Showing 162001 words to 165000 words out of 267381 words

Chapter 55 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

27

yace bazai iy

a moving arms dinsa ba she should feed him. Haka dole ba yanda ta iya ita ta basa abinci. Ko wani motsi nata kan idon Haidar. Ranar dai ta zamto tamkar personal nurse d’insa. Dan duk wani abu da suke na kula da majinyaci baya bari suyi ita takeyi saidai Wa

nda yafi k’arfinta ko layin ma’aikatan lafiya ne kawai. Dik yanda taso ta zille ma Haidar Ya kasa barinta.

Can dare tana kishingid’e saman sofa shi kaw sai kallonta yake daga nan saman gadonsa ta majinyata. Nan yaga ta tak’ure waje guda ta k’udindune cik

in hijab dinta.

A hankali Ya mik’e daga saman gadonsa da kyar. Ya tako zuwa yanda take. Zama yai gefenta yana k’are ma fuskarta kallo. Kallo irin Wanda bai tab’a tsayawa yai mata ba. Hannu yasa yana zare Hijab d’in hakan yai daidai da juyin da zatai. Tak

e yaji wani abu ya tsargar masa kaman electric shock. Nan yake binta da kallo head to toe. Ya jima sosai yana k’are mata kallo kafin ya karkatar da ita kad’an Ya kwanta nan gefenta kasancewar kujerar mai fad’i ne sosai. Ya matso da ita cikin jikinsa Ya jan

yo abin rufuwar Ya rufa musu.

**

A can gida kuwa yanda Anisa taga rana haka taga dare. Sai kai komo take a d’aki ita kad’ai tana safa da marwa. Ta lallaba ta tafi d’akin da aka sauki Amminta.

Ta tsaya tana kallon mahaifiyar nata dake sharan bacci tana

tunanin hirarsu da Mommy da ta sinkaya a asibiti gamed auren Haidar da Ummul.

Kodai ta tashi Ammi ne ta sanar da ita taji komai. Tasan komai a halin yanzu.? Toh Amma Hisham yace ta bar masa komai.. Ya mata alkawarin zai cire Ummul daga rayuwar Haidar ko t

a halin k’ak’a.. Idan ta sanar da Ammi wani abu yanzu shirinsu da Hisham ka iya b’aci. Bazata bari hakan ta kasance ba. Sauri sauri ta koma nata d’akin. Ta kagu gari ya waye ta bullo da wata hanyar da zata samu taje ta duba Haidar da Ummul tinda Haidar dai

ya mata iyaka da asibitin.

**

Asubahin fari ta farka tana mamakin yanda bacci mai nauyi ya dauketa itada take yawan farkawa cikin dare. Nan tajita cikin jikin mutum kuma. Zuciyarta ta tsinke. Ita tsoro ma abin ya bata dan Sam bata kawo a zuciyarta maji

nyaci irin Haidar ka iya mak’alewa gefen kujera har yayi bacci irin haka ba.

Ta yunk’ura a tsorace zata tashi sai ta sinkayo muryarsa yana sakin ‘yar k’ara had’ida rik’e gefen hak’ark’arinsa. Su duka biyu duban juna suke kasancewar akwai hasken dim-night

cikin d’akin.

Tai saurin mik’ewa tsaye daga kan kujerar tana kuma kallonsa.

Ganin da gaske na cikin pain dan har lokacin bai daina tamke ido yana dafe hakarkarinsa ya sanyata saurin duk’awa gabansa tana tambayarsa “Da zafi ne.? Na bige maka ciwo ko.? Da

n Allah kai hak’uri wllhi ban kula bane.!” Ta k’arashe maganar kaman mai shirin kuka.

Sai Ya daina tamke idon da yake yana Ware idanunsa a hankali yana kallon yanda take magana kaman itace cikin pain d’in.

Ta d’an saci kallonsa “Kai hakuri zan tabbata

na taho da abin rufuwa yau in sha Allah.”

Ya tsareta sosai da ido kafin ya girgiza kai kad’an had’ida lumshe idonsa “It’s fine..” Ya fad’i a tak’aice.

Ya mik’e a hankali yana fadin “I.. Will use the bathroom.. It’s subh prayer time already..”

Ta jinj

ina masa Kai a hankali “Kana buk’atan taimako na.?”

“No I.. Can manage.” Ya fad’i yana dingisawa har ya nufi hanyar bathroom din.

Yana shigewa ta zauna had’ida sauk’e deep breath. Hannunta na rawa ta janyo mayafin da ya rufesu dashi. Sai ta runtse idonta

da sauri wai yau ita Ummul ke bacci mayafi guda da Haidar.. Kunya ne.? Damuwa ne? tsoro ne? Duk sai ta ma rasa mai ke mata yawo cikin zuciyarta.

A b’angaren Haidar Shima haka nan ya lumshe idonsa a bathroom abubuwa fal zuciyarsa. Cikin zuciyarsa yake tu

humar kansa ‘What’s wrong with you Haidar.? Why are you so soft with her..?’ Take zuciyarsa ta shiga tuno kalaman mahaifiyarsa garesa ‘Ka ba ma kanka dama da Ummulkhair.. Kamin wann Haidar koda shine abu na k’arshe da zan buk’ata wajenka.’

A fili yake fur

ta “Sabida Mommy. You are doing it for Mommy and because of Mommy.. Kaman yanda ta buk’ata.”

Da safe kuwa su duka biyun yanayinsu ya dan sauya bayan baccin da sukayi tare musamman ma Ummul wacce ta kasa had’a ido dashi. Gaisuwa ma k’asa k’asa tai masa.

Haidar nata karantarta.

Sassafe take shirin tafiya gida dan ta samu ta kintsa kanta kafin ta dawo. Zata fice ta sinkayo muryarsa “Khairy.!” Cak ta tsaya tana sauraron sunan da ya kirata dashi.

Haidar yaci gaba “Don’t take long.. And.. kar ki sake ki z

o da wani abin rufuwa asibitin nan.”

Sai ta dubesa da mamaki “Amma maiyasa.?”

Ya tab’e baki kad’an “Hospital rules.!”

Ta jinjina Kai a hankali tace “Shikenan bazan zo dashi ba”

Haidar ya jinjina mata Kai sihirtaccen murmushi saman labb’ansa. (Kunji wan

i salon wayo wajen Haidar. Wai asibiti ta hana zuwa da abin rufuwa daga gida.)

Ita dai Ummul Haka ta fice tana mamakin wann wane irin asibiti ne masu tarin dokoki da k’a’idodi.

Bayan ficewar ta da kad’an Anisa tai knocking a k’ofa. Duk a tunaninsa Ummu

l ce ta dawo. Kai tsaye ya bada izinin shigowa.

Ga mamakin sa Anisa ya gani rik’eda jakan kaya. Ya tsareta sosai da ido alamun yana jiran ba’asi tinda yasan ya mata iyaka da asibitin.

Ta k’ak’aro murmushi tana masa gaisuwar da bata samu amsa ba.

“Wha

t are you doing here? I thought I made it clear to you…” Saurin katsesa tai ta hanyar d’ago masa jakar Kayan “Kayan Ummul… Mommy ce ta Aiko ni na kawo..” Sai ta d’an saci kallonsa “And.., I…wanted to check how you’ve been holding up.. Laifi ne hakan..? Aft

er all, we are cousins.”

Katseta yai “I just don’t want you here.. Don’t you get it”

Kuka ta fashe dashi tana mai barin d’akin. Ta rasa mai tai ma Haidar yake mata irin wann kiyayya.. Toh kodai ya fahimci da saka hannunta ne a had’arin da ya samesa.? Do

le ta nemi Hisham su san ta yanda zasu bullo ma al’amarin.

**

Hisham ya dubeta sai kuma ya girgiza Kai yana murmushi “Kar ki bani dariya mana Neesa. Quite alright Haidar na zargin had’arin mota da ya samu shiryayyen abu ne.. Amma ina mai tabbatar Miki ba

kece yake zargi ba.”

Anisa ta dubesa ta d’an girgiza kai “Ta Ya ka tabbatar da haka.? Sann waye yake zargi.?”

Hisham Ya murmusa “Wani hujja yakeda shi da zai zargeki.?”

Shiru bata basa amsa ba.

Hisham yaci gaba “A kalaman Haidar cewa yayi yana zargin

wani ne dake boyayyen agenda akansa. Waye keda dalilin ganin bayansa.?”

Shiru bata amsa ba.

“Dareen.! Ita ce kawai takeda motive na hallak’a Haidar tinda ta rasa shi bazata bari wata ta same shi ba. Haka ne.?”

A hankali Anisa ke jinjina kai.

Hisham ya

ci gaba da murmusawa “Which is why dole na cimma Dareen kafin Haidar Ya cimmata..” Ya kaikaito sosai yana duban Anisa “Duk abinda nakeyi.. Everything is calculated. Ki bar mun komai kaman yanda na fad’a.. Aikinki kawai shine ki saka ido akan Haidar da kuma

Ummul.”

Ta rausayar da ido “But it is not as easy as it seems. Haidar is making it difficult.”

Ya kurbi drink dake hannunsa had’ida d’age kafad’unsa kad’an ya tabe baki “You must do it. You don’t have a choice. Find a way to keep an eye on those two”

T

a shiga jinjina kai a hankali tana furzar da huci.

Basu ida maganar ba wayar Hisham tai ruri Haidar ke kiransa.

Ya murmusa yana duban wayar “Speak of the devil… he shows.!” Ya furta a fili kafin ya d’aga kiran.

Bayan Sun gaisa irinta abokai Haidar yace

“I sent you an email.. Since you can’t come to visit.”

Ya murmusa “Haba abokina ba haka bane.. Kasan asibitin naku ne na turawa. Komai d’an k’aida.. And work’s been too demanding lately.. Musamman da yake baka nan. On the other hand ga neman Dareen da nak

e. Kasan bazan tab’a barinta ba sai na nemota ta biya abinda ta aikata ma abokina.

“Speaking of Dareen. Are you free?”

Shiru kaman bazai amsa ba Ya soma yan kame kame Haidar Ya katse sa “You know me. I don’t take no as an answer. Ina jiranka.” Daga haka

katse kiran yai.

Duban Anisa yai yana huci. Cikin zuciyarsa yake ayyana Ya tsani yanda Haidar keyi kaman wani boss d’insa bayan cewa ko a haife ne shine gaba da Haidar d’in..

Anisa ta katse shirun da fad’in “See Kai gashi yana nemanka amma ni cewa yak

e anyi restricting zuwan visitors.”

Hisham Ya furzar da huci “Kinsan meye matsalar?”

Anisa ta girgiza kai alamun a’a.

“Bazai yuwu Ummul ta ganni wajen Haidar ba all our plans zasu lalace ne. No Ummul bazata ganni wajen Haidar ba. It will be a disaster.”



Anisa ta murmusa “But this is the perfect time da ya kamata ka visiting Haidar because Ummul bata wajensa ta tafi gida. I believe ma Shiyasa ya samu chance na kiranka.

Hisham yace “You sure.?”

“Hundred percent.!” Ta basa amsa tana mai jinjina kai.

“P

erfect! Yanzu abinda zaayi kiyi maza ki tafi gida ki rik’eta ki hanata barin gida Har sai nayi alerting naki. Ma’ana sai na bar wajen Haidar.”

Anisa tace “An gama Barinyi sauri na tafi kafin ta fito nasan sai ta tsaya tayi wanka tayi wasu abubuwan.”

D

aga haka sukai sallama da Hisham. Shi Ya nufi asibiti wajen Haidar ita kuma ta nufi gida wajen Ummul.

A can gida kuwa Mommy sai nan nan da Ummul take tana fad’in maza maza ta gama shiryawa driver ya maidata. Mijinta majinyaci ne bai kamata ta barosa shi

kad’ai ba. Asshe kanta sai mamaki take ganin yanda Mommy keyida Ummul. Lallai Anisa tayi gaskiya da tace idon Mommy ya rufe akan Ummul. Gani take kaman an canza mata ‘yaruwar tata da gaske ne. Gaba d’aya Mommy ta tashi daga Aunty Kwaise da ta sani ta koma

wata abu daban. Ita kanta Asshe lamarin tsoro Ya fara bata. Ta zuba ma sarautar Allah ido ta kasa katab’us.

A haka Anisa ta iso gidan ta taddasu sai karantar Mommy take tana ganin yanda take ingiza Ummul tayi ta tafi wajen mijinta. Makirin Murmushi Anisa

tai tana jinjina kai dan har ta hasasho ta yanda zata tarwatsa Auren Haidar da Ummul. Muddin ta fayyace ma Ummul komai zata fahimci Hajiya Kwaise Maitama azzalumar mace ce ba soyayyan gaskiya take nuna mata ba. Kawai tana mata duk abubuwan da take ne don a

mfanin kanta da D’anta. Tabbas Ummul zata tsani Kwaise da tsinann auren da tai ma da d’anta Wanda boka Ya had’a. Ta k’arashe tunanin tana mai kecewa da Makirin murmushi.

A k’ofan fita daga sashen Mommy Anisa ta cimma Ummul. Suka sakar ma juna murmushi ha

d’ida gaisuwa.

Anisa ta k’arada “Ba dai har zaki wuce ba.?” Kafin Ummul ta kaiga bata amsa ta kuma sakin murmushi tana mai dafa kafad’an Ummul d’in “It’s fine, Ya kamata ki tafi kin baro mijinki shi kad’ai… I Miss having you around Ummul.. Kinsan bahaush

e yace sabo turken wawa”

Suka murmusa a tare kafin Anisa ta mik’a mata jakan hannunta “Ga wann kar na rik’eki da surutu.”

Ummul ta d’an girgiza kai kad’an cikin rashin fahimta “Ta mecece.?”

“Kayanki ne a ciki. Nayi tunanin na kai miki su asibiti sanin c

ewa zaki buk’ata amma sai mijinki Ya koreni dasu.. Kamar dai ko yaushe.” Ta k’arashe tana mai k’ak’aro murmushi.

Jikin Ummul Ya d’anyi sanyi “Kiyi hak’uri Anisa…”

Saurin dakatar da ita Anisar tai “No no.. You don’t have to apologise for his behaviour. K

ar ki samu damuwa.. Nasan Haidar since childhood.. He’s rude, arrogant, short tempered.. and sometimes unpleasant to be around.. Ki yarda dani, idan da sabo na saba da halin d’anuwana..”

Da mamaki Ummul ke dubanta dan ko ba auren soyya sukai da Haidar ba

sosai taji zafin kalaman da take fad’i kansa. Amma sai ta danni zuciyarta ta murmusa “Baki tunanin kalaman da kike sunfi kama da cin fuska.?”

Shiru Anisa batace da ita komai ba.

Ummul ta murmusa had’ida dafa kafad’ar Anisa “Kar ki damu banyi fushi ba.

Dan dik abinda kika lissafo gameda shi kwalliya na d’aukesu. Domin kaw sosai suke k’ara masa k’warjini da birgewa.” Ta k’arashe murmushin nan nata dake tunzura Anisa saman fuskarta.

Murmushin da yafi kama da yak’e Anisa ta k’ak’aro “Of course. Haka ne..

Let me walk you to the car..” Ta k’arashe tana mai kamo hannun Ummul d’in suka nufi mota.

A hanya Anisa ke ci gaba da fad’in “Mutanen gidan nan sunyi kama da mutanen kirki koda ahalin ya kasance birkitaccen ahali mai tarin gib’i.. Haka ne.?”

Ummul ta du

beta cikin rashin fahimta.

Anisa ta murmusa “Ko wani d’an adam yanada sirrikansa.. Amma akwai wasu abubuwan da sirri baida muhalli cikinsu. Kamar dai Aure. Haka ne.?”

Ummul ta kuma girgiza kai tana karantar yanayin Anisa. Tana danganta maganganun Anisa d

a tunanin kodai Anisa tana so ta sanar da ita cewa tasan yanda akayi aurenta ne.? Amma batada wani sirri da ta b’oye ma Haidar gameda aurensu face iyaka da Umma tai mata da d’aukacin ahalinta Har na tsawon watanni uku ciki harda mahaifinta dake kwance yana

jinya. Bata Ida tunanin ba ta kuma sinkayo muryar Anisa daidai sanda suka isa jikin mota.

“Kina tunanin kinsan ahalin gidan nan ne Ummul.? Ko kina tunanin kinsan mijin da aka aura Miki ne.? Ina shawartar ki kar ki zak’e da yawa.. Don’t get too attached.

Be warned.!” Cikeda gargadi tai maganar kafin ta murmusa “Akwai abubuwa da dama dake cikin duhu. Ina fatan a lokacin da duhun nan zai yaye miki Ummul bazaki sameni cikin wad’anda suka ci amanarki ba. And you can count on me dan ciwon ‘ya mace ta ‘ya mace

ce.” Ta k’arshe tana murmushi had’ida bud’e mata marfin mota “A cikin gidan nan trust no one but yourself Ummulkhair. Tabbas Wani Auren nasara ne. Amma Wani Auren halak’a zai kaika.! Allah Ya tsare hanya.” Ta k’arashe da murmushi. Tana ida fad’in haka ta

juya ta shige cikin gida zuciyarta na mata fari k’al. Dan ta tabbata ko ba komai ta cika shakku cikin zuciyar Ummul. Wani abu ma sai randa k’wai Ya fashe gaba d’aya.

Tabbas Anisa tayi nasaran jefa mata waswasi da shakku cikin zuciyarta. Shin da gaske ne i

ta d’in ta zak’e da yawa.? Batasan mai Anisa take son sanar da ita ba. Sann koda wann auren tun usul bata tsammaci farin ciki ko wani abunda yai kama da wann cikinsa tun farko ba. ta tsinci kanta cikin tsananin shakku da rud’ani Wanda bataji irinsa a baya

ba. Sann sosai taji tana buk’atan sanin mai Anisa take son sanar da ita musamman gameda mijinta Haidar. Haka har ta isa asibiti tunanin da take kenan jikinta duk a sanyaye.

*

Asshe bata iya kwanaki garin ba ta tarkasa ta dawo Kano dan sosai ta firgita d

a lamarin ‘yaruwarta dole ta dawo gida ta samu ta shawo kan matsalar kafin komai Ya ida kwance mata musamman da idonta ya tabbatar mata idan ‘yarta Anisa bata k’arashi rayuwarta gidan yari ba toh kuwa ba shakka zata k’are a turu ganin irin abinda take wand

a yafi kama da hauka tuburan duk dan akan Haidar. Da fari ta saka ma Ummulkhair guba a turare sann ta d’aura alhakin kan Mommy har ta tafi jail tai kwanaki dik akan haka. Yanzu ga had’arin mota da ta shirya ma Haidar wanda k’iris bai rasa ransa ciki ba. La

llai ya zama dole tasan abinyi.. Dole ta raba wann jarabebben aure na Ummulkhair da Haidar wanda ta zamto silarsa a farko ko dan ta ceto ‘yarta Anisa.

*

Kano..

Sun had’e su uku a parlorn Hajiya Asshe. Mama Tani wacce bata jima da shak’an iskan ‘yanci b

a, Inna Dije sai kaw Uwar gayya Hajiya Asshe.

Tani ta girgiza kai cikin rashin fahimta tana duban Inna Dije “Dije kina nufin kice wann matar ita tayi belina ba sirakan Suwaiba ba.? Sann so kike kice mun duk zaman dad’I da naga kinayi da Suwaiba a halin ya

nzu dama ba na gaskiya bane.? Dije wai meke faruwa ne.?”

Inna Dije ta murmusa tana duban Tani “Tani banda abinki.. Wann ma ai sirkar Suwaiba ce. Kuma ke a tunaninki ni Tani zan tab’a yafe ma Suwaiba da ‘yarta Ummulkhair ne. Kar ki mance a dalilin bak’in

k’addarar Ummulkhairi na rasa tilon D’ana Fa’izu.! Kuma ke kinfi kowa sani Tani. Dije bata yafiya sai d’aukar fansa.! Yau d’in nan zan sanar dake wace kalan Aure Suwaiba taima ‘yar D’anuwana dake kwance yana jinya wanda zai zamto Miki makami da zaki kori S

uwaiba da Auren cin amana da tai miki. Tani na san komai Suwaiba zata Miki a halin yanzu. Duk wani halacci na k’arya da zata Miki bazaki tab’a mance bak’in cin amana da ta miki na aure Miki miji bayan kin aminta da ita da tayi ba. Haka ne?!”

Tani tai shir

u tana duban Inna Dije wacce ke sakin huci.

Tani sai ta girgiza kai a hankali “A’a Dije. Yo ni a halin yanzu wani makami nakeda shi Wanda zan yak’i Suwaiba dashi bayan yarana da a kullum nake goranta mata cewa sunyi aure suna d’akin mazajensu gasu nan du

ka sun dawo gida daga wacce miji Ya koroto sai wacce miji Ya gudu Ya barta. K’arewa ma Suwaibar ke kula dasu a lokacin da nake gark’ame gidan gyaran

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login