungume da matarsa dake d’aure da

towel ya toshe mata baki da hannunsa guda. Ga wani mummunar murmushi saman fuskarsa.

Daddy na huci yake duban mutumin Wanda ya saki Fannah bayan shigowan Daddyn. Ya duka jiki na kyarma yanda yake fad’in Engr ya masa sutura dole Yai ma Fannah bada amince

warta ba fyade yai mata.

Daddy ya shak’osa tamkar zai aikasa lahira ya kasa furta komai sai huci da kyarma da jikinsa keyi sabida b’acin rai. Da kyar Mommy ta janye Daddy. Ta isa ta yafa ma Fannah mayafi ta rufe mata jiki wacce towel ne kawai d’aure jiki

nta. Ta dawo ga Daddy tana fad’in “Engr kar ka biyesa kar Kai kisa. You are not like him. Ni dama tinda yake zuwa gidan nan ban yarda dashi ba.”

Daddy ya dubeta da mamaki “Dama ya Saba zuwa.?!”

Mommy ta jinjina Kai kaman gaske “Ai idan Baka nan yakan zo.

Da abubuwa na kwadayi irin na masu ciki yakan ce Kai ka aiko shi zuwa wajen Fannah. Sabida abinda take so yake sayowa.”

Asshe da fitowarta kenan sabida hayaniyar da taji ta dubi mutumin da Daddy dake duke yana kyarma tace “A’ah.. Wann mutumin ai mak’oci

n su k’awata Baana ce. Kuma ta…” Sai tai shiru ta kasa ci gaba da magana.

Mommy tace “Kuma me Asshe.. Meye Baana ta sanar dake..?”

“Ta sanar dani shi d’in Saurayin Fannah ne Wanda mutuwan mahaifinta ya hana aurensu… Hasalima mahaifin Fannah kafin ya rasu

ya masa alkawarin bashi ita..!”

Daddy ya dago jiki a sanyaye yana duban Fannah wacce kuka yaci k’arfin ta “Haka ne.? Wann D’an iskan saurayinki ne.?!” Ya tambaya yana dubanta.

Jin bata amsa shi ba ya sa ya kuma daka mata tsawa “Ki amsa min..! Haka ne..

!”

Auwalu ne ya bama Daddy amsa da fad’in “Duk Wanda zaka tambaya Rankayadade haka ne. Fannah toshuwar budurwata tace da nake matuk’ar so. Kuma mahaifinta ya min alk’awarin bani ita.. Amma ‘yanuwanta Sun karya wann alk’awarin sabida kwadayin abin hannunka

. Saidai ni da Fannah bamu rabu ba.. Washe garin ranar da ta tare gidanka ma ba aiki na tafi ba gidanka na taho.. Kuma duk randa nazo mukan mu’amalanci juna da yarda da amincewarta. Amma yau din ba da son ranta na aikata mata ba fyade nai mata sabida ta sa

nar Dani akwai ciki jikinta Wanda batasan nawa bane ko naka..!” Bai Kai aya ba yaji saukar naushi a bakinsa. Duka Daddy yake Kai masa ta ko ina yana hawaye tamkar zai aikasa lahira A haka mai gadi ya shigo a guje yana sanar da Daddy window din section dins

a a fashe dik yanda akai b’arawo ya shigo gidan. Dan shi dawowarsa kenan daga masallaci ya tadda haka.

Daddy ya ci gaba da huci “Ga b’arawon a nan. Ya Saba shigowa Shayibu ba tareda kayi la’akari ba. Yau da dubunsa zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login