Showing 12001 words to 15000 words out of 267381 words
Bazan bari wann d’an naki ya ruining d’ina ba.”
Izuwa lokacin cikin ta tunzura itama “Aw laifin Haidar kake gani..? Kai bakaga laifinka ba.. Kan wani dalili zaka cakume kwalan d’anka a bainar mutane.. Camera
s all over ba dole masu Neman ganin bayanmu suyi amfani da wann damar ba.. Yanzu sai ka yarda da maganan Haidar da yace maka akwai mai maka zagon k’asa cikin mutanen da ka aminta dasu..”
Katseta yai cikin b’acin rai “This is natural in a business world. W
e’ve business rivals and competitors. So ba abin mamaki bane idan sunada spy cikin Kampaninmu.. Amma babban abun takaicin shine yanda muka gaza handling such situations.. And this is all your Son’s fault.. He’s weak, idiot.. A pathetic loser.. Yana can ya
saka mata a ransa.. What do you expect..?”
Ya kuma jinjina Kai yana sakin huci sai yarfe gumi yake kai kace ba sanyin AC ne ke circulating cikin parlorn ba.
Isowar Haidar k’ofan gidan mahaifin nasa yai tozali da dandatson ‘yan jarida. Ai kuwa kaman jir
a suke suka nufosa suna jefo masa tambayoyi ta ko ina. “Yallab’ai Aliyu. Da gaske ne mahaifinka ya tareka da fad’a bayan cecekuce da ya kaure tsakaninku cikin Kampanin mahaifin naka..? Engr Maitama ka amsa mana..”
Da kyar ya samu ya kutsa cikin gidan sab
ida tambayoyi da kalaman da manema labaren keta jefo masa.
Yana dosowa parlorn Daddy ya nufesa a zafafe kaman zai shak’o sa Mommy tai saurin shiga tsakani cikin k’ok’arin dannar mijinta.
Sosai yake huci kaman zai kifa k’asa yana nuni da Haidar hannunsa
har rawa yake.
“You.. You and your entire existence is a disappointment..! Kai kayi kad’an ka lalata mun suna da sunan Company.. You better find a way to fix this mess kafin business rivals d’inmu su samu abun yawo damu kaji na fad’a maka.. Bazan tab’a b
ari bak’in cikinka yayi ajalina ba.. I will make sure to cut you off kafin hakan ta kasance..” Yatsanshi na rawa yaci gaba da nuna Haidar “So Kar ka sake kayi abinda zaisa na haramta maka amfani da sunana..!” Daga haka sa Kai yai ya haura sama dan a halin
yau fita ma bai ganshi ba ‘Yan jaridu ta ko ina. Dan yasan K’iris abokan adawansu na kasuwanci Ke jira. Har yayi step biyu ya kuma juyo ya dubi Haidar da idanunsa suka kad’a sukai jazir “Kaje ka sallami mutanen can da ka tara mun kof’ar gida.!” Yasa kai
yaci gaba da haurawa.
Furzar da huci Haidar yai yasa kai zai shige. Dan yasan mahaifinsa bazai tab’a sauraransa ba. Momy ta dakatar dashi
“Mom please not now.!” Ya katseta da fad’in haka.
Cikin rawar murya take furta “What’s wrong with you Haidar.. Wh
y are you doing this to us to yourself.. Meyasa ka maida iyayenka Abokan gabanka.. Why can’t you open your eyes and see my son.. Your Dad is only trying and struggling to make a proper man out of you..”
“Oh really Mom.! Is he really trying to make me beco
me a better person by pressuring me to meet all his expectations..?” Muryarsa ya soma rawa sanda yake furta “Na gaji.. Na gaji.. I’m fed up with everything around
here..!” Bai kuma tsayawa sauraronta ba yasa kai ya fice yana haki da huci ga wayarsa da ta g
aza yin Shiru. Kira ne keta shigo masa.
Saiga Mommy ta koma gefe tana hawaye. Meke faruwa da rayuwar ahalinta.. Meke damun Haidar.. Dik yanda akai something is wrong a wani wajen.. Zama bai ganta ya zama dole ta tashi tsaye. Da wann tunanin ta nufi nata
b’angaren duk jikinta a mace kaman dai ba Mommy ba. Mace mai zafi da jajircewa.
Jiki a sanyaye Anisa ta k’araso rik’eda waya ta mik’a ma Mommyn tana fad’in “Ammi Ke son magana dake tana ta kiran wayarki bata samu.”
Mommy tana amsar wayar ya fashe da ku
ka tana fad’in “Asshe ba lafiya.. Asshe gidana a hargitse yake..”
Jin haka yasa Anisa komawa dan ta baiwa ‘yan uwan waje su tattauna. Sosai hankalinta ya tashi da ganin yanayin Mommy dan tinda take bata tab’a ganin ‘Yaruwar mahaifiyar nata cikin irin wa
nn yanayi ba.
**
KANO
K’aton parlor ne mai d’aukeda kekunan d’inki kusan guda biyar. Yafi kama da wajen koyon d’inki.
Wata mata ce da ta d’an data a shekare tsaye cikin babban zauren tana duba kekunan.
Ummulkhairy ce ta soma halarta cikin d’aliban
nata. Dama ita d’in da wuri take zuwa kafin lokaci yayi dan ta taimaka da share share da gyare gyare.
Sallama saman bakinta ta shigo.
Matar ta fad’ad’a murmushinta “Wa’slaikissalam uwar alkhairi. Dan haka take kiran Ummul d’in a akasarin lokuta.
Ummul
khairy ta risina ta gaidata. Ta amsa kaman ko yaushe da sakin fuska “Uwar alkhairi kece dai kullum akan gaba kina masu wayo kina kwashe ladan. Wataran bazaki huta ba.. Jiki da jini Ummul kink’i ayi maku roster da kowa tasan ranan nata aikin.”
Ta murmusa
“Hajja ai nafi son na tara ladan da albarkan ni kad’ai ne..”
Hajja Fannah ta murmusa “Ai kuwa da izinin Allah albarka na bibiye dake.. Kinci sunanki uwar alkhairi..”
Murmusawa ta d’anyi kad’an jikinta na kuma yin sanyi da kalaman Hajja sakamakon tuno t
ashin hankalin da ta baro a gida. Ta mik’e da sauri gudun kar Hajja ta fahimci yanayinta ta d’auko tsintsiya zata soma shara Hajja da tuni ta karanci yanayinta ta dakatar da ita.
“Zo nan Ummul, zo ki zauna magana zamuyi kafin sauran d’aliban su k’araso. B
ar sharan nan.” Tai mata nuni da gefenta saman tabarma.
Jiki a sanyaye Ummulkhairi ta isa ta zauna.
Hajja ta gyara zamanta “Fad’a mun me Ya faru.?” Hajja Fannah ta jefo mata tambayar dan dama tana sane da halinda Ummul d’in ke ciki. Gidanta na bayan layi
n su Ummul layin da ke babban kwalta. Hajja Fannah tanada shagon d’inki da yara maza masu d’inki a shagon ta dake gaban gidan nata yayinda take koyar da ‘yanmata sana’ar d’inkin a cikin gidanta. Sunyi sabo mai tsafta da Ummul tin sanda ta soma koyon d’inki
wajenta. Tana bata shawarwari had’ida kwantar mata da hankali hakan yasa Ummul ke samun sanyi wajenta, takan kai mata damuwarta su zauna su tattauna ta kuma bata shawarwari masu amfani a gareta had’ida nitsa zuciya.
Ummul ta d’an share hawayen da suka g
angaro mata “Hajja wllhi na gaji.. Harga Allah na gaji.. Ita fah Umma ko wanne irin mutum so take na aura babu ruwan ta ko ina san wann mutumin ko bana so.. Ita burinta kawai nai aure da farin ciki ko babu. Ni kuma a halin yanzu wllhi batun auren nan ya f
ita kaina ni sana’ar nan da nake nafi samun kwamciyar hankali cikinsa fiyeda komai. Shin wai ita mace ba’a mata uzuri ne a rayuwar nan..? Hajja ba biye biyen
maza nake ba.. Allah shine sbiadana ina k’ok’arin tsare mutuncina.. Sann azumin litinin da Alhamis
duk basa wuceni ba wai dan na Gaza rik’e kaina ba sai dan sabida nasan shi azumi garkuwa ne Hajja.. Amma ita Umma duk fah bata ganin wann. Ita kawai damuwarta mutane da abinda suke Fad’i.. Shin Hajja menene laifin wacce Allah ya jarabceta da JINKIRIN aure
..?” Ta k’arashe damuwa fal fuskarta hawaye na kuma gangaro mata.
Girgiza kai kad’an Hajja Fanna tai, cikeda tausayi. Ta kuma gyara zama tana duban Ummulkhairy “Ummul, shi fah d’an Adam a koda yaushe bai rasa abin Fad’i.. Sann har abada bazaka tab’a Iya
r masa ba.. Mutum sai Allah..” Ta kuma gyara zamanta “Wato muna cikin wani irin Al’umma ne da k’addararka take iya zama zunubi a gareka.. Mai nake nufi da k’addararka tana zama zunubi a gareka? Macece Allah zai jarabceta da JINKIRIN aure sai kiji mutane s
una cecekucen cewa ta zauna a gida tak’i aure. Idan wacce take karatu ne sai kiji ance ta rungumi boko tak’i aure.. Idan ma Sana’a take dan ta rufa ma kanta asiri sai kiji ana cewa maza ke bata kud’i ta Kama Sana’a ne dan ya zame mata garkuwa kar a zargeta
.. Ita dai mace wai bazata rayu ba saida tallafin namiji. Mace ce Allah zai jarabceta da mutuwar aure sai kiji ana cewa ta kashe aurenta ta dawo gida bazaki tab’a Jin ance miji ya kashe mata aure ba sai k’alilan a’a itace dai Sarkin laifi. Kuma babban abin
takaicin mutanen da tafi kusanci dasu Sune mutanen da take soma fuskantar k’alubale daga wajensu. Kowa sai ya tsangwameta a cikin gidan baga iyayenta ba baga ‘yanuwanta ba a wasu lokutan. Kinga a nan k’addararta ya zama kuskurenta.” Ta d’an numfasa kafin
taci gaba “Ummul ba ina fad’a Miki haka bane dan kiga laifin iyayenki ko wani abu mai Kama da haka. A’a ko d’aya, burin ko wasu iyaye shine da zaran ‘yarsu ta isa aure su ganta a d’akin mijinta. Kuma babu iyayen da zasu so suga auren ‘yarsu ya Mutu. Toh am
ma idan jarabawan Ubangiji ya shigo ciki sai ayi hak’uri a fawwala masa lamuran. Ka tsara rayuwarka yanda kake burin Ubangiji ya tafiyar maka da ita tareda fatan mafarkan ka su cika ba laifi bane hasalima Wanda baya planning rayuwarsa baisan ina ya dosa a
rayuwar ba. Toh amma wasu lokutan yanda muka tsara ba haka rayuwar take zuwa mana ba. Dalili kuwa shine ba muke da hakkin tsara rayuwar ba iyakacin namu mafarkai da burika had’ida fata na gari. Ubangijin duka shike tsara mana rayuwar yanda yaso. Kuma tsari
nsa a koda Yaushe shine daidai. Idan ya amsa mana addu’anmu ya tabbatar mana da burinmu da fatanmu sai muyi farin ciki mu kuma gode masa. Sann idan ya jarabcemu ya janye wann fata daga garemu bamu samu abinda muke mafarki da buri ba shima sai mu masa godiy
a sabida shi yasan abinda yasa ya hana mu kodai abin mai cutarwa ne a garemu. Ko kuma ya mana tanadin Wanda yafi wann.” Ta kamo hannun Ummulkhairy cikin nata “In every delay, I believe there’s khayr.. Just like your name Uwar alkhairi. In sha Allahu JINKIR
INki zai zamto cikeda d’imbin alkhairi.. Babban abinda zan Miki wasiya dashi shine biyayya ma iyaye. Kar ki kuskura koda wasa ki fasa musu biyayya matuk’a bazasu ce ki sab’i mahaliccinki ba.. Idan kika rik’e biyayyan iyaye alkawarin Allah ne rayuwarki zai
cika da d’imbin alkhairi kinji ko..”
Ummulkhairy ta jinjina mata Kai a hankali kyakkyawan murmushi saman kyakkyawan fuskarta. Hak’ik’a tana samun relief da kalaman Hajja Fannah. Inama Ummanta zata kasance mai fahimta kamar haka. Sallaman wasu daga cikin d
’aliban yasata k’ok’arin saita kanta Hajjah Fannah na fad’in ta kwantar da hankalinta komai zai shige ya zama tarihi da izinin Allah. Ta mik’e tana amsa gaisuwan ‘Yanmatan da suka shigo tana fad’in yau dai Ummul d’inta zata huta Sune zasuyi shara su gyara
waje.
Daga can bakin Layi Alhaji Kamilu Ya aje motarsa Mama na biye dashi tana fad’in “Kai dai muje ka bama idonka abinci Alhaji.”
SameenaAleeyou
📚
*AUREN WATA UKU..!*
*06*
*©
️
Sameena Aleeyou…✍
🏽
*
K’ofan gidan Hajja Fannah Mama ke nuna
masa “Yauwa Alhaji. Nasan Kai mutumin kirki ne. Ance matanka ma ko fita unguwa basayi tsaban yanda kake kaffa kaffa da iyalanka. Toh kaga can yanda kaga mata da maza suna safa da marwa.”
Alhaji Kamilu ya kuma duba k’ofan gidan wanda shaguna suka saka a t
sakiya ga samari sai kai komo suke tsakanin shagunan can gefe harda shagon aski ga ‘yanmata masu sana’an koyon d’inki suna Kutsawa suna shiga gidan Hajja Fannah.
Mama taci gaba “Toh wann gida dai dake gani Ummul tana ciki da ita ake wann kai komo tsakanin
wad’ancan samari marassa tarbiya masu aski irin na shed’an.” Idanun Alhaji Kamilu ya sauk’a samarin da Mama Ke nuni dasu wanda suka fito shagon Aski gana ganinsu kaga samari marassa tarbiya ga wani aski da aka musu an kwashe gefe d’aya an bar d’aya. D’aya
saurayin ma harda sark’a a wuyansa.
Alhaji Kamilu yai Shiru kaman mai nazari. Sai kuma yace “Da zaran na aureta ta dena fita ko k’ofa dan mata na ko taron biki da suna basa zuwa babu yanda suke zuwa sai asibiti da ya zama dole.”
Mama tai ‘yar bazaurar
murmushi “Toh ai Alhaji ba a nan gizo Ke sak’an ba.” Ta kuma gyara tsayuwarta “Kaga wann gida da Ummul Ke zuwa da sunan koyon Sana’a. Matar gidan ba kowa bace face gasunk’umar kawaliya. Wllhi nake fad’a maka Alhaji ta addabi kowa ta fitini kowa a unguwar n
an. Mata take tarawa cikin gidanta maza kuma suna daga waje a shago. Maza take had’awa waje mata kuma cikin gidan ayita aikata masha’a ana aikata alfasha. Kuma ba zallan ‘yanmata harda matan aure a wann bad’ala da take had’awa. Na tabbata bazaka so ka auri
yarinyar da ta gama watsewa wajen wann hatsabibiyar Matar wacce ko aure bata dashi zaman kanta take zaman daduro.. Wann shago da koyar da sana’a da take cikin gidanta ba komai bane face rufa rufa gudun idon mutane. Amma mu da mukaga jiya mukaga yau a ung
uwar kowa ya kwana da sanin Kawaliya ce. Amma idan baka aminta da abinda nake fad’a maka ba zaka iya tare mutanen unguwar nan ka tambaya Kaji idan ba zaman kanta take ba. Ko aure bata dashi babbar Magajiyar karuwaice. Kaf ‘yanmata da matan aure dake zuwa w
ajenta da sunan koyon sana’a, karuwanci suke fitowa su fake da san’a. Meyasa Ummul tak’i aure..? Kai bakai ma kanka wann tambayar ba. Mace har mace kyakkyawa irin Ummulkhairy ta gaza samun mijin da zai aureta.. Ai kaima kasan da walakin wai goro a miya.”
Ganin Alhaji Kamilu ya kifa kansa had’ida maida hannayensa baya irin yanda manya suke idan suna tunani yasa Mama ci gaba “Ni wllhi ganin mutuncinka ne kuma ganin Malam zai yaudareka ya lik’a maka ‘yarsa da ta gama yawon ta zubar a kororo yasa nai wann shah
adar nace bari dai na sanar dakai gaskiya ka gane dalilin da Ke sa ko wani namiji mai kamala da mutunci Ke guje ma aurenta. Malam bai dubi amanar dake tsakaninku ba. Ba kalan suturan da baka masa ba amma ya zab’i ya maka lumbu lumbu dan dai kawai shima ya
rabu da alk’ak’ai.. Yo shima ya gaji da ita.”
Birki tai da kalamanta ganin Hajja Fannah ta fito biyeda ita Ummulkhairi ce rik’e da kayan d’inki suka shige shagon d’inki ga wani matashi ya fito daga cikin shagon ya gifta ta gefen Ummulkhairi.
Mama tai k
abbara tana hamdala “Ka gani ko.. Ka tabbata ba sharri nake ba. Wai ance gani ya kori ji.. Kana nan kanata rawar k’afa zaka angwance toh aikin banza kake wai rufin d’aki da b’arawo dan k’artai bila adadi sun rigaka..” Ta numfasa had’ida gyaran murya “Toh A
lhaji ni na gama nawa, Allah ya gani na fita na sanar dakai. Kuma ka gani ma idanunka. Ya rage maka ka amince ka sai ma kanka da iyalanka tikitin mutuwa dan k’anjamau ne zai maku sallama. Ka taimaki kanka kaman yanda saura suka taimaki kawunansu. Ni na Ba
rka lafiya Alhaji..”
Tana ida fad’in haka tasa kai ta shige zuciyarta fari tas.
Alhaji Kamilu kuwa sai kallon k’ofan shagon yake yana jira yaga ko Ummulkhairi zata fito amma shiru. Zuciyarsa sai tafarfasa take haka yaja k’afafunsa yana sab’a babbar rig
arsa da take ‘yar duk’unaso ya nufi motarsa.
**
Mama tana shigowa gidan ta cire mayafi ta soma zuba ruwan bala’i
“Iyi.. Kan wani dalili za’a tare ni a hanya ana mun cin mutunci kan laifin da banji ba ban gani ba.. Babu wanda ya huta a gidan nan duk ak
an rai guda.. Baga yarana dake gidan mazajensu ba yanzu abun har ya tsallako kaina… Toh wllhi bazan d’auki cin mutunci daga kowa ba kan ‘yar da ban haifa ba..!”
Umma ta fito daga kitchen afujajan tana goge idanunta da hayak’i ya sanya mata su hawaye “Yaya
lafiya.. Meke faruwa..? Wani abu ne aka miki..?”
Mama taci gaba da tururi “Yo uban meye ma ba’a mun ba.. Gashi can Alhaji Kamilu yake ko ya tareni a hanya ta yanda yake shiga ba ta nan yake fita ba saikace alhakin tarbiyan Ummul a hannuna yake.!”
Cikin
Umma ya bada wani irin sauti k’uuuu “Wani abu ne Ummul d’in tayi Yaya.?”
“Meye kuwa batayi ba bayan ganinta a gidan Matar nan da yayi wacce kowa ya kwana da sanin Gasunk’umar magajiyar karuwai ce.. Ai bansan shashashancinki ya kai har haka ba Suwaiba.. N
i na zata da kika samu wanda zai rufa ma Ummul asiri ya aureta kinyi mata iyaka da gidan wann Kawaliyar mai zaman kanta ashe saketa kikai kamar tinkiya tana ci gaba da zuwa.. Yo a haka ne kike buri da fata ta samu mijin aure bayan kowa ya kwana da sanin ga
hark’ar da Matar take d’aura ‘yanmata. Ai gashi can Alhaji Kamilu dik yanda akai yaji daga bakin mutane. ya tareni yana sanar dani dama munsan ‘yar mu yawon ta zubar take waye ya mutu waye tashi..” Ta kafe Umma da tuni duniya ya shiga juya mata kafin tac
i gaba “ Bari kiji Suwaiba nidai ban haifi Karuwa ba Allah ya gani ehe..!” Ta k’arashe tana mai shigewa fuuu.
Umma ta soma girgiza kai tana dafe kai ta shiga bin bayan mama tana “Na shiga uku ni Suwaiba..! Yaya kar kiga laifina.. Wllhi laifin Malam ne na
mata iyaka da wann koyon san’a amma shi ya k’yaleta yace dole ya koyi san’a tinda ba karatun take ba.. Amma anyi na farko anyi na k’arshe bazan bari Ummul ta kuma jaza mun ba..!” Ta k’arashe tana zaran mayafinta. Ta nufi waje a fujajan.
Mama ta bud’e mu
rya tana fad’in “Miyar tuwonki