Showing 3001 words to 6000 words out of 267381 words

Chapter 2 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

18

tin Ummulkhairy tana k’arama taci burin ta aurar da ita da k’anan shekaru saidai Allah bai nufa hakan ba. Haka zatai mata wanka tai mata ado tin tanada k’ananan shekaru taita mata wak’e tana

karanto baitika tana mata rawa tana fad’in saura k’iris ta aurar da ita saura k’iris ta kaita d’akin miji. Koda Mama kishiyarta zataita yab’a mata maganganu da fad’in ta jira dai taga girman ‘yar tata sam bazata tab’a tankata ba. Umma Ta kasance irin muta

nen nan ne masu san Barkwanci Wanda kowa ya mata wann shaidar Wanda hakan kesa wasu ke mata kallan shashasha a akasarin lokuta. Ko fad’a Abokiyar zamanta ta tareta dashi wasa take maidashi Sam batada abokin fad’a kaf unguwar balle gidan. Hakan yasa halinsu

itada Khulsum

yasha bam bam. Domin kaw albasa batai halin ruwa ba. Dukda kuwa cewa Ummulkhairi ma bata dauko barkwancin ba. Sai sanyi wann kuma wajen mahaifinta ta dauko.

Burin Ummulkhairi shine cikan burin mahaifiyarta. ta samu mijin da zai aureta koda

bata sonsa zatai hak’uri ta zauna dashi dan burin mahaifiyarta ya cika. Burin mahaifiyarta shine Ummul d’inta tai aure ta tafi d’akin mijinta.

Mahaifiyar su Ummulkhairy ta kasance itace mace ta biyu a gidan mahaifinsu. Matarsa ta fari itace Mama Tani yar

a uku gareta kuma duk sunyi aure suna d’akin mazajensu. Badi’a itace babba sai Salima sann autarta wacce Ummulkhairy ta girme mata da shekaru uku itama tuni tayi aure tana d’akinta. Autar Mama tani sunanta Azeema. Mama ta kasance d’aya daga cikin matan ung

uwar Wanda basu da aiki sai aibata duk macen da Allah ya jarabceta da JINKIRIN aure ko mutuwar aure. Nan zakaji bakin Mama tana alfahari tana fad’in ita nata yaran kaf suna d’akin mazajensu kai kace wayonta ne ya kawo hakan ko dabararta.

Mahaifinsu baida

wani karfi saidai basu rasa abinda zasu saka bakin salati, saida manja da mangyada yake a kasuwa dukda dai jarin ba wani mai yawa bane amma sunfi k’arfin abinda zasu saka a bakin salati daidai talaka. JINKIRIN auren Ummulkhairy ba shine ke tada hankalin

mahaifinsu ba kaman yanda ake maganan aure magana yabi iska. Dukda ya kasance Dattijo kuma mai k’ok’arin danne damuwarsa ya fawwala wa Ubangijinsa lamuransa can k’asan zuciyarsa na damuwa da al’amarin ‘yarsa Ummulkhairy saidai Sam baya nuna hakan. Kullum c

ikin cewa yake Allah ne bai nufa ba. Ga manema Sam basu fasa nemanta ba domin kaw d’iyarsa tubarkallah ce batada makusa saidai ace d’anadam tara yake dama bai cika goma ba. Yayi imani lokacinta ne kawai baiyi ba.

Gyara zamansa yai yana sauraron kukan da

Umma ke ci gaba da yi tana fad’in “Abban Ummul dan girman Allah ka nemo min mafita wllhi bansan ya za’ayi na sake fuskantar mutanen unguwar nan ba. Toh ma da wani fuska zan sake fita ana nunani ana k’irga fashin auren Ummul da akai.. Dan Allah ka nemo min

mafita Wayyo ni Suwaiba..” Ta k’arashe tana kuma rusa wani kukan.

Abba ya girgiza Kansa, ya kasance mutum maras San hayaniya kaman dai ‘yarsa Ummulkhairy. Shi irin mutanen nan ne da zakai abu su kauda idanu suyi kaman basu gani ba sann irin mutanen nan ne

masu nuna kulawa da k’auna kan duk Wanda Allah ya hukunta kasancewarsu tare Kama daga iyalansa har zuwa kan ‘Ya’yansa da danginsa dukda kuwa k’annensa dake zaune cikin gidan basu d’aukesa bakin komai ba hasalima gaba suke dashi. Hakan baisa ya fasa masu n

asiha da wasilci da zumunci ba.

Cikin b’acin rai ya tsame hannunsa daga cikin kwanon tuwon dake gabansa ya katse Umma da fad’in “Haba Suwaiba! Ya isa haka nan.. Shin yau ne aka fara amsar lefen Ummulkhairy ko sadakinta..?”

Batace komai ba sai gunjin kuk

a da take ci gaba.

Ya kuma girgiza Kai “Toh tinda ba yau bane na farko sai ki kwantar da hankali dan na tabbata bazai zama na k’arshe ba tinda dai kink’i amincewa ‘yarki ta koma makaranta tai karatu kaman yanda ita Ummul d’in ke so.”

Cikin zuban hawaye t

a d’ago tana duban mijin nata “Yo wani karatu fisabilillahi .. Aima shekarun ta Sun wuce shekarun zaman aji.”

“A ina kika tab’a ji an girma ma neman ilimi Suwaiba..? Waima dakata Suwaiba. Da kika damu kika daga hankali duka nawa Ummul d’in take ne..?”

Um

ma ta dago a zabure jin yace nawa Ummul d’in take. Tai karaf tace “Ta fah haura talatin Abban Ummul.”

Taci gaba “Yo wani ilimi zata nema ya wuce ilimin zama a gidan miji da naketa k’ok’arin bata.. Allah na tuba abu kaman jifa ko sa hannu.”

Abba ya kuma k

atseta “Kinga Suwaiba na rabaki da wann gurb’ataccen tunani.. Ki je kina jefa kanki cikin damuwan abinda Allah bai d’aura Miki ba.. Ko an fad’a Miki bansan kina amso ma Ummulkhairy Neman Taimako bane.. Nasan komai kawai ina kauda ido ne ina Miki uzuri.. Am

ma ki sani kar kawar da idanun da nake bana magana yasa kije ki auka ga sab’awa mahaliccinki kiyi shirka.. Ki natsu ki san mai Kike ciki.. Allah yana sane da duk abubuwan da suke faruwa.. Addu’an da zaki mata Har sai yafi na Wanda zaki saka wani ya mata d

omin kaw ke mahaifiyarta ce.. Idan har da gaske so kike tai auren kaman yanda kikaci buri. Sai ki rage bacci ki tashi cikin dare ki Kai kokenki ma Ubangijin duka. Ki zubda hawaye a yanda zuban hawayen zai amfani domin kaw wajen Allah ne hawayenki

keda amf

ani ba mutanen da zasuyi murna da ganin hawayen naki ba. Haba Suwaiba kiyita korototo kina kin shiga uku..? Da irin wann korototo da ambaton uku da kike ma kanki toh fa babu abinda zaki gani sai ukun..”

Ta kuma kamo bakin zani tana share hawaye “Haba Abba

n Ummul dan Allah ka fad’a alkhairi..”

“Kece zakiyi ma kanki karatun ta natsu ki dinga fad’in alkhairi gameda ‘yarki ko dan rayuwarta ta inganta. Domin kuwa su ‘ya’ya amana ce Allah Ya bamu kuma za’a tsaida mu a tambayemu akansu ranan gobe.” Ya k’arashe

yana mai janyo kwanon tuwon sa.

**

A can d’aki kuwa Khulsum ce ta duk’a gaba ga Ummulkhairy, tayi zaman rak’umi tana fuskantar ‘yaruwar tata da tin shigowarsu gidan take aikin abu guda wato kuka.

SameenaAleeyou

📚

*AUREN WATA UKU.!*

*03*





Sameena

Aleeyou…✍

🏽

*

Cikin gunjin kuka Ummul taci gaba “Mai kuma zaki fad’a mun Khulsum.. Ba dai kinyi abinda kike so ba kin tari matan nan da fad’a har Zubair ya iso ya taddamu a haka.. Toh me kuma yai saura tinda gashi ko wayata bai d’agawa.. Khulsum, Nifa

burin mahaifiyata kawai nake son cikawa..!” Ta k’arashe wani kukan na taso mata.

Khulsum ta girgiza Kai “Adda Ummul dan Allah ki saurareni.. Wllhi mutumin nan bai cancanceki ba.. Ba son gaskiya yake Miki ba.. Da ace son gaskiya yake Miki da ya baki dama y

a saurara daga b’angarenki, amma baiyi haka ba ya hau kan dokin fushi..”

“Har akwai Wanda ya cancanceni ne Khulsum..?” Tai maganar tana nuni da kanta cikin rawar murya irinta mai kuka.

Khulsum ta girgiza Kai “Dan Allah kar ki bi maganganun Umma da mutane

.. Kar ki kaskantar da kanki Adda Ummul.. Wllhi kin wuce gaban duk mazan dake fasa aurenki.. Kimarki da ajinki ya wuce nasu. Shima wann zubair din bai cancanceki ba shiyasa ya kasa ganin kimarki kaman dai sauran.”

Ummul tai murmushi mai ciwo “Watak’ila ba

nida wani kima da gaske Kulsum.. Watak’ila abubuwan da mutane ke fad’i kaina gaskiya ne.”

“K’warai kuwa Ummul mace mai shekarunki batada wani kima matuk’a ba d’akin mijinta take ba..!” Muryar Ummansu ya katsesu wacce tai tsaye tana sauraron tattaunawar y

aran nata.

A tare suka d’ago suna duban Umma dake aika masu mugun kallo tana huci.

Khulsum ta lumshe idanunta had’ida furzar da huci “Umma wai dan Allah meyasa Baki saka farin cikin yaranki a farko.. Mutanen nan fah tuni sunzo Sun amshe kayansu, wllhi ko

Zubair baizo ya tadda Adda Ummul na rabon fad’a ba bazasu bari ya aureta ba tinda sunyi furuci kuma sun amshe lefensu.. Haba sai kace ana Neman Kai da ita.. Dik anbi an tsangwameta a gida da waje duk bata huta ba.. Umma auren nan fah ba’a ce yana cikin ci

ka cikan musulunci ba.!”

Umma ta danna mata dak’uwa “Kinci ubanki Khulsum.. Idan baya cikin cika cikan musulunci ai sunna ce mai k’arfi… Ke baki San ko gawan mace mai aure yafi daraja ba.. Cikan mutuncin mace shine a ganta a d’akinta..” Ta

d’an numfasa ka

fin taci gaba “Kina jina idan baki daina korarwa ‘yaruwarki mazajen aure da wann bak’in Zuciyar naki ba wllhi kinji na rantse zan saka k’afar wando d’aya dake.. Maimakon ki duk’afa Neman naki mijin auren kin tsaya kina lalata na ‘yaruwarki koh.. Toh ahir

d’inki Khulsumu aure dai da izinin Allah ina numfashi sai Ummul ta tafi d’akin mijinta ko mai zai faru kuwa.!” Ta k’arashe sai tsuma take.

Khulsum ta d’ago tana duban mahaifiyar tasu da mugun mamaki. Lokaci guda ta girgiza Kai kad’an tace “Umma dan Allah

a dinga Neman zabin Allah dai.. Kuma a dinga k’ok’arin furta alkhairi.. Auren nan duk yanda aka so bazafa ayi shi ba sai lokacin da Allah yace kuma yaso.”

“Aw Nima rashin kunyar zaki min.. Toh bismillah.. Nace bismillah Khulsumu..” Tai k’wafa tana mai k’a

rawada “Rikakkiya kawai.. Bazan dai Miki baki ba dan bana fata ki Kai shekarun Ummul a gabana baki tafi d’akin mijinki ba.”

Ita dai Khulsum bata ma ce komai ba dan tsanar mazan ma tai balle wani aure tin bayan abinda ke faruwa da ‘yaruwarta.

**

ABUJA

Akasarin gidajen da kake iya hanga tapka tapkan benaye ne masu tsananin kyau da tsari. Yanda aka tsara su aka kuma inganta gininsu zakace a k’asar turai kake. Tapkeken gida ne da ya amsa Sunansa, ga korayen shuke shuke da ciyayi masu d’aukan idanu da ban s

ha’awa. Komai na gidan fari ne k’al tamkar fadar White House.

A hankali yake Jin hasken ranan hantsi yana haske masa fuska sakamon baccin da ya d’aukesa a balcony d’insa saman wasu kujeru na shakatawa tin bayan da ya gabatar da sallar asuba. Sautin motoc

i da tsuntsaye jifa jifa suka soma gauraye masa kunnuwansa da bai cika shiri da hayaniya ba. Nan take kuwa suka katse masa baccin nasa.

Tafukan hannayensa yasa ya shafe fuskarsa dasu kana ya mik’e zaune yana duba agogon dake fuskar wayarsa. A kasalce ya j

efo k’afafunsa k’asa ya mik’e tsaye yana kuma stretching gabb’ansa.

Kai tsaye bathroom ya shige bayan ya tura k’ofar glass da ta raba balcony d’insa da d’akin nasa.

Cikin mintuna k’alilan ya shirya tsaf ya fito cikin black business suit d’insa. Kallo g

uda zaka masa ka tsarkake Ubangijin da ya tsara halittarsa.

Koda ya sauk’o k’asa yana iya sinkayo muryar mahaifiyarsa tsakanin ma’aikatan gidan ta yanda take shiga bata nan take fita ba. Ya d’an furzar da huci had’ida girgiza Kai. Wann morning routine d’

in mahaifiyarsa ce. Idan da sabo duk mai rayuwa cikin gidan ya saba da wann. D’an girgiza kansa yai ba tareda ya nufi cikin gidan ba. Lokaci guda yasa Kai ya fice cikin sauri ya nufi yanda motarsa ke ajiye. Nan da nan yaja motar ya fice daga gidan a gaggau

ce dan Sam baiso yai arba da mahaifiyar tasa a safiyar.

Bai zarce ko ina ba sai wani makeken building maiji da tsawo da kuma girma had’ida tsari. Daga saman ginin anyi rubutu da k’araffa masu ruwan zinari *MAITAMA BUILDERS*. Rubutun anyisu ne da Manyan ba

k’ak’e.

Cikin sassarfa yake taku a katafaren ginin mai k’unshe da ma’aikata sahu sahu. Waya manne b’angaren kunnensa na hagu. Dik yanda ya shige kaw sai ya d’ibi gaisuwa Dikda ba amsawa yake ba.

Lift ya shige ya diresa a third floor. Wani hamshak’in offi

ce mai tsananin girma da tsari ya nufa, still waya yake.

Nan da nan wata mata cikin shiga cooperate ta biyo bayansa.

Cikin muryarsa mai cikeda k’warjini Yaci gaba da furta “You find a way to fix this Hisham…Honestly, I’m highly disappointed. I did not exp

ect my team members to be so unprofessional like this… Iyakacin abinda na sani shine we must cover the deal by all means possible.” Yana Ida fad’in haka ya katse kiran ba tareda ya jira amsar Hisham ba.

Matar da tin isowarsa yai mata alama da hannu da ta

biyosa sakatariyar mahaifinsa ne Wanda kuma ya kasance mammallakin wann shahararren Construction Company d’in wato Maitama Builders.

Ta d’an risina tana gaidashi “Good morning Sir.”

“Morning Jane.” Ya fad’i sanda yake kaikaitowa har lokacin idaninsa na

kan fuskar wayarsa. Lokaci guda ya k’arada “Is my Dad here..?”

Ta d’an girgiza Kai alamun a’a “He….hasn’t arrived yet. Sir.”

Shiru yai kaman mai nazari. Securities masu tsaron gate d’in gidansu sun tabbatar masa Dad d’insa ya fita tun sassafe toh ina ya

tafi idan ba Office ya taho ba. Yasan mahaifinsa mutum ne mai matuk’ar girmama aikinsa.

Jinjina mata Kai yai “Alright, let me know the minute he arrives.” Ya Fad’i yana mai nufan k’ofa.

Jinjina masa Kai tai had’ida amsawa kafin ta take masa baya suka ru

fo ofishin Wanda ya kasance ofishin mahaifinsa.

Engr Aliyu Aliyu Maitama kenan. D’ah d’aya tilo ga Engr Aliyu Maitama. Shid’in sunan mahaifinsa yaci sann same profession suke da shi da mahaifinsa. Su duka biyun Construction Engineers ne. Mahaifiyarsa ita

ta tilasta masa yin karatu irin na mahaifinsa ba wai dan yanada buri ko mafarkin hakan ba. A cewarta ta ginasa Akan karatu da aiki irin na mahaifinsa ne domin kaw shine zai gaji mahaifin nasa. Wann dalili yasa harta da suna saida ta maida masa da sunan mah

aifin nasa.

Second floor ya dawo ya nufin wani hanyar. Babban ofishi ne da ya k’unshi tables da dama, saman ko wanne table akwai na’urar computer bisa. Daga gefen ko’far glass d’in da zai sadaka da lobby an rubuta daga sama kad’an *Marketing Development

Department*

Wani madaidaicin d’akin taro ya nufa. Daga tsakiya akwai doguwar table kewaye da kujeru a k’alla goma.

Tin daga nesa employee guda ya hangesa. A guje ya shigo Office d’in yana sanar dasu “Guys guys…” kowa ya kakaito yana dubansa. Saurayin yac

i gaba “Sir Haidar is here and he seems to be in a very bad mood. Let’s all behave ourselves.” Ya karashe yana daga masu gira lokacin da yake daidaita zamansa cikin kujeransa.

Take kowa ya shiga taitayinsa.

Ai kaw yana shigowa mutanen dake zaune saman

table d’in alamun isowarsa suke jira nan suka soma kwasan gaisuwa.

Bai amsa ba saima nufan kujeran dake daga tsakiya da yai. Laptop d’in da ya shigo dashi ya bud’e ba tareda ya tanka kowa ba ya shiga danne danne.

Wannan ya kalli wancan wann ya kalli wan

n. Ganin shugaban nasu ya had’asu ya kuma samu isowa sann baice komai ba.

Shiru mintoci suka shud’e kafin ya kaikaito masu da fuskar computer d’in kowa ya na gani.

“This is our new marketing development plan… I suppose..”

Kowa ya jinjina Kai alamun ha

ka ne.

Haidar ya gyada Kansa kafin yaci gaba “Wanda mukai discussing kuma muka b’ata lokaci sosai muna aiki akai in our last meeting.. Haka ne..?” Nan ma gyada kawunansu sukai alamun eh haka ne.

“But unfortunately, we can’t go on with this new strategy..

And do you know why..?” Ya k’arashe cikin tsananin tsarewa yana dubansu d’aya bayan d’aya. Babu Wanda ya iya basa amsa.

Lokaci guda ya jinjina Kai kafin yaci gaba “Sabida bansan ya akai other company suka samu irin wann strategy d’in har suka rigamu appl

ying cikin kasuwancinsu..”

Nan kuma suka soma maganganu k’asa k’asa kowa yana duban d’anuwansa yana mamakin ya hakan ta kasance.

Cikin bud’e murya ya katse k’anan cecekucensu “So tell me now.. who is selling our company..? And I’m pretty sure is someone

from this department.. Kuma yanzu zaku sanar dani yanda akai abinda muka tattaunawa ya fita har wasu company suka samu.!”

Kowa yaci gaba da cewa baida masaniyan yanda akai hakan ta kasance.

Table d’in ya buga da k’arfin gaske. Cikin tsananin b’acin rai

yake furta “Do you even realize the kind of loss we are going to suffer..? What do you want me to tell the board members..! Mai kuke so na sanar dasu..? Let me tell you this..!” Yai maganar yana nunasu da yatsa d’aya bayan d’aya “I don’t tolerate incompet

ency. And I don’t work with traitors. A cikinkun nan zaku nemo mai mana zagon k’asa. Before the day ends.!”

Baikai aya ba sukaji an banko k’ofar zauren taron. Gaba d’aya suka juyo suna duban Wanda ya shigo.

Engr Aliyu Maitama mammalakin Kampanin shine ya

shigo cikin tsananin b’acin rai. Ko la’akari da mutanen dake zauren taron baiba ya k’arasa ya cakumo matashin nan cikin tsananin karaji sai sakin huci yake. Yana k’arasowa bai wata wata ba ya d’auke Aliyu da mari mai kyau.. Yana d’agowa ya kuma Kai masa w

ani Marin Wanda saida ya tsaga masa baki jini ya fita.

Rintse idanunsa yai yana k’ok’arin nitsa zuciyarsa.

Ganin haka yasa mutanen suka soma kokawan ficewa daga cikin zauren. Kowa ya kwana da sanin rashin jituwar dake tsakanin Engr Maitama da tilon D’a

nsa amma zasu iya cewa basu tab’a ganinsa cikin yanayi irin na yau ba.

Engr Maitama ya kuma shafe fuskrsa da tafukan hannayensa yana nuna ma Aliyu fuskar iPad d’in da ya shigo dashi “Ka amsa min.. Menene wann.. What is the meaning of this.?”

Aliyu bai iy

a furta komai ba sai sadda idanunsa k’asa da yai dan yasan haka zai faru tinda shi dai dama a idanun mahaifinsa kullum ba daidai yake ba.

Mahaifinsa yaci gaba “Na zata Kai d’in kasan abinda kakeyi by now.. Na zata bazaka bani kunya ba wann karon.. Na zata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login