Showing 66001 words to 69000 words out of 267381 words
bayan auren rashin galihu
da kikai ma ‘Yaruwata shine saida kikai mata rakiya. Shin baki gudun maganganun mutanen ne Umma..?”
“Allah tsari gatari da saran shuka.. Aure auren gata nai ma d’iyata irin Wanda kaf lungun ku ba’a tab’a samu ba. Ki koma ki tambayi ‘yan lungun naku kiji w
ani irin aure akaima Ummul. Aure na bajinta auren da na tabbata bazaa daina kambabasa ana labarinsa ba. Ke harta da masu shigewa saida suka shaida.. Kuma ban rako Ummul ba saida zuciyata ta tabbatar min zaki iya zuwa… Gashi kaw kin zo d’in kaman yanda nai
tunani.. Zuwanki na sani ba Alheri bane.. Dan na tabbata kaman yanda nai alwashin aurar da Ummulkhairi haka Kikai alwashin lalata mata aure. Tinda ba yau kika saba korar mata maza ba. .Ke ni fah akan auren nan wllhi Khulsum sai mu raba gari dake.!” Ta k’ar
ashe tana sakin huci.
Khulsum ta jinina kai a hankali tana duban mahaifiyar tata “Umma kin kaw ji abinda kike fad’i..?” Tai maganar cikin rawar murya.
“K’waraiii kuwa.. Wllhi sai kiyi yamma nai gabas muddin kikai yunk’urin lalata auren ‘Yaruwarki Wanda B
abu kalan fad’i tashi da banyi ba dan ya tabbata. Tsaf zan yafeki Khulsum muddin kika kawo mishkila.”
Hawaye suka gangaro ma Khulsum “A’a Umma. Abun bai tsanani haka ba. Har kullum ke mahaifiyata ce banida tamkar ke.. Bazan b’ata auren Adda Ummul ba.. Na
Miki alk’awari Umma.. Amma dan Allah alfarma d’aya nake so kimin..”
Yanda Umma ke dubanta a dak’ile sai ka rantse ma wata tsararta take jifa hararan.
“Umma dan Allah ki bari nai Sallama da Adda.. Na rok’eki..!” Ta k’arashe tana had’e tafukan hannayenta
biyu waje guda alamun rok’o.
Umma bata amsa ba sai k’ofan waje da ta shiga nuna mata “Fita.. Wuce ki fita.. Wllhi idan ni na haifeki kuma na haifi Ummul bazakiyi Sallama da ita ba.. Shige ki fita nace kar na bud’e idanuna na ganki..”
Khulsum ta dubi maha
ifiyarta da mamaki “Umma kin Sallamanin kenan..?”
“Idan haka kika d’auka.. Kije duniya da yawa..”
Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un Khulsum ke nanatawa cikin zuciyarta. Wai mahaifiya ke fad’a ma ‘yarta haka.. Anya Umma ita ta haifesu..? Anya akwai iyaye
irin Umma..? Anya mutum zai d’auki D’ah a cikinsa tsawon watanni tara Ya haifosa duniya yaci gaba da rainonsa rana tsaka Ya k’isa sabida wani buri nasa na duniya..? Anya akwai irin wad’ann iyayen..? A iya saninta harta dabba yasan dadin d’ansa. Meyasa tas
u mahaifiyar ta zama haka..? Shin dama ana jarabtan bawa da iyayensa..? Ashe ba iyaye bane kawai ake jarabtarsu da yaransu ashe Yaran ma akan jarabcesu da nasu iyayen.. Ta lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata. A hankali take ja da baya hawaye na gangar
o mata tana duban Umma.
Umma kaw bayan ta tabbata Khulsum ta fice cikin gidan ta koma harda ce ma maigadi idan wann yarinyar ta dawo ya koreta.
Suna zaune parlor itada Asshe bayan k’awayen Asshe Sun watse. Asshe ta dubi Umma tace “Yarinyar nan taki ak
wai fitina, sam batai halin ‘yaruwarta Ummul ba.”
Umma ta tab’e baki “Ai mutane biyu ne mabanbanta halayya. Fitinanniya ce ga taurin kai tsiya da masifa yacce kikaga k’anwar Ubanta. Bata rage ma Dije komai a d’abi’a ba.”
Asshe tace “Wacece Dije..?”
Kafi
n Umma ta kaiga bata amsa suka sinkayo wata murya daga k’ofa “Ni ce nan Dije k’anwa d’aya tilo ga Isubu..!”
Daram.! Daram!! Daram.!!!
Haka k’irjin Umma ya bada wann sauti cikin sakan guda.
SameenaAleeyou
📚
*AUREN WATA UKU.!*
*20*
©
️
Sameena A
leeyou…✍
🏽
*
Inna Dije taci gaba da takowa cikin parlorn. Yayinda Umma keta faman k’ifta idanu, zuciyarta bata daina tsinkewa ba.
Daidai saitin Umma Inna Dije ta k’araso ta tsaya. Umma ta kasa d’ago idanu ta dubi Dije.
“Dole ki kasa d’ago idanu ki
dubeni Suwaiba. Idan Har kinada sauran kunya bazaki dago ki dubeni ba..”
Umma ta soma girgiza kai hawaye na zubo mata Har lokacin bata d’ago idanunta ba.
Fincikota Dije tai tana fad’in “zo nan.. Yau sai naji uban da ya tsaya miki a garin nan Suwaiba har
kike buga wasanki da sunan wauta da shashancin gangan..!”
Ta kuma janyo Umma a zafafe. Hajja Asshe tai saurin raba tsakaninsu “Inaga dai ya kamata ayi komai gaban idona.!” Ta k’arashe tana duban Inna Dije data cakumo Umma.
Umma ta k’walalo idanu waje Ji
n zaa kwance mata zani gaban Hajiya Asshe. Ta had’e hannu biyu waje guda alamun rok’o “A’a Dije.. Kar kiyi haka.. Wann matsala ne da ya danganci ahali..”
Inna Dije ta murmusa tana duban Umma “Dole kice matsala ce da ya danganci ahali Suwaiba.. Sabida baki
so a bankad’o sirrikanki gaban sirakanki ko..? Kin masu rufa rufa kin aura masu ‘yarki da lak’anin mahaifinki ya fad’a kanta cewa ita d’in bazata tab’a aure ba.. Sabida wani babban Dalili Wanda nida ke muka binne hakan tinda jimawa..!”
Umma ta zaro idanu
waje tana duban Inna Dije da Jin wani batu Wanda ta kasa fahimtar ina ya dosa..
Asshe ma idanu waje take duban Umma da Inna Dije cikin tsananin d’aurewar kai “Wa.. Wani batu kenan..?!”
Dije ta murmusa cikeda cin nasara. Cikin zuciyarta take ayyana lokac
i yayi lokacin d’aukan Fansan rasa tilon D’anta Fa’iz da tai a dalilin Ummulkhairy.
Umma ta kuma girgiza Kai “Dije wa.. Wani dalili ne wann.. Kuma.. Wani magana muka tab’a binnewa mu biyun Wanda ni ban sani ba.?”
Dije ta murmusa “Suwaiba kar ki fara mana
dramarki a nan.. Dan kinsan tar nake kallonki.. Kin shashantar Dani Karon farko na rasa Fa’iz dalilin ‘yarki bazan kuma bari ki shashantar Dani ba..!”
Umma ta kuma girgiza Kai hawaye na Neman b’allo mata.. Zatai magana Asshe ta dakatar dasu “Wai meke far
uwa ne..?”
“Abinda yake faruwa shine D’anku ka iya zama gawa na gaba kaman dai yanda Fa’iz d’ina ya mutu..!”
Asshe ta mik’e tana kuma zaro idanu dafe da k’irji “Na shiga uku gawa fah..! Haidar ne zai zama gawa na gaba..?!”
Dije ta dubeta sosai tace “K’w
arai kuwa.. Domin Ummulkhairy da kike gani ba mace bace..!”
Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.! Shine abinda Asshe take nanatawa tana ganin duniyar na Neman juye mata “Ba mace ba..? Mecece toh..?! Na shiga Uku ni Asshe me na aura ma D’an ‘Yaruwata..?!”
Umma na kuka take girgiza Kai tana duban Inna Dije jin irin sharrin da ake ma ‘yarta akan idonta “Dije kiji tsoron Allah..!”
“Idan banji tsoron Allah ba tsoronki zanji ko tsoron mushurikin mahaifinki wanda ya maida Ummulkhairy yanda take a yanzu..!”
Izu
wa lokacin kan Asshe ya gama k’ullewa.. Ta dubi Umma dake duk’e wajen tana hawaye tace “Ke Suwaiba..! Fad’a mun.. Meke faruwa..? Wacece ‘yarki..?”
Umma bata iya cewa komai ba sai kuka tana girgiza Kai..
Inna Dije ta kuma murmusawa “Ai bazata iya sanar d
ake komai ba domin kuwa batada amsar baki.. Amma ki tambayeni ni zan sanar dake komai.. zan sanar dake Wacece Suwaiba da badak’alan data k’ulla a doron k’asa..!”
Asshe ta d’ago tana duban Inna Dije cikin tsananin shock.
Lokaci guda Inna Dije taci gaba “Y
arinyar da kuka aura ma D’anku ba mace bace.. Domin kuwa a lokacin da Suwaiba ta samu cikinta ba cikin ‘Ya mace tai fatan samu ba.. Mahaifin Suwaiba ya kasance gasunkumin malamin tsubbu ne Suwaiba ta tafi wajensa amsar taimako a lokacin tana d’auke da ciki
n Ummulkhairy kan cewa ya bata
lak’anin haifo d’a namiji... Sabida Sun mance Allah shi kad’ai yake halitta mahaifinta bai isa ya sauya halitta ba.. Wann dalili yasa aka haifo Ummul a idon duniya mace ce mai kyau son kowa k’in Wanda ya rasa.. Amma a zahiri
ne kawai. A magana ta auratayya namiji bazai tab’a amfana da Ummul ba domin kuwa ita d’in an tsafeta tun a ciki.. Hakan na nufin Ummulkhairy bazata tab’a aure ba.. Idan kuma tai toh fah duk mijin da ta aura zai mutu. Idan bai Mutu kafin ta kaisu ga aure b
a kaman dai yanda Fa’iz d’ina ya mutu toh zai mutu idan wata alak’a ta auratayya ta gifta tsakaninsu.!”
Duniyar Asshe ya shiga juyawa.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Meke shirin faruwa dasu.. Shin ta yaya zata sanar dasu suma auren warware asiri k
awai na watanni uku sukai da Ummulkhairy Wanda sai ya mu’amulamceta wann sihirin da aka masa ya karye.. Ta ina zata soma sanar da ‘Yaruwarta abinda ke faruwa.. Lallai tana tsaka mai wuya..!
Muryar Umma ne ya katse mata tunanin yanda take fad’i cikin kuka
“Haba Dije..! Dije kiji tsoron Allah.. Ki tuna akwai mutuwa.. Dije har zaki iya tsara wann babban k’arya kan D’iyar D’anuwanki.. Dije baki tsoron hakki.. Baki tuna yau idan babu mahaifin Ummul ita amanace a gareki..?!”
“Rufe mun baki annamimiya..! Ke Har
akwai maci amana irinki ne Suwaiba.. Kin mance Ya aurenki ya kasance ne na tuna miki Suwaiba..?”
Umma ta kuma kifa kanta a k’asa kuka na kuma zuwa mata. Lokaci guda Dije taci gaba “Talla kike kawowa cikin gari a lokacin Tani da mahaifiyarmu wato sirkart
a kenan basu jituwa mahaifiyarmu tana so Yayana Isubu ya k’ara aure kafin ta bar duniya sabida yara mata da Tani ke haifa masa. Mahaifiyarmu tana son samun jika namiji daga wajen D’anuwana Isubu.. Ke Suwaiba kika yaudari Tani kikace a garinku mahaifinki m
alamin zaure ne kuma yana bada lak’anin mallaka, Tani ta biyeki kika kaita Har rugarku da sunan tana neman lak’anin mallaka. Shakuwa ya shiga tsakaninku kika d’auki Tani tamkar Yaya. Tani ta daukeki tamkar k’aramar k’anwa ta baki dukannin yardarta. Kika z
amto mata ingiza mai kantun ruwa.. Kika zaga Tani kikaci amanarta. Maganin bakin jini keda Ubanki kukaita tura ma Tani Wanda zaisa mijin Tani ya tsaneta ya soki. Haka ne..?”
Idanun Umma suka kuma firfitowa waje tana jin sirrikanta kaf Dije na fito dasu. D
an wann b’angare da Dije take fad’i bata da haufi gaskiya ne. Cikin rawar murya irinta mai kuka take furta “Amma nayi nadama kuma mahaifina ya daina wann aikin kafin ya bar duniya Dije. Ke shaida ce mahaifina bai Mutu yana wann mummunan sab’o ba. Dije Alla
h Algafur ne kuma mai rahama.”
“Ke yimin shiru! yau ne kika san Allah Suwaiba.? Ashe kinsan da haka kika rufe ido kika doge sai kinga auren Ummul kaman lokacin baya da kika doge wajen ganin kin haifo d’a namiji.? Kaman yanda burinki na farko bai ta bata
ba Suwaiba haka burinki na biyu ina nufin ganin ‘yarki Ummul a d’akin aure kaman ko wace ‘ya mace bazai tabbata ba.!”
Dije na huci taci gaba “Kusanci da yarda da Tani ta baki da shi kikai amfani kika aure mata Miji. Mahaifiyarmu babu irin soyayyar da ba
ta Miki ba Dik a tinaninta zaki haifo mata jika namiji.. Wanda hakan yasa kukaje kukaita tsibbace tsibbacenku keda mahaifinki dan ki haifo d’a namiji..Idan kin mance na sake tuna miki da cikin Ummul mahaifiyarmu ta bar duniya bataga abinda kika haifa ba Wa
nda ta k’wallafa ran D’a namiji zaki haifo.. Bayan mutuwar Inna wato mahaifiyarmu mahaifinki ya Mutu shima. Daga nan ne Tani ta fara cuzguna Miki… Kika koma mata tamkar baiwa.. Duk abubuwan da kikai a baya basu isheki ba Suwaiba har saida kika saka mutanen
da basuda hakki ciki.. Idan ni na rasa Fa’iz Watak’ila sabida tsanar da na Miki a baya.. Su wad’ann mutanen mai suka Miki kika jangala masu Ummul...? Suwaiba dole ki haukace da son ganin ‘yarki tayi aure kota halin k’ak’a tsoron kar tsafin da mahaifinki y
a jefi ‘yarki dashi a lokacin da kike d’auke da cikinta ya tabbata.!”
Girgiza Kai kurum Umma take tana hawaye ganin Dije ta d’aureta ko ta ina.. Babu bayanin da zatai ta wanke kanta. Dije taci gaba “Ke fah akan cikan burinki Suwaiba babu Wanda bazaki ci
Amanansa ba. Koda kuwa wann mutumin ya Miki halarci kaman yanda Tani ta Miki..!”
Asshe ta shiga jinina Kai bakinta yana furta “Tabbas haka ne..! Sai yanzu nake fahimtar komai.. Tani taso nusar Dani gaskiya na rufe idanuna.. Ashe ita ce mai gaskiya.. Tabb
as na Miki rana Suwaiba.. Babu abinda ban Miki amma kika zab’i ki b’oye mun wann bala’i dake k’unshe jikin ‘Yarki.. Da niyyan taimako na nema ma D’an ‘yar uwata auren ‘yarki.. Ashe ke akwai k’ulli cikin zuciyarki.. Kin cika butulu Suwaiba.!” Muryar Asshe y
a soma rawa hawaye na gangaro mata “Ki sanar Dani mai zan fad’a ma ‘Yaruwata da ta aminta Dani Akan Tilon D’anta ta mallaka min wuk’a da nama.! Ki sanar Dani Suwaiba..!” Ta k’arashe kuka na kuma b’allo mata.
Umma na girgiza Kai tana hawaye take fad’in “Ki
yarda dani Hajiya Asshe.. Wllhi cikin maganganun Dije akwai Wanda sam ba gaskiya bane.. D’anta had’arin mota shine ajalinsa amma ba auren Ummul d’ina da Ya tasamma bane.!”
“Wani gaskiya kike dashi da har zan yarda dashi..?” Asshe ta katseta cikin d’aga
murya.
Lokaci guda taci gaba “Wann auren babu yanda zaije..! Bazan saka rayuwar D’an ‘Yaruwata Akan layi ba.. Za’a Warware wann aure tun kafin ‘yarki ta bar gidan nan.. Zan kira ‘Yaruwata na sanar da ita komai.. Ita zatai umarni ma D’anta ya datse auren Am
aryar da aka aura masa wacce ko saninta bai ba..!” Tana ida fad’in haka ta mik’e zata nufi sama..
Umma ta bita a guje ta duk’a gabanta ta kamo k’afafunta tana kuka sosai take fad’in “Ki rufa mun asiri dan girman Allah Hajja Asshe.. Dan Allah kar ki bari
a warware wann aure.. Dan Allah kar ki bari a maida sadaki.. Wllhi Ummul mace ce kaman ko wace ‘ya mace.”
Asshe ta fuzge k’afarta “So kike na kashe D’ah na Akan cikan makahon burinki Suwaiba..! Aure dole a warware..!” Tana ida fad’in haka ta kuma fuzge k’
afar ta ta nufi sama a fujajan kaman zata kifa.
Hannu biyu Umma ta saka aka tana kuka maras sauti tsoron kar Ummul taji muryarta tasan abinda ke wakana. A fili take furta ta shiga uku ta Mutu ta lalace.
Daga yanda Dije ke tsaye tana dubanta murmushi ta s
aki. Cikin zuciyarta take furta “Da kyau Dije.. Fansan ran Tilon D’anki kike d’auka.. Aima baki shiga uku ba tukuna Suwaiba.. Dan yanzu ne aka fara buga wasan.. Ba ke kad’ai bace kika iya buga wasa.. Saima kin ci karo da duk tanadin da na miki..
Asshe ta
na haurawa zama tai gijif saman gado tana jin wani irin tashin hankali na ziyartarta. Yanzu ta ina zata fara b’ullo ma wann al’amari..? Mai zata soma sanar da ‘yar uwarta bayan d’inbin kud’ad’en da ta asma daga wajenta..? Ta sanar da ‘yaruwarta d’iyan muta
ne masu mutunci mai irin matsalar da boka yace a aura ma Haidar ta samu dukda kasancewansu talakawa amma sunada dattako. Sabida Hajiya Kwaise bata amince D’anta ya kasance da d’iyar matsiyata marassa dattako k’ark’ashin kalmar aure ba koda kuwa na tsawon w
atanni uku ne kacal. Shin ta yaya zata soma gabatar da wann ahali masu dabaibaye da matsala Wanda tashin hankali yai ma rayuwarsu marfi, dangin tsiya dangin matsafa. Ba’a nan ta tsaya ba Ita kanta yarinyar an tsafeta tin a ciki.. Sann ita d’in barazana ce
ga rayuwar Haidar. Ta rintse idanunta tana jin tashin hankalinta na kuma ninkuwa.. Meyasa Tai komai a gaggauce..? Meyasa bata saurari Tani ba..? Meyasa Tai zaton kishi ne kawai da Hassada yasa Tani gaza zaune wajen ganin auren bai tabbata ba..? Ta Ware ida
nunta sanda zuciyarta ke ambato mata . ‘Mutuwar Kwasko kenan Haidar zaiyi da wann yarinyar da kika aura masa. Shin AUREN WATA UKU zaki ambaci auren ko Auren ajali.? Tabd’ijam! Wann shi ake kira cuta ta d’au cuta.!’
Ta kuma mik’ewa tsaye zufa na kuma tsar
tsafo mata. Zuciyarta ta shiga amsa mata d’imbin tambayoyin da sukai karan tsaye cimma Zuciyar nata ‘Me kike tunani a auren da aka faro bisa umarnin boka..? Me kike tunani a auren da ba’a nemi zab’in Allah cikinsa ba..? Me kike tunani cikin auren da ba’a d
’aukesa umarni daga Allah ba..? Me kike tunani cikin auren da ba’a ginasa bisa ginshik’in auren ba..? Ma’ana ba’ayi sa domin cika sunnar ma’aiki (SAW) ba. Dole abubuwa su biyo baya.. Dole bazaku ga da kyau ba. Kaman yanda kika rufe ido kikai ma ‘yar mutane
auren Mutuwa da D’anku haka nan wann matar da kika d’auketa shashasha tai auren mutuwa ma d’anku da nata ‘yar. Tirk’ashi. Lallai yau akeyinta.
Asshe taja wani irin gauron numfashi tana mai kuma mik’ewa tsaye daga zaune. Lokaci guda take furtawa a fili “M
e zan aikata ni Asshe.. Me zan sanar da ‘Yaruwata..? Zata fahimci k’arya naita shera mata kenan ina amsar mak’udan kud’ad’e hannunta..? Shin waye zai fanshe kud’ad’en da na amsa hannun Kwaise da sunan AUREN WATA UKU ma d’anta. Shin ma ta ina zan iya mayar
mata da kud’ad’en da ta bani na yak’in nemo ma Haidar matar wata uku..? Dan nayi imani nawa mijin ba biya zaiyi ba dan shi mutum ne da mata bata cin kud’insa sai wacce yake yayinta. Nida ‘Yaruwata kuma k’ar tasan k’ar ne akan kud’i. Zamu iya samun matsala
ta tarwatsewar ahali akan kud’ad’en da ta tafka asara ba tareda ta samu biyan buk’ata ba. Uwa uba taji auren mutuwa na shirya ma tilon D’anta Wanda ita kanta ta saka nata Auren cikin had’ari domin ta ceto sa daga mugun asirin da aka jefesa dashi. Mijina wi
ll come to know everything. Duk abubuwan da na aikata harda zuwa wajen boka da AUREN WATA UKU da na k’ulla Wanda Ya k’unshi kisan kai. Zai rabu dani rabuwa ta har abada. Even my children will leave me. Kowa zai gujeni na zama banida tsuntsu banida tarko. K
ishiyoyina su samu abun yawo Dani. Lallai ina tsaka mai wuya ni Asshe. Suwaiba ni ta cuta a duka wann al’amari. Gashi garin k’ok’arin gyara ahalin ‘Yaruwata ni zan tarwatsa nawa ahalin da farin
cikina.