Showing 126001 words to 129000 words out of 267381 words
ya hakan zai zama laifina idan kaima da kake amininsa baka San da labarin Auren ba.?”
“Because he doesn’t tell me everything. Har sai ya zartar da hukunci yake sanar dani.. Kaman dai tafiyar ku Cuba, aurensa da iyayensa suka m
asa dama abubuwa da dama.. I had to find out about them all bayan abubuwan Sun wakana.!” Ya dago yana duban Dareen sosai “Amfaninki shine ki samu kusanci dashi fiyeda ni, ki rayu dashi under same roof dan musan mai yake ciki.”
Taci gaba da jinjina Kai “D
oes Haidar love her..? Yana son matar da iyayensa suka aura masa..? Tell me pls Hisham.” Ta k’arashe tana fito da idonta waje.
Hisham ya kareta da ido sai kuma ya girgiza kai “Don’t think of going near her.!” Yai maganar cikeda gargadi yana nunata da D’a
n yatsa kafin yaci gaba “Kar ki kuskura Dareen. I love Ummul.. She’s the love of my life. Kuma zanyi komai to take her back from Haidar.!”
Dareen ta d’ago tana dubansa “What about Haidar.. you know I love him too.”
Hisham ya jinjina Kai “You can’t make
any move sai abinda nace. Ummul ta shigo ciki ya zama dole na bincika naji meye asalin labarin aurenta da Haidar. Ta haka ne kawai zan iya d’auketa daga gare shi. After all ban yarda da zamanta tsakanin azzaluman mutane irin ahalin Maitama ba. Tin ba aje k
o ina ba sun soma yunk’urin kasheta. I need to take her away from them. Wann auren na Haidar da Ummul bazai je ko ina ba.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice kaman zai kifa.
Zama yai cikin mota bayan ya fice yana tuna duk wani shirinsa akan Ahalin Mai
tama. Ahalin da suka tarwatsa masa rayuwa, ahalin da ya ranste sai ya tarwatsa su tin sanda yasan ko shi waye. He vows to take them down for ruining his Mom’s life. Zai komai Akan mahaifiyarsa. Zai d’aukar mata fansa koda Abu na k’arshe kenan da zai a rayu
warsa. Ya ranste sai ya mayar masu da duk k’uncin da suka fuskanta a rayuwa ta dalilinsu. Sai yanzu yake gano dalilin Hajja na b’oye masa waye Ummul ta aura. Dama ta sani kenan. Ta San Dan azzalumin tsohon mijinta ne ya auri Ummul.? Ya jinina Kai a hankal
i yana ayyana bazai tab’a bari ta fahimci akwai alak’a tsakaninsa da ahalin Maitama ba. Bazai tab’a bari ta fahimci yasan wani Abu ba har sai ya k’arashi fansarsa akansu. Idan kuma na numfashi Ummul zata dawo gare shi. Meyasa shine gaba da Haidar amma koma
i nasa Haidar ke samu. Shi ya kamata ya fara zama D’a wajen mahaifinsa bai zama ba Haidar ya zama. Yanzu Ummul da ya fara ganinta wacce shi ya kamata ace ya aureta sai gashi Haidar ya rigasa samunta. No way.. Bazai bari hakan ta kasance ba. Bayan fansarsa
da yake so Akan ahalin he needs to fight for Ummul. Ita din tashi ce.! Cikin sauri ya tada motarsa had’ida barin wajen.
*
A hankali Ummul ke k’ok’arin bud’e idonta har ta sauk’e su tar kan Likitan dake tsaye gabanta. Ta yunk’ura zata mik’e amma sai ta ka
sa. Muryar Likitan ta sinkayo yana fad’in “Ah sorry. Bazaki iya mik’ewa a yanzu ba. Sannu ko…”
Ummul taci gaba da rage girman idonta tana dubansa a hankali tana kuma duban d’akin da take. Ta dubi hannunta taga drip.. Ta girgiza Kai kad’an “Aaaah… Ina ne n
an..? Ina nake meke faruwa dani.?”
Dr ya murmusa “I’m Dr Faruk.. Ni ne Likitan da ya kula dake da aikin da aka miki..?”
“Likita..? Aiki..?” Sai ta yunk’ura taji zogi kad’an wajen hak’ark’arinta.
Dr ya jinina Kai “Mun Miki aiki dan fitar da guban da kika
shak’a cikin lungs dinki..”
“Guba.! Lungs..!” Ta fad’i cikeda mamaki tana duban Dr Wanda ya soma duba file din dake hannunsa “There’s nothing to be worried about.. the poison is completely out of your system in sha Allah. Akwai maganin da zamu dauraki ak
ai na dan wani lokaci.”
Ummul ta katse sa cikin girgiza Kai “Amma Likita dan Allah waye ya kawo ni nan.. Meyasa banga kowa ba.?”
Dr ya murmusa “Ina ta jira naji kinyi tambayar nan dan yanda mijin nan naki ya damu dake na kwana biyu banga irin haka ba. A
nan yake kwana kwanaki biyun nan da kikai a kwance.. Yanzu haka ma gida ya tafi nasan nan bada jimawa ba zaizo musamman idan yaji labari mai dadi cewa kin farka.” Ya k’arada akwai yanda ke Miki ciwo ne.?”
Ummul bata samu zarafin amsa sa ba sai mamaki da y
a cika ta wai mijinta kuma a nan yake kwana. A hankali ta furta “Mijina.?!”
Wayar Dr ne ta soma ringing ya dubi Ummul “Please excuse me. I have to answer this… Akwai wani Dr da zai shigo anjima ya dubaki. Zai instructing dinki gameda abubuwan da suka kama
ta ki fara ci.” Bai tsaya sauraronta ba ya fice cikin sauri yana amsa kiran dake shigo masa.
Har lokacin mamaki ne ya cika Ummul. Toh wane irin guba ta shak’a..? Sann wani Miji Likitan nan yake magana akai.? Bata Kai ga samo amsa ba Anisa ta turo k’ofa t
a shigo gaba d’aya ta rasa sukuni. Bata san ya zatai da Leenah ba. Bata tab’a tsammanin Leenah zata zame mata tashin hankali irin haka ba. Wato dama plan d’in Leenah kenan da tace ta incriminating Mommy. Shine ta tasta kudi jikinta. Yanzu idan ta bud’e bak
i ta fad’i abinda ya faru Tabbas kashin ta ya bushe. Hango idon Ummul da tai a bud’e ta sanyata k’arasowa cikin sauri tana fad’in “OMG.! Finally you are wake.. Oh thank goodness.!” Ta k’arasa tana mai kwantowa jikin Ummul dake kwance had’ida bata light hug
.
Anisa ta kuma duban Ummul tana mata sannu. Murmushi Ummul take sakar mata tana amsawa.
Anisa taci gaba “We were so worried about you Ummul. We all thought you were going to die.. Especially Mommy. Kai Alhamdulillah kin tashi.”
Ummul ta k’ak’aro murm
ushi kad’an. Sai kuma ta fara lek’e kaman tana Neman wani. “
“Ina Mommy.. Tare kuke da Mommy.?” Ummul ta tambaya.
Take Anisa tai rau rau da ido had’ida girgiza Kai “Ummul to be honest with you Mommy is in jail right now.. And it’s all because of you.”
U
mmul ta dubeta da mamaki “Mommy kuma a jail..? Kuma dalilina.. Wai meke faruwa ne Anisa.?”
Anisa ta sauk’e ajiyan zuciya kaman gaske “Turaren da Mommy tai miki kyautar sa an tabbatar akwai guba ciki Ummul.”
Shaye da mamaki Ummul ke dubanta “Guba kuma.?”
Anisa ta jinjina mata Kai alamun tabbatarwa “And that’s why you ended up here in a hospital. Mommy kuma aka tura ta jail.”
Ummul ta soma girgiza Kai “A’a Anisa… Wani Abu ba daidai bane a nan.. Mommy bazata tab’a saka mun guba ba. Tana sona sosai ni sha
ida ce.. Bata tab’a min wani Abu na cutarwa ba.. Meyasa zata saka min guba.”
Anisa ta jinjina kai “Nima dai abinda nai tunani kenan. Mommy tana sonki Ummul sosai.. She’s shown nothing to you but immense kindness. She defended you so many times.. She loves
you tamkar itace ta haifeki. Bazai tab’a yuwa ta cutar dake ba. Idan ma har akwai guba ciki Tabbas bata sani ba.” Anisa ta dafa hannayen Ummul dan babu yanda ta iya dole tayi convincing Ummul ta janye k’ara Akan Mommy ta haka ne kawai zata samu ta rabu da
Leenah cikin ruwan sanyi tinda idan Ummul ta janye k’ara ko ta sanar da Mommy bazai amfanin komai ba sann Mommy bazata yarda da Leenah ba tinda dama kwanakin baya Leenar ce ta k’ulla ma Ummul sharrin sata balle yanzu idan taga da taimakon ita Anisar ta fi
ce a jail. She needs to play her card well. Cikin kwantar da murya take ci gaba “Ummul janye k’ara da zakiyi akan Mommy shi zai fidda Mommy daga jail a halin yanzu.”
Cikin rudani Ummul ke girgiza Kai “Wai wani k’ara kike magana Anisa..? Dama babu wani k’a
ra.. Koda Mommy da gaske tayi niyyan kashe ni wllhi bazan tab’a yin k’ararta ba. Mommy uwa ce a wajena.!”
Ta kuma duban Anisa a daburce “Ina Likita..? Ya kamata na tafi daga nan.. Ina so na tafi na samu Mommy please..!” Ta k’arashe tana yunk’urin mik’ew
a.
Anisa tai saurin dafata “A’a Ummul a hankali. Bakida k’arfi har yanzu.. Mu jira Likita yazo..” Bata Kai aya ba wayarta ya soma ruri Leenah ce mai kira. Cikin zuciyarta ta furta ‘Damn it.’ Ta dubi Ummul tana sakin murmushi “Zan amsa kiran nan ina dawow
a.”
Ummul bata iya ce mata komai ba dan ita har lokacin mamaki take wai Mommy na jail dalilinta. Bata da burin da ya wuce ta fita daga asibitin taje ta samu Mommy.
A hankali ya turo k’ofan d’akin ya shigo. Nan ya hangeta kwance saman gadon wann karon ido
nta a bud’e suke tar. Kullum a rufe yake ganinsu amma yau d’in a bud’e ga gansu. Ya kasa janye idonsa daga cikin nata idon.
Ummul kaw ganin wann mutumi da ya shigo tayi zaton d’aya Likitan ne da Dr ya sanar mata cewa wani Likitan zai shigo ya dubata tind
a ba sanin kamannin Haidar tai ba.
Tin kafin ya ida shigowa ta soma fad’in “Dr dan Allah ku Sallameni.. Wllhi naji sauki. Wani abu ya Sami Maman mijina.. Ya kamata naje na dubata.. Bazai yuwu na kyaleta cikin halin da take ba. Dan Allah ka cire min drip
din nan na tafi na samu Mommy tana buk’atata a daidai wann lokacin.” Ta k’arashe tana k’ok’arin cire drip din dukda ba iyawa tai ba ganin ya kareta da ido ko motsawa bai yi.
Haidar yai sauri ya rik’e d’aya hannun nata da take k’ok’arin cire drip din dash
i.
“Ke.!” Ya daka mata tsawa.
D’agowa tai tana dubansa sai kuma ta dubi yanda ya tamke mata hannu da k’arfin gaske ga wani irin huci da yake.
Bata iya fad’a ba, ba d’abi’arta bane. Khulsum bata nan balle ta k’wace ta kaman yanda ta saba. She needs to s
tand up for herself.
Ta d’ago ta dubesa tana huci har lokacin rik’e yake gam da hannunta bai kuma da niyyan sakar mata hannu. Sai ta soma tuno yanda Khulsum ke fad’a.
“Malam sakar min hannu..!” Ta fad’i tana firfito da ido waje.
Bai sake ba sai tsaret
a da ido da yai har lokacin yana kuma matse hannun nata cikin nasa.
Hakan ya kuma tunzura Ummul dan ta kula wann Likitan baida mutunci.
“Ka sakar min hannuna Malam. Ni matar aure ce. Idan ka bari mijina ya shigo nan ya sameka ka kuka da kanka..!” Tai
maganar tana ci gaba da kiciniyar k’wace hannunta amma ta kasa.
Kwanto da fuskar yai kusan nata “Call him.! Go ahead and call that husband of yours.!”
Sosai tsoro da tashin hankali suka bayyana saman fuskar Ummul. K’irjinta yaci gaba da bugawa.
Ana
a haka Likitan da bai jima da fita ba ya kuma turo k’ofan ya shigo.
Hangosa da Ummul tai yasa ta soma fad’i cikin rawar murya “Yauwa Dr. Dan Allah ka ceceni hannun wann abokin aikin naka.. Dan Allah ka sallame ni daga wann asibitin yanzu.. Ya kamata na t
afi naji sauk’i.” Tai maganar da kyar dan d’an magana da firgicin da tai har wajen aikinta ya soma mata zafi.
Dr da bai wani saurareta ba dan maganar nata ba fita sosai yake ba. Ya fad’ad’a murmushinsa ganin Haidar “A’a Engr kaji kiran Madam kenan dole k
a taho Akan k’afafunka.. Matarka is finally awake.!”
Zuciyar Ummul yai wani irin tsinkewa tana duban Likitan Jin kalaman sa. ‘Matarka.’ Ta nanata cikin zuciyarta. Ai sai taji kaman Cak numfashinta ya d’auke. Ta kasa juyowa ta dubi mutumin da Likitan ya ki
rata da matarsa. Sai ji da tai hannunsa na sakin nata a hankali.
Haidar ya dubi Dr sukai masabaha kafin ya k’arada “Sallama nake so Dr as soon as possible.”
Dr ya d’anyi jim “Da wuri haka. Ya kamata mu ajeta a nan for observation. Wait I’ll be back.. Dr
Charles needs to see her first.”
Yana ficewa Haidar ya isa ya zame drip din. Batai aune ba sai ji tai ta sunkuceta cikin hannunsa.
Ummul ta kasa gane meke faruwa. Ta rasa ihu zatai tsalle zatai saima taji tamkar wacce aka d’aureta. Har lokacin cikin ma
maki mai gauraye da tsoro take. Ji tai yawun bakinta kaf ya k’afe. Bata tsammanin akwai jijiya mai motsi cikin jikinta a wann lokacin. Bai direta ko ina ba sai cikin motarsa.
Anisa da fitowarta kenan daga wani hanya taga kaman bayan Haidar take gani ya gi
fta mutum cikin hannunsa. Zuciyarta yai wani irin yankewa kar dai Ummul ce.? A hanzarce ta nufi d’akin Ummul saidai tana zuwa bata tadda kowa ba sai gado. Nan Anisa ta fito a guje tana kwalla ma Likita kira.
**
Suna tafe saman kwalta ta kasa tantance w
ace duniya take ciki har kawo wann lokacin. Ta kasa duban b’angaren da Haidar yake. Iyakacin abinda ta sani shine anata falfala gudu da ita saman kwalta.
Da wutsiyar ido Haidar dake falla gudu dasu saman kwalta ya dubeta. Nan yaga har lokacin a tak’ure
take harda kaman rawar d’ari da take. Ya maida dubansa ga kwalta ba tareda yace komai ba.
Har lokacin Ummul bata dubesa ba. Ta kuma kasa furta koda kalma. Kana ganinta zaka fahimci har wann lokaci ba daidai take ba.
Haidar ya karya kan motar suka shiga
wani close da babu gine gine sosai saiko gida je da basu wuce uku ba. Ga yawan bishiyoyi da shuke shuke.
A daidai k’ofan wani madaidaicin gida Wanda kaman tsakiyar forest yake tsaban yawan bishiyoyi da shuka dake kewaye da wajen yai parking.
D’ago Kai
tai cikeda tsoro tana duban gidan dake tsakiyan jeji a idonta dan sai wann lokacin taji kaman an Zare electric shock d’in da aka saka mata.
SameenaAleeyou
📚
*AUREN WATA UKU..!*
*36*
*©
️
Sameena Aleeyou…✍
🏽
*
A tsorace ta d’ago tana dubansa.
“Can you walk.?” Ya tambaya yana dubanta itama shi take duba. Ganin bata ce masa komai ba sai ma rawa da jikinta keyi alamun dai batada strength har lokacin yasa bai kuma yin wata wata ba ya fiddota daga cikin motar.
Ganin haka yasa ta soma girgiza m
asa kai tana fad’i cikin rawar murya “A’a dan Allah.. Ina ne nan… Ina ka kawo ni..?!” Cikin muryarta da bai fita sosai take maganar.
“Shut up. Just shut up.!” Ya fad’i still tana cikin hannunsa. A haka ya tura k’ofan parlorn suka shige. Ko ina an rufe da
farin kyalle alamun dai babu mai zama cikin gidan. Wani d’aki ya bud’e ya ajeta saman gado.
Ta d’ago a tsorace tana dubansa had’ida girgiza Kai ganin na k’ok’arin ficewa. Da tangadi ta nufo k’ofa tana fad’in “Dan Allah.. Kar ka barni a nan.. Ka Kaini waj
en Mommy dan Allah ina buk’atan ganinta.”
Haidar ya d’auki lokaci yana dubanta kafin ya tako zuwa gabanta “Look, I don’t intend to keep you here for good. If you cooperate with me.. Bazaki jima a nan ba zaki tafi.!” Yana ida fad’in haka ya janyo k’ofan ya
rufe kirif.
Ummul ta duka a wajen tana dukan k’ofan da d’an sauran strength dinta tana fad’in dan Allah ya bud’e ta ya barta ta fita.
Shiru babu agaji ba taimako, Haidar bai bud’e ta ba sai sautin tashin motarsa da taji. Ta rarrafa da kyar ta isa jikin
window nan ta hangi hancin motarsa na barin wajen. Wani irin kuka ta fashe dashi tana Jin zazzabi mai zafi na sauko mata.
**
Anisa ta dubi Dr “Dr wann ai kidnapping ne. We need to see your security footage.”
Dr ya murmusa “How is that a kidnap.? Haidar
shi ya d’auke matarsa.. He’s her legal Husband.. So wann ba kidnapping bane.” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa.
Anisa ta furzar da huci “But still you are her Dr. And it’s your duty to call him and tell him exactly the consequences of what he’s done..
I mean, she’s still recovering.. She needs to stay here at the hospital.”
Dr ya dubeta still murmushi saman fuskarsa “If you excuse me Miss. I have some patients to attend to.” Ya k’arashe yana mai shigewa.
Anisa taci gaba da huci “Ahhhg! Imbecile.!”
Ta fad’i tana sakin huci. Wayarta ne ya soma ringing. Ta duba taga Leenah ce. Gajeren tsaki tai had’ida kin d’agawa. Leenah ta kira har kusan sau uku Anisa bata daga ba sai ta turo mata SMS.
_Remember you only have 2 days_
Tsaki Anisa tai tana sakin hu
ci. Yanzu ya zatai ga wann D’an zafin Kan ya d’auke Ummul wacce take tunanin itace last alternative d’inta. Kodai Hilal ne zata kira.? Ta d’anyi gajeren tsaki kafin ta soma Neman layin Hilal.
Bugu biyu Hilal ya d’aga “How’s my fish brain sister doing.?”
“Zanci k’aniyarka Hilal.” Anisa tace a hasale Jin ya kirata da sunar tsokanar da ya saba kiranta tin yarinta fish brain.
Hilal ya dara “Hey easy. Nayi kewar tsokanarki ne. How have you been.. Bazaki zo bane sai na tafi.?”
Ta dan rausayar da ido had’ida
furzar da huci “Yaushe zaka koma school din.?”
“Nayi postponing akwai abinda nake a nan.” Ya bata amsa Kai tsaye.
Anisa ta dan zaro ido “Kuma Abba na sane da haka.?”
Hilal ya dara kad’an “He doesn’t need to know.. Wani Abu kawai zan k’arasa sai na tafi
.”
Anisa ta jinjina Kai “Hey Hilal, brother… Alfarma nake nema.”
Hilal ya kuma d’an darawa tinda yaji ta fara kashe murya tana kiransa brother yasan abu take nema wajensa “Fad’a kawai meye