Showing 228001 words to 231000 words out of 267381 words
murya take tambayarsu “Ina Ummulkhair..? ina ‘yaruwarku.?!”
Bata rufe baki ba ta hango U
mmul na shigowa cikin matuk’ar sanyin jiki, kanta kife ga jariri sabon haihuwa nad’e cikin hannunta. Mommy da Aunty Asshe na biye da ita.
Umma ta mik’e cikin matuk’ar sanyin jiki tana duban Ummul dake shigowa. Tuni Umma ta soma tafiya ta nufi Ummul. Tana
k’arasowa gareta taja ta tsaya kukan da taketa k’ok’arin dannewa yana kuma fizgarta “ ‘Yata.. ‘Yata Ummulkhair..!” Sai Umma tai bursting cikin kuka yayinda Ummulkhair ma kuka ya kufce mata.
Asshe ce ta amshe jaririn daga hannun Ummul wacce tuni ta zube
k’asa gaban Umma tana kuka sosai.
Sai Umma ma ta duk’a ta rungumeta ‘ya da uwan suka b’ige da kuka mai ban tausayi..
SameenaAleeyou
📚
*AUREN WATA UKU..!*
*58*
*©
️
Sameena Aleeyou…✍
🏽
*
Kan Ummul bisa cinyar Umma hawaye naci gaba da gangaro m
ata yayinda Umma ke ci gaba da Shafa kanta a hankali itama d’in hawaye ke gangaro mata.
“Nayi kewarki… Nayi kewarki sosai Ummata.. Dan Allah Ki yafe mun..!”
Umma taci gaba da Shafa kanta a hankali murmushi gauraye da hawaye saman fuskarta “Baki na goma
kenan kike neman gafara na Ummul.. Ni mahaifyarki ce kuma na yafeki tun kafin ki nemi yafiyata.. Babu abinda yake tsakanin ‘ya da uwa face yafiya da afuwa.!”
Sai Ummul ta sake bursting cikin kuka mai tsuma zuciya. Daidai nan Mama Tani ta shigo da Baba A
li dake yan k’anan kuka tana sanar da Umma tafiyar su Hajiya Kwaise da Hajiya Asshe.. Umma ta amshi jaririn tana lallashinsa lokaci guda take ce da Ummul maza ta mik’e ta kintsa kanta ta kula da yaron kafin Abbanta ya shigo.
Ummul ta d’ago ta dubi Umma t
ana goge ragowar hawayen dake fuskarta. Murya a sanyaye tace “Umma da gaske Abba ya samu lafiya Har ya fara fita kasuwa.?” Tai maganar tsantsan farin ciki na nunawa a fuskarta.
Umma ta murmusa “K’warai kuwa. Abbanki ya samu lafiya.. Nan bada jimawa ba zai
shigo da yardar Allah.”
Sai Ummul ta mik’e jiki a sanyaye tana tunanin yanda had’uwarsu da mahaifin nata zai kasance.
Wanka sukai ita da jaririnta dan tuni Mama Tani ta d’aura ruwa bisa murhu tin isowarsu. Yaron Ya samu bacci da yaji ruwan d’umi. Umma
ta saka yaron gaba tana kallonsa sassanyar murmushi saman fuskarta. Yau ga D’an Ummul dinta nan tana gani za kuma ta sab’asa a baya ta goya da izinin Allah. A haka Mama Tani ta shigo ta taddata. Su duka biyun suka tasa yaron gaba suna kallo. Mama Tani Tai
saurin bud’e net d’insa tana k’ok’arin rufa masa Umma tace “Yaya naga dare baiyi ba da an kyalesa da gidan sauron nan tuk’uri ne dashi.”
Mama Tani ta rufe gidan sauron ruf tana fad’in “Um um Suwaiba gwara dai mu killacesa jikan Manyan mutane ne wann.. In
a mai baki labari gobe zakiga Hajiya Kwaise sassafe gidan nan matuk’a tana garin nan.. Muddin taga alamun cizon sauro jikinsa na tabbata bazata bari ya kuma kwana gidan nan ba.” Ta gyara zama tana kame hab’a “Umm Suwaiba am.! mu muka sha kallo yanda ake ta
ltala yaron nan da kyar Ubansa Ya amince a taho dashi nan.” Ta k’arashe tana gyara zaman net d’in sosai.
Umma ta murmusa tana girgiza kai kad’an. Sai suka dubi juna itada Mama Tani sanda suka hangi ‘ya’yansu ras zaune daga parlorn Umman.
Mama Tani ta g
irgiza kai tace “Wato Al’amarin Allah sai a bar masa kayansa Suwaiba. Duk Wanda yace zai shishigi ko k’atsalandan a hurumin Ubangiji toh fah Tabbas sai Allah Ya nuna masa iyakarsa. Yanzu dai ki duba kiga yaran nan yanda muka ci musu burin zaman gidan miji
gasu nan ras a gabanmu yanzu. Ba wai basu je gidan mijin ba sunje amma sai Allah Ya dawo mana dasu gabanmu dan mu hankalta mu kuma dauki darasi. sabida a lokacin da mukaci musu burin zama gidajen mazajensu bamu nemi zab’in Allah ba sann mun zata iyawan mu
shi zaisa su samu mazajen aure kuma su natsu a gidajen Aurensu. Ashe ba iyawan mu bane ba kuma wayonmu bane.”
Umma ta jinjina Kai “Wann gaskiya ne Yaya. Allah yasa hakan ya zamto izna a garemu da masu hali irin Wanda mukayi a baya.”
Mama Tani ta amsa da
Ameen Suwaiba.
A b’angaren Ummul kuwa sabon tashin hankali ta shiga dan tinda Abba ya dawo daga kasuwa yak’i ya dubi koda yanda take balle ya amsa gaisuwarta. Ko jaririnta bai kalla ba balle ya amshe sa.
Tai kwance lamo saman cinyar Umma hawaye naci gab
a da gangaro mata “Umma Abba yak’i ya min magana. Yak’i amsa gaisuwata.. Yak’i ya dubi jaririna.. Umma Abba bazai tab’a yafe min ba..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.
Saurin toshe bakinta Umma tai “Kul Ummul. Kar ki sake magana irin haka..Kiyi ma
Abbanki uzuri dan tinda ya farka daga jinyar nan nasa al’amarinsa sai a hankali. Musamman idan ya hau dokin fushi. Masana sun alak’anta hakan da magunguna masu k’arfi da yake sha ga kuma ya hadu da girma. Ki basa lokaci a hankali zai sauk’o ya huce kinji
koh. Maza tashi ki daina kukan nan haka.. Kici abinci ki sha ruwan d’umi kafin Babban mutum ya tashi a nasa barcin.”
Ummul ta mik’e zaune tana goge hawayenta tana tunanin irin soyayya da shak’uwar dake taakaninta da mahaifinta yau an wayi gari itace Abba
take gaishesa ya juya mata baya ba tareda ya dubi koda yanda take ba balle ya amsa gaisuwarta. Jiki a matuk’ar sanyaye ta nufi band’aki nan cikin d’akin Ummanta. Dan a gyaren gyaren da Haidar yasa akai ma gidan harda band’aki akai masu gaba d’aya kowa ciki
n d’aki aka kuma kawata ginin gidan kaman ba shi ba.
Zama tai ta saka abincin gaba ba tareda taci ba. A haka Umma ta shigo d’akin ta taddata zaune saman pillow kaman yanda ta shirya mata wajen zaman. Umma ta soma da lallashi amma Sam Ummul bata iya cin a
bincin ba har dai Umma ta dan soma mata fad’a maimakon taci abincin kawai sai ta b’ige da kuka. Ta kasa yarda wai ita Ummulkhair d’in Abbanta Abba ke fushi da ita irin haka. A haka Khulsum ta shigo rik’e da waya tana fad’in “Adda Ummul ga Ya Haidar a waya
yace a baki.”
Ko sauraron Khulsum batai ba balle ta amshi wayar.
Khulsum ta dan furzar da huci tace dashi “Tak’i ta amshi wayer.”
Umma ta tsare sosai tace maza ta amshi wayar. Ba don taso ta amsa Umma da Khulsum suka fice suka barta rik’e da wayar ba
tareda tace dashi komai ba. Mugun takaicinsa ne ya kuma taso mata. Ita gani take duk laifinsa ne Abba ke fushi da ita. Watak’ila da bai amince da Auren Wata Uku da yai da ita ba tun a fari da duk wad’ann abubuwan basu faru ba. Duka laifin na Haidar ne da
ya amince zai AUREN WATA UKU da ita.
Maganan duniya Haidar ya mata tak’i ta amsa. Yayi magiyar yayi lallab’in duk bata amsa shi ba har saida suka sinkayo kukan Baba Ali alamun ya tashi a bacci. Dan ta k’ara basa haushi sai kawai ta barshi yanata suararo
n kukan D’ansa cikin wayar. Har lokacin ba abinda tace sai kukan yaron dake k’aruwa.
Zuciyar Haidar yaci gaba da masa zafi. Ya sani intentionally ta kyale yaron yana kuka dan yaji zafi.
A zuciye yace “Khairy wai ina karatunki ya tafi ne.? Ta ya kike pun
ishing k’aramin yaro for his Dad’s mistake.?!”
Bata amsa shi ba har lokacin sai hawaye dake gangaro mata.
Haidar ya jinjina Kai yana Jin zuciyarsa na masa zafi sosai “Fine Ummulkhair.!” For the first time da taji ya ambaci sunanta kai tsaye ba kaman yand
a Ya saba fad’a ba. Haidar yaci gaba “Do as you wish.! Mommy tana nan cikin garin Kano bata dawo Abuja ba.. Zata zo ta d’aukar min D’ana zai iya rayuwa da baby formula.. Bazan bari tarihin abinda ya faru Dani ya maimaita Kansa Akan D’ana ba..!” D’if ya kas
he wayar ba tarda ya kuma cewa komai ba. Aiko yana kashe wayar kaman ance nan ta b’ige da kuka sosai jaririn nayi itama tanayi a haka Umma ta shigo ta taddasu.
**
Washe gari kaw su Mommy da Aunty Asshe suka zo duk a tunanin Ummul sunzo su tafi da Baba Al
i ne kaman yanda Haidar yace. dan tayi zaton Haidar ya sanar da Mommy kaman yanda yace amma sai bataga hakan daga Mommy ba. Kayyaki ma taga ta kawo musu ita da jaririn da wasu abin buk’ata. Nan take sanar dasu washe gari zata bi jirgin safe ta tafi Abuja k
afin ran suna. Umma sukaita mata godiya da san Barka.
Mommy ta dubi Ummul dake zaune daga mazauninta kanta a k’asa. Ta murmusa tace “Toh Daughter ni zan wuce gobe in sha Allah. Na samu urgent call daga Daddynku. Duk dai bazai wuce magana akan yaransa ba
ga kuma case din Anisa da ba’a warware ba har yanzu. Naso na tsaya ayi suna kafin na koma.. But still idan na samu dama zanzo ayi suna Dani idan kuma ban samu Aunty Asshe zata wakilceni in sha Allah.”
Ta jinjina Kai a hankali ba tareda ta iya cewa komai b
a.
Mommy ta kuma murmusawa tana duban jaririn dake baccinsa peacefully tace “Gameda batunku keda Haidar.. You have the final say here.. Kin cancanci hakan. Dan a baya an Miki dole. Idan aka sake Miki dole wann karon ba’a Miki adalci ba… He’s my son.. Ina
son shi fiyeda komai a rayuwar nan.. Amma hakan ba yana nufin zan sake fifita shi sama da komai kaman yanda nayi a baya ba.” Mommy ta dan numfasa kafin taci gaba “ I couldn't manage to change him for years.. Amma cikin buwayan Ubangiji you came and change
d him.. Ina nufin kece sanadi.” Mommy taci gaba da jinjina Kai tana duban Ummul “Ki sani, You are the most precious truth in his life.. But still zab’i naki ne Ummulkhair.. Bazan sake tilasta Miki kasancewa da D’ana ba kaman yanda nayi a baya.. Sabida ke
d’in ma ‘ya ce a wajena.” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta. Ta k’arasa ta sumbaci Baba Ali dake bacci kafin ta kuma yima Ummul Sallama. Har Mommy takai k’ofa Ummul ta mik’e cikin sauri tana duban Mommy. Ta ambaci Mommy a hankali.
Mommy ta ju
yo tana dubanta. Sai Ummul ta isa da sauri bata san sanda ta fad’a jikin Mommy tana hawaye.
Mommy ta rungumeta sosai tana bata baki tareda mata fatan alkhairi. A haka dai suka sake wani sallaman.
Ummul ta kuma yarda kaunar dake tskaninta da Mommy daga A
llah ne ba wai dan ta kasance mahaifiyar Haidar ba. Dan ita dai tin farkon haduwarsu tin kafin ta saka Haidar a idonta Allah ya jefa mata k’aunar matar.. Matar da tai defending dinta a gidan da babu kowa nata cikinsa gidan da mijin da taje domin sa ya guje
ta. Koda ace Mommy da manufa ta nuna mata so a fari itakam bataji son da take ma Mommy ya ragu ba ko kadan.
**
Abuja…
Isowan Mommy gidan ta hangi sashen Haidar a bud’e ana fiddo da wasu kayayyaki. Mamaki ya cika Mommy. Ta dubi d’aya daga cikin ma’aika
tan ta tambayesa lafiya meke faruwa meyasa suke fiddo da wasu kayayyakin.
Kafin ma’aikacin ya bata amsa ta hangi Hisham ya fito daga sashen sai stretching hannayensa yake yana Ware su alamun duniya tana masa dad’i.
Mommy ta zuba masa ido tana duban ikon
Allah. Daidai nan Hisham ya k’araso yana mata sannu da zuwa. Bata iya amsa shi ba sabida mamaki da ya daure mata Kai. Can ta hangi Daddy na k’arasowa da murmushi saman fuskarsa. Ganin Daddy sai Hisham ya koma ga ma’aikatan yana ci gaba da nuna masu abubuw
an da yake so da Wanda baya so a sashen.
Daddy na mata sannu da sauk’a bata iya amsa shi ba sai nuni da tai da sashen Haidar cikin tsananin shock “Engr. Meke faruwa..? Ya naga ana fidda wasu kayayyakin Haidar daga sashensa.?”
Sai Daddy ya murmusa “Banda
abinki Kwaise Haidar kam ai yanzu bak’o ne a gidan nan.. Ko kin mance tin bayan bikin tariyarsa saidai yazo mana bak’unta..”
“But still.. Sashen sa ne.. Akwai sections da yawa a gidan nan.. Meyasa na Haidar..?” Cewar Mommy har lokacin a shock take.
Murmu
shi Daddy ya kumayi “Haba Kwaise is just a section.. Ba wani abu bane dan D’anuwansa ya zab’i ya zauna a nan. Hisham da Kansa ya zab’i wann section d’in.. Ni kuma ganin yanzu Haidar ba mazaunin gidan nan bane yasa nace zai iya amfani da wann b’angaren. Aft
er all, nan ne ya kamace shi ba b’angaren bak’i ba.”
“Amma Engr.. Haidar ya sani.? Kasan yanda yake. Kasan yanda baya so ayi invading space d’insa ba tareda saninsa ba..”
Muryar Haidar ta sinkayo daga bayanta yana fadin “Is ok Mommy..” Yai maganar kyak
kyawar murmushi samar fuskarsa.
Ta waigo tana dubansa murmushin ne saman fuskarsa. Yana k’arasowa ya bud’e mata hannaye alamun hug. Sai ta fad’a’da murmushinta suka rungume juna yana fad’in “welcome Mommy.. Ya hanya.. Ya kika baro Little Haidar.?”
Daga
Mommy har Daddy murmushi sukai Mommy tana fad’in ba ko kunya D’ansa kawai yake tambaya. Su duka ukun raha ne saman fuskokin su yayinda Mommy ta Ciro wayarta tana nuna musu hoton littile Haidar yanda Ya k’ara wayau. Daddy na fad’in dashi yake Kama ga hancin
sa da sumarsa ya d’auka. Mommy na cewa hasken fatanta da manyan idanunta ya d’auka. Haidar ya saka iyayen nasa gaba yanda ko wanne yake fad’in jikan nasu dashi yake kama. Sai murmushi kurum Haidar yake. Hisham na tsaye daga gefe rik’eda hoton Haidar da Umm
ul Wanda aka musu ran bikin tariyar su ya fito dashi daga sashen Haidar d’in. zuciyarsa sai faman tafarfasa yake.
Basu Ankara ba sai karan fashewan abu sukaji. Hisham ya saki hoton ya fad’i k’asa ya fashe.
Suka juyo gaba d’aya suna duban Hisham Wanda t
uni ya d’uka yana k’ok’arin tattare hoton yake fad’in Haidar yai hakuri bai sani bane. A garin k’ok’arinsa na tattare hoton glass ya yanka masa hannu. Daddy ya k’arasa da sauri ya rik’o hannun Hisham d’in yana duba yankan da yai. Hisham yana fad’in Daddy
ya bari ba komai it’s nothing serious. Tuni Daddy ya rikosa ya nufi cikin gidan dashi yana fad’in “You are bleeding Son.. Are sure ba sai anje asibiti ba. Come We need to clean your wound.” Ya k’arashe suna nufan cikin gidan.
Mommy da Haidar suka bi baya
nsu da kallo kafin Mommy ta kamo fuskar Haidar “Son..”
Saurin girgiza mata Kai yai ya kamo hannayenta murmushi saman fuskarsa “I’m fine Mommy.. Don’t stress yourself..” Ya rik’o hannunta yana fadin “You just arrived.. Ki shiga ki huta..”
Saida ya tabbata
ya mata rakiya har cikin gidan kafin ya dawo yana duban hotonsu shida Khairy Wanda Hisham ya fasa. Duk’awa yai ya d’auki fasasshen hoton yana kallo. Daga bayansa ya sinkayo muryar Hisham “I’m sorry Haidar.. It wasn’t my intention to break your photo..” Sa
i yai aya har lokacin Haidar bai tankasa ba.
Hisham ya zira hannayensa cikin aljihun jeans d’insa “Koda yake dan na breaking hotonku bazai zama matsala ba.. After all, kayi breaking auren naku da kanka.”
Haidar ya had’iyi abinda ya tok’are masa mak’oshi
. Ya mik’e tsaye ba tareda ya dubi Hisham ba. Yayinda Hisham yaci gaba da sakin muguwar murmushinsa silently dan ya tabbata ya tarwatsa Zuciyar Haidar da kalamansa kaman yanda ya tarwatsa hoton aurensu. Ga mamakin sa murmushi yaga Haidar ya sakar masa. Ya
tako zuwa gaban Hisham d’in k’adan. Saida dak’ik’a ya gauta Haidar na duban Hisham na sakin murmushi kafin yace “You can do your worse Hisham. Amma bazaka tab’a iya raba tsakanina da Khairy ba.. Kasan dalili..?” Sai ya nuna masa fuskar wayarsa dan D’ansa n
e Akan fuskar wayar.
“Wann kawai ya isheka amsa. Kuma ka yarda dani.. Zan kawo k’arshen karyarka da fuska biyunka.. Sai nayi unmasking dinka.!” Yai maganar yana jinjina Kansa alamun tabbatar da kalamansa kafin yasa kai ya shige.
Hisham ya bisa da kallo
yana shafa hab’arsa muguwar murmushinsa saman fuskarsa.
Washe gari da safe Haidar da ya fito cikin shirin fita Office kaman yanda Daddy ya buk’aci yaran nasa da su shirya da wuri sabida gabatarwa na musamman da zai musu a company nan ya iske iyayensa sama
n dining table. Ya k’araso ya gaishesu Mommy tace ya zauna suyi breakfast.. Ba musu Haidar ya zauna.. Zai soma serving Kansa Daddy yace ya jira D’anuwansa ya shigo. It would be rude a fara breakfast ba tareda an jirasa ba musamman da yake bak’o ne shi a gi
dan.
Da mamaki Haidar ya dubi Daddy sai ya aje serving spoon din cikin sanyin jiki. Mommy ta dubi D’anta cikeda tausayawa tasan an fara kaisa mak’ura da al’amarin sabon D’an mahaifinsa. Hannunta ta d’aura saman nasa cikin k’ok’arin calming d’insa. Sai ya
murmusa yana girgiza mata Kai alamun ba komai she shouldn’t worry.
Time Haidar ya duba saman agogonsa dake daure hannunsa na hagu. Ya dan furzar da huci kad’an.. Yana tapping yatsunsa a hankali saman table d’in.. Ba jimawa gogan ya shigo cikin shirinsa
tsaf irin shirin da bai tab’a irinsa a baya ba idan zai tafi office. Da ka gansa kaga D’an manya. Ga wata expensive suit da ya saka da wata tsadaddiyar cover shoe bak’a sai shining take. Ga k’amshin turaren TomFord dake tashi jikinsa. Irin dai turaren Haid
ar yau shi ya saka. Haidar ya kauda fuska gefe yana sakin murmushin takaici. Ba shakka wann banzan competing yake dashi a halin yanzu.
Daddy ya mik’e