Showing 180001 words to 183000 words out of 267381 words
Zuciyarta yaci gaba da bugu. Yanda kasan bata tab’a sanin shi ba haka takeji. Da kyar ta
iya fitowa k’irjinta sai bugu yake.
Tin daga saman bene masu camera ke haskota har zuwa saukowarta parlorn basu daina d’aukarta hoto ta ko wani angle ba.
Anisa ta dubeta ta saki murmushi “Relax Ummul, ki natsu a Miki hotuna masu kyau dan wad’ann hotunan
a manyan mujallu zasu fito.. Mrs Haidar Maitama.” Ta kashe mata ido guda tana fad’in a d’auke su tare.
Mommy ta k’araso tana dubanta kwalla kaman zai zubo mata ta k’arasa ta rungumeta “Kinyi kyau daughter.. May yours be among the best.” Ta k’arashe murm
ushi saman fuskarta. Nan aka d’auke su hoto. K’wallan da Ummul take makalewa ya gangaro. Mommy tai saurin goge mata tana girgiza Kai “A’a Ummul, yau fah ba ranan kuka bane.. Bana so hawayen nan ya bata Miki kwalliya.” Ta waigo cikin k’ok’arin danne nata ku
kan tana tambayar wai ina Haidar d’in ne.?
Anisa da takaicin acting Mommy ya isheta sai ta juya ido tana furzar da huci. Tana k’ok’arin barin wajen ta hango Haidar na shigowa cikin shiga ta farar shadda k’al babbar riga harda hula. Shigan da zata iya cew
a bata tab’a ganinsa ciki ba. Sosai ya amshe sa dan ba Anisa kawai ba harta ita Ummul d’in saida ta shagala da kallonsa.
Ya k’araso aka musu su uku da Mommy. Ta shige tsakiyar su ta rungumesu su duka biyun akaita kashe musu pictures.
Daga bisani aka som
a yima amarya da ango. Masu hoto suna bada direction. Aka ce ta d’aura hannunta guda saman chest d’insa sai ta d’an d’ago tana dubansa. Duban irin na mai yake nufi.? Ita fah har kawo wann lokacin bai mata magana ba gashi duk yanda aka ce ya rik’e jikinta k
afin ma ace yayi. Wann fah shine mutumin da a baya he’s allergic to cameras. Ummul bata Ankara ba saiji tai ya d’ago hannunta ya d’aura saman chest d’insa.
Anisa taji wani k’atutun bak’in ciki ya tokare mata makoshi. Ga wani kallo da suke bin juna dashi.
A hankali take calming kanta cikin zuciyarta ‘Patience Neesa.! Patience.!! Na yau ne kawai.. Daga rana mai kaman ta yau ta zama tarihi a rayuwar Haidar dinki.’ Ta kuma murmusawa ‘I can’t wait for things to get chaotic.’
**
A can waje kuwa zabga zabgan
bak’aken jeep d’in sukai parking. Motar farko Hajiya Asshe ce ta fito sai Inna Dije daga d’aya b’angaren. D’ayar motar kuwa daga can seat din ‘yanuwan Ummul guda biyu ne Badi’a da Azeema yayinda Umma da Mama Tani ke daga tsakiya. Suka neri suka fito sahu s
ahu.
Kallo guda zakai ma Umma ka fahimci tsananin tashin hankalin da take ciki. Tayi tsuru tsuru da ido ko motsi mai kyau bata iyawa. Badia da Azeema kuwa kasa rufe baki sukai ganin irin gidan da Ummul wai take aure ciki.. Ummul fah. Wacce kowa ke gudunt
a cikin ahalin su. Wann maras sa’an.. Wacce ake mata lak’abi da mai farar k’afa.. Wann wacce maza da yawa ke guje ma Aurenta.. Allah mai iko. Gashi daga sauk’an su wasu ma’aikata masu uniform suka taho suna masu sannu da zuwa cikin harshen turanci cikeda l
adabi suna amsan jakkunansu. D’aya daga ciki tai directing nasu zuwa masauk’i. Sukaja suka tsaya wann ya dubi wancan wancan ya dubi wann. Asshe ta furzar da huci kad’an ganin duk sunja sun tsaya suna duban tsoro ma juna “Ku taho muje mana. Wai ko Baku gaji
bane.?”
Sai Inna Dije ta murmusa da shike ita ta tab’a zuwa lokacin auren Ummul. Tace “Kunga ba masu yankan kai bane ko Shan jini. Ku taho muje..”
Sai Mama Tani wacce ta kasa gasgata wata duniya ma tukunna take ta janyo Inna Dije tana rad’a mata “Ke Dije
.. Da gaske kike.? So kike kice min nan shine gidan da Ummul take ko kuma dai matar nan ta shanshantar damu ne gaba d’aya Kama Suwaiba. Dije nan fah fadan shugaban k’asa ne. K’ur’ani shine a talabijin nake gani.!” Ta k’arashe harda dangwala yatsa saman har
she.
Inna Dije taci gaba da janyo Mama Tani tana fad’in “Kin dai gani da idonki.. Na tabbata bazaki so ki bar Ummul cikin wann daula ba. Duk bala’in da za’ayi bazamu fice daga gidan nan ba saida Ummul.” Cikin sigan rad’a suke ma juna magana.
Duk magana
r da sukeyi ita dai Umma bama tasan mai ke faruwa ba jefa k’afafunta kawai take tana tuna kalaman Asshe a gareta tana tuna a daidai wann rana sukai AUREN WATA UKU da tai ma Ummul da d’ansu zaizo k’arshe.
Azeema da abin ya fara bata tsoro ta dan jada baya
tana janyo ‘yaruwarta Badia. Tai k’asa da murya “Badia nifah wllhi naga gidan zama.. Wllhi bazan koma Kano ba ina nan tareda ‘Yaruwata.!”
Badia ta dara kad’an tace “Toh kiyi yaya da Habibinki kuma idan ya dawo miki.?”
Azeema ta galla mata harara “A’a Ma
k’iyi dai ba Habibi ba. Ai ni idan kinga na fice a gidan nan saidai idan fadan shugaban k’asa zan tafi..”
Badia ta kuma darawa daidai sanda suka isa guest section din.
Asshe ta dubesu tace su saki jiki su huta ga abinci dama tuni an jere musu idan da ak
wai abinda suke buk’ata ga ma’aikata zasuji dasu. Zata shiga cikin gida ta sanar da isowarsu. Inna Dije ne kawai ta amsa mata yayinda Mama Tani ta rakata da harara duk cikin acting ne da suke dan su shashantar da Umma. Badia da Azeema kam basu tsaya saurar
onta ba suka tashi suka soma zaga gida suna kallon aljannar duniya a cewarsu.
Bayan ficewar Asshe jikin Umma yaci gaba da rawa. Ba tareda ta dubesu ba take fad’in “Yau ne.. Yau ne tai alk’awari.. Wa’adin auren zai cika.. Yau d’ansu zai sakar mun Ummul d’
ita.. Zan d’auki Ummul d’ita mu tafi.. Shine kawai abinda ya kawoni..!”
Mama Tani da Inna Dije suka dubi juna.. Tani tuni shiga bud’e buden kayayyakin abincin da aka jere musu Wanda da yawa ma bama ta tab’a ganin irinsu ba. Da ta ga dai bata gane wasu abu
n ba sai ta d’auki Wanda takeda tabbacin naman kaza ne ta soma gwagwiya dama Tani da kaza. Tana ci tana Zare ido kaman za’a k’wace. Ta dafa Umma “Shiyasa na rakoki ‘Yaruwata. Kinga wann mata mai zubin akwati (Wai Asshe) kina ganinta kinga makira.. Wani abi
n take shirya Miki.. Ni da tuni kin sanar Dani ga yanda auren Ummul ta kasance ai da tuni anyita da wajewa an gama komai.. Haba Tani fah nake.!” Ta k’arashe tana kurban wani abu da bata tabbata kunu ne ko madara mai ‘yan’yan itatu ciki ba. Ta lumshe ido ta
na fad’in “Dole ace masu kudin nan kunci rabonku na Aljannah ehe.!”
Inna Dije ta harareta sai ta dafa Umma tace “Suwaiba mu duka muna nan tare da ke bazan bari aci zarafin ‘yard’anuwana ba. Kafin su wulak’anta Ummul zamu d’auketa mu tafi dan kinsan masu
kudin nan su wulak’anta D’anadam ba komai bane wajensu. Tinda auren ma a wulak’ance suka nema dan haka a wulak’ance zasu nemi rabuwa bacin haka meye dalilinsu na gayyato mu a wann rana da sukai alk’awarin kashe Auren. Kinga Suwaiba tashi ki shiga band’aki
kiyo alwala.. Muje na nuna miki yanda ake amfani da irin bandakinsu kinsan ni na tab’a zuwa.” Ta k’arashe tana mai kamo Umma suka nufi band’aki. Ta nuna mata yanda zatayi kafin ta dawo ga Tani. Ta kafe ta da ido “Ke kuma Tani ba sallah ba salati kin fara
ciye ciyen abubuwan da cikinki bai saba da irinsu ba.. Idan cikinki ya tsure kika kasa zuwa wajen shagalin bikin tozarta Suwaiba da ‘yarta saidai na kulleki a d’akin nan dan nidai billahillazi bazaki b’ata min shiri ba ehe..”
Mama Tani ta saki gyatsa mai
k’arfin gaske tace “Yo ka iya ibada ciki bai d’auka ba. Ibadanki ma maje ina Dije.. Yo naga k’eta ce da fansa ya kawo ki nan..”
Inna Dije ta galla mata harara yayinda Mama Tani ta shek’e da dariya.
**
Jikin Mommy ya d’anyi sanyi. Ta kuma duban Asshe “A
sshe kika ce harda Mahaifiyar Ummul akazo..? Asshe ina Jin nauyi.. Ina matuk’ar Jin nauyin bayin Allahn nan.. Mu ya kamata mu fara zuwa musu ba su ba.. Kuma a yanda na shirya da anyi bikin tariyar zamu d’unguma mu tafi gaba d’aya mu gaida iyayen Ummul da d
anginta musamman iyayenta.. Mu kuma musu godiya sann a k’ulla alak’a da zumunci mai kyau.. Munada shirin zuwa gaba d’ayamu.. Ni, Haidar harma da Engr da Kansa. Sun cancanci haka Asshe.. Dama kawai na buk’aci wasu daga cikin danginta suzo ne dan itama taji
dad’i kar taga ba danginta ko d’aya wajen shagalin. Dan farin cikin Ummulkhair.” Duk jikin Mommy a sanyaye take maganar.
Asshe ta furzar da huci kad’an tana mamakin dan dai Mommy batasan waye Suwaiba ba. Da bazata d’aga hankalinta kan wann shashasahar m
atar ba.
Ta dan girgiza Kai “Aunty Kwaise ke ya kamata ki musu godiya ko su ya kamata su Miki godiya.? Yau kece zaki duk’a kiyi godiya ma talaka Aunty Kwaise.? Aunty Kwaise Anya kece kuwa ba’a canza ki ba.?” Asshe ta k’arashe tana bin‘Yaruwar tata da kal
lon mamaki.
Sai Mommy ta dubeta ta shiga jinjina Kai “K’warai kuwa ni ce Asshe. Saidai ba Kwaisen da kika sani a baya bane.. Wancan Kwaise da kika sani capitalist, maison mulki, izza da d’agawa ta tafi kuma bazata sake dawowa ba. Wann Kwaise ce da ta fah
imci duniya da rayuwa. Kwaise ce mai Neman dacewa da tsira duniya da lahira.”
Asshe ta furzar da huci kad’an sai kuma tace “Aunty Kwaise nidai.. Da an kashe auren nan kawai mu basu d’iyarsu kaman yanda muka tsaro daga farko kawai a huta.. Aunty Kwaise wa’
adin ya cika.. Kawai mu basu ‘yarsu kawai and save Haidar..” Ta k’arashe cikin rawar murya.
Mommy sai ta d’an girgiza Kai kad’an cikin rashin fahimta “Save Haidar kuma Asshe. Kaman ya save Haidar.. If there’s someone to save here is Ummul. Balle ma boka m
akaryaci ne kinga dai yanda Al’amra suka kasance bayan mun bar hanyar b’ata mun kama hanyar gaskiya. Kinga bana ma so ana d’ago wann maganar kije ko da akwai abinda suke buk’ata sann kizo kimin iso na gaishesu.”
Asshe ta kuma fruzar da huci “Wai Suwaibar
zakije gaisarwa Aunty Kwaise.? Matar nan fah ko a ‘yar aikatau d’inki bata isa tazo ba.”
Izuwa lokacin Zuciyar Mommy ya soma tunzura. A fusace ta dubeta wann karon “Matar da ta haifo Ummulkhairi idan ta kama na duk’a gabanta na mata godiya ne zanyi haka A
sshe. Domin kuwa tinda Ummulkhair ta shigo rayuwarmu banda alkhairi babu abinda muke gani. Ke shaida ce a gabanki komai ya faru Asshe.. For years ina kuka kan ahalina.. Ahalin da na ruguza da hannu na.. Akan idonki Haidar da baisan hawa ba baisan sauk’a ba
ya d’auki burden din da ba nasa ba tsawon rayuwa. Shin ba Akan haka bane muka tassamma kauce hanya.? Yau sai gashi cikin ikon Allah Haidar ya zauna da iyayensa lafiya. Ahalin da na jima ina mafarki ya dunkule waje d’aya. Ummul ta shigo ta farfado da duk
wasu kyawawan d’abi’u da muka mance dasu ta cika gidan da nargartanta da alkhairanta.. Kinga kuwa ko duk’awa nai na mata godiya ban fad’i ba. Mahaifiyar Ummul ko wace iri ce Asshe tanada k’ima da mutunci a idona. Danginta ko yaya suke mun zama d’aya irres
pective of our social differences. I expect you to do the same with them. Kin fahimta.!” Ta k’arashe cikeda umarni like a big sister.
Zuciyar Asshe yaci gaba da tafasa. Ta kula Aunty Kwaise tsaf zata iya zab’en dangin Ummul ta mance ita ce danginta ta asa
li. Gaba d’aya itakam kaman an canza mata ‘Yaruwa.
“Magana nake Miki Asshe..!” Mommy ta kuma tsawatar mata.
Sai Asshe ta jinjina Kai da kyar tana k’ok’arin k’wak’ulo hawaye. Cikin muryar kuka take fad’in “Aunty Kwaise yanda kike magana kin fara bani tso
ro.. Aunty Kwaise karfa k’warin gwiwar da kike dashi Akan yarinyar nan yasa ki mance komai.. Aunty Kwaise ni fah amana ce wajenki.. Iyayenmu Sun bar Miki amanata.. Banida wacce ta fiki kaf fad’in duniya.. Aunty Kwaise dan Allah kar ki tab’a mance hakan.. I
dan kika rabu dani bansan ya zanyi ba… Duk abinda nakeyi kawai dan na damu dake ne.”
Jikin Mommy ya d’anyi sanyi. Sai taji dan dafa Asshe “Haka ne Asshe. Idan ba mutuwa ba babu abinda zai rabamu ‘Yaruwata. Likewise banida wacce ta fiki. A lokacin kuka da
lokacin dariya duk muna tare. Ta dalilinki Ummulkhairi ta shigo rayuwarmu Asshe.”
Bata k’arasa sauraronta ba zuciyarta ya shiga tafarfasa. Dole dai sai ta ambaci wann mayyar yarinyar. Gaskiya ta fara yarda da batun su Dije yarinyar mayyace dan gashi ta l
ashe Zuciyar ‘yaruwarta.
Sauri sauri Asshe ta nufi kiran Dije da Tani. Suka keb’e tana sanar dasu tsarin yanda zasu tarwatsa wann biki.
Asshe ta rik’e kunne tana duban Tani da Inna Dije alamun kashedi “Kunaji biki ne na manyan mutane. Biki ne da zai s
amu halartan manema labarai. Dole ‘Yan jarida zasu sanin ‘yar gidan wane hamshak’i tilon D’an Aliyu Maitama yake Aure. Inaso da zaran manema labarai sun soma jefo muku tambayoyi ku fara amo duk abinda muka shirya.”
Tani ta chab’i zancen da fad’in “Zan fed
’e musu daga buzu Har fata. Zasuji wacece Ummul da kuma yanda auren Ya kasance. Wayyo wayaga Tani cikin talabijin tana bayani.”
Asshe ta furzar da huci had’ida yin gajeren tsaki. Ta dubi Inna Dije alamun tana jiran nata ba’asin.
Dije ta murmusa “Ita ce t
ayi sanadin mutuwan tilon D’a na Faizu sabida bala’in farar k’afarta. Maza bila adadi sun mutu ta dalilinta.”
Asshe taci gaba da jinjina kai tana sakin murmushin cin nasara.
**
Su Badia tuni Sun nufi cikin gidan suna fad’in a kaisu wajen Ummul. Da kyar
Anisa ta kyale su suka shige wajen Ummul d’in a Cewar Anisa ana gyara mata kwalliyarta dan tuni ta canza zuwa wani shigan.
Sai kallonsu take tana yatsina fuska tana toshe hanci wai dik warin talauci suke.
Azeema tana hankalce da ita jira take su fito d
aga wajen ‘yaruwarsu Ummul suji da ita.
Suna shigewa katafaren bedroom d’in suka tafi a guje suka rungume Ummul.
Ummul wacce ta gansu a bazata sai ta mik’e cikin tsananin shock tama rasa mafarki take ko gaskiya. ‘Yanuwanta take gani. Sai ta rungumesu
ta k’ank’ame tana mai fashewa da kuka.
Saida tai mai isarta suna bata baki suna fad’in kar ta bata kwalliyarta.
Ummul ta kuma dubansu dan ta kasa yarda “Azeema, Badia.. Wai dan Allah kune.?”
Azeema ta murmusa tace “K’warai kuwa mune ‘Yaruwa. Kawo hann
unki ma ki kuma tabbatarwa. Ta had’e hannuwansu su duka uku waje guda. Ummul ta murmusa tana share guntun hawayen da ya digo mata da tissue “Ina Abba na.. Ya jikinshi..? Ina Khulsum da Anty Salima.? Meyasa basu biyoku ba..? Ina Mama da Umma.?”
Azeema da B
adia suka dubi juna sai Badia ta kamo hannun Ummul tace “Abba jikinsa da sauk’i sosai Ummul.. Yana tashi yana zama saidai maganar ne da sauki. Sann har fita dashi waje yasha iska anayi. Abubuwa ne dai har yanzu ba kasafai yake ganewa ba. Likitoci sunce sai
a hankali..Kinsan ciwo idan ya had’u da shekaru.”
Ummul ta jinjina Kai a hankali tana addu’an samun lafiya ga mahaifinta.
Azeema taci gaba “Anty Salima tana tana gidanta yaranta ba lafiya kyanda suke gaba d’ayansu. Amma tace muce Miki tana tayaki murna
kuma taso zuwa Allah bai nufa ba. Mun taho da Mama da Inna Dije.. Da..”
Sai Badia ta dan dubeta dan Umma ita ta rokesu cewa ko sunga Ummul cikin gidan kar su sanar da ita zuwanta tukuna. Basu kawo wani abu ba dan Umman ta kwana biyu cikin wane irin yanay
i.
Ummul sai bata tambayesu Umma ba dan tinda sukace Mama ta taho sai tayi tunanin Umma ke tare da Abbanta.
“Khulsum fah.? Meyasa batazo ba..? Har yanzu tana fushi dani koh.?” Ta tambaya jikinta a sanyaye.
Murmushin da yafi kama da yak’e sukai.
Badi
a tace “A’a ko kad’an bata fushi dake Ummul…” Ta d’anyi fasali sai kuma tace “Ummul ki yafe mana duk abubuwan da muka Miki a baya..”
Azeema ma ta saka baki suna rok’on Ummul yafiya.
Dadi gauraye da farin ciki Ya mamaye Ummul. Ta kamo hannayensu tana fad
’in komai Ya wuce Allah Ya yafesu gaba d’aya.
Nan ta soma tambayarsu labarin gida.
Badia ta d’an numfasa tace “Abubuwa da dama Sun faru a lokacin da baki nan.. Kedai sai mun samu lokaci kawai.. Yau ranar ki ce bani so wann hawayen yaita b’ata Miki kwall
iyarki na ‘yan gayu.” Cewar Badia tana k’ok’arin gyara mata fuskar.
Azeema tace “Wai Ummul kece kika zama haka.? Kin ganki kuwa.? Saikace wata shahararriyar ‘yar gayu irin Wanda muke gani wayoyin mutane ana turawa..” Ta mik’e tana zaga d’akin Wanda Ya ams
a sunansa wajen kyau da girma “Dank’ari mak’ari wani aikin sai amale. Rayuwa kenan Ummul kiga yanda Allah Ya sauya miki rayuwa lokaci guda.. Tabbas kinyi hak’uri kuma kinga ribar hak’uri.. Sai na tuna Zubairu dasu Hajiya Dudu irin tijaran da suka zuba loka
cin da suka amshe lefenki dashi Zubairun. Ai wllhi yanzu kam saidai Zubairu yazo a direbanki.” Ta k’arashe suna darawa daga ita Har Badi’a.
Ummul ta murmusa had’ida girgiza kai “A’a Azeema ni duk wad’ann kayan kyalekyalen basu dameni ba matuk’a akwai kwan
ciyar hankali da zaman lafiya..”
“Chab ai kudi sune kwanciyar hankali wllhi.. Yo ina cikin wann daular k’aryar bak’in ciki Ya tunk’areni ai.” Azeema tace tana mai hayewa saman gadon.
Anisa ce ta banko k’ofa ta shigo tana fad’in maza