Showing 129001 words to 132000 words out of 267381 words
kike nema wajena.?”
Anisa ta furzar da huci “Money Hilal. Kudi n
ake nema wajenka.”
Hilal ya kuma darawa teasingly yake fad’in “Kuda kuke Abuja gaki ga shugaban k’asa ina zan samo kudi a state na baki.”
“Hilal I’m being serious here. Da gaske kudi nake nema. And it’s urgent.”
“Ok fine. Nawa kike nema.?”
“1M..!” Ta
fad’i kaman mai tsoro.
Dariyar rainin hankali Hilal yai “What.! Are you kidding me Neesa.. 1 million a wajen D’an makaranta irina..? You’ve got to be kidding me. Why not ask Abba. shine D’an kasuwan bani ba. And hey I’m not his manager.”
Anisa tace “Ha
ba Hilal. Nasan kanada hanya Shiyasa na kiraka.. Wllhi ina tsananin buk’atar kudin nan. Look zan biyaka da zaran na samu.”
Hilal ya d’anyi Jim Jin tayi sounding serious. Shima sai ya daina wasa “Wait Anisa. Be honest with me.. What have you got yourself
into..? Gambling kika fara..? Dan nasan dai ba business din da kike. Kodai kinje kin hadu da wasu scammers ne.?”
Anisa ta rausayar da ido “Hilal dan Allah ka taimaken mana nasan Abba naji dakai wllhi na rantse maka da Allah matsala nake ciki. Haba Hilal
meye amfanin ‘yanuwa ma junansu idan bazasu rufa asirin juna ba. Nasan Mommy zata bani idan tasan ina nema amma bana so ta sani. Kasan masu kudin nan the moment suka gane abun hannunsu ya rufe maka ido akwai matsala.”
Hilal ya d’anyi jim “Anisa ni fah kud
in dake account dina pocket money na ne. Kuma idan har na baki su yanzu za’azo a shiga tsakiyan semester ne ina nema. And kinsan Abba komai da lissafi yake bazan zo masa da labarin rashin kudi ba tinda yasan ya sallameni. Cewa zai wasa nake da kudi sai naj
e nai ko aikin k’arfi ne a can na ci da Kaina.”
Anisa tace “But you are his favourite.”
“Even so Neesa. Kinsan yanda mahaifinmu yake idan aka zo maganar kudi.”
Zata kuma magiya Hilal yace “Fine… Zan tura miki.. Amma ko da wasa kar ki bari ko Ammi tasa
n na baki banso na hadasu fad’a da Abba.”
Anisa tai alaman zipping bakinta da yatsa kaman Hilala na kallon ta “An gama my dear Brother. That’s why I so much love you.”
Da haka Anisa taita gwada Hilal tana fad’in irin son da take ma tilon dan uwan nata.
Gama wayar da zatai ta waigo gabanta yai wani irin fad’uwa samakon ganin mutum da tai tsaye bayanta. Taci gaba da yatsina fuska tana dubansa “Malam lafiya.? Wanene kai.?”
Huci kurum Hisham yake yana dubanta kaman zai shak’ota. Yaci gaba da jinjina Kai
yana fad’in “Nasan kece.! Kece kika tassama kashe Ummul.!”
Anisa ta zaro ido waje ganin stranger da ko saninsa batai ba yana fad’in laifin da ita da Laila suka binne. Ta soma girgiza kai tana fad’in “No.. I don’t know what you are talking about Malam. Me
yasa zanyi yunk’urin kashe Ummu. What could be my motive.? Wait why am I even explaining myself. I don’t even know you. Excuse me.” Tasa kai zata shige.
“You are the only person with the motive to kill her.. Because you love Haidar.. Haka ne.?” Ya k’aras
he yana tsareta da ido.
Anisa taja Birki tana dubansa shaye da mamaki. Sai ta soma girgiza kai kad’an ganin dai guy d’in nan da gaske ya sansu “Mai kake nufi..? Wanene Kai.?”
“Na tuna miki ne. Kwanakin baya lokacin da motar ki tabi bayan motar Haidar. C
ikin k’ok’arin bin bayansa da kike dan ki gano yanda yake zuwa. Someone hit your car and stopped you from following him.. That someone.. Was me.. Ni ne na bigi bayan motar ki na hanaki bin bayan Haidar.”
Anisa ta soma tuno kwanakin baya Mommy tasa ta bi
bayan motar Haidar dan gano yanda yake zuwa amma sai tai accident a hanyar ta wata mota da bata tantance ba ta bugi bayan motar ta Wanda hakan Ya hanata bin bayan Haidar.. Kenan wann mutumin ne Ya bigi bayan motarta. Ta d’ago a d’an firgice tana dubansa “W
ait.. Kaman nasan fuskarka.. Wait… Aren’t you friends with Haidar.?” Ta dan murmusa tana girgiza kai “Oh now I understand.. Are you his watchdog.? Trying to play best friend of the year.? Wow you try..” Ta d’anyi shiru tana dubansa “Don’t you think… you ar
e over reacting.. I mean, matar abokinka kake karewa irin haka.”
Hisham Ya fahimci Anisa shashasha ce kuma zata zamto makami mai k’arfi da zai amfani da ita wajen k’watan Ummul daga wajen mortal enemy d’insa Haidar.
Anisa ta murmusa tana dubansa “Or may
be it’s the other way around.. Mai kake tunanin Haidar zai yi.? if he finds out that his coworker or should I put it this way… His friend is in love with his wife… Kodai ku masoya ne dama tintinin.?” Ta k’arashe tana tsaresa da ido.
“Think whatever you
want to think.!” Ya k’arashe yana matsowa kusanta kaman zai shak’ota tana k’ok’arin matsawa baya.
Anisa taci gaba da Zare ido “Malam idan baka k’yaleni ba zan maka ihun b’arawo.!”
Yaci gaba da jinjina Kai “Go ahead and shout! Let see waye yakeda abun f
ad’i ma ‘yansanda.”
Sai kuma tai shiru tana ci gaba da Zare ido. Hisham yaci gaba “If you dare think of hurting Ummul.. Believe me I’ll deal with you myself.!”
Cikeda tsoro had’ida mamaki Anisa ke dubansa. Sai kuma ta girgiza Kai tace “And… who are you
to Ummul.? Dan ban yarda kana son kareta ne kawai dan kana abokin Haidar ba.”
Kallon shashasha yaci gaba da yima Anisa dan da tasan lokacin da ya bugi bayan motarta Ya hanata bin bayan Haidar ba don Ya kare Haidar yai ba sai dan ya hanata gano Matar Haida
r da Ahalin Haidar d’in basu san da ita ba wato Dareen da wann doluwar bata tsaya tana bata bakinta ba.
“Idan kika sake yunk’urin cutar da ita .. Sann ne zaki san ko ni waye.”
Anisa ta murmusa tana dubansa “Ta Ya zan cutar da ita balle Har ka bata kari
ya bayan an riga an d’auketa.”
Hisham Ya dubeta ya kuma girgiza kai da mamaki “Kina so kice mun Ummul bata asibitin nan.?! Is she kidnapped or something.? Waye ya saceta.?”
Anisa ta kuma murmusawa “One question at a time. Wanda ya fimu kusanci da ita dag
a ni har kai shi ya saceta.. Ina nufin mijinta..!” Ta k’arashe da murmushi saman fuskarta. Zuciyarta na tabbatar mata abokin Haidar son Ummul yake ba tareda sanin Haidar d’in ba. Amma ita idan har haka Ya tabbata ribanta ne dan zasu had’a team mai k’arfi w
ajen ruguza tsakanin Ummul da Haidar.
“Ina Haidar Ya kaita.?” Ya tambaya yana duban Anisa.
Anisa ta murmusa “Why not ask him.. After all, abokin ka ne… Kasan me.? Although Haidar never introduce his friends to his family na rasa gane ya akai nasan fuska
rka matsayin abokinsa… Koda yake wann Dan uwan nawa bamuyi zaton ma nada abokai ba.. Maybe kaima d’in dan wajen aikinku d’aya ne Shiyasa.. Im sure na tab’a ganinka ka kawo masa wasu takardu da Ya danganci aikin company gida.”
“Shut up.” Hisham ya katseta
jin tana sunbatun da babu Wanda Ya tambayeta. Yaci gaba da dubanta “Kina jina.. Yes ina son Ummul. With every fibre of my being. Hasalima ni na fara sonta kafin ta zama matar Haidar.. You and I are going to help each other out. Ina so ki tabbatar min cewa
my secret is safe with you kaman yanda naki ya zama safe dani. That is idan kina so mu raba su biyun.. Ki mallaki Haidar na mallaki Ummul.. Zan iya tabbatar Miki with my help.. Haidar will be yours forever..”
Anisa ta zaro ido waje “Da gaske kake.. Let’s
team up then.. Zanyi komai.. In fact kokari kullum nake dan burina Ya cika.”
“Your wish has been granted..” Ya fad’i yana jinina kai.
Take sukai exchanging phone number cikin k’ok’arin yanda zasu fara zartar da plan dinsu na k’ok’arin raba Haidar da Um
mul.
Tsaye Hisham yai a dakinsa na sirri Wanda hotunan Daddy Mommy harma da Haidar sune kawai a cikin d’akin an mammannasu jikin wall. Had’ida dangin magazines masu d’auke da labarun Maitama Builders. Da duk wani article da ya k’unshi scandals wanda suk
ai popping a labarun kasuwanci wad’anda suka danganci Kampanin Maitama da ahalinsa. kaf shi yake fitar da scandals d’in. Yai tsaye gaban hotunansu yana kallo lokaci guda yake furta “Why Ummul.? Why her..? Menene dalilinku na kawo Ummul cikin wann messed
family din naku.!” Yakai dubansa kan hoton Mommy, lokaci guda yaci gaba “Kwaise Maitama ya kikaji zaman kurkuku.? you are the one who instigated everything.! You should suffer the consequences.. All the hardships nida mahaifyata had to experienced. Kece ki
ka jawo.!” Yaci gaba da jinjina Kai “It is your fault that I had to search for people who would accept me all my life..?!” Ya k’arashe hawaye na gangaro masa. Yaci gaba da jinjina kai “You are now in Jail… Ke d’in yanzu kina tsare a kurkuku.. Abin takaici
n kuma D’anki ne Ya kaiki. Did you know that… I was born in a prison..? Did you know that I grow up thinking ni ba kowa bane but a son of a criminal..?! Yai maganar cikin tsananin sakin huci kafin yaci gaba “This is the perfect time for me to ruin your lif
e completely kaman yanda kika lalata nawa. Yanzu ne lokacin da ta kamata na fitar da labari akanki. Kinyi yunkurin kashe matar D’anki. Ya kika ji labarin Kwaise.? Abun zai matuk’ar k’ayatarwa musamman a shafukan labarun kasuwanci. Dan na tabbata Aliyu Mait
ama ba korar wulakanci kawai zai Miki ba muddin kika bata masa suna irin haka a duniyar kasuwanci. Zai tabbata dake da D’anki da kika koreni sabida shi naku rayuwar ya daidaice fiyeda yanda nawa rayuwar da na mahaifiyata ya daidaice. Saidai kashh.! Ummul t
a shiga cikin wann ahalin naku. She shouldn’t get involved..! She shouldn’t.!” Yaci gaba da jinjina Kai yana sakin huci “Kaman yanda nai alk’awarin tarwatsaku haka nai alk’awarin fitar da Ummul daga wann ahalin naku. Sai na rabaka da Ummul Haidar domin kuw
a ita d’in tawa ce.!” Ya k’arashe yana duban hoton Haidar da idanunsa da suka gama rinewa zuwa ja.
**
Ba shi ya dawo gidan ba sai yamma lis. Tana nan kwance k’asa zazzabi Ya gama lullub’e ta. A hankali Haidar Ya tura k’ofan d’akin hannunsa rik’eda manya
n ledodi. Hangota da yai kwance saman rug ya sanyashi saurin sakin ledojin Ya k’arasa gareta. Ya kai hannu ya tab’a goshinta ganin sai rawan d’ari take. Nan yaji jikin nata zafi k’au. A hankali ya furta “Oh no she’s burning up. What do I do..?!” Ya furta
yana dubanta gashi ya mance magungunanta a pharmacy din da ya saya. Wani tunani ne yazo masa yai saurin d’agota daga k’asa Ya daurata saman gado ya shiga janyo bargo yana rufa mata ganin sosai take rawan sanyi.. Ya soma rurrufe windows trying to keep her w
arm. dan dik shi a tunaninsa haka ne zai sauk’ar mata da zazzabin ta daina jin sanyi. Amma sai yaji kaman zafin jikin ya karu ga rawan sanyin da take ya karu.
Yai tsaye yana kallonta yana tunanin abunyi.. Ko room heater zai fita Ya nemo Yai warming dakin
dashi..? Ya nufo waje sauri sauri yana tunanin nemo room heater. Cak kuma yaja Ya tsaya kaman Wanda aka dakatar dashi.
“Dr Faruk.” Ya furta a hankali kafin ya soma jinjina kai “Yes I need to call him..” Ya k’arashe yana mai Ciro wayarsa daga aljihun jea
ns d’insa. Nan ya soma dialing layin Dr.
Dr yana dauka Haidar Ya soma sanar dashi cewa jikin Ummul yayi zafi sann Ya mance bai taho da maganin ba. Meye first aid da ya kamata ya soma bata.
Dr Faruk ya murmusa daga d’aya b’angaren. Soyayyar Haidar ga ma
tarsa na kashesa “A cool shower will help.. And she should wear lighter and more breathable clothing.”
Haidar ya jinjina kai yana nanatawa “A….. cool shower.. Ok, cool shower..”
Dr ya kuma amsawa yana mai fatan samun sauk’i ga matar Haidar d’in. Haidar
yai masa godiya kafin yai hanging up.
Dawowa d’akin yai Ya ganta nan yanda ya barta saman gado tana rawar sanyi. Yai saurin k’arasawa Ya yaye bargon da ya rufa mata. Ya soma k’ok’arin rage mata tufafin jikinta amma sai ta takure jikinta waje guda tana fa
d’in Ya kyaleta dukda rawan sanyi da take.
Cikeda takaici Haidar yai jifa da hulan da ya zame daga saman kanta “Fine then, take the shower like this.” Ya k’arashe yana mai dagota daga saman gadon Yayinda Ummul ke k’ok’arin tattaro sauran strength da ya r
age mata tana janyewa daga jikinsa tana fad’in ina zai kaita ya kyaleta.
Bai tsaya amsata ba Ya nufi bathroom da ita cikin hannunsa. Taci gaba da k’ok’arin turasa Haidar na rik’eda da ita yana fadin “Stay here and take a shower. You are burning up.” Ya k’
arashe cikin k’ok’arin tsaida ita kan k’afafunta amma sai ta soma k’ok’arin zubewa a k’asa sakamakon rashin karfi. Bai bari takai kasa ba yai saurin k’arasowa ya rungumeta cikin jikinsa a daidai lokacin hannunsa ya tab’a switch na shower din ai kaw nan ruw
an ya soma zubowa kawunansu su duka biyun. Sauk’an ruwan da taji saman jikinta a bazata ya sa ta sakin ajiyan zuciya Wanda yasa Haidar yai mata cover da arms d’insa kaman mai tsoron kar ruwan Ya cutar da ita. Ya shigar da ita sosai cikin k’irjinsa ruwan n
aci gaba da zubowa kansu. Yana jin yanda ruwan ke ratsa dumin jikinta zuwa nasa jikin. A hankali Haidar ke lumshe idanunsa yana jin harbawan da zukutansu keyi kaman a tare.
Sun d’auke minutes a haka kafin yaji temperature dinta na sauka a hankali. A haka
Ya fito da ita daga bathroom din su duka biyu jikkunansu a jik’e. Cikin kayan da ya shigo dasu Ya Ciro towel sabo Ya rufa mata. Ya d’auki hand towel din yana tsane sumarsa. Lokaci guda yake furta “Change those clothes before you catch cold.” Yana ida fad’
in haka yasa zai fice yayinda Ummul ta mak’ale sosai cikin towel din da ya rufa mata. Tabbas zazzabin da takeji ya dan sauka. Sanda taga haikan zai kuma ficewa ya kulleta a wann dakin tai saurin bud’e murya tace “Dan Allah ka dakata.”
Haidar Ya tsaya Cak
sanda yaji muryarta.
Ganin Ya tsaya yasa Ummul ci gaba “Meyasa ka kawoni nan ka kulleni..? Dan.. Dan Allah.. Ka fitar Dani daga kurkukun nan.” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.
Juyowa yai yana dubanta sai ya dawo da baya. Yai tsaye kanta hannayens
a hard’e yayinda Ummul ta soma k’ok’arin jada baya. Sai taji ya soma fad’in “Who are you.? Meyasa kika yarda da auren mutumin da baki taba sani ba. Is that even possible.?”
Shiru tai ba tareda ta iya amsa masa tambayarsa ba sai bugun zuciyarta dake karuwa
.
“Did Mommy buy you with money.? Nawa ta biya ta sayeki dan kawai kizo cikin rayuwana.?!” Ya k’arashe cikin d’aga murya.
Ta soma girgiza kai tana hawaye. Abinda baison gani a rayuwarsa. Yai gajeren tsaki yana kauda fuska gefe jin bata amsa shi ba sai h
awayen dake gangaro mata.
“Fine.. Since you don’t want to talk. Enjoy your stay here. Dan bakida ranan fita a nan.!” Ya k’arashe yana mai jifa da hand towel din da ya gama tsane sumarsa dashi zuwa gefenta Wanda saida ya dan firgitata.
Da taga haik’an da
gaske zai kuma ficewa ya sanyata saurin fad’in “Nayi ne sabida Iyayena.!” Tai maganar cikin rawar murya irinta mai kuka.
Haidar Ya kaikaito yana dubanta. Ya tako zuwa gabanta “Kin amince da auren mutumin da baki tab’a sani ba sabida iyayenki .? Are you
that desperate.?!”
Ta girgiza masa kai tana hawaye “Kud’in aure na.. Shi…. Shine kudin jinyar Abba na… Sann mahaifiyata…” Ta kasa ci gaba da magana sakamakon rawa da muryarta keyi.
Haidar ya kafeta sosai da ido. Ya dan d’ibi dak’ik’ai a haka kafin yace
“So I was right. Mommy sayenki tayi da kudi.. Nawa ta sayeki dashi.?!” Ya k’arashe maganar zuciyarsa na masa zafi.
Ta rintse idanunta sosai hawaye na zubo mata. Ba yanda ta iya dole ta fad’a ma Haidar mak’asudin aurensa koda zai kawo karshen zamansu. Ita
dai burinta taje ta fidda Mommy daga kurkukun da ake k’ok’arin kaita. Zatai komai dan ta kub’utar da Mommy matar da tun shigowarta gidan bata nuna mata komai ba face zallan k’auna.
Muryar Haidar ta kuma ji cikin tsananin huci yana fad’in “You sold yours
elf to her.. You don’t deserve to go free.!” Yana maganar yana jinjina Kansa. Lokaci guda yasa kai ya fice rai bace. Kallo d’aya zaka masa ka fahimci abun ya masa zafi sosai.
Ummul ta kuma runtse idonta wasu hawayen na gangaro mata.
Can dare ta kuma ji
n shigowarsa dan har tayi zaton bazai kuma dawowa ba. Wann karon bai ko kalli yanda take tak’ure ba ya aje mata wasu ledodi. D’aya na abinci d’aya na magani.
Baice da ita komai ba ya nufi k’ofa. Yana k’ok’arin fita ta rarrafo garesa tana rok’onsa “Dan All
ah ka fitar Dani daga gidan nan.. Wllhi tsoro nakeji.. Dan Allah kar ka barni a nan..!” Ta k’arashe tana had’e hannu alamun rok’o.
Wani kallo ya watsa mata kafin yasa kai ya fice yana mai rufe d’akin.
Ummul tai lamo a wajen tana mai lumshe idonta Wanda
kuka ya zame masu jiki. Ga dare ga jeji. Bata jin komai sai kukan tsuntsaye. Addu’a kawai take tana kai kukanta ga Rabbil Izza da Ya jibinci