Showing 30001 words to 33000 words out of 267381 words

Chapter 11 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

73

suka tarbes

a.

Murmushi saman fuskarsa ya girgiza mata kai “It’s nothing. Ki daina min godiya.. I’m glad I helped out.. Ummul-khair.”

Yanda ya ambaci sunan nata da wani irin siga sai yasa ta sadda idanunta kad’an.

A d’an daburce tai masa sallama had’ida komawa waj

en Khulsum cikin sauri.

Shi kaw kallo ya bita dashi har saida ta b’ace ma ganinsa kafin ya nufi mota yanda Hajjarsa ke jiran karasowarsa.

SameenaAleeyou

📚

*AUREN WATA UKU.!*

*12*





Sameena Aleeyou…✍

🏽

*

Tinda suka koma gida ya gaza samun

sukuni. Tunaninta ya addabesa. So yake ya tambayi mahaifiyarsa gameda ita. Sosai yaji yana son sanin labarinta.

A parlor ya tadda Hajja tana had’a wasu kayan d’inkinta. Ya zauna daga gefe.

Ta d’ago ta dubesa “Har kaci abincin kenan..?”

D’an furzar da

fuci yai kad’an yana mai shafe fuskarsa da tafukan hannayensa “Naci Hajja ya isheni..”



Ya d’anyi gyaran murya kad’an yana duban kayyayakin dake gabanta “Wai Hajja har yanzu bazaki hak’ura da d’inkin nan ba. Yanzu fah Allah ya rufa mana asiri I can take c

are of you , you don’t need to do all these things.”

Murmusawa tai “Ban raina k’ok’arinka ba Hisham. Amma kasan idan ba idona ne ya tafi ba ko k’arfina ya k’are bazan iya daina sana’ata ba. Sana’ar da na raineka da ita har ka zama abinda kake a yau cikin

k’udirar Ubangiji. I love being independent kai kafi kowa sanin hakan.”

Ko shakka babu ta tuna masa zamansu a Maiduguri, hardships da suka fuskanta da ma duk wani k’alubale na rayuwa. Ya d’an jinjina kai ba tareda yace komai ba.

Ta kuma d’agowa tana duba

nsa. Sai ta aje abinda take ta bada hankalinsa akansa sosai. Ta ambacesa da sunansa na yanka. Ya d’ago yana dubanta. Taci gaba “Ni a halin yanzu nafi buk’atan ka gina naka ahalin. Ka haura talatin

already. Kayi karatu ka samu aiki mai kyau. Rayuwarka ta in

ganta Mai kuma yayi saura bayan iyali. Bazan tak’ura maka ba ko na tilasta maka amma ni a nawa tunanin ya kamata ka fara making efforts. Kaga yanda kake tafiya ka barni ni kad’ai d’in nan sai ka barni da abokan wasa.”

Ya d’an murmusa dan ya d’ago mai ta

ke nufi.

“Toh Hajja ki sama min Matar mana kawai a nan tinda ni dai har yanzu ban samu ba.”

Tab’e baki tai tana mai ci gaba da abinda take “Idan na zab’a maka zaka amince da zab’ina ne.. Kasan ku yaran zamani ba’a maku katsalandan a wann sha’ani. Yanzu s

ai ku ba wa mutum kunya.”

Ya kuma murmusawa “Haba Hajjata. Nasan bazaki tab’a zab’a min abinda zai cutar dani ba. So na baki wuk’a da nama.”

“Ta d’an kuma tab’e baki “Na Jika dai.. Amma tina kace haka shikenan.. Ka jira kaga.. Next zuwa da zakai zaka tad

da iyalinka na jiranka ne..”

Ya d’an zaro ido waje “Hajja ina kika tab’a jin anyi aure Ango bai halarta ba..?”

“Za’a fara akanka tinda Wakili kawai zan tura ya karb’ar maka. I already have someone in mind dama.”

Ya d’an fito daga cikin kujeran cikin za

k’uwan san jin yaji ko wacece “Da gaske Hajja.. Who’s she.. A ina take..?”

Ta d’an dubesa “Idan lokacin yayi ka ganta.”

Ya kuma murmusawa kad’an. Shiru kaman babu mai cewa komai sai Hisham yai gyaran murya kad’an “Nikam Hajja nace… Ita yarinyar nan Ummul

-khair…”

Hajja ta zuba masa idanu jin yanda yake maganar cikeda kulawa ga wani k’alk’ala na musamman da ya ambaci sunan Ummul dashi “Umhum ina sauraronka.” Ta fad’i still tana dubansa.

“Wai dama kun jima da sanin juna ne.. Or do you have any relationship

with her family.?”

Hajja ta d’an murmusa “ Banda abinka Hisham yanzu ak’alla shekaru hudu fah muke nema a garin nan. Kaga ai ya kamata na saba da mutane kuma idan baka mance ba na sanar dakai ina koyar da sana’ar d’inki ma ‘yanmata. Toh Ummul tana cikin

d’alibai na.”

Hisham ya jinjina kansa a hankali “And she’s from around this neighborhood..?”

Hajja ta kuma murmusawa kad’an dan ta lura da curiosity na d’an nata gameda Ummul. Ita idan har abinda take hasashe ya tabbata zatafi kowa farin ciki. Dan Ummu

l yarinyar kirkici wacce jarabawa da k’alubalen rayuwa sukai marfi ma rayuwar nata.

Gyara zamanta ta d’anyi ta kaikato sosai tana duban Hisham “Naga alama dai tambayoyi ne kazo dasu wann karon.. Amma ka bari har Allah ya wayi gari lafiya kaga yanda ranar

yau d’in ta kasance mai tsawo. Idan ka samu ka huta zuwa gobe da safe idan Allah ya nufemu da kaiwa sai na amsa maka duka tambayoyinka.. Maza tashi kaje ka kwanta haka ka huce gajiya kuma. Kaga nima kwanciya zanyi haka nan.” Ta k’arashe tana k’ok’arin tat

tare kayan.

Hisham ya amshe yana linke mata su . Dan yanda ya kwana biyu baya tareda ita d’in nan dik abinda zaisa ya samu albarkanta baya wasa da wann abun komin k’ank’ancinsa.

**

Sassafe Mommy ta fito da zummar komawa Abuja dan dama day trip tayi ni

yyan yi amma sabida accident da suka d’an samu dole ta bari sai Washe gari bayan an duba lafiyan motar an tabbatar zata iya tafiya.

Ta dubi Asshe “Na bar miki wuk’a da nama amma ki tabbata wacce duk za’a samu tanada futures da qualities da zamu iya jan ra

’ayin Haidar dasu in just a short time. Lafiyayya wacce batada wani cutan da zai iya shafan d’ana.”

Asshe ta d’an numfasa “Bakida matsala Aunty Kwaise ai kaman yanda kikace ne a duniyar nan babu abinda kud’i bazai sai maka su ba. Ni yanzu damuwata matar d

a muka bige wacce har yanzu Ke asibiti gashi babu wani means of identification tareda ita balle a samu wani nata.”

Mommy tace “Aff kinga ni na mance ma da batun wann matar. Yanzu tareda waye aka barta a asibiti.?”

Asshe tace “Mai aikina Marka ita ta kwan

a da ita suna can tare yanzu haka..”

Mommy ta jinina Kai dan dama wani private hospital suka kaita “Duk abinda ake ciki dai kin sanar dani. Ni yanzu tafiya ya kamani, dan kinsan na fad’a miki Engr baisan na taho ba shima baya nan ya tafi Lagos tafiyar da

ta shafi Kasuwancinsa.. So bani so ya dawo gidan ya tarar bana nan. Anisa ce kawai gidan kinsan kuma yanda take saitin da sauk’i.

Asshe ta kuma jinjina kai “Zakiji komai in sha Allah Aunty Kwaise. Allah ya tsare hanya.”

Suna tsaka da sallaman Hilal ya k’

araso wajen. Mommy ta dubesa “Bazan amsa goodbye d’inka ba tinda har zaka zo hutu k’asar nan kuma jirginka ya sauk’a a Abuja ka kasa zuwa ka dubani.. Inji kaima kabi sahun d’an uwanka Haidar ne.?”

Hilal matashin saurayi d’a ga k’anwar Mommy Wato Asshe ya

d’an murmusa yana shafa kansa. Baifi sati da zuwa Nigeria ba karatu yake a k’asar Cyprus. Ya samu zangon hutu.

“Haba mana Mommy ta kinsan bazan miki haka ba. Tareda Abba da matarsa muka dawo Kano daga Abuja shiyasa. Nasan duk Anisa ce ta had’ani dake. A

mma kafin hutuna ya k’are zaki ganni in sha Allah. I still have 2 weeks here.”

Mommy ta murmusa “Toh shikenan sai na ganka.. Ina nan Ina zuba ido.”

Hilal ya murmusa yana tabbatar mata zaizo. Ya nufi wajen driver yana tambayarsa hope motar bata samu mats

ala ba.

Mommy ta dubi Asshe ta d’anyi k’asa da murya “Oh kiji min Hilal wai Abbansa da matarsa. Kinji yaro na taya mahaifiyarsa kishi.”

Asshe ta tab’e baki “Yo yarinya ce k’arama Anisa ma ta fita Kinga kuwa yaushe zai wani bata matsayi.”

Mommy tai yar b

azawarar dariya “Allah ya rufa asiri dai bai had’eku gida d’aya ba dan nasan da sai an kwashi ‘yan kallo tsakanin yarinyar da Anisa wataran.”

Asshe ta kuma tab’e baki “Ai Anisa gaba take da Uban nasu tinda yayi wann jarababben Aure. Sun had’e kai da saura

n ‘yanuwanta ‘yanmata yaran uwar gidana suna gaba da ubansu ya auro sa’arsu. Shiyasa ma bata cika son zaman Kano yanzu ba tafi son zama can Abuja wajenki to avoid seeing her father here.”

Mommy tai shiru tana tuna case d’in dake nata gidan. Ta d’an numfa

sa “Gwara su idan sunyi gaba da Ubansu sunada dalili.” Tai maganar tana k’ok’arin shigewa mota suna kuma sallama da ‘yaruwarta.

Kasancewar fitan sassafe tayi yasa ta samu isowa da wuri. Tuni tasa ma’aikata an soma dafe dafen abincin da za’a tarbi Daddy da

su.

Suna zaune shida ita a parlor bayan ya ida cin abinci magazine rik’e cikin hannunsa yana dubawa.

Mommy dai sai digesting maganganun da boka ya sanar da ita take. Ta rasa ta yanda za’ayi ta soma sanar da mijinta batun. Toh ma mai zata soma sanar das

hi. Cewa d’ansu yayi Aure ba da saninsu ba.? Kodai mugun asirin da aka jefesa dashi.? Ko kuma auren da Malaminta yace a masa wanda shine makarin sihirin. Ta ina zata faro. Tana tsaka da tunanin kaman wanda aka jefo sa suka sinkayo sallamansa.

Yau Mommy t

a rasa duban tausayi take masa ne ko duban sakacinta akansa.

Kallo d’aya mahaifinsa ya masa ya watsar.

Ya k’ariso hannunsa rik’eda shud’in Folder mai d’aukeda logo na Kampanin mahaifinsa jiki Wato (MB).

Gaisar da iyayen nasa ya soma yi daga nan yanda

yake tsaye bayan kujera dan yasan he’s always not welcome. A gidan da ya kamata ya kira da home.

Mommy ce ta amsa gaisuwarsa yau d’in da sakin fuska. Ga wani mugun sanyi da tayi. Mahaifinsa kaw bai samu zarafin amsa masa ba.

Mommy ta d’anyi murmushin da

yafi kama da yak’e tana duban mijin nata da kacaukam hankalinsa Ke bisa Magazine d’in dake hannunsa. Wani article ne ya d’auki hankalinsa yanda aka rubuta ‘FG to approve the billion dollars bridge project to Maitama Builders.’ Project din da Haidar keta f

ad’I tashi akai ganin an zab’esa matsayin Project Manager.

Mommy ta d’anyi gyaran murya “Engr Haidar na gaidaka.”

Har lokacin idanunsa naga magazine d’in “Na ganshi ai.. Sai ya fad’i abinda ya kawo shi. Yai maganar ko kallon yanda Haidar yake baiba.

Ha

idar ya had’iyi bak’in cikin da ya tokare masa mak’oshi.

Mommy dai gaba d’aya jikinta a sanyaye yake yanzu tinda Malaminta ya sanar da ita abinda Ke faruwa. Ya zama dole ta bada himma wajen had’in kan ahalinta bazata bari azzalumai suyi nasara akansu ba.

Ta dubi Haidar wanda ya kafe mahaifina da ido kaida gani kasan ba kallon komai yake masa ba face tsana. Ta k’ak’aro murmushi “Haidar you heard your Dad.. Ka shigo ka gabatar masa abinda ya kawo ka nasan ya shafi aiki tinda ga company’s folder hannunka.

B

ai dubi Mommy ba tinda dukansu haushi suke basa ya k’arasa yanda mahaifinsa yake. Ya aje folder d’in gefensa kad’an “This is the new proposal my team and I have been working on.. It contains all the details, the construction deliverables.. The scope and bu

dget of the project..” Ya d’anyi fasali jin bai amsa sa ba kafin yaci gaba “You..can go through it and see, before we present it to the board of directors..”

Har lokacin bai amsa sa ba. Kaman ba dashi yake ba haka Daddy yayi. Haidar ya kuma had’iyan k’un

cinsa. Duk abinda mahaifinsa zai masa akan wann project d’in ya zama dole ya shanye. Alk’awari yayi sai yasa mahaifinsa ya cinye duka kalamansa. He never backs down. He must fulfill all his promises. Zai wanke kansa zai kuma sa mahaifinsa ya cinye kalamans

a sann daga k’arshe he will personally take the company down to the ground. To the last kobo. Ya ranste sai ya tarwatsa mahaifinsa da kansa.

Sai matse file d’in yake cikin hannuna jijiyoyin jikinsa na kuma tashi kaikace ketata zai.

Muryar Mommy ya sinka

yo tana tausan mijin nata da yaji bayanan d’an nasa ya kuma sauraresa.

Kaman bazaice komai ba sai yai masa nuni da hanyar da zai sadaka da study d’insa daga nan cikin parlorn.

“You can leave it over there. Maybe, I’ll go through it when I’m less busy…

” Daddy yace yana mai rufe magazine d’in had’i da zame farin glasses na k’ara k’arfin gani “I just hope it is not one of your foolishness.”

Haidar ya rintse idanunsa yana jin abun har cikin k’ahon zuciyarsa. Bai kuma juyowa ya dubi mahaifan nasa ba yasa

kai ya shige cikin sauri kafin zuciya ta d’ibeshi.

Yana shigewa Mommy ta mik’e tabi bayansa da sauri dan wani tunani ne ya fad’o mata wanda k’ila damarta kenan akansa.

A waje yanda ya aje motarsa ta cimmasa.

Ta bud’e murya ta kirawo sunansa.

Kaman

bazai tsaya baya, sai kuma ya dakata ba tareda ya juyo ba yana mai furzar da huci a hankali.

Mommy tai saurin k’arisowa yanda Haidar ya kaikaito yana dubanta.

“What now.? Kin mance ne baki bani naki insults d’in ba shine kika biyoni waje..?” Ya fad’i ida

nunsa akan mahaifiyarsa.

Mommy tai k’ok’arin dannewa dan yanzu ta tabbata he’s not in his right state of mind.

“Kaga Haidar I’m not your enemy here.. In fact taimakonka nake so nayi.. Naga yanda kake matuk’ar so kai handling project d’in nan… Kuma nima

na tabbata kai kafi cancanta kayi d’in… I can be your ally until your achievement.”

Murmushi Haidar yai hannayensa dafe da kunkumi yake duban Mommy. Sai kuma ya girgiza kai yace “Seriously Mommy.. You wanna be my Ally..? Since when Mommy..? Yaushe kika f

ara damuwa dani da abinda ya shafe ni..?”

Mommy ta zuba masa idanu.

Haidar yaci gaba “Kinsan meye damuwarki Mommy.. Shine ya amince na jagoranci aikin sabida personal interest d’inki. Kinsan na jima da sanin ni a wajenki ba komai bane face weapon. Makami

nki.. Kuma kar ki mance na fad’a miki bazaki sake amfani dani ba wajen cimma wasu mnufofinki. Wancan Aliyun ya Riga ya mutu Mommy.. He’s long been dead.!”

Yana ida fad’in haka yasa kai ya shige motarsa sai sakin huci yake.

Zai bud’e marfin motar kenan M

ommy tai saurin dafa hannunta saman nasa. Hawaye suka soma gangaro mata. Cikin tsananin rawar murya take furta “Haidar… What did they give you.. What have they done to you to turn you against us like this..?”

Cikeda k’osawa ya zame hannun Mommy daga sama

n nasa “Ba hawayen da zaki zubar da zaisa na yarda dake Mommy. You destroyed that bond tin da jimawa. So kar ki saka ma kanki ciwo Mommy.. I do not give a damn about this family. I’m doing this project for my own personal interest of course. Kuma bazaki ta

b’a sani ba until my mission is accomplished.” Yana ida fad’in haka yasa kai zai shige motarsa.

Mommy ta bud’e murya tace “Idan ni ce Matar Aliyu Maitama har sai kazo nan ka amince da buk’ata ta kafin ya saka hannu da sunanka saman project d’in nan.!” Tan

a ida fad’in haka tasa kai ta juya cikin gida ba tareda ta kuma sauraronsa ba.

Juyowa yai yana duban Mommy yana so ya fahimci mai take nufi cikin kalamanta. Yasan mahaifiyarsa tinda ta fad’i haka tanada wani babban dalili a k’asa tana kuma so ya tank’war

a shi ne yayi wani abinda take so. Zaiyi duk yanda zaiyi ya tabbata bai fad’a tarkon da take k’ok’arin d’ana masa ba.

**

Kano.

Waya ta ida yi da Marka yanda ta sanar da ita Matar ta farka amma bata cewa komai. Kuma bata fad’i yanda danginta suke ba ba

lle a nemsu. Ga dukkan alamu idan ba mai tab’in kai bane k’ila had’arin ya tab’a mata kai.

Hilal ne ya tuk’ota zuwa asibitin. Ta dubi Marka ta dubi matar wacce Ke ta zabga kuka saman gadon asibiti.

Marka taci gaba da fad’in “Ayya Hajiya ‘yan jikokina su

na gida basu ganni ba tun jiya. Wllhi duk na gaji gida nake son zuwa ga wann asibitin babu mutane sosai balle likitoci kinsan yanda asibitin kud’in nan suke zuwan likita nada k’aida da lokaci. Tak’i magana tinda ta tashi kuka take. Inaga Hajiya kawai idan

likita yazo ruwan da aka d’aura mata ya kare kisa a sallameta ai kunyi naku Allah ya gani.”

Hilal ya girgiza kai yana duban Matar cikeda tausayi “No Ammi. Ba haka za’ayi ba. Inaga kamata yayi akaita wajen k’wararru su sake dubata. Watak’ila ta sami wani i

nternal injury. Kamata yayi akaita a dubata a bata all the treatment that’s needed. Idan ya kama mu mik’a case d’inta ma hukuma su zasu bincika yanda danginta suke. But we can’t abandon her not knowing ina danginta suke. Watak’ila sunata nemanta tin faruwa

r had’arin.”

Asshe ta katsesa “Kai Hilal nayi na musulunci tinda har asibiti mun kawota. Har wacce zata kwana da ita na bari. So bazanyi treating ciwon haukanta ba. Tafiya take tsakiyar kwalta dama can k’ila da guntun haukarta.” Ta dubi Marka tace “Marka

jeki abinki zan fad’awa nurses d’in da suke bakin duty da zaran likita yazo suna iya sallamarta.”

Marka tai godiya da fatan samun sauk’i ta fice.

Hilal ya girgiza kai zai kuma magana ta nuna masa waje “Fita mota ka sameni ina zuwa zanyi magana da mutane

n asibitin.”

Ba Don yaso ba ya girgiza kai ya fice.

Asshe zata take masa baya kenan ta sinkayo muryar Matar tana fad’in “Lafiyata garau. Kuma duk ina sauraronku. So nake ku d’aukeni ku kaini can babban asibitin koyarwa yanda mijina yake ko zan samu na ga

nshi. Tani ta hana ni ganin shi tace nida Ummul mu muka taru muka saka masa ciwo.. Ta ina zan soma neman kud’ad’en da Tani tace na nemo na jinyar Malam. Tani takai mak’ura wajen makirci da zalunci.” Ta soma kokawan sauk’owa daga gado dikda drip dake d’aure

hannunta. Fad’i take “Na tabbata tana can ta d’aura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login