Showing 168001 words to 171000 words out of 267381 words
gidan ke kuma ya kamata ki zamto event planner. Baki tunanin abin zai k’ayatar.?” Ya k’arashe yana kashe mata ido guda.
Shiru tai kaman mai nazari sai kuma ta shiga jinjina kai “Yes. K’warai ka kawo shawari. Idan Har zaka kasance ma
i gyara gidan da zasu zauna ni yafi cancanta na zamto wacce zata shirya shagulgulan bikin tariyar. Kaga a sauk’ak’e zamu rufta komai mu lalata komai.. Duk shirin Mommy na ganin Ummul da Haidar sun tabbata ma’aurata zamu lalata shi. Ko wannenmu ya kasance d
a abun k’aunarsa haka ne.?”
Hisham Ya kuma murmusawa “Perfect.! Ni yanzu aiki na ya shigo hannu saura kiyi naki k’ok’arin ta dank’a Miki ragamar jagorancin shagalin bikin tariyar.”
Anisa ta murmusa kafin tace “Bikin da Aunty Kwaise Maitama bazata tab’a m
ancewa dashi ba. Bukin da zamu gayyat manyan bak’i ciki harda Dareen.. Tsohuwar sirkar ta da basu tab’a had’uwa ba.!”
Suka kece da dariya suna ci gaba da ayanna manufofinsu.
**
Hospital..
Haidar ya dubeta dan ya kula yanayinta a kwanakin ya d’an sauya
gashi in less than 2weeks za’a musu sallama.
Ta k’araso ta bashi magungunansa fuskarta Babu wani walwala. Zata mik’e Ya kamo hannunta.
Ta juyo ta dubesa still babu wani walwala tattareda ita.
Ganin Ya tsareta da ido ya sata sauk’ar da idonta kad’an.
“Khairy…!” Ya ambato sunanta a hankali.
Still bata d’ago ta kallesa ba saima hawaye da taji na yunk’urin zuwa mata. Zuciyarta cike yake da tarin abubuwa. Ga maganganun Anisa Wanda ta sanar da ita kwanakin can ga kewar ahalinta da ta baro gida da ya adda
beta. Tana nan tana lissafin watannin da Umma ta d’ibar mata ta waiwayi gida wato watanni uku bayan aurenta. Dukda cewa bai shige sauran sati biyu watannin su cika ba ji take kaman bazasu cika ba. Majinyacin Mahaifinta da bata san wani hali yake ciki ba. ‘
Yanuwanta musamman ‘yaruwarta Ummukhulsum da ko bacci bai rabasu a baya sann da ita kanta Umman koda itace ta bata wann sharad’in. Tayi kewarsu gaba d’aya sann ta k’agu ta gansu taji daga garesu.
“Look up Khairy.. Kalleni..” Yai maganar softly.
Sai ta
d’ago ta dubeshi.
Hawaye Ya hango kwance cikin idonta.
“Are you crying.?” Ya tambaya yana k’ok’arin kai hannunsa had’ida d’ago hab’arta kad’an.
Baisan Ya akai ba saiji yai hannun nasa a kasan idonta . Gently ya shiga share mata hawayen dake mak’ale c
ikin idonta Wanda tuni sun ziraro k’asa. Ai kaw kaman wacce ke jiran dalili sai ta soma kuka maras sauti.
Haidar yai mata k’uri yana kallonta.
A hankali Ya furta “Come here.” Ya janyota zuwa b’angaren jikinsa. Kaman wacce ke jira nan ta soma kuka sosai k
anta cikin k’irjinsa.
SameenaAleeyou
📚
*AUREN WATA UKU..!*
*44*
*©
️
Sameena Aleeyou…✍
🏽
*
Sun d’auki lokaci sosai a haka Har saida kukan nata Ya tsagaita yayinda Haidar yaci gaba da Shafa kanta zuwa bayanta a hankali cikin k’ok’arinsa na calm
ing dinta.
D’akin yai shiru tana nan kamo cikin k’irjinsa sai zukatansu dake bugawa kusan a tare.
Bata San dalili amma sosai ta samu natsuwa da kwanciyar hankali tattareda shi. Cikin rawar murya irinta mai kuka take furta “Nayi kewarsu..! Nayi kewarsu s
osai..?”
Ya kuma shigar da ita k’irjinsa. Ba ra’ayinsa bane bin diddigin matsalolin mutane. Baisan dalili ba amma sai yaji yana son jin nata matsalan “Su waye kikayi kewarsu.?”
A hankali take furta “Abba.. Umma.. Khulsum.. Da sauran ‘yanuwana..!” Ta k’ar
ashe wani kukan na zuwa mata.
Haidar yaci gaba da Shafa bayanta yana kokarin kwantar mata da hankali. D’akin yai shiru har kaman bazai ce komai ba sai kuma yace “Then… give them a call..”
Shiru bata ce komai ba.. Shima saida yai maganar ya tuna duk zama
nsu shidai bai tab’a ganinta da waya ba sann bai tab’a ganin ta kira kowa ba. Ya d’an kamo arms dinta Ya d’ago ta kad’an “Where is your cell phone… Do you have one..?”
Shiru kaman bazata ce komai ba sai kuma ta girgiza kai a hankali.
Mamaki Ya cika Hai
dar. ‘Ta Ya za’a ce mutum baida wayar salula. Is this even possible.?’ Ya dan girgiza kai kad’an, Kasancewar shi kansa mutum ne da bai cika son magana da bin diddigin al’amari ba yasa shi jinjina Kai a hankali. Sai Ya mik’a hannun Ya d’auki nasa wayar. Sai
gani Ummul tai yana mik’a mata nasa wayar.
“Here..! You…. can use mine.. If that’s.. ok with you..” Ya k’arashe yana dubanta sosai.
Ta dubesa sai ta dubi wayar. Jikinta ya kuma yin sanyi sakamakon tunowa da kalaman Umma ‘Kar ki neme mu koda a waya ne ha
r sai kin cika watanni uku a gidan aurenki . Sai ta girgiza kai a hankali. Cikin rawar murya tace “Ban rik’e lambobinsu akai na ba..”
Wann karon ma da mamaki yake dubanta sosai. Dukda shima bai tab’a damuwa ya kiyaye lambobin ahalinsa ba tin yaranta yasan
hakan nada alak’a da rashin jituwa da k’alubale da ya fuskanta da iyayensa tin yarinta. Amma ita tanada alak’a mai kyau da iyayenta ga dukkan alamu, musamman mahaifinta dan bai mance ta sanar dashi sabida shi ta amince da aurensa. Amma sai bai ce komai ba
ya jinjina Kai a hankali.
Kallonta ya kuma yi dan shidai baisan wani aba lallashi ba a rayuwarsa sann bai iya ta ba. Sai ya
kamo hannunta cikin nasa ya kuma kwantar da ita gefen kafad’arsa, yatsun hannunta cikin nasa. Calmly yake fad’in “You know, I’m n
ot used to seeing you like this.. Murmushi yafi Miki kyau.” Ya k’arashe kaman ba daga bakinsa maganar ya fito ba.
Sai taji Murmushin ya kufce mata out of nowhere. tai saurin kare fuskarta da tafukan hannayenta.
Hannu yasa ya d’ago fuskanta kad’an suna
duban juna. Ya tsareta sosai da ido kafin yace “Do you feel better now..?” Ya tambaya fuskarta tallafe cikin tafukan hannayensa.
D’an lumshe idanunta tai kafin ta jinjina masa kai a hankali.
Shima ya jinjina nasa kan. Su duka biyun murmushi ne saman fusk
okinsu.
**
Anisa ta shigo a guje tana nuna ma Mommy Pages na different professional event planners. Ta murmusa tace “Yauwa Mommy ya kikaga wann. The event should be grand and super elegant. Ya kamata ayi komai to perfection. I’ll be the coordinator.. And
trust me, it will definitely be a sight to behold.!” Ta k’arashe tana juyi gaban Mommy had’ida juya ido. Cikin zuciyarta kuwa cewa take ‘Dan na miki alkawari Mommy, akwai abubuwa da dama da zasu faru a wann rana Wanda idaniya bazasu tab’a mancewa ba.’
M
ommy ta tab’e baki tana dubanta sama da k’asa “Toh ce Miki akayi shiririta zaayi wajen ne.? Bani son shashashan cin nan naki.”
Anisa ta turo baki kad’an “Haba Mommy.. I’m just being concerned here… Kuma kinsan abu idan aka ce biki toh a nan wayota da basi
rata Ya k’are.. Mommy kinsan bazaki iya dealing da wani headache na event a yanzu ba. Kuma Haidar cousin dina ne Ummul kuma I consider her friend. Ni ce yafi cancanta na shirya shagalinsu Mommy. Just assign me to do the work please.. Please Mommy. And kuma
kinsan abu na zamani sai d’an zamani.. Gwara a shirya komai daidai da zamani da yayi.” Ta k’arashe tana juya ido da rangwad’a Wanda d’abi’ar ta ce.
Mommy ta kuma girgiza kai yayinda Anisa taci gaba da mata magiya tana fad’in ta dank’a mata ragamar shiry
a shagalin.
Murmushi Mommy tayi had’ida girgiza kai kad’an “Fine, naji Anisa.. Amma kinsan bani so a samu wani mishkila.”
Anisa harda ‘yar tsallenta tana fad’in baza’a samu mishkila ba, kama daga shirya wajen taro, live entertainments har zuwa guests li
st.
Mommy ta murmusa tana duban Anisa tana jin dadin yanda kowa ke marmarin biki. Batai k’asa a gwiwa ba taci gaba da kiran k’awayenta da matan abokan kasuwancin Daddy tana sanar dasu. Sann hakan wani dama ne da zai goge scandal din da yai erupting kwana
kin baya. Labarin da wani gidan jarida ya wallafa cewa Engr Aliyu Maitama yayi ma d’ansa auren sirri da ba’asan ko wacece Amaryar ba. A wann rana zata gabatar da Ummulkhair matsayin matar D’ansu Haidar ga duk abokan alk’allarsu dama sauran jama’a gaba d’ay
a.
Anisa kaman ta zuba ruwa a k’asa ta sha dan murna. Haka ta kirawo Hisham tana sanar dashi plan dinsu Ya tafi yanda suka tsara. Mommy dai ta dank’a mata ragamar jagorancin shagalin bikin. Sann Gidan Haidar da Hisham ke renovating nan ne venue kaman yan
da Mommy ta buk’ata . Hisham yai muguwar murmushi yace komai Ya tafi daidai.. A ranar wann shagalin zasu striking plan d’in su. Ranan da Kwaise Maitama take tunanin farin cikin ahalinsu zai soma wann ranar komai zai wargaje.
A haka ko wani b’angare suka
ci gaba da gudanar da shirye shirye yahinda b’angaren Haidar da Ummul sabo da shak’uwa ke dad’a shiga tsakaninsu.
A b’angaren su Tani ma suna nan suna nasu tanadin dan Hajiya Asshe ta sanar dasu ‘yaruwarta Hajiya Kwaise na shirya gagarumin bikin tariyar
Ummul da Haidar Wanda suma a nasu shirin wann ranar zasu k’addamar da shirinsu. Zasu fayyace ma Ummul komai gameda mahaifiyarta da wulak’antaccen auren da tai mata. Zasu jefa rayuwar Suwaiba cikin garari a wann ranar. Zasu d’auki duk wani fansarsu dake kan
Suwaiba.
A b’angaren Ummul dad’i da k’arin sakin jikinta da Haidar yanada alak’a da tsananin farin ciki da take ciki. Watanni uku Sun kusa cika zataga ahalin ta kaman yanda ta d’aukar ma mahaifiyarta alk’awari cewa bazata waiwayesu ba har sai ta cika wa
tanni uku da aure kaman yanda mahaifiyar tata ta buk’ata daga gareta.
Shi kuwa Haidar dukda shiryawa da yai da mahaifiyarsa saidai har kawo wann lokacin bai saka mahaifinsa a idonsa ba. Daddy bai kuma dawowa asibiti ya dubasa ba. Abun bai basa mamaki ba
tinda yasan shidai tsakaninsa da mahaifinsa Babu komai face tsangwama tsana da kuma kyara. Amma saidai a wann lokacin abun bai masa ciwo sosai kaman a lokutan baya sanin cewa da yai ko Babu komai a halin yanzu yana tareda soyayyar mahaifiyarsa da k’aunart
a. Uwa uba idan Ya kalli Ummul sai yaji duk wani k’unci dake zuciyarsa ke ciki ya yaye.. Bai sani ba ko tsananin sabon da sukayi a yanzu ne ke haifar masa da hakan Wanda a baya idan aka ce zai zauna da ita under same roof zai musa. Sai gashi a halin yanzu
Har bacci suke cikin mayafi guda. Ya lumshe idanunsa a hankali murmushi na kufce masa.
A reception wani staff na asibitin Ya bata wani shud’in folder mai d’aukeda logo na Maitama Builders daga fuskarsa. cewa wani abokin aikin Haidar d’in ne ya bari a bas
hi. Ita dai ta amsa folder d’in ta nufi d’aki dashi. Hisham Wanda shine ya kawo folder d’in yana lab’e yana kallon Ummul Har ta shige da folder d’in. Cikin zuciyarsa yake furta ‘Saura kad’an.. Saura kad’an na d’aukeki Ummul.. Saura kad’an mu kasance tare..
Saura kad’an ki kasance da masoyinki na gaskiya.’ Yana ida fad’in haka yaja Pcap d’in dake kansa ya kuma rufe face dinsa dashi kafin ya fice daga asibitin.
Haidar yai zaune yana duban folder d’in Wanda ke k’unshe da wasu bayanai da wani waje na rattaba
hannu gameda babban aikin da suke gab da farawa da zaran ya fito daga asibiti. Long awaited project dinsu. Project d’in da yai alwashin kai mahaifinsa k’asa warwas dashi. Project d’in da yai niyyan ruguza Maitama Builders dashi. Project d’in da Ya jima ya
na tanadin duk wani fansa nasa kan iyayensa musamman mahaifinsa Wanda Har kawo wann lokacin basu fuskanci juna ba.
Shiru yai yana juya folder d’in cikin hannunsa a hankali yake furta “You deserve this Daddy.. You deserve this.. I can’t backdown now.. Ka
cancanci haka Daddy.!”
Ummul ta dubesa da d’an mamaki ganin irin hucin da yake. Ga wani yanayi da Ya shiga tinda ta kawo masa wann folder d’in Wanda ta jima bata gansa cikin irin yanayin ba. Tai k’ok’arin zama gefensa a d’arare. Ta dubesa kaman mai tsoron
magana “Lafiya kake..? Kaman naji magana kake.? Ko.. Akwai abinda zan iya taimakawa dashi.?” Tai maganar a sanyaye.
Kallonta yayi, wann karon irin kallon da yake mata a baya kafin su saba da juna . Ya kafeta sosai da ido sosai Wanda Ya soma bama Ummul
tsoro Har saida taji dama bata tambayesa ba.
Jiki a sanyaye tace “Kai.. Hak’uri.. Ba nufi bane nai maka shishigi a almarinka..”
Tana k’ok’arin mik’ewa taji ya kamo hannunta. Ta lumshe idanunta cikin k’ok’arin saita kanta. Bugun zuciyarta na sassauta a
hankali.
Ya dawo da ita Ya zaunar kafin ya kuma d’ago folder d’in yana gani. Idonsa na kan folder d’in yake furta “He sees me as a failure.” Yai murmushi da za’a iya kira da murmushin takaici “That I create a circus out of his business life.” Yaci gaba da
jinjina Kai yana dubanta “I’ve been planning.. To take him down.. To take Aliyu Maitama down.. To ruin him.. To bankrupt his business.. The business he valued all his life more than his own son..” Fuskarsa tai jazir haka idanuwansa sanda yake maganar.
Ya
d’ago yana duban Ummul dake dubansa cikin wane irin yanayi mai kama da tausayi.
Haidar yai murmushi yana juya folder d’in, irin murmushin nan da ake kira da murmushin takaici “He values this more than everyone around him. Tell me, shin nayi laifi idan
nace zan kaishi k’asa.?”
Sai Ummul ta shiga jinjina kai tana dubansa “K’warai kuwa.. Ka tapka kuskure. Kuskure mai muni. Dik yanda kaje kazo shine mahaifinka… Wanda kasancewarsa hakan Ya haramta maka fad’a dashi..”
Katseta yai da fad’in “You don’t know a
nything.!” Ya sassauta murya “If only you knew the kind of hell he made me went through tin daga yarinta na, har kawo girma na.. Har zuwa aiki da nayi a k’ark’ashin kampaninsa. Ki yarda dani wann aikin da zanyi shine zai zamo aikina na k’arshe k’ark’ashin
kampanin sa. Sann shine fansar duk wani wulak’anci da cin zarafi da na fuskanta a wann kampanin.!” Ya k’arashe yana kuma tamke folder d’in cikin hannunsa.
“Kar ka bari fushi yai maka jagora..” Bata Kai aya ba ya dakatar da ita.
“O c’mon Khairy.!Stop m
inimising the issue here. Don’t act like I’m making a big deal out of it.!” Yaci Ya k’arashe maganar a zafafe.
Dukda zuciyarta dake bugu hakan bai hanata k’ok’arin tattaro courage dinta ba, ta d’aura hannunta saman nasa, tana dubansa da fuskarta mai cike
da rauni “Duk abinda Ya faru dakai a baya. Na d’auka mun riga mun wuce wann. Na d’auka ka goge duk wani k’unci na rayuwar da ka fuskanta a baya da yafiya.. Su d’in iyayenka ne ba ma’asumai ba. Girman hakkinsu akanka Ya shige ka nemi fansa akansu..”
Murmus
hi mai ciwo ne saman fuskarsa “You always talk about hakkinsu.. Have you ever bothered talking about hakkin ‘ya’ya. Shin su basuda hakki ne kan mutanen da suka zamto sanadin tsintar kansu a wann duniyar..?”
Shiru tai tana dubansa.
“Answer me. Basuda hak
ki.?”
“Eh.. Su.. su..”
Katseta yai “Why are you stuttering now..? Kin kasa furta kalma d’aya sabida kinsan gaskiya nake fad’a. Sunada hakki and they will be questioned kan wann hakki na yaransu.” Yaci gaba da jinjina kai “Shin kinsan most of children da
suka tsinci kansu a yanayi na Allah wadai are victims of circumstance. Wasu sun fuskanci abuse and negligence from their own parents. And don’t you think this can cause behavioural issue in the children later in life.?” Yaci gaba da jinjina Kai yana duban
ta “Idan kayi shuka zaka bashi ruwa zaka kula dashi Har wann shukan ya girma ka girbi amfaninsa. Kaman haka idan kayi shuka baka kula dashi ba zaka samu akasin amfani mai kyau. Kaman misalin haka ne tsakanin ‘ya’ya da iyayensu.” Ya dan rage girman idanunsa
yana dubanta “Wait a minute, do you really think you can change the dynamic of this family.?”
Ummul ta jinjina kai a hankali “Bank’i maka duk abinda kace ba. Shiyasa na sanar dakai tin daga farko. Iyayenmu ma suna kuskure. Sann kuma idan akwai wad’anda z
amu fi ma uzuri sune Iyaye.” Ta d’an gyara zamanta “Jinin Daddy shike yawo through your veins tun a fari.. Sann daga baya da ka samu had’ari ka rasa jininka jininsa ke yawo cikin jikinka a karo na biyu..!” Ya kaikaito yana dubanta da mamaki. Ummul taci gab
a da jinjina Kai tana sakin murmushi. Lokaci guda taci gaba “Zan sanar dakai wani sirri da baka sani ba. Sabida tsananin k’aunarka da yake Ya zab’i a ajiye hakan matsayin sirri a wajenka harma da Mommy. Bai zab’i ka sani ba, sabida yayi ne don soyayyar da
yake maka.”
“What do you mean.? What secret are you talking about.?” Ya tambaya cikin rashin fahimta.
Ummul taci gaba “A lokacin da mukayi accident Daddy ne ya bada jininsa aka k’ara maka. Cikin yardar Ubangiji, You are alive today sabida jinin Daddy na
yawo through your veins.” Ta k’arashe murmushi had’eda k’walla tab idanunta.
Haidar ya shiga girgiza kai “No. no, no way… No, this can’t be… You must have got this wrong.. Tsakanina da mahaifina babu komai face k’iyayya, kyara da hantara.. I’m the last p
erson da Daddy zai baima jininsa. Na sani bazai tab’a ba koda mutuwa zanyi.. Ta Ya mutumin da ko zuwa Ya dubani baiba zai bani jini. I almost lost my life amma.. Bai damu yazo Ya dubani ba. Ta Ya zai bani jininsa.?”
“Amma yayi hakan. Idan Har hakan na ci
kin wani hakkoki naka akansa toh ka tabbata Ya cika wann hakkin. Kana iya karb’an hospital report d’in and see for yourself.” Cewar Ummul.
Haidar ya girgiza Kai