Showing 177001 words to 180000 words out of 267381 words
silale ta bar shi shi kad’ai.. Ba kowa wajen ma sai shi kad’ai. K’ila Sun shige yin wa
ni abin cikin gidan. Ya dan tab’e bakinsa kad’an.
Amma sai yaga wani hannu na mik’o masa abinda yake nema. Haidar yabi hannun da kallo. Ga mamakinsa Daddy ya gani. Kyakkyawan murmushi saman fuskar mahaifin nasa. Haidar yasa hannu ya amshi board d’in had’i
da godiya ma Daddy. Jinjina Kai Daddy yai. Sai Haidar yaga Daddy na nad’e hannun long sleeve shirt din dake jikinsa alamun zai tayasa.
Sai Haidar ya girgiza Kai “No Daddy you don’t have to.. Ya kamata kaje ka zauna.. I.. I’ll serve you some.” Ya fad’i aw
kwardly dan abu ne da bai saba faruwa ba koma bai tab’a faruwa ba tsakaninsu.
Murmushi ne saman fuskar Daddy ya dafa kafad’an Haidar din “No Son, let’s do it.. Together.”
Haidar yai murmushi yana tuna lokacin yarantarsa wann shine mafarkinsa. To make me
mories with both his parents… To strengthen their bond. Ya samu kusanci sosai da mahaifinsa. To have some quality time together.. To build something together. To play sports, video games, go horse riding da dai sauransu. Sai ya murmusa yana duban mahaifin
nasa sosai. Kaman mafarkinsa ne yake zama gaskiya. Yana k’ok’arin yanka naman saman board din Daddy ya dafa hannunsa wana hakan Ya dakatar da Haidar. Suka dubi juna sai Daddy yace “Be careful Engr, this is not a construction side.”
Su duka sai suka d’an d
ara kad’an. Daddy yace “You know Son, if I were to turn back time.. Da munyi aiki tare hand in hand.. Like professional Engrs.”
Jikin Haidar Ya d’anyi sanyi Ya fahimci abinda sukeyi a yanzu d’in Ya K’wadaitar ma mahaifinsa inama lokacin da sukeda damar ka
sancewa tare a company sunyi ayyuka tare tare babu tsangwama babu hantara. Gashi yanzu Ya sanar da mahaifinsa Ya aje aikin company meaning ba lallai su sami irin wann damar ba. Muryar Daddy ya kuma sinkaya “Bana so na tak’uraka. Da na rok’eka wani alfarma.
”
Haidar yai saurin girgiza kai “No Daddy.. Ka wuce wann.”
Daddy ya murmusa “Haidar, I can understand you, if you… don’t want to manage the project due to.. your personal priorities.. But please kar ka aje aikinka.. Kar ka bar Kampanin… Let this be the l
ast abu da zan buk’ata ka mun.”
Haidar yai saurin girgiza kai “No Daddy, I’m your son.. Hakkina ne matsayinka na mahaifina nayi maka biyayya cikin abinda bai sab’a ma mahaliccina ba. Kuma wann bazai zama abu na k’arshe da zan maka ba. Umarni kawai zaka ba
ni a koda yaushe.. Kuma na maka alk’awari bazan aje aikina ba in sha Allah. Bazan bar company ba. Together we will take the company to greater heights.!” Ya k’arashe da murmushi saman fuskarsa.
Sai Daddy ya kamo k’afafunsa Ya rungume “Thank you son. Alla
h ya maka albarka.”
A haka Mommy ta k’araso wajen ta iskesu. Farin cikinta ya ninku. Itakam a halin yanzu tana jin babu sauran abinda zata nema da ya shige taita gode ma Ubangijinta da ya cika rahamarsa ga ahalinta.
Bayan cin abincin suna zaune itada H
aidar a parlor. Haidar ya kuma murmusawa ya dubeta “You know Mommy, After all these years it's today that I feel like… I'm part of the family.”
Mommy ta rik’e hannayensa cikin nata. Kyakkyawan murmushi saman fuskarta “We gonna have some family bondings t
o makeup for all the time we've lost… Kuma.. Zamu fara da shagalin bikinka. Aurenka da Ummul ta cancanci biki na gaske irin na ‘yan gata.”
Ya dan girgiza Kai yana murmushi “Mommy na kasa yarda bisa yarjejeniyar Wata uku na amince da auren Khairy.. Dan kaw
ai Daddy ya bani wann project d’in.”
“Shiii.” Mommy ta dakatar dashi “Babu wann maganar Haidar.. An rufe shi har abada. D’ago baya irin haka baida wani amfani. Bazaka sanar da Ummul wani abu mai suna auren yarjejeniya ko AUREN WATA UKU ba.”
Sai ya d’an
dubeta can k’asar zuciyarsa yana jin zuciyarsa ta katsa samun natsuwa har sai ya sanar da ita.. Sabida a halin yanzu Aure yake so ya gina da ita bisa zallan gaskiya.
Ya d’an dubi Mommy “Mommy I want to build my marriage with her base on trust and transpa
rency. Bana so daga baya tazo ta fahimci cewa na aureta ne bisa yajejeniya zuwa wani k’ayyadajjen lokaci. I want her to hear it from me first kafin taji daga wani waje.”
Mommy ta jinjina Kai “Na fahimceka Haidar.. Amma kafin nan ka d’an dakata har a gama
wann bikin tariyarku can gidanku da na saka nan da kwanaki biyu kacal. Idan yaso sai ka sanar da Ummul yanda al’amarin ya kasance..”
Sai ya d’anyi jim kafin kuma ya jinjina Kai a hankali “Shikenan Mommy. Idan hakan kike so.”
Ta murmusa cikeda jin dad’i.
Burin ko wasu iyaye shine su samu ‘ya’ya masu biyayya a garesu. Lallai mai rai kar ya cire tsammani daga rahamar Ubangijinsa. Who would’ve thought za’a zo lokacin da Haidar zai d’auki umarnin mahaifyarsa ba tareda jayayya ko nuna k’in amincewa ba.? Ya ke ‘
Yaruwa da Allah ya Miki jarabawa da D’an da kika haifa, kar ki tab’a yanke k’auna daga rahamar Ubangijinki domin kuwa shid’in rahamarsa mai yalwa ne. Kar ki karaya, kici gaba da mik’a lamuranki ga Ubangiji. Duk Wanda Allah ya zama majib’icin al’amarinsa sh
i keda babban rabo.
Haidar ya mik’e da zummar mata sallama ta dakatar dashi.
“Yauwa nace ba sai abu na gaba..”
Haidar ya jinjina kai yana sauraron Mommy.
“Kanaji.. Ummul zata dawo nan sashena da zama har sai anyi bikin an kai maka ita.”
Wann karon z
aro ido yai kaman wani abin tausayi ya langab’e kai “Haba mana Mommy does it have to be this way.. I just came out of hospital fah..I’m still a patient.”
“Mommy ko kin daina tausayina ne.” Ya kuma fad’i a marairaice.
Dariya yaso bata amma ta gimtse tace
“Ba tausayinka na daina ba. So nake kai d’aukin d’iyata idan an kai maka ita.. Waima dakata shin kai ka biya sadakin nan ne.?”
Haidar ya sauk’e ajiyan zuciya kaman wani maraya “Shikenan Mommy.. Saida safe.. Amma please a k’yaleta ta kawo min coffee.”
“
Naji… Just coffee..” Tai maganar tana jaddada masa. Ta k’arada “Jeka Allah bamu alkhairi.”
Haka ya fice duk jikinsa ba kuzari. Shi fah maganar gaskiya wann gadara da Mommy take masa da mata akan sadaki ya fara isansa. Shidai kawai gwara ya biya Mommy sada
kinta ya huta.
Bayan ficewar Haidar shiryawa tai ta nufi sashen Daddy.
A parlor ta iske shi. Daddy ya dubeta da mamaki. For days yana k’ok’arin shawo kanta daga fushin da take dashi sai gashi yau ta kawo kanta har yanda yake. Murmushi yai cikin zuciyar
sa yake ayyana lallai sai a bar uwa da D’anta. D’anta shine rauninta.
Ta k’araso kanta a k’asa. Kaman mai shirin zama sai kuma ta silale gabansa. Ta kifa kanta tana hawaye. Cikin rawar murya irinta mai kuka take fad’in “Engr ka yafe min.. Ka yafe mun duk
abubuwan da nai maka.. Na shekarun baya da na kwanakin nan..” Kuka ya hanata ci gaba da magana. Daddy ya duk’a shima suna fuskantar juna. Sai ya rungumota zuwa jikinsa. Kamar wacce take jira kukanta sai ya k’aru. Shima ya saka d’an yatsarsa ya goge kwalla
n da ya mak’ale masa cikin ido.
“Is Ok Kwaise. Ya isa haka.. Dukanmu ‘yan adam ne masu kuskure. Mafiya alkhairi sune masu tuba. Bayan tsawon shekarun nan idan akwai Wanda yafi cancanta ya nemi yafiya ni ne. I supposed to be the head of this family.. Amma
duk sai na bar Miki nauyin.. Kece kika jajirce Akan wann ahalin Kwaise.. You never give up despite the challenges.. Kin tsaya Akan k’afarki ganin cewa ahalinki bai watse ba. Kinyi abinda ni na kasayi Kwaise.. Thank you for not giving up on us..” Murmushi n
e gauraye da hawaye saman fuskarsa. Sai suka rungume juna wani kukan na kuma zuwa ma Mommy.
**
A b’angaren Haidar kuwa koda ya koma sashensa zama yai shi kad’ai a balcony d’insa yana tunanin rayuwarsa. Da yanda shigowarta cikin rayuwarsa Ya canza komai
lokaci guda cikin ikon Allah. Yana jin wani shauk’i can k’asar zuciyarsa Wanda bai tab’a jin hakan ga wata mace ba. He wants to build something special with her.. base on trust and transparency wanda hakan ke nufi dole ya sanar da ita wasu abubuwan daga p
ast d’insa musamman abinda ya danganci personal rayuwarsa. Aurensa da Dareen Wanda ko family d’insa basu sani ba har ya faru ya k’are da kuma yanda nasu auren da ita Ummul d’in Ya kasance. Yarjejeniya sukai da mahaifiyarsa zata shigo rayuwarsa a matsayin m
atar wata uku dan kawai Ya mallaki project d’in da yai niyyan tarwatsa mahaifinsa dashi. Ya lumshe idanunsa a hankali yana furzar da huci.
Shigowa Ummul Tai rik’eda kofin coffee da ya buk’ata a hannunta. Ta mik’a masa cikeda risinawa.
Ya amsa yana mata
godiya. Sai ya nuna mata gefensa “Come sit here... let’s talk.”
Haka kurum taji gabanta ya fad’i sai ta d’an girgiza kai kad’an “Magana kuma.?”
Haidar ya jinjina Kai bayan ya sipping coffee din “Kar ki damu yau magana zamuyi ba akan kowa ko komai ba... M
agana ce akanmu.. Let’s talk.. about us.” Ya k’arashe yana kashe mata ido d’aya gajeren murmushi saman fuskarsa.
Bugun zuciyarta Ya dan karu musamman da taga yanda yake binta da kallo. sai ta k’arasa a d’an sanyaye ta zauna a yanda Ya nuna matan.
Dak’i
k’ai suka d’an shige kafin Haidar Ya aje coffee din dake hannunsa bisa teburin gefensa. Ya gyara zamansa Ya karkato sosai yana facing dinta gwiwarsu na gogar juna.
Sai ta d’an sadda idonta kad’an ganin irin yanda ya tsareta. Hannayensa ya d’aura saman na
ta dake bisa laps dinta.
Ummul ta dubi hannayensa da Ya d’aura bisa nata dake bisa cinyarta. Sai ta d’ago ta dubesa a d’an sanyaye.
“Khairy..!” Ya ambace sunanta kaman yanda Yake kiranta.
“You came into my life to make it better.. You’ve changed all
areas in my life..” Ta dube shi sai ta dan murmusa “Bani nayi ba duka yin Allah ne..”
Ya jnjina kansa “Kece sanadi...” Yaci gaba da jinjina Kai hannayenta cikin nasa “I.. know there’s still a lot.. to do.. But you showed me the way Khairy..” You made me
want to be a better son… You made me wanna wake up and reflect. You made me wann be.. a better business man, take my brand far.. And above all, you made me believe,.That I can be a better person. Thank you.. For coming into my life.” Ya k’arashe labarin na
neman sauya direction.
Jiki a sanyaye ta soma k’ok’arin zame hannunta sabida zuciyarta dake bugawa cikin sauri.
“Dare yayi.. Ya kamata ka kwanta ka huta… Kaifa patient ne.”
Ya kamo waits dinta ya zaunarta saman laps d’insa. Cikin sigan rad’a yake fad
’in “Wa yace miki ni patient ne har yanzu.? Bari ma na nuna miki na warke.”
Ta zaro ido tana k’ok’arin turasa “Kaga.. Ni tafiya ma zan..” Bata kai aya ba ya rufe bakinta da nasa.
SameenaAleeyou
📚
*AUREN WATA UKU..!*
*46*
*©
️
Sameena Aleeyou…✍
🏽
*
Da kyar ta samu ya k’yaleta yai mata rakiya har k’ofan parlorn Mommy. Suna isowa ta zame jikinta daga nasa. Sai ya mik’a mata k’aramar paper bag d’in dake hannunsa.
Ta d’an girgiza Kai “Ta mecece.?”
“Don’t open it yet sai kin shiga.” Ya fad’i yana
kashe mata ido d’aya . Bai kuma tsayawa sauraronta ba ya soma tafiya yana waving dinta kaman kar ya tafi ya barta.
Ta girgiza Kai kurum tana binsa da kallo a haka har ya shige.
Anisa tana nan ta kasa ta tsare tana jiran dawowarta dan kusan komai Akan
idonta ya faru.
Sam Ummul batasan da mutum a parlorn ba sai muryar Anisa da ta sinkayo. Batada lokacin sauraron maganganun Anisa hakan yasa tuni tasa kai ta nufi upstairs ba tareda ta tsaya sauraron maganganun Anisa ba. Amma sai Anisa ta bud’e murya tace
“Auren Haidar Maitama might seem to you like a golden opportunity na samun nasarori da Jin dad’in rayuwa.. Musamman duba da irin rayuwar da kika baro cikinta… But what if, this golden opportunity comes at a very high price.?”
Ummul taci gaba da k’ok’ari
n dannar kanta. Dan a yanda ta tsara ba a wann lokacin zata fuskanci Anisa ba. Ta gama shirya lokacin da zata tunk’ari Anisa da kalamanta. Sai ta bud’e lumsassun idonta a hankali taci gaba da tafiya ba tareda ta juyo ta dubi Anisa ba.
Anisa ta take mata
baya tana ci gaba da fad’in “Abinda yasa kikaga na dage miki Ummul dan inada gaskiya ne. Bana so ki saki jiki cikin auren da zakiyi danasani a gaba. Kuma ciwon ‘ya mace ta ‘ya mace ce.. Ba komai cikin wann auren face k’ask’anci.”
Ummul ta dubi Anisa da mu
rmushi saman fuskarta. Sai kuma ta maida k’ofan d’aki ta rufe ba tarda tace komai ba. Dan Sam bazata bari ta b’ata shirinta ba.
Anisa taci gaba da sakin huci dan ta tsani wann silent treatment din da Ummul ke bata dan bata mance karonsu da Ummul d’in ba.
Tasan she’s sharp and smart dik yanda akai wann shirun da take tana murmushi wani abin take shiryawa tinda Tasha lalata mata shiri ba d’aya ba. Taci gaba da sakin huci ita kad’ai.
Ummul tana shigewa d’aki ta lumshe idonta tana karanto addu’o’in samun sauk
’i da sukuni cikin zuciyarta dan sosai take Jin maganganun Anisa har cikin k’ahon zuciyarta da b’argonta.
Ta isa saman gado ta zauna gijif sai ta dubi ‘yar jakan da Haidar ya bata. Ta soma k’ok’arin bud’ewa.
Nan taga wayar salula ce ta yayi mai d’ankaran
kyau. Da alama komai an saka cikin wayar. Kaman daga chaji har zuwa simcard.
Taita juya wayar kafin ta kunna. Sak’o ne ya fara mata Sallama _I've bought a new book.. and open a brand new page… together with you_
Taita karanta sak’on yayinda jikinta ya
kuma mutuwa. A b’angare na kunnenta guda kalaman Anisa ke mata yawo a d’aya b’angaren sak’on Haidar cikin yanayin muryarsa na mata yawo. Ta rasa wanne d’aya zata saurara sai ta toshe duka kunnuwanta biyu kuka na zuwa mata. Ganin koke koke da tunanin bazasu
fishheta ba kawai sai ta mik’e ta d’auro alwala ta soma Kai kukanta ga Mabuwayin Sarki da babu kaman shi.
Tana bisa darduma tayi lamo tana duban wayar kira na shigowa Wanda tasan kiransa ne tinda lambarsa ne kawai kan wayar. Bata bi takan wayar ba haka
akaita kira har dai ya hak’ura. K’arshe ya tura sakwanni Wanda suma batabi takansu ba.
Duk Haidar sai ya damu ya fara tunanin ko bataji dad’in kyautar da yai mata bane. Kodai ya mata wani abin ne.
Washe gari da safe Fashion designer tazo har gida da man
yan bridal dress catalog dan amarya Ummul ta zaba yanayin rigar da za’a mata. Anisa ita ke tayata zabe. Ummul sai duban Anisa take tana mamakin wai wacce ke mata gargadi da kashedi da auren Haidar sai gashi itace mai zakewa wajen zaba mata Kayan da zata sa
ka.
Aka nuno wani farin gown mai dankaran kyau Anisa tace “Yauwa perfect. I think this one is ok.”
Kaman daga sama suka sinkayi wann muryar nasa daga bayansu “This is too revealing.. My wife can’t wear this.” Ya fad’i cikeda gadara hannayensa sakale ciki
n aljihun jeans d’insa yasa kai ya shige upstairs gaida Mommy ba tareda ya dubi ko yanda Ummul d’in take ba. Ta bisa da kallo duk jikinta a sanyaye. Toh ko dai fushi yake da ita sabida yayita kiranta a Daren jiya bata d’aga ba har sakwanni ya turo bata ams
a shi ba. Gaba d’aya sai taji babu dadi.
Anisa na hankalce da ita da Haidar d’in. Lokaci guda tana mamakin wai Haidar ke cewa kaya is too revealing dik girma da tasowa cikin gogaggun wayayyu da yai. Lallai ta yarda ya fara nisa cikin soyayyar wann Bagidaj
iyar. Idan batai sauri ta rabasa da wann Bagidajiyar ba haka zata maida mata Haidar d’inta Bagidaje irinta.
Haka har aka gama zaben rigunan ita dai bama tace ga rigar da aka tsaida ba. Duk tunaninta na kan Haidar.. Bata san ta damu da fushinsa har haka b
a. Abinda yafi bata mamaki shine ko ta kanta bai sake bi ba.. Bai nemeta bata ma sake saka shi a idonta cikin gidan ba. Ta d’auki wayar kaman zata kira layin sa amma sai ta kasa. Haka kaman wasa har ranan da ake saka ran ranan ne Mommy ta tsaida dan shagal
in bikinsu bata saka Haidar idonta ba. Wani abinda ya k’ara bama Ummul mamaki shine Anisa batai k’asa a gwiwa wajen shirya komai ba. Ita Mommy tasa ta kaita saloon aka gyara mata gashi sann ta d’auko mai lalle da makeup artist har gida. Kaman wata maid of
honor haka Anisa ta zak’e tana mata komai. Ummul bata daina karantarta ba.
Cikin wata farar doguwar riga da dinkin ya zauna jikinta ta shirya. An mata dauri na zamani da irin fabric d’in rigar Wanda da gani zaka san an b’arar da kudi wajen sayensa da d’i
nkasa. Ba’a cika mata kwalliyar ba amma tayi kyau har ta gaji. Duk Wanda ya kalle ta sai yaso sake kallonta. Haka masu kwalliyan da shiryata sukaita santin kyaun da tayi. Ita dai Ummul gaba d’aya ranan ta kasa gane kanta gaba jinta take ba daidai ba. Somet
hing feels wrong. Sai kawai ta danganta hakan da fushin da Haidar keyi da ita.
Koda akace ta fito su d’auki hoto da Haidar sai rashin nutsuwar da take ciki ya ninku.