Showing 201001 words to 204000 words out of 267381 words
da shugaban committee yanda yake sanar dasu ana kan k’ok’arin kama yaran dan a hukuntasu sabi
da rashin hukuntasu da ake yasa suke abinda suka so cikin Al’umma.
Hajja ta girgiza kai tana amsawa. Ta k’arada “Allah dai ya shirya mana zuri’a amma al’amarin dad’a ta’azzara yake.”
Shugaba ya girgiza Kai yace “Sai ka rasa ina matsalar take. Shin iyayen
ne ko kuwa dai halin yau da muka tsinci kanmu ciki ne. Wai nan abinda suka fito sunayi na tada hankalin Al’umma sunansa shara. Ko mai suka gani sai Sun lahanta.. Yara k’anana samari da basu wuce ace suna makaranta ba.”
Hajja ta jinjina kai “D’an yau ne
ka haifesa baka haifi halinsa ba.”
Ya jinjina Kai “Tabbas akwai jarabawa a wasu lokutan kuma sakaci na iyaye. Mutum karma ka haifo yaran da bazaka iya kula dasu ba yaran da bazaka iya basu tarbiya. Tarbiya Ya k’unshi kula da d’aukan nauyi tareda sauk’e wa
su hakkoki da suka ratayu wuyan iyaye. Sai kaga mutum matansa hud’u d’akuna hud’u gareshi wani ma gidan haya ne. Kai shekaran jiya aka kawo mana wani case d’aki d’aya aka raba da labule aka aje mata biyu labule ne kawai Ya rabasu. Ina addini cikin wann al’
amarin. Ga yaran nan haifo su ake ba mai zuwa makarantan islama balle na boko.. Ta ya za’a ce kana mutum mai hankali da Allah Ya halicceka da k’wak’walwa bakada tsari a rayuwarka.? Haka zakiga yaran Sun girma wasu ma a mak’ota suke kwana dan babu d’akin kw
anansu a gidan mahaifinsu. Yarinya budurwa ace ita zata nemo ma kanta abinci ubanta mahaifi na nan da rai amma baisan yaya d’iyarsa take cin abinci ba. Kuma zaki samu bai fasa aure ba bai fasa haifo wasu yaran ba.. An bar yara kara zube an jefa rayuwarsu c
ikin garari Tun suna k’anana. Ta ya za’a tsammaci Al’umma mai nagarta da irin wann tauye hakki da ake ma wad’ann yaran da tuni Sun zama victims of circumstances.”
Hajja ta jinjina Kai “Haka ne Suhaga.. Da yawa an sha’afa da hakkin yara na iyayen kawai ake
hangowa. Tabbas iyaye sunada girman hakki akan ‘ya’yansu wanda bayan biyayya ga Allah da manzonsa sune suka biyo baya. Amma sai muna mance kafin mu Gina irin wad’ann yaran sai mun fara sauke nauyi da hakki nasu dake rataye wuyanmu Wanda za’a tambayemu aka
i. Dole mutum yai k’ok’arin Gina yau dinsa da kyau dan gobensa Ya inganta. Allah ya iyar mana da tarbiyar yaranmu ya bamu ikon sauke nauyi na zama iyaye da ratayu wuyanmu gwargwadon iko.”
Suka jinjina kai suna amsawa da Ameen.
Ummul dake mak’ale daga k’
ofa ta juya da baya a hankali ta nemi waje ta zauna tana tunanin nan zuwa wani lokaci kadan wann nauyin zai hau kanta. Cikin zuciyarta take addu’an Allah Ya iya mata Ya dafa mata Ya bata ikon sauke nauyin dake gab hawa kanta.
**
Gaba d’aya hankulansu ya
karkarta ya koma ga jinyar Hisham. Daga Hajja Har Ummul Sun aje zancen tafiyar Ummulkhair Kano. Zuciyar Hisham fari tas dan dama wann dalili yasa yai ma kansa abinda yai. Ya d’auki wann risk din dan ya karkatar da tunaninsu da hankulansu. Sunyi waya da Ha
idar ya sanar dashi cewa Sun tafi da mahaifiyarsa can wani k’auye ne garin magani Shiyasa bai samu komowa bakin aiki ba. Sam Hisham bai sanar da Haidar cewa shine baida lafiya ba.
Haidar yai shiru yana saurarensa sai kuma yace “Amma.. Meyasa baza’a kawo
ta nan Abuja Asibiti ba Hisham. Idan ta kama a fitar da ita meyasa bazaa fitar da ita ba..? I see no reason da zaisa ka dauki mahaifyarka ka kaita wani jeji da sunan neman magani.. Meye amfanin karatun ka ne wai.?”
Hisham Ya k’ak’aro murmushi “Engr kenan
. Kasan ku yan bokon nan kunyi imani da boko amma ita Hajja tafi son na gargajiyan kuma kasan ance magani dace.” Yana maganar yana tamke fuskarsa sabida zogi da yake ji.
Haidar Ya jinjina kai ba tareda yace komai ba.
Hisham ya k’arada “Nace.. Ya labarin
Ummulkhair kuwa..? How have you been coping..?”
Haidar ya dan lumshe ido had’ida furzar da huci kadan “Every minute passes by feels like a century…”
Cikeda nuna kulawa Hisham yace “Haidar I’m sorry.. I’m so sorry brother bana tareda kai a irin wann loka
ci mai matuk’ar wahala.”
Haidar ya katsesa “You have your own problems to deal with Hisham.” Ya danyi fasali kafin yaci gaba “Abu d’aya da nakeda yak’ini is that I will find Khairy… I will definitely find her no matter the cost… I will never give up.!”
Yanda yake maganar with so much courage and determination sosai ya haifar ma Hisham fad’uwan gaba. Ya had’iyi miyau da kyar kafin ya k’ak’aro murmushi yace “I trust you Abokina. The word giving up has never been in your vocabulary.. Keep searching until yo
u find her.”
Haidar baice dashi komai ba sai duban Anisa dake tunkaro yanda yake da yai. Taci Uwar ado kaman mai zuwa gidan biki. Sai yace da Hisham “We talk later..” Daga haka sukai sallama ya katse kiran.
Anisa ta k’araso tana ci gaba da k’wark’warsa
hannunta rik’eda k’aramin paranti.
Fuska d’aukeda murmushi Tai masa sallama. Ya amsa babu yabo babu fallasa. Ta aje masa tray din tana fad’in “Sannu da hanya. Mommy tace yanzu sauk’ar daga Kano.. Ya hanya..? Ya ka baro su Ammi.?”
A tak’aice ya amsa mat
a sai gani tai ya mik’e yana amsa waya Wanda ga dukkan alamu aiki Ya Shafa. Baiko bi takan ta ba ya fice yana amsa kiran.
Anisa tabi bayansa da kallo kaman zata rusa ihu. Ko kallo fah bata ishesa ba.. Tazo tana tarbansa amma ko kallanta bai ba balle yaci
abinda ta kawo masa. K’atutun bak’in ciki Ya tokare mata mak’oshi sanda ta waiga ta kalli k’atoton hotonsu shida Ummul Wanda akai masu a ranar bikin tariyarsu an kafa a parlorn kaman ka kirasu su zo. Nan taji k’walla ya ciko idonta ta mik’e ta isa jikin ho
ton. Cikin zuciyarta take fad’in ‘Meye ta fini dashi Haidar.? Meyasa bazaka mance da ita ba.? Meyasa bazaka hak’ura da ita ka so ni ba. Wllhi zan maka komai matuk’a kaso ni.. Ni Kai kawai nake so.. Dan Allah ka fahimce ni.’ Ta k’arashe zancen zucin nata ta
na Shafa hoton daidai fuskar Haidar.
Mommy dake daga jikin staircase tanata kallonta tana karantarta daga nan yanda take tsaye.
A hanakali Mommy ta soma takowa cikin parlorn.
Anisa ta waigo da sauri tana duban Mommy. Murmushin da yafi kama da yak’e ta
sakar ma Mommy. Mommy ma ta maida mata Martanin murmushin.
“Sannu da sauk’owa Mommy.” Anisa tace tana risinawa.
Da murmushi saman fuskar Mommy ta amsa “Sannu Daughter.” Sai takai dubanta ga parantin dake aje saman side table “A’ah! Ina Aliyun.. Har ya f
ice ne wai.?”
Anisa ta jinjina Kai Jiki a sanyaye “Ya fice ko ruwa bai sha ba Mommy..” Ta marairaice fuska “Mommy I’m worried about him.. Bakiga yanda ya fice ba duk bashi a hayyacinsa. Ina fata a samu Ummul very soon..” Ta k’arashe tana kai dubanta go ho
ton Haidar da Ummul fuskarta fal damuwa.
Mommy taci gaba da takowa tana jinjina Kai a hankali. Ta isa jikin pic din itama. Idonta naga hoton take fadin “Wherever she is. I hope she’s safe.”
Anisa ta jinjina Kai. Cikin zuciyarta tace ‘Tana d’aukeda jariri
n ciki. Jikanki da bazan tab’a bari ki sani ba. A fili kuwa sai ta kuma marairaice fuska tana duban Mommy cikeda kulawa “But.. Mommy mai zai faru idan bata dawo cikin rayuwar Haidar ba. Haka nan.. Zai k’arashi rayuwarsa a gantale Mommy..? It’s been three m
onths now.” Tai maganar kaman zatai kuka.
Mommy ta tsareta da ido sai ta d’an girgiza Kai kadan had’ida furzar da huci “I don’t know Anisa.. Bayan yarinyar can da tai masa asiri bana jin Haidar Ya taba son wata mace except Ummulkhair..” Ta danyi fasali “B
an sani ba.. Kodai zai so wata a gaba kodai ni ce zan sake aura masa wata.”
Anisa tai sauri ta dubi Mommy “Mommy kina nufin zaki sake aura ma Haidar wata matar idan Ummul bata dawo ba..?”
Mommy ta dubeta sai tace “Why not.! Idan har a baya lokacin da ba
i daukan magana na da mahimmanci Ya amince da zab’ina Maiyasa yanzu bazan sake zab’ar masa mata ba. Matsalar kawai ban san wace zan zab’o masa mai hankali kaman Ummulkhair ba..”
Anisa ta sha jinin jikinta kanta a k’asa.
Mommy ta kafeta Da ido sai ta gyar
a zama tace “But.. I have someone in mind already.. Saidai ban sani ba ko zata amince dukda itama inada iko akanta..”
Anisa ta d’ago a zabure tana duban Mommy. Murya har na rawa take furta “Mommy.. I don’t think akwai macen da zata guje ma auren Haidar du
k had’uwar ta da isarta.. He’s every girl’s dream.”
Mommy taci gaba da dubanta murmushi saman fuskarta tace “You think so.?”
Anisa ta jinjina Kai “Hundred percent sure.!”
Mommy ta kuma jinjina Kai “Anisa what if.. Kece wann yarinyar da nai sha’awa ma D
’ana Haidar..”
K’iris ya rage Anisa bata yanki jiki ta zube k’asa ba dan a bazata taji maganar Mommyn.
Tama kasa yarda da abinda kunnenta yaji mata. Ta girgiza Kai cikin rashin yarda tana duban Mommy “Mommy… Ni..? Kike so Haidar ya Aura.?!”
Mommy ta jin
jina mata Kai “Why not.!” Mommy tace cikeda kulawa. Ta k’arada “You are his cousin sann ko da ace Ummul ta dawo gidan Haidar nasan baza’a samu matsala daga wajenki ko wajenta ba.. I’m sure ku biyun zaku fahimci juna… But I’d have to ask you this question.
Do you love Haidar..?”
Anisa wacce ta koma tamkar statue baki sake take duban Mommy. Ta kasa gaskgata abinda ke faruwa. Mommy ta kuma jefa mats tambayar sai Anisa ta fashe da kuka.
Mommy ta kamo hannunta tana girgiza Kai “A’a Anisa meye kuma abun kuka. K
inga idan baki sonshi bazan tak’ura ki ba zan nema masa wata can daban..”
Mommy bata Kai aya ba Anisa ta shiga jinjina Kai tana murmushi “Mommy kukan farin ciki ne.. I never thought a day like this would come… I mean… Not this soon… Mommy I.. I can’t beli
eve it… My dream is finally coming true.”
Da tsananin mamaki Mommy ke dubanta sai ta girgiza Kai kadan tace “Do.. You love Haidar.?”
“I’ve always loved him Mommy.. I love him since childhood…”
Mommy tace “Aw..! wai so kike kice tuntuni kina son Haidar..
?”
Taci gaba da jinjina Kai yayinda farin cikinta ke ninkuwa. Tin ina yarinya nake son shi Mommy.. Kawai kun kasa fahimta ne.. But he’s the love of my life..”
Mommy taci gaba da jinjina Kai tana dubanta “Does your Mom know..? Asshe tasan kin jima kina s
on Haidar..?”
Sai a nan ne Anisa ta d’an ja jinin jikinta.. Sai ta girgiza Kai alamun a’a “Kawai.. Ni kad’ai na rik’e abuna cikin zuciya.. Ko Hilal bai sani ba.”
Mommy ta jinjina Kai kaman mai nazari sai kuma ta sakar ma Anisa murmushi “Yazo gidan sauk’
i had’aku aure bazai wahala ba.”
Anisa ta d’an dubeta. Fuska dauke da alamun tsoro “Amma.. Mommy what if Haidar rejects the idea.. What if yak’i aminta da Auren.?”
Murmushi Mommy ta kuma sakar mata “Kar ki damu. Yarona Haidar mai biyayya ne.. Ko a baya b
aya sab’a umarni na balle yanzu.. Kawai muyi fatan naki iyayen su amince musamman ma Amminki tinda har yanzu bamu koma kaman da ba.”
Anisa ta waro ido tace “Haba Mommy dani da Ammi fah ke d’in duka uwa ce a wajenmu.. And a halin yanzu Ammi dalilin da zais
a zumuncinku ya sak’e k’ulluwa take nema kinga kuwa zatafi kowa farin ciki da wann had’in.. Abba kuma kinsan baida matsala tinda ba kudinsa zaa karb’a ba.”
Mommy taci gaba da duban Anisa mamaki bai saketa ba. Lokaci guda take jinjina Kai “Shikenan.. Zan s
amu Asshe da maganar..”
Cikeda zak’ewa Anisa tace “Toh Mommy shi kuma fah..? Ina nufin Haidar..” Ta k’arashe cikeda sakarci.
Mommy ta jinjina Kai “Haidar bazai zama matsala ba dan haka kar ki samu damuwa kinji.”
Anisa ta daka tsallan murna ta nufi hany
an kitchen a guje tana rangada ma ma’aikatan kitchen k’ira tana fad’in duk su fice zatai ma mijinta abincin dare.
Mommy ta bita da kallo har ta shige kafin ta jinjina kai kadan tace “Sannu a hankali.”
Daren ranan Anisa bata sama bata k’asa. Sai kai kom
o take da sunan tana shirya ma Haidar dinner. Mommy ta shigo kitchen din tana dubanta fuska d’aukeda murmushi “Iyye lallai.! Ashe d’iyar tawa gwana ce wajen girki.” Mommy tace tana bude dishes din da Anisa Ke shiryawa.
Anisa ta wani murmusa tana sadda kai
alamun kunya.
Mommy ta kuma murmusawa “Yau kuma Mommyn taki kike jin kunya..? Kinga ni ba wata surkunta tsakaninmu ki saki jikinki Dani fiyeda yanda muke a baya.”
Anisa ta kuma murmusawa “Shikenan Mommy.. I’ll be open with you.. Ina so ki kaunaceni kama
n yanda kika k’aunaci Ummul koma fiyeda ita.”
Mommy ta jinjina Kai “Ko ba Haidar ni mamarki ce Anisa. You shouldn’t be hiding things from me haka ne..?”
Anisa tai saurin jinjina Kai cikeda jin dadi.
Mommy tace “Good. And if you want anything.. Don’t h
esitate to let me know kinji koh.”
Nan ma da sauri Anisa ta jinjina kai kafin Ta k’arada “Mommy ni kin gama min komai a rayuwar nan… Ina jin babu wani abu da zan nema kuma da Ya wuce Auren Haidar. Duk duniya ke kadai kika fahimci mai nake ciki. For so lon
g Ina dakon soyayyarsa Babu Wanda Ya fahimta. Sai Allah Ya share mun hawaye yasa kika fahimta.. Thank you Mommy.”
Mommy ta dafa kafad’arta “Anything for my Daughter..”
Anisa na wangale hak’wara tasa kai zata shige cikeda jin dadi.
Mommy ta tsareta da i
do sai ta dan riko hannunta alamun dakatarwa “Ina kuma zakije Daughter..?”
“Zanje na sake kwalliya ne kafin Haidar ya shigo.”
Mommy ta girgiza mata Kai alamun a’a “Bana so kina rawar k’afarnan a gabansa sai ya rainaki. Ki dinga jan ajinki matsayinki na m
ace. And kar Ki mance Haidar baisan da zancen ba tukuna.”
Anisa tai raurau da idanu had’ida tab’e fuska kadan. Ta dubi Mommy kaman zatai kuka “Amma Mommy zaki sanar dashi.?”
Hannunta Mommy ta kamo “Taho nan kiji.”
Suka zauna saman kujera. Mommy ta dube
ta tace “Anisa nasan kinsan al’amarin aure ba abin wasa bane. Balle Haidar dake fuskantar k’alubalen rashin Ummul. Matuk’a muka tunk’aresa da irin wann batu a daidai wann gab’ar za’a iya samun matsala ne. Kinsan sa yanzu sai ya kwance mana ya koma Haidar d
’insa na da. Sann Daddy ma bazai yuwu muzo masa da batu irin wann a daidai wann lokaci ba. Kowa zaiga rashin dacewar hakan musamman da yake Mahaifin Ummul na nan asibiti a Abuja. Ya kamata mu bar komai har sai an sallamesa sun koma can gida Kano ta yanda b
a wani tashin hankali da zai bullo mana. A tsanake zamu tunk’ari lamarin. Kedai kawai ki kwantar da hankalinki kiyi duk abubuwan da na umarceki tinda kinada yarda da amincewata ki k’addara tamkar kin Auri Haidar an gama.”
Anisa ta danyi jim sai kuma ta ji
njina Kai tace “Gaskiya ne Mommy. And its a once in a lifetime in sha Allah. Kuma so nake Aurenmu Ya karad’e ko ina dan babban biki nake so Mommy.”
Mommy ta jinjina Kai tana duban Anisa murmushi saman fuskarta.
**
A haka Anisa taci gaba da mafarkinta na
kasancewa matar Haidar cikin kwanciyar hankali sanin cewa tana tareda yarda da amincewar Mommy. Ba abinda yake gabanta a halin yanzu tamkar taga wann mafarki nata Ya zama gaskiya. Dole ta dad’a daure belt dinta da kyau dan ta tabbata Ummul bata dawo ba. B
urinta bai wuce taga wann ragwababben uban Ummul d’in Ya bar garin ba.
A can b’angaren su Ummul ma Hisham yanata samin lafiya saidai da yaga hankulansu zai karkata zuwa wani abin daban sai ya b’ullo da wani abin wanda zai dauke hankulansu.
A haka aka k
washe kwanaki satuttuka Har aka soma k’irga watanni. Kowa da abinda yake burin cimmawa. Ummul na nan tana rainon cikinta. Hisham bai fasa kudirinsa da shirinsa ba. Haidar bai fasa neman Ummul ba. Mommy ta maida hankali kan Anisa yayinda Anisa taci gaba da
mafarkin cikan burinta. Abba yanata samun lafiya. Daddy nata zarya tsakanin SouthAfrica da Nigeria kasuwancinsa na dad’a bunk’asa a k’asashen k’etare.
Cikin Ummul nata girma cikin k’oshin lafiya. Saidai tinda cikin Ya fito ta kuma rok’on Hajja da cewa da
n Allah ta barta tai rainon cikin gabanta ko dan guje ma abinda zaije yazo cikin ahalinta.
A b’angaren Haidar kuwa dukda ayyuka da suka sha gabansa bai fasa k’udirinsa na nemanta ba. Dan tinda tafiye tafiyen Abba ya k’aru Sai ayyukan cikin gida Nigeria s
uka dawo wuyan Haidar gaba d’aya. Kusan shi yake kula da ragamar Kampanin.
*
Watan Abba uku a Abuja aka sallamesa daga asibiti. Tuni Haidar Ya kira Sadis ya sanar dashi tinda dama duk wani hidindimun asibitin Sadis d’in keyi.
Kai tsaye gidan Daddy suka
taho. Abba har tafiya yake da sanda, idan ka gansa bazaka gane sa ba ya samu lafiya da kula cikin ikon Allah. Sai son barka. Mama Tani da Abba ne a bayan motan yayinda Azeema ke zaune mazaunin mai zaman banza Sadis na tuk’awa.
Koda suka iso gidan Mommy d
a kanta ta tarbesu. Tuni tasa an shirya musu sashen bak’i sai haba take dasu Anisa kaw sai cika take tana batsewa dikda cikin zuciyarta fal annashuwa ne an sallami nakasashen uban Ummul zasu fice daga rayuwarsu gaba d’aya su huta.
Suka raka juna da mugun
kallo itada Azeema dan dukansu basu mance