Showing 90001 words to 93000 words out of 267381 words
banida ikon taka yanda yake.
Muryar Tani ya kuma katseta cikin karaji sanda ta soma janyo Umma tana fad’in “T
ashi ki tafi Suwaiba. Ki tashi nace ki tafi kuma kar ki sake takowa yanda nake.!”
Kuka Umma take tana girgiza kai “A’a Yaya.. Dan Allah ki saurareni.. Wllhi ko d’aya banzo nan dan abubuwan da kika zayyano ba.. Yaya ki saurareni..” Sai Umma ta rungume Tani
tana kuka.. Su duka biyun kuka suke Wanda yafi kama da kukan nadaman rayuwa.
Mama ta fincike jikinta daga rik’on da Umma tai mata. Zata sa kai ta shige Umma ta kuma rik’o hannunta “Yaya dan Allah ki saurareni.. A halin yanzu bamuda kowa sai mu biyun..”
Mama Tani ta goge hawaye da bakin zaninta Wanda yai duk’un duk’un “Yayane Suwaiba..? Ki sanar Dani yayane..?”
Umma ta goge hawayenta da bakin mayafi “Yaya yanzu ba lokaci bane da zamu rik’e juna abokan gaba. Lokaci ne da zamu fahimci dukkanmu masu kusku
re ne.. Kuma Allah yana sonmu da ya nuna mana kura kurenmu tun a nan gidan duniya.. Saura ya rage namu mu d’auki darasi ko mu bijire.”
Jikin Tani ya kuma yin sanyi wasu hawayen na zubo mata yayinda Umma taci gaba “Yaya babban abinda ya jefa mu cikin halin
da muka tsinci kanmu shine son kanmu, rashin tawakkali da yin abu dan mu burge mutane Wanda Har yasa mun mance su waye mu. Mun mance auren mu, mun mance ‘ya’yanmu da Allah ya dank’a mana amanarsu. Mun mance mijinmu da yakeda girman hakki akanmu.. Sabida so
n zuciya irin namu.. Mun mance mu masu kiwo ne kuma za’a tambayemu bisa abinda aka bamu kiwo.. Yaya duk mun mance wad’ann mun saka son zuciya a farko.. Wanda shi ya kai mu ga halinda muka tsinci kawunanmu.” Ta kuma jinjina kai tana hawaye “Watak’ila Ummul
tayi aure.. Amma ba irin auren da naci mata buri ba.. Dije ta rabani da Khulsum kaman yanda ta rabani da mijinmu.. Nida ke bamuda wani maraba Yaya. Yanda kike rufe a nan babu walwala nima a b’angare na haka take.. Kullum ina kulle ne cikin d’aki Babu walw
ala.” Ta kuma share hawayenta yayinda Tani ta katseta “Wani irin aure ne Ummul Tai Wanda baki ci mata buri ba Suwiaba.?”
Tambayar da ya haifar ma Umma fad’uwan gaba. Koda Ummul AUREN WATA UKU Tai bazata so ta sanar da Tani ga irin auren ba. Hasalima baza
ta iya ba. Batada wann k’warin gwiwar.
Girgiza mata kai tai “Ki yarda dani Yaya na tapka babban kuskure..” Tai maganar cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.
Mama ta jinjina kai “Na yarda da duka abubuwan da kika fad’a Suwaiba.. Mun tapka kuskure..
Kuma idan bamu had’e kawunanmu yanzu ba bazamu tab’a k’wato mijinmu daga hannun Dije ba. Tazo Har nan ta min d’iban albarka ta kuma jaddada min tinda naci amanar d’anuwanta dake kwance nida fita a gidan yari sai Randa jakin Baba yayi k’aho. Zata tabbata ba
n samu wani k’ofa da zan tsira ba. Sann yarana sun guje ni. Salima ce kawai ke zuwa nan ta dubani. Amma Azeema da Badia Wanda nake gark’ame nan sabida su sun wofantar dani Suwaiba..” Ta kamo hannayen Umma “Suwaiba dan girman Allah ki taimaka min kafin a ta
fi Kotu. Sunce cikin satin nan za’a shiga Kotu da mutumin k’auye mai kudi. Dan girman Allah Suwaiba ki taimaka ki nemo kud’d’en nan a fitar dani.. Naga Sirakan Ummul masu hannu da shuni ne. Ki taimaka min Suwiaba ko wajensu kije ki nemo kud’ad’en nan ki f
itar Dani a nan..” Ta k’arshe tana tsare Umma da ido. Zuciyarta na tabbatar mata hanyar da zata bi kenan ta samu ta fita daga wann tuggun. Ta nuna ma Suwaiba nadamarta a fili Har dai Suwaiban Tai mata hanyar fita..
Dum!! Haka k’irjin Umma ya buga dan ita
kanta bata isa tace ga kalan sirakan Ummul ba. Uwa uba rabuwar da sukai da Asshe Wanda Asshe tai mata iyaka da gidanta.
Tani ta tsare Umma da ido. Cikin zuciyarta take ayyana tinda na sauko da kaina Suwaiba dole kimin abinda nake so. Ta haka ne kawai zan
samu na fito har na fahimci mai kike b’oye min gameda auren Ummul.
“Ke nake sauraro Suwaiba, zaki min wann alfarmar.?” Mama tace tana tsareta da ido.
Zuciyar Umma ya kuma tsinkewa. Ta d’ago tana duban Mama cikin sanyin jiki…
SameenaAleeyou
📚
*AUREN WAT
A UKU..!*
*27*
*©
️
Sameena Aleeyou…✍
🏽
*
Umma ta girgiza kai a hankali “Kiyi hak’uri Yaya.. Bazan iya Miki alk’awarin komai ba a halin yanzu.” Tai maganar ba tareda ta iya duban fuskar Mama Tani ba.
A dak’ile Mama ke dubanta “Suwaiba.. Kina
nufin bazaki taimake ni ba..? Kenan kema kin zab’i a tura ni kurkuku kaman Dije.?”
Umma tai saurin d’ago kai tana girgizawa alamun a’a.
Tani ta gyara zama “Toh idan ba haka ba yaya ne.? Bakida wani maraba da Dije Suwaiba.. Banyi zaton haka daga wajenki b
a Suwaiba..” Sai ta fara hawaye “Bayan ke banida kowa Suwaiba.. ‘Ya’ya na Sun guje ni.. Mijina na kwance jinya ta cinyesa.. Ke da nake zaton zamu taru mu rufa asirin juna kema kin juya mun baya Suwaiba.?” Sai ta fashe da kuka tana fad’in bata zaci haka dag
a Umma ba.
Lokaci guda Mama ta mik’e tana huci “Tinda haka kika ce Suwaiba.. Shikenan kije abinki.. Kije kici arzikin sirakanki ke kad’ai. Ni kuma in sha Allahu babu ni babu Ke Suwaiba. Kar ki sake tako inda nake idan har ba taimako na zakiyi ba.” Tasa k
ai zata shige Umma tai saurin mik’ewa ta tareta “A’a Yaya. Dan Allah kar kice haka.. Ni ahalin yanzu banida kowa nima sai ke. Bamuda kowa sai mu biyun.. Amma..”
Katseta Tani tai “Amma me Suwaiba.?” Tai maganar tana tsare Umma da ido.
Gaba d’aya Umma ta
daburce bata San mai zata sanar da Mama Tani ba. Bata san ta yanda za’ayi ta sanar da ita cewa itama ta riga ta k’are mata ba. Tai saurin jinjina kai “Toh. Toh.. Yaya.. In sha Allah zan nemo hanyar da zaki fita..”
Mama ta jinjina kai “Yanzu naji batu Suwa
iba. Kar ki mance fitowa zanyi muyi yak’in k’wato mijinmu daga hannun azzalumar ‘yar uwarsa wacce babu komai cikin zuciyarta face burin fansa dan nayi imani ba tsakani da Allah Dije ke ma Isubu jinya ba. Shi kansa yasan halin Dije Shiyasa tun yanada lafiya
ya mata iyaka da yanda yake. Ko dan wann Suwaiba bazamu bari Dije ta rab’esa ba. Ki nemo kud’ad’en bak’auye a biyasa na fito mu k’wato mijinmu uban ‘ya’yanmu. Ta haka ne kawai ahalinmu zai kuma samun daidaito. Kin fahimta.”
Umma tai Shiru kaman mai nazar
i sai kuma ta shiga jinjina kai “Na fahimta Yaya. Nima zanso muyi jinyar mijinmu mu samu ladansa. Kuma kuskure ne mun riga Munyi amma munyi nadama. Kuma Allah mai afuwa ne mai yawan gafara.”
“Yauwa dai Suwaiba ko ke fah. Nasan kinada fahimta Shiyasa munaf
ukai basu tab’a samun nasaran shiga tsakaninmu ba. Ni ‘yaruwa na d’auke ki Suwaiba ba kishiya ba. Kuma ‘yan sa’insa da sab’ani da muke samu a baya zama ne Ya kawo haka. Dama shi kansa rayuwar zo mu zauna ne zo mu sab’a. Harshe da hakori ma suna samun sab’a
ni ballantana mu ‘yan adam.”
Umma ta jinjina kai “Haka ne Yaya. Zanyi iyaka kokari na in sha Allahu. Allah ya mana jagora.”
Mama ta murmusa had’ida amsawa da “Yauwa yanzu naji batu Suwaiba. Ina nan ina saka tsammani. Na d’aura duka yardana akanki Suwaiba
.” Ta k’arashe cikin yanayi na tausayawa.
A hankali Umma ta jinjina kai duk jikinta a mace haka sukai Sallama da Tani. Tana ficewa Tani ta kece da dariya. A fili take furta “Saidai ba Suwaiba matar Malam Isubu ba. Muje zuwa, da kanki zaki fiddani ni kuma
na fidda ‘yar naki a gidan auren nata. Tinda ‘ya’yana basu zauna d’akin miji ba naki ‘yarma bazata zauna ba. Abun yazo gidan sauki dan da alama akwai abinda kike b’oyewa gameda auren. Bazan yi k’asa a gwiwa ba har sai na shak’a iskar ‘yanci dan na cimma bu
rina.” Ta kuma murmusawa daidai sanda wata ‘yar sanda tazo maidata cell dinta.
Umma tana tafe tana lazimi da tinanin ta yanda zata b’ullo ma al’amarin Tani. Zatai iyaka yinta dan ta taimaki Tani tinda ta tabbata idan yau mijinta ya farka Ya gansu sun had’
e kawunansu kuma sunyi nadaman duk abubuwan da suka aikata a baya zaifi kowa farin ciki kuma Watak’ila fushin da yake dasu ya gushe. Watak’ila hakan ya zama silan yafe masu duk wasu kurakuren da sukai sanda yake kwance. Toh amma ina ta nufa..? Ina zataje .
? Wajen waye zata je ta samo kud’ad’en da za’a fidda Tani.? Asshe kawai ta fad’o ranta. Dan idan ba Asshen ba bata kuma san wajen waye zataje ba. Toh amma sanin irin rabuwar da sukai da Asshe sai ya kuma haifar mata da sanyin jiki. Asshe ta bada umarni ma
masu tsaron gidanta cewa ko mai kamanninta suka gani kar su bari ta shiga. Uwa uba had’e kan da Dije da Asshen sukai mata kafin a tafi da Ummul. Ta tabbata idan Har Dije ta k’ulla aminta da Asshe zuwa wajen Asshe had’ari ne. Dan idan har Dije ta fahimci Ma
tan Isubu Sun had’e kai. Wato ita Suwaibar da Tani wani sabon wuta zata kunna masu. Snn abinda take k’ok’arin b’oye ma Tani gameda auren Ummul kuma shikenan ya tashi daga sirri. Dan tayi imani Dije bazata so taga wann had’in kan ba Wanda yake nufin rugujew
ar shirin duk wani fansarta akansu. Dole tai taka tsantsan. Dole tabi komai a tsanake idan har tana so ta taimaki abokiyar zamanta Tani ta fita daga kurkuku. Da wann tunanin ta sallami mai adaidaita ta shigo gida. Saidai tana shigowa abinda Tai karo dashi
ne Ya mugun bata mamaki. Dije ta gani tsaye tsakar gidan ga kayan abinci da kwanaki Suwaibar ta kawo lokacin sunayi da Asshe lokacin yak’in auren Ummul jirge gaban Dije ta kirawo yara tana fad’in maza su fidda mata kayayyakin su kai mata cikin adaidaita da
ke jiranta k’ofar gidan.
Umma ta saki baki tana kallon ikon Allah “Dije.. Lafiya mai nake gani haka..? Ina zaki kai mana kayan abincin.?”
Kallonta Inna Dije Tai daga sama zuwa k’asa “Makauniya ce ke.? Bayan shahshanci kuma idonki Ya rufe ne Suwaiba.? Taf
iya dasu zanyi. Tinda na tabbata da kud’ad’en da kika saida d’iyar D’anuwana kika sayi kayan abincin nan. Ko ma ince su suka baki. Kaman yanda kika sani da zaran an sallamesa daga asibiti ko gidan nan bazai taka ba balle yayi karo da wani tashin hankalin d
a tsautsayi. Dutse zan wuce dashi ya samu hutu da jinya a can. Kayan abinci kuma zamu buk’ata.” Ta k’arashe tana d’aura ma yaro guda kwalin taliya akai.
Umma ta girgiza kai “Amma Dije mai zamuci.? Kar ki mance ba ni kad’ai ce a gidan nan ba. Akwai Badi’a
sann akwai Azeema. Idan kika kwashe komai mai zaki barmu dashi.?”
Dariya Inna Dije tai harda shewa kafin tace “Lallai Suwaiba. Yau kece mai fafutakan abinda yaran Tani zasu ci.? Saikace ba kece Tani ke hana naki yaran abincin da ubansu Ya kawo ba. A cewa
rta bazata girka ma k’artan banza Wanda suka ki aure abinci ba.? Ikon Allah sai gashi yau ke Suwaiba kece kika nemo abinci kika ba ma yaran Tani da suka k’i zaman aure harma girka masu kike. Yaran da ko ganin mutuncinki basayi. Lallai na yarda kin tabbata
shashasha Suwaiba.”
Umma ta girgiza kai “Dije rayuwar duka nawa take. Ciyar da rai lada ne dashi balle ‘ya’yan mijina Wanda jarabawar rayuwa ya fad’a kansu suka baro gidan mazajensu. Babu mahaifinsu a gidan Babu mahaifiyarsu. Gatansu Allah sai ni kad’ai d
a na rage masu cikin gidan kuma in sha Allahu bazan wofantar dasu ba. Idan Allah ya bani dama da iko na zama mahaifiya a garesu zan zama. Idan ban samu daman gyara kura kuran da nai a baya kan nawa ‘ya’yan Ummulkhairi da UmmuKhulsum ba zan kwatanta gyara
akan Azeema da Badia cikin yardar Ubangiji Dije. Ki kirani da duk sunan da kikaga dama amma in sha Allahu ni Suwaiba bazan sake maimaita kura kuren da nai a baya ba.”
Inna Dije ta murmusa ta matso kusan Umma sosai “Idan dai Tani da iyalanta ne gaki gasu.
Sai ki fita ki nemo ki dafa ki basu. Idan ma aikatau zakiyi ki nemo masu wann ke ta shafa. Amma kinga wann abincin Ya haramceku daga ke Har su.” Ta k’arashe tana sunkuman kwalin taliya. Kaman daga sama taga Azeema da Badia kanta ko wacce tana sakin huci. S
higowarsu gidan kenan.
Azeema ta nuna mata kwalin taliyar “Ajiye.” Ta fad’i cikeda gargadi.
Inna Dije ta dubeta da mamaki “Ke Azeema ni zaki ma rashin kunya.”
“Zaki ajiye ne ko zaki jira na tayaki ajewa.” Cewar Badia tana shan d’amara.
Inna Dije ta sa
ki baki da mamaki “Ke Badi’a.. Ni zaku ma d’iban albarka ina kanwar Ubanku.?”
“Allah yasa k’anwar uban kikace ba uban ba. Rashin kunya kuma ai mai sauk’i ne wann. Billahillazi akan abincin nan sai mu tara Miki na jaki a nan mu bama idon mak’ota abinci da
n kinsan dai wann ba bak’on abu bane a wann k’ofar.” Azeema tace tana kuma shan d’amara.
Har lokacin mamaki take baki bud’e “Ni Dije zaku daka ke Azeema.! Eh Lallai! Ai idan bakuyi ba baku cika jinin Tani ba. Ba laifinku bane Kunsha a nono.”
“Wllhi Inna
Dije zakici bugu a banza dan kin fad’a da bakinki nida kunya dama munyi hannun riga. Ke d’in banza tinda na tafi na tari fad’a da budurwar Habibu mai tak’ama da uniform da bakin bindiga banga uban da bazan taresa ba. Ke mu fah fad’a ma rancenta muke ko ya
kikace Badia.?”
Badia ta dubi Inna Dije da bakinta ya gaza rufuwa sabida mamaki “Inna billahillazi idan baki kira yaran nan sun maido da abincin da suka fitar ba wllhi Kinji na ranste Miki kaf takaicin duniya da Tasi’u Ya juye mun zan juyesu akanki. Dan
wllhi yanzu a haka hannayena k’aik’ayi suke.!”
Inna Dije ta jinjina kai “Eh na yarda dole ku kasa zaman gidan aure dan babu Wanda zai zauna da shed’anu Irinku. Me za’a tsammata daga wajen yaran da uwarsu ke tsare a gidan gyaran hali.”
“Saki nawa aka Miki
.? Yaji sau nawa kikayi da wayonmu kafin ki zauna gidan auren.?da wayonmu muna rakaki kome. Naga gado mukai wajenki” Badia tace tana fincikan kwalin taliya dake hannun Inna Dije.
Inna Dije ta jinjina kai tana duban Umma da ta zuba ma sarautar Allah ido.
K’wafa tai tasa kai zata wuce Badia da Azeema suka shiga janyota suka nufo waje suna fad’in saita maido kayan abincin da ta sace ta saka a keke napep.
Haka Azeema da Badia suka tirsasa ma Inna Dije ta dawo masu da kayan abinci.
Suka k’araso da kayan su
ka jirge gaban Umma. Har lokacin ko waccensu da d’amara a kunkuminta. Azeema taci gaba da nuna ma Umma kayan abincin “Kema kiji da kyau bamu k’wata abincin nan sabida Ke ba sai don yunwar cikinmu. Kici gaba da girkawa kina bamu.”
Umma bata ce komai ba har
suka gama maganganun da zasuyi. Dan tun bayan abubuwan dake faruwa kaman abun nasu k’aruwa yai. Cikin Zuciyarta tabi su da addu’ar shiriya. Ta d’au alwashin zatai hak’uri dasu kuma bazata fasa masu nasiha ba har lokacin da abubuwa zasu daidaita da taimak
on Allah.
**
Abuja…
Anisa taci gaba da juya kwalaben turare da Mommy ta bata tace ta kaisu ma Ummul.
Waya ta d’aga ta kira Amminta. Asshe na ganin wayar Anisa Tai saurin d’agawa “Ina sauraronki Anisa meke faruwa.? Shin Haidar yazo gidan.?”
Anisa ta
rausayar da ido “No Ammi he hasn’t shown up until now. And I don’t think zaizo gidan anytime soon.”
Asshe ta jinina kai “Toh ina sauraronki, wani abun ne Ya faru.?”
Anisa taci gaba da juya kwalban turaren “Ammi Kince duk abinda ake ciki na dinga sanar da
ke.”
Asshe tace “Eh K’warai. Remember you are my eyes there.”
Anisa taci gaba “Ammi Mommy ta bani wasu kwalaben turare guda biyu.. Kaman turaren black khumra amma banaji suna k’amshin khumra.. Tace na bama Ummulkhair.. Lallai Lallai na bata na kuma sanar
da ita had’in khumra ne na musamman Mommyn Tai mata kyautar su.”
Ai Asshe bata San sanda ta mik’e daga zaunen da take ba. Ta soma tuna lokacin zuwansu wajen boka sanda za’a masu aiki akan makarin asirin Haidar. Boka Ya basu wani turare mai launin bak’i y
a kuma ce lallai lallai duk matar da za’a karya asirin jikin Haidar da ita sai ta zamto tana amfani da wann turaren domin kuwa turaren tamkar shine kuran k’arfe da zai janyosa zuwa gareta Har dai sihirin Ya lalace. Idan kuwa haka ne bazata bari Ummulkhairi
Tai amfani da turaren ba tinda ita d’in barazana ce ga rayuwarsa.
Baki na rawa Asshe tace “Turaren humra.? Kar ki bata su Anisa..!”
Anisa tace “Meyasa Ammi.?”
“Na fad’a Miki no asking questions Anisa. Just do as I say. Ki zubar ki zuba turaren Khumra
cikin kwalban ki bata. But koda wasa kar ki bata wann turaren idan har kina son ki mallaki Haidar.”
Anisa ta kuma juya ido “But Ammi what if Mommy ta ba ma Bagidajiyar nan turaren da zata mallaki Haidar ne since she wants her for her son. What if I use it
instead.. Kinga sai ya soni bai sota ba..”
K’iris Ya rage Asshe bata kurma kururuwa cikin waya ba jin nata ‘yar zata zama makarin asiri “Ke Anisa. Zan tsine miki albarka idan kikai amfani da turaren nan.. Wai ke wace irin shashasha ce. Nace duk abinda na
ce kiyi kawai kiyi zan