Showing 45001 words to 48000 words out of 267381 words

Chapter 16 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

16

da Yaya daga yanzu dan kin Riga kin amshe girman. Ummul d’inki ta k’wace Miki girman..” Ta aje mata hanshak’in handbag shak’e da kud’i ‘yan dubu dubu ciki tace “Wann naki ne ki razani Tani dasu.”

Dan tinda Asshe ta gane Suwaiba ba kwad’ayayya bace burinta kawai shine ta burge kishiyarta harma da sauran jama’an dake tsangwamar ‘yarta su shiga taitaynsu sann Ummul d’inta Tai irin auren da yaran Tani basuyi ba ta k’udiri niyyan cika ma Umma wann bu

ri nata. Dan sosai matar ke sakata nishad’i.

Asshe ta fice tana fad’in bara ta duba Hilala ko ya shirya dan shine zai kaisu.

Umma ta jinjina Kai tana kuma murmusawa. A fili take furtawa bayan Asshe ta fice “Tani kenan.. Dake da ‘ya’yanki Kun gama mana w

ulak’anci.. Yau idanunki zasu gane Miki abin mamaki.. Yau zakiyi nadaman duk wasu abubuwan da kika jima kina min cikin gidan nan.. Ummulkhairy da kike aibatawa Har kina ambatonta da Ummulsharri toh yau sharrinki zai koma kanki Tani.. Ki jira bayyanata.!”

SameenaAleeyou

📚

*AUREN WATA UKU..!*

*16*





Sameena Aleeyou…✍

🏽

*

Safiyar Washe gari gidan Hajja Fannah suka fara nufa ko an samu wani bayani gameda Umma. Saidai har kawo wann ranar babu Umma babu labarinta babu wani bayani tak’amaime da ita

. Ummul sai juya wayar Umman take cikin hannunta nokia k’irar 3310 duk taji jiki ta kod’e. Hawaye suka kuma gangaro mata. Gashi sun tadda Hajja Fannah ma bataji dad’i ba kwance take lik’is dan tin bayan tafiyar Hisham jikinta ba dad’i k’ok’ari kawai take.

Ummul ta dubeta tace “Hajja ko dai asibiti zamuje.?”

Hajja Fannah ta murmusa cikeda jin dad’in yanda Ummul ta damu da damuwarta “A’a Ummul, ba sai naje asibiti ba.. Zuwa anjima zazzab’in zai sauk’a in sha Allah.”

Ummul ta jinina kai suna masu mata fata d

a addu’an samun lafiya itada Khulsum.

Khulsum ce ta soma mik’ewa yayinda Ummul ma ta mik’e suna mata Sallama da fad’in zasu biya Asibiti wajen Abba su dubasa daga can zasu k’ara komawa police station ko an samu wani batu gameda mahaifiyarsu.

Ummul ta d

’an dubeta “Hajja zamu iya barinki ke kad’ai naga kaman yau jikin naki da d’an nauyi.”

Hajja Fannah ta murmusa tana mai mik’ewa zaune sosai dan hankalin Ummul d’in Ya kwanta “Kinji Ummul nifa zazzab’i ne ke damuna nasan kuma bazai shige typhoid d’in nan d

a ya sakani gana kwana biyu ba. Banison zuwa asibiti ne su tara min magani dan bana shiri da had’iye k’waya Shiyasa ko Hisham ban sanar dashi ba dan nasan yanda kika dage naje asibiti haka shid’inma zai dage. Toh kafin ku min taron dangi gashi can na dafa

ruwan zogale ma inata sha dan nafi gane wann.” Ta k’arashe cikin k’ok’arin nuna jarumta irinta maras lafiya.

Ummul ta murmusa kad’an. Sosai take jin Matar har cikin ranta. Sun mik’e suna kuma mata Sallama ta k’araso hannunta rik’eda ‘yan kud’ad’e ta mik’a

masu “Ungo nan kuyi kud’in abun hawa.”

Dukansu biyu girgiza kai suke suna fad’in a’a ta barshi.

Ta d’an b’ata fuska tana fad’in “Au baku d’aukeni uwa ba kenan idan har zan baku abu kuk’i karb’a.” Ta dubi Khulsum “Ungo nan karb’a maku ita Ummul ai tasan

karonmu. Idan bata amshi kyauta na matsayin malamar ta ba ai ta amsa matsayin ‘Yata.” Can k’asar zuciyarta kuwa Matar D’anta ta kirata.

A dole dole suka amsa dukda dama basuda ko sisin da zai kaisu asibiti wajen Abba balle Har su tafi police station magan

an case d’in Umma.

Suka kuma mata godiya had’ida fatan samun lafiya kafin suka fice.

Suna tafe cikin adaidaita Khulsum ta dubi Ummul “Adda mai zai hana mu fara zuwa police station d’in tinda kinga asibiti ko munje ba Lallai Mama da yaranta su bari mu

shiga wajen Abba ba.”

Ummul ta girgiza kanta “A’a Khulsum, koda zasu hanamu mu je d’in dai. Muji ya jikin nasa Ya kwana tinda idan muka tafi maganan neman Umma ba Lallai mu dawo da wuri ba har sai munji yanda al’amarin Ya kwana. Kinsan ofishin ‘yansanda

cases da yawa. Inaji a jikina da izinin Allah yai za’a samu Umma.” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irin na Wanda Ya gama karaya amma tawakkali Ya hana furta hakan.

Khulsum ta jinina kai tana amsawa da Allah Ya sa a samu Umma ya kuma bawa mahaifinsu

lafiya. Ummul ta amsa da Ameen daidai sansa mai adaidaita Ya diresu k’ofan asibiti.

Suna dosowa haraban ward d’in suka hango Mama da Badi’a. Ga Azeema a gefe harma da mijin Azeemar Habibu. Sai wallahi tallahi suke baka ma gane mai suke fad’i dukda wai k’

asa k’asa sukeyi basa d’aga murya kar ajisu a fatattake su.

Azeema fad’i take “Wai kuna so kuce mun tun yammacin jiya kud’ad’en suke hannun Tasi’u kuma wayansa a kashe.?”

Habibu yaci gaba da salati yana tafa hannu. Ya dubi Mama wacce ko iya cewa komai b

atayi. Huci kurum take. Fuskar Tasi’u ne kawai ke mata gizo cikin ido. Allah ya gani da zataga Tasi’u yanzu a gabanta zata iya shak’esa Har sai an k’wacesa.

Cikeda zak’ewa Habibu yaci gaba “Wann ai zancen banza kenan.. Ta Ya za’a ce kun kira shi Tasi’u k

un dank’a masa ragamar komai irin haka. Mai zai hana baku tuntub’i ita Azeema ta kirawo nata mijin matsayin shaida ba..Wann ma ai ba magana bace tinda kud’in nan ba kud’in Bad’ia bane ita kad’ai.. Ehe kud’i ne na magada.. Kuma shago da ba shagon sata ba ya

ma za’ace an sayar cikin rahusa haka. Nawa kowacce zata samu cikinku.?”

Badi’a dake aika masa mugun kallo tace “Toh wai kai Malam naka a wanne.. Ko harda kasonka ne cikin gadon.?”

Azeema ta katseta “Ai naga gadon na uban Tasi’u ne da kika gayyatosa Ya k

washe kud’ad’en Ya gudu. Toh wllhi na ranste da Allah bazata tab’a sakuwa ba wai bindiga a ruwa. Wllhi yanzu zan kirawo Yaya Salima tinda duk abinda ake itama bata sani ba. Na ranste da Allah sai an mana kashin hakkinmu ehe. Ko kuma wllhi na gayyato maku h

ukumar hisba nace Kun saida gadon mahaifinmu dake kwance gadon asibiti.!” Ta k’arashe sai huci take.

Habibu sai bud’e hannaye yake yana kuma ingiza Azeema. Fad’i yake Ahtoh magana kenan a fito masa da hakkin matarsa.

Azeema ta Ciro waya da zummar kiran

Salima kenan suka sinkayo kukan Mama. Ta kamo bakin mayafi tana matse idanunta “Ni Tasi’u zai tona ma asiri a garin nan.. Na rufa masa asiri yana d’an wiwi na d’auki ‘ya na basa a tunanina zaiyi hankali ashe ni ce ‘yar wiwi.”

“Mama ba fah kuka zakiyi ba

, nemo Tasi’u Ya kamata kuyi yanda ya shiga Ya fita dan wllhi muddin Tasi’u baizo ba daga nan ofishin hukuman hizba na nufa na zayyane masu komai. Kun raba gadon mahaifinmu da ransa.!” Azeema tace tana huci.

Habibu yai saurin shiga tsakiya kaman wani alk’

ali “A’a a’a baza’ayi gaggawan gayyato hukuma ba tinda abin duka na gida ne. Kamata yayi a binciko yanda Tasi’u yake duk rintsi. Yanzu zan tafi yanda shi Tasi’un ya cika zama na tuntub’i abokansa tinda dai baza’a samesa a gida ba. Na tabbata baiyi nisa ba.

” Ya k’arashe yana mai wucewa cikin sauri.

Ummul da Khulsum suka dubi juna cikin tsananin shock. Mama da Badi’a saida shagon Abba sukai kenan ko mai hakan yake nufi.? Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.

Suna a haka aka zo neman kud’in magungunan Abba wa

nda kusan kwana biyu kenan yana skipping wasu treatments d’in masu matuk’ar mahimmanci.

Mama sai ta hayyayako ta soma bala’i tana fad’in ta gaji da zaman asibiti ma jinyar da yak’i ci yak’i cinyewa.

Nurse yace “Yanzu babu kud’in da za’a masa jinyar.?”

A

zeema tace “Kurma ne kai baka ganin tashin hankalin da muke ciki ne.. Damfararmu fah akayi..”

K’arasowan su Ummul suna tambayan mai ake nema gameda jinyar mahaifinsu yaja hankulan su Badi’a. Ita kam Mama har yanzu fah bata wani gane mai ake ciki ba hankal

inta kacaukam naga Tasi’u da kud’ad’enta.

Badi’a tace “Kud’in jinya ake nema ko zaku biya ne tinda wancan karan ma ku kuka biya. Sai aje a sake saida jiki a kawo kud’i. Ko mazan ne babu.?”

Khulsum ta dubeta Har lokacin mamakinsu bai saketa ba “Da dai a

kiramu b’arayi marassa imani masu saida k’addaran mahaifinsu da ransa gwara ace jikinmu muka saida muka biya kud’ad’en jinyarsa. Kin fahimta B’arauniya matar b’arawo.!”

Badi’a ta nufota a zafafe tana fad’in “Ke ni sa’anki ne dan ubanki.. Sai na gurje bak

in ki yanzu a nan..!”

Saida aka shiga tsakanin Khulsum da Badi’a.

Nurse yace “Yanzu haka Dr zaizo babu abinda aka buk’ata.. Shin ba hanyar da za’a bi a samu a saya magungunan..?”

Kaman daga sama suka sinkayo wata murya “K’warai akwai hanyar da za’a say

a!”

Mama dake shirin barin wajen dan batada lokacin cecekucen rashin kudin jinyar Malam da malaman asibiti burinta kawai ta isa ta cimma Tas’u. Nan tai birki jin wann murya dai tai ma me muryar farar sani. A hankali take k’ok’arin juyowa har dai ta karkat

o gaba d’aya.

Mama ta daskare. Ta shiga mutsuka idanunta tana duban wacce take gani gaba gareta “Suwaiba.!” Ta furta cikin tsananin mamaki.

Suwaiba ce fah.. Suwaiba Amaryar Malam Isubu nata take gani sanye cikin tufafi na alfarma. A gidan Uban wa Suwai

ba tayi arziki dare d’aya. Karfa hausar nan da ake cewa dare d’aya Allah kan yi bature ta tabbata kan Suwaiba.

Ta kuma mutsuke idanunta dan har lokacin gani take kaman gizo ne ba gaskiya ba. Wai Suwaiba shashashar matar Malam Isubu ce haka kaman wata matar

shugaban k’asa ko gwamna.

Khulsum da Ummul ma da mugun mamaki suke duban mahaifiyar tasu wacce kaman an canzata. Suka dubi juna suka kuma duban Umma shaye da tsananin mamaki, cikin tsananin shock suka furta “Umma.!”

Umma taci gaba da takowa gaba garesu.

Azeema da Badi’a ma da mugun mamaki suke duban Umman.

Kai tsaye nurse d’in Umma ta nufa tace “Nawa ake nema..?”

Nurse d’in Ya d’ago takardan na list d’in abubuwan da ake buk’ata Ya soma karantowa.

Kafin Ya gama karantowa Umma ta d’aga masa hannu alamun

dakatarwa lokaci guda ta bud’e tsadadden handbag d’in dake rik’e hannunta ta Ciro sabbin kud’ad’e ‘yan dubu dubu sai walk’iya suke. Mama ta zaro ido waje ganin dubabe bugun habuja suna walk’iya suna kashe mata ido. Wai Suwaiba ke fiddosu.

Ko k’irgawa ba

tai ba ta mik’a ma nurse d’in “Ungo nan.. A saya duk abinda ake buk’ata, idan yayi canji ka rik’e canjin idan kuma akwai abinda bai isa ba ka sanar Dani.. Ko menene..” Ta k’arashe tana gyara zaman tsadaddan mayafin dake bisa kanta.

Nurse ya murmusa “A’a H

ajiya saidai na Miki jagora ki biya da kanki.”

Umma ta jinjina kai yayinda Umma ta take masa baya.

Tin daga k’afafu Mama ke dubanta Har zuwa tsadadden leshi da yan kunne da sark’a dake kwance wuyanta. Wann ko taron manyan matan gwamnoni Suwaiba taje a h

aka ai ta cinye taro.

Akan idonsu Umma ke gudanar da komai da taimakon nurse d’in kafin daga bisani ta amso receipts ta dawo yanda ta baro ahalin mijin nata Wanda kowa shock Ya hanasa aiwatar da komai. Baga Mama da yaranta ba baga Yaran Umma ba wanda zasu

iya cewa Har yanzu basu tabbatar idan mahaifiyarsu bace.

Ko takan Mama batabi ba ta dubi su Ummul wacce suma kansu ta koma masu tamkar bak’uwa. Kallon rashin sani ne ko na mamaki suke bin mahaifiyar tasu dashi. Tsakiyan yaranta ta shiga wato Ummulkhairi

da Ummukhulsum ta kamo hannayensu tace “Mujenku kuga mahaifinku..”

Tamkar rak’umai da akala haka Umma ke janyo su Ummul da Khulsum. A haka suka zo suka shige gaban Mama da yaranta wanda suka koma kaman an dasa su.

Har suka shige cikin ward d’in Mama da

yaranta basu daina binsu da kallo ba.

Suna shigewa Mama ta dubi Azeema tace “Ke wanke ni da mari dan ubanki.”

Azeema ta dubeta a yatsine “Ban gane na wanke ki da mari ba Mama..”

“Nace ki mareni na tabbata ba mafarki nake ba.. Ba Suwaiba bace Ke min gi

zo ba. Inji ba itace yanzu ta shige gaba na ba ko.? Ku amsa min mana.. Na shiga uku ni Tani..”

Bata kai aya ba taji zafi Ya tsunkuri ‘yar yatsarta na k’afa. Badi’a ce ta take mata ‘yar yatsar cikin k’ok’arin dawo da Mama hayyacinta.

Mama ta saki k’ara

tana d’ingile k’afarta “Wayyo kunama ta cijen.!”

Badi’a tace “Ba kunama bane ta cijeki, take maki k’afar nai ki tabbata ba mafarki kike ba..”

Azeema tace “Mama wllhi Umman su Ummul ce. Amma nima nafi zaton canzata akai.. Mama ina ta samo kud’ad’e irin ha

ka dare d’aya.. Kinga Har fari da shek’i ta k’ara dare d’aya. Mama kin kaw ga suturan dake jikinta. Wllhi iriinsa matar Gwamna ta saka ranan da za’a rantsar da mijinta.. Mama Ina matar nan ta samo kud’i haka wai.?”

“Yo Ina zan sani ina tareda ke a nan..”

Mama tace tana kuma lek’en bayan Umma a tsarace.

Badi’a ta tab’e baki tace “Kar canzawarta ya zautar daku. Abu ne a bayyane matar nan dama barikinta kawai take son yi auren mahaifinmu ya taka mata burki.. Yanzu da take ganin zai Mutu shine ta baje kolint

a da kyau zatai barikinta mai dalili..”

Azeema tace “Kai wllhi amma fah ta mun kyau, kinga shegen mayafin da ta watsa. Irin mai walwalin nan fah da ake talla online.. Inama ta bani aro naje dashi Bikin k’anwar Habibi na yak’i shegun danginsa.”

Bata kai

aya ba Mama ta hamb’are bakinta “Kud’in shan jini da tsafin zakije a baki.. Toh Idan shaye shaye kike kije Azeema.. Kije Suwaiba ta shanyeki.. Ni nayi imani itace ta asirce Ummul mazan dake nemanta ke gudu sabida Allah Ya rufa masu asiri da sauran kwanaki

nsu. Shi Fa’izu dake kwanansa Ya k’are gashi ta lashe kurwansa. Yanzu kuma abun yazo kan Malam Shiyasa data mik’a sa gashi a kwance kafi gawa.. Kuma yanzu ba sai anjima ba zan fiddata daga cikin asibitin nan..”

Fiuuu Mama ta shige ta nufi ward d’in yarant

a na biye da ita.

Bata damu da majinyata dake kwance wajen ba Mama ta shiga kururwa tana fad’in Suwaiba mayyace yar K’ungiya asiri ne na shan jini.. Ta tsafe ‘yarta Ummul tana amfani da ita tana cinye mutane kaman yanda Fa’izu d’an ‘yar uwan Malam Isubu y

a mutu. Bai isheta ba yanzu ta mik’a mijinsu zata cinye.. Sai dukan k’irji take tana fad’in wllhi bazaayi ma mijinta amfani da dukiyar ‘yar shan jini irin Suwaiba ba.

Sauri sauri wasu nurses da cleaners suka tafi kiran securities. Hango securities d’in d

a Mama tai ya sanyata had’iye kalamanta.

Securities suka k’araso suna muzurai suna fad’in waye zasu fidda.

Take Mama ta shiga masu nuni da Umma tana fad’in “Ga Suwaiba ita zaku kama ita zaku fidda.. Yar shan jini ce..”

Ai sai Mama taga securities sun

isa gaban Umma suna duk’awa suna kwasan gaisuwa lokaci guda suna tambayar ko da abinda kike so a miki Hajiya.

Mama sai ta saki baki tana duban ikon Allah. Suwaiba.? Suwaibar ne Hajiya..?

Umma ta murmusa tana gyara zaman mayafinta “A’a babu komai Kar ku

damu. Haukar wancan Matar ne Ya motsa inaga b’allewa tayi daga b’angaren masu jinyar hauka.”

Mama jin an ambaceta da Mahaukaciya ya sanyata kuma hayyak’owa. Jikinta Har rawa yake.

Sauran mutanen dake wajen Wanda dama fitinan Maman a ishesu sukace da ga

ske ne batada saiti kullum fama ake da ita.

Aiko nan take securities suka fidda Mama da k’arfin gaske sai ihu take tana tsine ma Umma. Yaranta suka bi bayanta a guje suna ambato sunanta.

Umma ta zuba masu idanu har aka fice dasu kafin ta sauk’e ajiyan z

uciya ta juyo tana duban yaranta Khulsum da Ummul Wanda Har lokacin kallon mamaki ko muce kallon tsoro suke binta dashi musamman bayan da Mama ta gama fad’e fad’enta.

Umma ta kuma dubansu sai ta k’arasa ta rungumesu. Basu iya maida mata martanin rungumar

ba.

“Ummul, Khulsum.. Ni ce fah mahaifiyarku Ummanku.. Meyasa kuke dubana kaman bak’uwar fuska. Shin ko baku shaida mahaifiyarku bace.?”

Girgiza mata kai Ummul tai “Mun shaida kamanninki Umma amma yanayi ki yafi kama da bak’uwar Fuska.. Umma mai ya canza

ki cikin kwanaki k’alilan..?”

Murmushi Umma ta saki kafin ta dafa Ummul “K’addararki itace ta canza ni cikin kwanaki k’alilan Ummul.. K’addaranki Wanda a baya naita Allah wadai dashi shine ya zamto mabud’in Alherinmu..”

Girgiza kai Ummul tai cikin tsana

nin sanyin jiki “Umma ban fahimceki ba..”

Umma ta kuma murmusawa “Kar ki damu ‘Yata da sannu zaki fahimci komai.. Kuzo muje..” Ta shiga janyo hannuwansu suka nufo waje yanda suka hangi Mama har lokacin huci take bayan an tilasta mata yin shiru.

Mama ta z

abura zata nufo Umma amma sai taga wata jibgegiyar jeep taja tayi parking gaban Umma. Mama taja wani wawan birki tana dafe k’irji.

Mamaki da sanyin jiki Ya kuma sauk’ar masu Ummul.

Umma ta dubesu “Toh yarana ni zan tafi, in sha Allah zan kuma dawowa na

n bada jimawa ba.”

Da tsananin mamaki suke duban mahaifiyarsu. Tasa kai kenan zata shige mota Ummul tai saurin kamo hannunta. Hawaye na gangaro mata take girgiza kai “Umma.. Ina zakije ki bar Abba cikin halinda yake ciki..? Umma ina kikaje kika barmu mu n

ata nemanki.. Shin Kinsan abubuwan dake faruwa a nan.. Umma wai meke faruwa.. Umma meke faruwa ne..?”

Dafata Umma tai “Da sannu zaki fahimci abinda ke faruwa Ummul.. Zan rok’i alfarmarku. Kar ku bar kusan mahaifinku.. Ku zauna ku kula dashi.. In sha Allah

daga yanzu duk wani abinda za’a kashe sabida jinyar mahaifinku bazai zama matsala ba. Na barku lafiya yarana..”

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login