Showing 63001 words to 66000 words out of 267381 words
ganin wann al’amari. Kaman yanda Asshe tace da ita akwai dalili ta tabbata akwai dalilin.
**
A can police station kuwa motar ‘yan sanda na shigewa na Hilal ma ya sako kai.
S
auri sauri Hilal ya take mata baya ganin ta nufi hanyar da aka shige da Mama sai kururuwa Maman take tana fad’in wllhi bata ci kud’ad’en ba.
Mama taci gaba da fad’in “Wayyo Khulsum ‘Yata ki cece ni ki ceci Mamanki kar a rufeni. Idan aka rufeni babu mai k
ula da Abbanku dake kwance gadon asibiti Khulsum.”
Khulsum ta samu zarafin dakatar da ‘yansandan ga bak’auye a gefe yana fad’in kwarankwatsa sai an karb’ar masa hakkinsa. Baici nanin ba nanin bazata cisa ba. Takardun bogi suka kawo masa ya saka hannun. Sa
rkin kasuwa yace baisan da zancensa ba. Idan sama da k’asa zasu had’e sai an fitar masa hakkinsa.
Police ya dubi Khulsum yace “Ke kuma fah.?”
Mama tai saurin bud’e murya tace “‘Yata ce. “
Tsananin mamaki sai ya hana Khulsum furta koda kalma. Wai yau M
ama ce ke kiranta da ‘yarta. Ikon Allah, Ashe har akwai ranan da Mama zata danganta kanta da jinin Ummanta. Bata kaiga furta kalma ba ta hango Habib mijin Azeema da police woman d’in da kwanaki suka kawota nan police station d’in. Sai wani mannewa take jik
insa. Mama ganin Khulsum tayi shiru ya sanyata duban yanda Khulsum d’in ke duba.
Ta zaro ido waje tana kuma mutsukesu. Waye take gani haka.? Habibu ne mijin Azeema Sun fito daga wani ofishi yana faman gyara kwalan rigarsa sai washe baki yake ga wata ‘yar
sanda gefe sai kashesa da kallo take kaman zata shige cikinsa. Ta dafe k’irji tana furtawa da k’arfin gaske “Na shiga uku mai nake gani.! Habibu..!”
Hankalin Habibu da ‘yarsandarsa ya dawo kansu.
Mama ta soma nunasa da yatsa “Habibu mai zan gani mai kak
e a nan..? Amanan Azeema kake ci da wann ‘yarsandan.?”
“Madam ki iya bakinki police station kike ba Tasha ba.” ‘Yarsandan ta fad’a cikin dakatar da Mama wacce tai sokoko tana kallonta.
Habibu ya wayance “Haba Mama ya kike magana haka.? Nan fah police s
tation ne. Zuwa nai inata fafutuka ina fad’i tashin yanda za’a samu a kamo mana Tasi’u mana Mama..”
Ya dubi mutanen dake wajen ya kuma dubi ‘yansandan da suka kamota “Meke faruwa a nan.. ya na ganki da ankwa.?”
Sai Mama ta soma kuka “Habibu ka ceceni.. K
amo ni sukai.. Ka fad’a masu waye yaci kud’in shagon Malam. Kai shaida ne wllhi banci ba. Habibu kar ka bari a rufe ni.”
Kaman daga sama suka sinkayo muryar Khulsum “Ni kuma zan bada shaidan kece kika sayar da shagon koda kuwa Kotu za’a je na shirya zuwa.
!”
Mama ta kaikaito tana duban Khulsum “Fitsara zaki min a nan Khulsum.? Inji kin biyo ni ne dan ki taimakeni ki bada shaida kaina.”
“K’warai kuwa Mama. Zuwa nai dan na bada shaida akanki na kuma tabbata kin biya abinda kika aikata wa mahaifina Wanda ya
ke kwance baida ikon kare kansa balle dukiyarsa.”
Mamaki ya cika Hilal. Ya dubi wann ya dubi wancan “Wait. D’an dakata, wai dama ba zuwa nan kikai dan ki taimaki matar nan ba.. I thought I heard you call her Mama or something.. Is she not your Mom.? Ba na
ji ta kiraki ‘yarta ba. Ta ya kike bada shaida mai muni kan mahaifiyarki.. Are you going to let them arrest your mother just like that..? Don’t tell me we came all the way here just for you to make sure anyi arresting Mamanki..”
“Malam kar ka sake kiran w
ann matar Mamata. Ni ba uwata bace. Kuma ka fad’i daidai zuwa nan nai na bada shaidan abinda ta aikata kafin wancan surkin nata yayi amfani da damarsa ya fiddata.” Ta k’arashe tana nuni da Habib dake tsaye gefen budurwarsa ‘yarsanda wacce ya kawo ta kama K
hulsum d’in lokacin da ta mari Azeema.
“Amma nafi uwarki da ta saida ‘yar Malam Isubu yana kwance. Gwara ni shago kawai na saida.” Mama tace tana huci.
Hilal ya kuma duban Khulsum da mamaki Wanda kalaman Mama ya haifar mata da sanyin jiki.
Bakauye ya
kafe sai an rufe Mama idan ba kud’ad’ensa aka lalo aka basa na. Haka dole aka jefata cikin cell Habib na kwantar mata da hankali da fad’in zai iya k’ok’arinsa yaga ta fita.
Khulsum kaw bata kuma fahimtar komai ba tun bayan maganan da Mama ta fad’a mata
. Take taji wani irin kuka na zuwa mata. Tabbas Mama ta fad’i gaskiya gwara ita Akan Umma. Ita abun duniya kawai ta saida amma Umma fah mutum ta saida. ‘Yarta da ya kamata ace ta zamto tamkar lu’ulu’u a hannunta. Abu mafi daraja fiyeda shago da
abinda ke c
ikinsa Umma ta sayar. Ko kusa baza’a had’a laifin Mama da Umma ba. Bata San yanda take jefa k’afafunta ba tafiya kawai take tana kuka. Tana Jin wani abu mai kama da k’iyayya Wanda shine zata iya cewa iyakacin alak’arta kenan da mahaifiyarta.
Tana tafe ge
fen kwalta Hilal na biyeda ita cikin mota. Yaci gaba da fad’in “You know you are unbelievable.. Da nasan Akan wann dalilin kika taho all the way to police station da ban b’ata lokaci na na kawoki nan ba. Because of you na rasa d’aurin auren d’an uwana.”
“
Malam idan baka Kama gabanka ba duk abinda na maka Kai ka saya da kud’inka.. Da ace baka b’ata min jiki ba Watak’ila da ban tsaya na b’ata lokacina wajen ji da kai ba balle har nayi gamo da Mama. Watak’ila da na samu damar dakatar da auren zalunci da ake y
unk’urin yima ‘Yaruwata..”Ta fad’i tana ci gaba da sakin huci ga hawaye dake ci gaba da gangaro mata.
“Blame your step mother then.” Hilal ya bata amsa Kai tsaye.
Khulsum taci gaba da tafiya tana hawaye.
Hilal yai parking ya fito ya tare gabanta “No I
can’t just leave you here. After all, Ni na kawoki nan. Idan wani abu ya sameki I’ll blame myself for the rest of my life. Please get in the car. Ki bari na maida ke yanda na d’aukoki. At least.”
Bata amsa shi ba sai kukan da take ci gaba da yi dan mugu
n takaicinsa take.
Ya d’an waiga yana duban mutane masu giftawa sai kallonsu suke.
Ya d’an kuma gyaran murya “Look, I don’t want people to think that I hurt a girl. Dan Allah ki shiga.. At least ki bani dama na fitar dake daga nan.. Dare ya soma yi duba
ki gani.. And is not safe for you to walk alone a babban kwalta irin haka.”
Cikin kuka Khulsum ke dubansa “Na tsaneka.! Na tsani mugayen ahalinka da sukai amfani da raunin mahaifiyata suka sayi ‘Yaruwata da sunan aure.!”
Hilal ya zuba mata ido “Look, ba
nsan meke faruwa tsakanin ahalinmu ba. But the only abu da zan fad’a Miki shine my cousin is a good person.. He has his faults as human. But I can assure you he’s a good person.” Ya d’an tab’e baki “Idan yar uwarki ta kasance matarsa abun kiyi mata murna n
e.”
Takaici ya hanata furta koda kalma tasa kai tana ci gaba da tafiya. Hilal ya kuma tareta “Yamma yayi sosai ki shiga na kaiki gida. That’s idan Kinaso ki cimma ‘yaruwarki kuyi Sallama kafin a tafi da ita. Dan na tabbata kawo wann lokacin an d’aura aure
n. Tinda bakiyi nasaran dakatar da auren ba. Watak’ila zakiyi nasaran samun dama kuyi Sallama idan har kika shiga mota ta.” Ya k’arashe yana nuni da motar.
Bata k’aunan abinda zai kuma had’ata da d’aya daga cikin wann ahalin. Toh amma gaskiya ya fad’a ida
n batai saurin cimma Addanta ba Watak’ila bazata samu suyi Sallama ba za’a tafi da ita. Saida ta rakasa da harara kafin ta nufi motar.
Hilal ya d’an tab’e baki yana bud’e mata marfin motar “Sorry to say a daidai yanda na d’aukeki zan ajiyeki. Kinga ko ba
komai na rage Miki hanya.”
Ta kula nema yake ya dad’a tunzurata hakan yasa bata kuma bi takanshi ba balle ta amsa shi.
Saidai suna isowa bakin babban kwalta da zai shigar da kai layinsu suka hango motocin amarya na ficewa. Alamun Sun makara amarya ta ri
ga ta hau hanya.
Hilal ya tab’e baki kad’an “Looks like someone didn’t make it on time. Unless zaki bi bayansu.”
“Ajiyeni a nan.” Ta fad’i tana k’ok’arin bud’e motar.
“Are you serious.?” Hilal ya fad’i yana k’ok’arin juya kan motar cikin k’ok’arin bin
bayan motocin.
Da mamaki Khulsum ke dubansa ta kuma jan marfin motar ta jita a rufe alamun ya rufe daga wajensa.
“Malam ka ajiyeni a nan nace ko na maka ihun b’arawo.!”
“You and I both know this is what you want. Kiyi Sallama da ‘yaruwarki. Just admit i
t.” Ya d’an dubeta sai yai murmushi da gefen bakinsa “Don’t worry, I’ll do you a favor and take you to your sister. After all, Nima can na nufa..” Ya maida idanunsa ga kwalta “Kar ki damu ba sai kin biya kud’in abun hawa ba. A simple thank you will be okay
.”
Bai kuma cewa komai ba yaci gaba da tuk’a motan.
Izuwa lokacin ta rasa ma mai zatce ma wann d’an rainin hankali. Shiru tai tana duban titi yanda Hilal taketa fifila gudu da ita.
**
Abuja..
Zaune yai gaban mahaifinsa yana sauraronsa yanda Daddy
yaci gaba da fad’in “I will be meeting with our international clients in Nairobi.. Daga can zan wuce Cape Town, southAfrica gameda business alliance da muka fara a can months back.” Ya gyara zaman glasses d’in dake mak’ale idonsa kafin yaci gaba “Maybe it
will take me two to three weeks before I return..” Ya k’arashe yana ci gaba da duba documents d’in dake gabansa.
Haidar ya jinjina Kai yana duban mahaifinsa “So why are you telling me all these Daddy.? Are you.. Do you want to hear from my own perspectiv
e.? I mean regarding the alliance.?”
D’agowa yai had’ida d’an zame glasses d’insa yana duban Haidar d’in sosai. “I did not send you to those expensive schools dan kawai ka dawo na saka ka a gaba naita kallonka. But unfortunately it is unfolding.. Watak’il
a ba kai bane wann D’an da zanyi alfahari dashi. By now ya kamata ace na huta. Ya kamata ace Kai ke wakiltana a tafiye tafiye irin wann. Saidai Kai d’in banida k’warin gwiwa akanka. It is enough da na amince ka jagoranci project d’in cikin gida..!” Ya kuma
dubansa sosai kafin ya k’arada “You are a complete failure to my name Aliyu!” Ya k’arashe yana maida glasses d’insa.
Haidar yai murmushi mai ciwo yana jinjina Kai “Is this the kind of legacy you wish to leave behind for your Son.?” Ya jinjina Kansa zuciy
arsa na kuma masa d’aci kafin yaci gaba “I wouldn’t be surprised of course. But You know what Daddy. No matter how insignificant you keep insisting I’m to you.. You can’t deny the fact that your company needs me.. And you need me too.. Kuma shine dalilin d
a yasa ka kirani kake sanar Dani duka shirye shiryenka.. So Daddy, deny it all you want. But the truth is that I’m very much important to you.. And your company is nothing.! Absolutely nothing without me.!” Yana ida fad’in haka ya mik’e zuciyarsa na masa z
afi.
A daidai k’ofan fita daga sashen ya had’u da Alhaji Gimba na shigowa. Alhaji Gimba na ganinsa ya fad’ad’a murmushinsa. Bai damu ba idan Haidar bai gaishesa ba. Shi dai bazai tab’a cire hope Akan Haidar d’in ba. Alhaji Gimba yaci gaba da fad’in “Con
gratulations to you and your team. Naji dadin wann al’amari kuma inada yak’inin company bazatayi danasanin zab’en gwarazan da zasu jagoranci wann aiki irinku ba..I trust you and your team.” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba “Wann aikin kampani ne so ina sha
wartanka kar ka bari wani matsala da kake dashi tsakaninka da mahaifinka yasa kai ma aikin rik’on sakainan kashi ko ka yanke hukunci cikin fushi. Na yarda da Kai amma tunasarwa yanada kyau. The company’s future relies on your hand Aliyu. And we have high e
xpectations of you.. Let’s set our differences aside so we can reach our common goal. Ko dan mu ba ma abokan Adawa kunya.” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa.
Tinda ya soma magana Haidar da hannayensa ke sakale cikin aljihu yake dubansa lokaci guda yana
nazarinsa “Trust me, it’s just a matter of time before we find out who the real traitor is.”
Murmushi Alhaji Gimba ya kuma sakar masa kafin yai nuni da parlorn “Baringa mahaifinka. Have a good evening.” Ya fad’i yana mai shigewa cikin parlorn.
Lumshe i
danunsa kad’an Haidar yai had’ida furzar da huci “Fake life fake people. Everything around this family is fake nothing is real.” Lokaci guda yasa kai ya shige cikin sassarfa zuciyarsa na masa wani irin k’una.
Ya fito daga sashen mahaifinsa kenan ya hang
i k’atuwar mota ta shigo cikin gidan shak’e da kaya ta nufi nasa b’angaren. Yabi motar da kallo kafin ya nufi hanyar sashen nasa. Nan ya hangi Mommy da Anisa sai nuna ma masu interior d’in yanda zasu jera kayayyakin suke. Ga tsaffin Kayan duka an fito dasu
.
Yai tsaye yana dubansu da mamaki. Can Anisa ta hangosa. Sai ta matso kusan Mommy tai mata rad’a a kunne “He’s here Mommy.”
Mommy ta d’ago tana tambayan wane kenan. Ganin Haidar ya sanyata fad’ad’a murmushinta. Ta k’arasa da sauri ta kamo hannunsa “Haid
ar my son, today is the happiest day of my life.. An d’aura aurenka yau Haidar.”
Sai yaji abun banbarakwai. Shi ya ma mance da wani batun aure da yarjejeniya. Wani irin duba yake mata irin na da gaske take.? Da gaske auren suka masa sabida son zuciya irin
nasu.
Mommy taci gaba da fad’in “Wann shine Mafarin had’in kan ahalinmu da yardar Ubangiji. Cikin ikon Allah komai zai daidaita.” Bakinta ya gaza rufuwa har mamaki Anisa take yanda Mommy ke matuk’ar d’aukin wann aure. Taci gaba da nuna ma Haidar kayayya
kin “Look duba kaga. I know you have high taste so I ordered everything to your taste.” Ta saka hannu ta tallafo fuskarsa “Yau d’in ina Jin na cika wani gurbi na zama uwa a gareka D’ana. Burin ko wata uwa kenan taga D’anta yakaiga cikan kamala.”
K’ok’arin
cire hannun Mommy daga fuskarsa yake Jin tana wasu irin sunbatu “Mommy will you please stop.! Enough of this drama.” Ya dakatar da ita kafin yaci gaba “Quit the act already! Stop acting like you care.. Like you are responsible.! Like you are doing your mo
therly duties wad’anda kika makara bakiyi ba tun a baya. It doesn’t suit you at all Mommy.!” Ya k’arashe jijiyoyinsa har fitowa suke.
“Haidar.” Ta ambaci sunansa kaman mai shirin kuka.
Dakatar da ita ya kumayi “Mommy you and I both know ba auren tsakan
i da Allah bane. Ba don ci gaban rayuwana matsayina na d’anki kikai ba. You are doing all this for your own advantage.” Ya d’anyi fasali “Mommy my day is bad enough, thanks to my Dad. bazan bari ki k’ara mun wani akai ba.!” Yana ida fad’in haka yasa kai y
a fice daga gidan a gaggauce.
Jiki a matuk’ar sanyaye Mommy ta juyo. Anisa ta k’araso ta taddata.
“Mommy seems like ke kad’ai kike son auren nan a gidan nan. Shin bazaki hak’ura da auren nan ba kawai tinda Wanda akayi dominsa baya so. Kawai ki d’aga waya
ki kira Ammi ki sanar da ita an fasa tin kafin a kawo matar cikin gidan nan. Dan na tabbata wann auren ba mai d’orewa bane.”
Mommy ta harereta “Ke dalla rufe mun baki. Bansan shashanci, Wann aure da kika gani mutuwa ce kawai zata raba matar da Aliyu. Ida
n kinga auren ya Mutu ki tabbata matar ta Mutu ne.!” Tana ida fad’in haka tasa kai ta shige tana neman layin Asshe dan Jin mai ake ciki.
Anisa ta tab’e baki tana mamakin wann irin al’amari.
**
Kano…
Dik maganganun da Hilal keyi cikin motar ba saurar
onsa take ba. Hasalima bazata iya tantance mai yake cewa ba da za’a tambayeta. Damuwarta kawai su isa ga ‘yaruwarta tai k’ok’arin shawo kanta su gudu tinda babu idon Umma. K’aran bud’e gate ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da tai nisa ciki. Zuciyarta
sai tsinkewa yake tana addu’an Allah ya bata ikon shawo kan Addarta Ummul cikin sauk’i. Tana ji a jikinta wann aure babu wani alheri cikinsa.
Hilal yana Ida parking tai saurin kama handle tana kokawan bud’ewa.
Ya tsareta da idanu “Easy kar ki balla min
marfin mota bayan kin b’ata min da tab’o..”
Bata amsa shi ba dan bata da lokacinsa. Tana Jin sanda motar ta fita a lock tai saurin bud’ewa ta fito. Sauri sauri ta nufi cikin gidan har kaman zatai tuntub’e.
Hilal ya bita da kallo had’ida tab’e bakinsa k
ad’an kafin ya nufi bangarensa.
A daidai mashigar gidan Khulsum taji ance da ita “dakata..!”
Cak taja ta tsaya sakamon muryar taji ya dakatar da ita.
Umma ta gani ta tsaya tayi k’ebebe rik’e da kunkumi tana duban Khulsum d’in.
“Umma..!” Khulsum ta f
ad’i mamaki kwance saman fuskarta.
Umma ta jinjina kai “K’warai ni ce nan.!” Tai maganar tana kuma k’obarewa bakin k’ofa.
“Umma.. Me kike a nan..?” Khulsum ta tambaya cikeda mamaki.
“Ke zan tambaya mai kike a nan..? Wani munafuncin ne Ya kawoki..? Awho
kinzo ne ki kashe mata auren Tun kan ta tare ko..?”
Mamaki Ya hana Khulsum furta koda kalma sai duban Umma da take. Da k’yar ta iya furta “Umma a ina uwar amarya ta tab’a yima ‘yarta rakiya d’akin miji.. Haba Umma fisabilillahi,