Showing 78001 words to 81000 words out of 267381 words

Chapter 27 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

88

Sabuwar Mamanki..!” Ta k’arashe tana mai tallafo fuskar Ummul wacce ta kasa d’ago idonta ta dubi matar amma jin kalamanta na k’arshe yasa ta soma k’ok’arin d’ago idonta masu cikeda raun

i hawaye tab cikinsu.

Dubanta Mommy take Har lokacin tana rik’eda hab’arta murmushi saman fuskarta.

Sai Ummul taji kuka da gaske na zuwa mata musamman da taji matar ta ambaceta da sabuwar Mamanta. Shin tasan Ummanta ta datse alak’a da ita ne..?

Mommy

ta soma girgiza mata kai alamun banda kuka. Ta shiga share mata hawayen tana fad’in ta daina kuka ta saki ranta kaman tana cikin Ahalinta.

Mik’ewa Anisa Tai cikeda k’osawa tana rausayar da ido. Ta dubi Amminta ta furta a hankali “I’m tired of this drama

.!” Tana fad’in haka tasa kai ta shige.

Su Inna Dije Anci an sha an masu tarban girma ta kuma yarda Lallai Ummul gidan girma ta arziki ta shigo dan ko matar nan bata masu tarba da kayan arziki ba tarban fuska da ta masu da yanda ta amshi Ummul kawai sun

isa ta shaida gidan girma da arziki Ummul ta shigo. Koda yake amma Asshe ta sanar da ita Auren na wata uku ne sann ga dalilin auren cewa kwangila suke so a bama d’ansu a kampanin mahaifinsa mahaifin nasa yace bazai bada ba har sai ya kawo masa mata ma’ana

Har sai yayi Aure. Shin duk akan AUREN WATA UKU matar nan tai masu irin wann tarba ta kuma karb’i Ummul hannu bibbiyu kaman ‘yarda ta haifa.. Anya kuwa..? Ita fah duka abubuwan dake faruwa Sun fara kwance mata kai. Ji take ta gaza fahimtar komai. Koda suk

azo tafiya da Ummulkhairi b’angaren Haidar Mommy ce ta rik’e Ummul da kanta tace ita zatai ma ‘yarta rakiya. Kan Inna Dije Ya kuma d’aurewa. Suka dubi juna itada Asshe. Asshe ta k’ifta mata ido alamun kar tace komai.

A haka dai aka bama Inna Dije ma nata

masauk’in nan cikin gidan da nufin washe gari idan Allah yakai rai zasu koma Kano itada abokiyar tafiyarta Asshe.

Ita kad’ai a d’aki sai sak’awa da warwarewa take. Ta d’au d’amarar kafin su bar gidan kafin su koma garin Kano sai tayi yanda tasan ta fahim

ci duk abubuwan dake wakana. Batai ma Ummul rakiya zuwa garin ba sai don su koma tare da Ummul d’in. Amma yanda taga Uwar mijin Ummul na kaffa kaffa da ita tana nan nan da ita bata tsammanin Auren zai Mutu a sauk’ak’e. Abu guda ne zai kashe auren nan shine

kawai ta bud’e bakinta ta sanar da matar cewa ajalinta D’anta Asshe ta kawo mata cikin gida.

Ta mik’e da zummar fitowa nan taga Asshe tsaye gabanta.

Girgiza mata kai Asshe Tai tace “Koma ki zauna Tun muna mu biyu.”

Inna Dije ta dubeta da mamaki. Sai k

uma Tai ‘yar bazawarar murmushi “Aw baki so mu kasance mu uku ne. Ina nufin ni da Ke da kuma ‘yaruwarki wacce kikai mata rufa rufa ki aura ma D’anta ajalinsa. Kar ki tausareni da abun duniya dan yanzu na fahimci kema gaban ‘yaruwar taki almajira ce. Sunan

mijinki ne kawai kike tink’aho da tak’ama dashi amma da alama Babu abinda auren naki ke tsinana Miki. Da alama yayinki ya k’are wajen miji dole ki nemi hanyar neman kud’i kota halin k’ak’a.”

A zuciye Asshe ta dakatar da ita “Kar ki kuskura ki bada shaida

kan abinda bakida masaniya. Ina shawartanki kar kiyi gangancin shiga tsakanin ‘yanuwa guda biyu. Ina nufin nida ‘yaruwata.” Ta k’arashe maganar nata tana sakin murmushi kamar ba itace ta sha mur ba.

Lokaci guda Asshe ta k’araso ta dafa kad’an Inna Dije g

uda tana sakin murmushi “Ki kwanta a saman gado irin Wanda baki tab’a mafarkinsa ba. Ki yada gajiya, kafin ki d’auki hanyar gida gobe dan ba Lallai ki sake karo da irin wann gadon ba. Kar ki mance ‘yarku wata uku kacal zatai a gidan nan.!” Ta k’arashe tan

a k’irga uku da yatsunsa. Lokaci guda ta zaunar da Dije saman gado sai itama ta zauna a gefenta “Ya kamata mu tab’a hira ta k’awaye kafin safiya.. Baki tunani.?” Ta k’arashe tana kashe ma Dije ido. Daidai lokacin Anisa ta shigo da tea cups guda biyu.

As

she ta fad’ad’a murmushinta “Yauwa ‘yar albarka. Kin kawo mana shayin nida k’awata.”

Anisa ta jinina kai tana mai ajewa gaba garesu.

Asshe ta d’auko ta mik’a ma Dije “Ga shayin gidan shugaban k’asa. Irin wann ganyen shayin a gidan shugaban k’asa kawai

kike gani ki sha ki kafa tarihi ki goranta ma sirakanki ina nufin Tani da Suwaiba.” Ta k’arashe tana kurb’an wanda ke d’aya hannun nata.

Ganin Dije ta k’ek’ashe ido tana dubanta Ya sanyata sakin murmushi “Aw na zaci k’awa kika d’aukeni. Kindai san k’awar

arziki bazata baki guba ba. Ko dama k’arya kike da kika kirani k’awa.?” Ta murmusa tana kurban shayinta hankali “Ashe k’aryar gogewa kike Dije.” TaI maganar tana kuma kurban shayin. Harda lumshe ido tana fad’in “Wani abu sai a fadan shugaban k’asa.” Ta s

hanye nata tana k’ok’arin janyo na Inna Dije da niyyan shanyewa Inna Dije Tai saurin rik’e hannunta ta amshe tea d’in.

Inna Dije na murmushi tace “Yo Dije nake muricin kan Dutse . Idan baki sani ba ban fito ba saida na shirya. Ba wani barikinki da gogew

arki da zai bani tsoro.” Ta k’arashe tana kafa kai ta soma kurb’an shayi tana lumshe ido.

Kan kace me Inna Dije ta zube kan gado bacci yayi awon gaba da ita. Asshe ta kece dariya tana jinjina k’ok’arin ‘yarta Anisa da ta kawo wann plan d’in. Lokaci guda t

a gyara ma Inne Dije kwanciyarta tana furta “K’awata ki sha bacci lafiya. Keda bud’e ido kuma sai gobe da safe in sha Allahu.” Ta k’arashe tana kuma kecewa da dariya.

A haka Anisa ta kuma shigowa ta tadda Amminta “Gobe da safe jirgin Daddy zai tashi. Mom

my zata masa rakiya zuwa airport. Sai kiyi amfani da wann dama Ammi ki fitar da matar nan daga gidan nan da zaran Mommy ta fice. Kinga hakan na nufin bazata samu zarafin sanar da Mommy abinda kike tsoro ba wanda kika kasa sanar dani.” Ta k’arashe tana tab’

e baki had’ida rausayar da ido Wanda d’abi’anta ne.

Bakin Asshe Ya gaza rufuwa dan farin ciki bata tab’a tsammanin zata samu solution na yanda zatai da matar nan cikin sauk’i ba. Ta dubi Anisa tace “Ni yau kin gama min komai. Ina Miki kallon marar wayau

ashe zaki iya had’a plan irin wann. Lallai na yarda banyi ganganci ba da nace You’d become my eyes here.”

Anisa ta murmusa “I’m your daughter after all, Ammi.”

Asshe ta jinina kai “K’warai yau kin gama tabbatar min. Kuma na yarda zakiyi kaman yanda nace.

Koda wasa kar ki bari D’anuwanki Haidar Ya samu kusanci da yarinyar nan. Kiyi duk irin makircin da kikaga Ya dace ki tabbata basu samu kusanci ba a tsakanin watanni uku.”

Anisa ta girgiza kai kad’an “Amma Ammi meyasa kika canza ra’ayinki akan yarinyar ba

yan da kince mun na zama mabudin k’ulla shak’uwa tsakaninsu da Haidar.. Ammi what’s with all the mystery behind this marriage.. Ke yanzu kin nuna baki so amma a b’oye ba tareda kin bari Aunty Kwaise ta fahimci haka ba. Ita Aunty Kwaise tana son auren tana

son yarinyar da duka zuciyarta. And at the same time baki so wann matar tayi magana da Aunty Kwaise..” Ta k’arashe tana nuna Inna Dije dake zube saman gado tana bacci. Ta kuma girgiza kai “Ammi wai menene b’oyeyyen al’amarin gameda Auren Haidar.?”

Asshe t

a sauk’e ajiyan zuciya ta kamo hannayen Anisa “Ki yarda dani Anisa. Zan fayyace miki komai amma ba a daidai wann lokacin ba. Akwai lokacin da zaki fahimci duk abubuwan da nayi. Iyakacin abinda zan fad’a Miki a k’arshe shine zaki mallaki Haidar da izinin Al

lah. Amma fah sai kinyi aiki tuk’uru Anisa. Kar ki bari Ya kusanci yarinyar nan. Daga k’arshe zamu nemo mafita.”

Anisa ta sauk’e ajiyan zuciya “Shikenan Ammi zanyi yanda kikace. After all, bana son auren tin daga farko. Yanzu zan d’auko makaman yak’i na

da kika sa nai watsi dasu daga farko.” Ta kuma murmusawa kafin tace “Tinda inada ke Ammi, I know I’m not fighting a losing battle.”

Suka sakar ma juna murmushi a tare kafin Anisa tasa kai ta fice zuciyarta na mata sanyi. Zatai whatsoever it takes dan ta t

abbata yarinyar nan ta fita daga rayuwar Haidar duk tsananin son da Mommy ke mata kuwa. Ta kuma rausayar da ido kafin ta shige.

Asshe ta janyo ma Inne Dije k’ofa kafin ta fito daga b’angaren bak’in ta nufi wajen ‘yaruwarta daketa faman neman layin Haidar

bata samu.

Zama tai gefenta ganin damuwa ya nuna k’arara saman fuskar Mommy.

“Aunty Kwaise, ya na ganki haka. Allah sa dai lafiya.?”

Mommy ta furzar da huci kad’an “Na gaza samun layin Haidar Har yanzu. Ga amaryarsa ta iso.”

Asshe ta jinina kai kad’a

n “Relax Aunty Kwaise. Ki kwantar da hankalinki.. Yarinyar nan tana nan a gidan nan har tsawon watanni uku. Ki basa space kar ki tak’ura masa da batun a yanzu. Tinda an samu Ya amince kuma yarjejeniya akai dashi so I believe zai zo Har nan kan k’afafunsa.”

Mommy da har lokacin ta gaza samun sukuni girgiza kai take “What if ya janye fah Asshe.? What if wancan makirar ta kuma jifansa da wani mugun asirin fah..? Asshe what if Malaminta yafi namu..? Asshe I’m scared.. Tsoro nake kar duk efforts d’ina su tafi a

banza.”

Asshe ta kamo hannun Mommy ta zaunarta saman gado “A’a Aunty Kwaise ke uwa ce. Da izinin Allah k’ok’arin ki bazai tafi a banza ba. Haidar zai dawo gareki. D’anki zai dawo gareki. Munyi komai kaman yanda Malam yace. Inada yak’inin hak’armu zata ci

mma ruwa. Just relax, ki zama calm kuma ki tunk’ari Haidar a tsanake. Yanda kike ta rawar k’afa akan yarinyar zai k’ara tunzura Haidar ne. Kinsan halinsa hasalima kinfi kowa sani tinda ke kika haifesa. Ki bashi gobe zuwa jibi koma satin nan. A hankali sai

ki tunk’aresa da batun.”

Mommy ta girgiza kai “Sati Asshe..? Toh me zaman me yarinyar zatai a gidan nan idan Har babu wanda tazo domin shi.. Asshe no sati yayi yawa. Kema uwa ce ya kamata kifi kowa fahimtar mai nake ji.”

Asshe ta jinjina kai “Na fahimcek

i Aunty Kwaise. Shiyasa nake k’ok’arin fahimtar dake abinda na hango.”

Mommy ta jinjina kai a hankali tana duban Asshe wacce gaba d’aya batada wani kuzari “Asshe.” Ta kirawo sunanta in a serious tune.

Zuciyar Asshe Ya tsinke. Kai da ganinta kaga maras ga

skiya.

Mommy taci gaba “Akwai abinda ya kamata na sani ne..? Ina nufin, tinda kuka kawo yarinyar nan kin canza. Kaman akwai abinda ke damunki ba kaman lokacin da muka soma shirya auren nan ba. Tell me, is there something I should know.?”

Asshe tai Shiru

zuciyarta naci gaba da yankewa sai tanajin tamkar ‘yaruwar tata ta riga ta fahimci komai abinka da maras gaskiya.

“Asshe.!” Mommy ta kuma ambato sunanta su duka biyun suna duban juna.

Sai Asshe ta fashe da kuka tana girgiza kai.

Hakan yai mugun tada ha

nkalin Mommy. Bata San sanda ta mik’e ta k’araso wajen ‘Yaruwar tata ba. Ta dafata tana tambayarta meke faruwa.

Asshe na hawaye take bama Mommy hak’uri tana girgiza kai.

Cikin rashin Hajiya Kwaise ke girgiza kai “Asshe meyasa kike kuka irin haka. Kuma me

yasa kike bani hak’uri.. Wani laifi ne kika min..?”

Cikin zuban hawaye Asshe taci gaba “Na miki laifi mai girma Aunty Kwaise..”

Mommy ta girgiza kai “Laifi.. Wane irin laifi..?”

Anisa da isowarta jikin k’ofan kenan nan tai tsaye ta kasa kunne tana saura

ron wani laifi ne mahaifiyarta ta aikata ma Mommy. Cikin zuciyarta Addu’a take Allah yasa taji amsoshin duk tambayoyin da takewa mahaifiyarta gameda wann murd’add’en aure da sukai ma Haidar.

Muryar Amminta ta sinkayo tana fad’in “An sace komai Aunty Kwa

ise. Kayan lefe na gani na fad’a da kika sa akai ma yarinyar. A lokacin da kayan ya dawo gidana bayan an kai gidansu yarinyar.. A lokacin b’arayi suka biyo dare suka kwashe komai.. Maganar millions of Naira ake.. Shiyasa kikaga dik jikina yayi sanyi ko zar

afin fad’a ma yarinyar ma ban samu ba balle danginta.”

Shiru Mommy tai tana dubanta. Sai ta jinjina kai a hankali “Kan haka kika tada hankalinki.. Idan dan wann ne Babu wani matsala tinda kwalliya ta biya kud’in sabulu yarinyar ta riga ta shigo hannunmu.

Akan auren nan har property na na d’aga na sayar a garin nan.. Kwabon Aliyu Maitama baiyi ciwon kai cikin yak’in neman auren nan ba. So ko nawa zan kashe akan yarinyar nan bazan Ji ciwo ba Asshe because it worth it. Gobe idan Allah Ya kaimu sai ita yarinya

r su fita da Anisa ta tayata da shopping kafin mu shawo kan shi gogan. Kinga fitan nasu da Anisa ma zai d’an sa ta kuma sakin jiki sann Anisa ta koya mata wasu abubuwan yanda zamu samun daman shawo kan Haidar Ya amince ya zauna da yarinyar matsayin mata a

sauk’ak’e.

Jin haka yasa Anisa sakin tsaki tana juya idanu cikeda takaici tasa kai ta shige dan batai tsammanin abinda za’a ce ba kenan. Ji yanda Mommy keta rawar k’afa kan wann yarinyar. Ita taji ta tafi taje ta k’are mata kallo taga me take dashi haka

da Har Mommy ta kasa hangowa tattareda ita.

A b’angaren Asshe kuwa sauk’e ajiyan zuciya Tai dan dama kaya hayansu ta karb’o ta coge kud’ad’e. Dan a wann auren Ummul da Haidar da ta had’a ba k’aramin jari taja ba tinda a halin yanzu mijinta baya yayinta

amaryarsa yarinyar Sa’ar Anisa ke cinye kud’in harta da yawon k’asashen waje ya daina yi da ita da amaryarsa yake. Abin sosai yake mata ciwo musamman idan ta tuna yanda tayi nata zamanin kafin ya auro yarinyar. Da alama bokan yarinyar da iyayenta yafi nata

aiki ne inji Asshe. Hakan yasa ta buga business d’inta da auren d’an ‘yar Uwar nata. Dan haka koda wasa bazata tab’a bari Kwaise tasan gaskiyan al’amari ba.

Sanda Anisa ta tafi sashen Haidar sai cika take tana batsewa ita kad’ai. Ji take tamkar cin fu

ska ake mata da matar Haidar. Ta ya ma za’a kawo wata kucakaa ajiye gidan da sunan matar Haidar. Gidan da ita da kanta ta shirya komai to her taste wanda takeda tabbacin Haidar d’inta zaiso. Bata hango Haidar tareda wata cikin gidan ba. Gida ne data shirya

masu su biyu take kuma hangosu da kalolin soyayyar da zasu sha a cikin gidan harma da yaran da zasu haifa. Ta kuma rausayar da ido tana furzar da huci kad’an kafin ta nufi sama.

Ga mamakin Anisa zaune ta tadda Ummul a parlor har lokacin kanta rufe cikin

mayafi. Ta saki baki tana kallon ikon Allah kafin ta girgiza kai had’ida juya ido “Seriously.! Da gaske kina nan kina k’unk’ume a wajen. Kina jiran miji yazo ya bud’e fuskarki.. Lallai kuwa zaki jima kina rufe kaman kwab’in cincin dan ba mijin da zai bud’e

wann fuskar naki.!” Ta k’arashe tana fincike rufin fuskan Ummul.

Damm! Haka k’irjin Ummul ya buga sanda taji mai maganar ta finciki mayafin da Mommy ta rufa mata bayan sun kawota sashen.

SameenaAleeyou

📚

*AUREN WATA UKU..!*

*24*





Sameena Ale

eyou…✍

🏽

*

Zuciyarta yaci gaba da tsinkewa. Ta sani bata tsammaci farin ciki cikin Auren ba. Kaman yanda bata tab’a mafarkin akwai wani rayuwa mai dad’i gaba gareta ba. Saidai tafi zaton tashin hankalin daga wajen mijin. Tinda mutum ne da ko saninsa bat

ai ba. Sann shima bata tunanin ya santa.

Ta d’ago a sanyaye tana duban Anisa dake ci gaba da aika mata mugun kallo.

Anisa bata daina sakin huci ba ta finciko Ummul ta tadata tsaye “Tashi makira. Sai wani sanne fuska kike tinda kikazo. Irinku kunfi kowa

iya makirci.” Ta shiga zagaye Ummulkhairi dake tsaye tana k’are mata kallo. Sai ta tab’e baki dan ido ba mudu ba yasan kima. Dukda nad’e take cikin lafaya tasan ko kusa bazasu zo d’aya ba. Hasalima Anisar bazata nuna mata komai ba face farin fata.

Anisa

ta rausayar da ido cikeda takaici. Tai tsaye gaban Ummul wacce Har lokacin ko motsawa batai ba “Kar kiyi tunanin zaki tadda farin ciki a wann gidan dan kinyi nasaran saye zuciyar Mommy. Bariki ji na fad’a Miki wani abu. Mommy mace ce da take tamkar Hawain

iya.. Babu wuya ta canza launi. And Haidar.?” Ta kuma sakin murmushi tana ci gaba da zagaye Ummul “Hello, I’m sorry to say sai kin gwammaci mutuwa da auren wann miskilin. Bansan dalilinki na amince ma aurensa ba amma ina mai tabbatar Miki Kinyi babban gang

anci. You’ve made a grave mistake, because Haidar Maitama would never ever fall for someone like you.!” Ta k’arashe muguwar murmushi saman fuskarta ga wani wulak’antaccen kallo da take bin Ummul d’in dashi.

Saida ta gama juye ma Ummulkhairi buhu buhun wu

lak’anci kafin tasa kai zata fice.

Ummul ta sakar mata murmushi tace cikin sanyin muryarta “Baki sanar Dani sunanki ba.”

Anisa ta kalleta a dak’ile “Mai sanin sunana zai miki.?”

Ummul ta kuma murmusawa “Sanin suna nada mahimmanci ko dan hakkin zamantak

ewa. Allah yasa hakan ba matsala bane.”

Anisa ta tsareta da ido tana kallon salon makirci daga wajen wann bagidajiyar. sai kuma ta girgiza kai tana rolling eyes “I don’t have your time.”

Har tasa kai zata fice ta sinkayo muryar Ummul “Ina tunanin tinda

har kika tako yanda nake kinada lokaci na.” Tai maganar murmushi saman pale face d’inta da taci kuka.

Anisa ta kuma dubanta da mamaki. Wanda mamakin Ya hanata magana. Bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login