Showing 108001 words to 111000 words out of 267381 words

Chapter 37 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

48



“N

ice performance Mommy.! I’m here already. I guess the show is over.” Yace yana k’arasa shigowa parlorn.

Mommy ta juyo cikeda mamaki tana dubansa. Ta kuma mutsuka idonta. Sai taji murmushi na zuwa saman fuskarta.

“Haidar.. My Son..!” Ta furta cikin rawar

murya hawaye basu daina ambaliya a fuskarta ba.

Sai Ta isa da sauri ta rungume shi kukanta na k’aruwa. Tsam ta rik’e sa cikin jikinta. Tana hawaye take furta “I knew it.. I knew You’d come back to me.. To your family. Nasan zaka dawo garemu Haidar.. Nasa

n bazaka bani kunya ba. Sabida kai d’in D’ana ne..”

Duk sunbatun nan da take ji yake ta cika masa kunne. Yai k’ok’arin cireta daga jikinsa da k’arfin gaske.

“Don’t get it wrong Mommy. Idan na dawo na dawo ne kawai sabida project d’in amma ba sabida ke d

a k’udirinki ba.” Yace yana duban mahaifiyar tasa dake tsaye gabansa tana kuka cikin sanyin jiki.

Mommy ta jinjina kai “Even so Haidar. I’m glad ka dawo sabida project d’in. Nafi kowa farin cikin dawowarka. Your wife is waiting for you Aliyu.. She’s been

waiting for you for the past two weeks..”

Bata kai aya ba suka soma sinkayo hayaniyar wata ‘yar aikin gidan tana ihu tana kiran Mommy.

Gaba d’aya Haidar da Mommy suka juyo a tare sanda maid din ta shigo tana haki.

Anisa da hayaniyar ya sanyata fitowa b

a shiri ita ta tari maid din da tambayar meke faruwa ta shigo haka tana ihu.

Cikin haki take sanar dasu ta shiga kai abinci section d’in Ummulkhair amma ta tararta a kwance lifeless.

Mommy da taji batun bagatatan saurin k’arasowa tai tana jijjiga mai aik

in tana tambayarta mai take cewa. Mai aikin ta kuma nanata binda tace.

Babu shiri Mommy ta fice ba tareda ta bi takan kowa cikinsu ba ta nufi sashen Haidar.

Yayinda Anisa taji kama an yaye mata duka damuwarta. Daga k’arshe dai burinta Ya cika.

Yanda M

ommy taga Ummul kwance k’asa tamkar maras numfashi sai ya kuma gigitata. Ta shiga jijjigata tana ambaton sunanta.

Mik’ewa tai cikin kuka tana fad’in ma’aikatan gidan su kira ambulance amma kafin tai wani aune sai ganin Haidar tai ya ciccib’i Ummul d’in Y

a nufi motarsa da ita yana Anisa ta isa ta bud’e mata bayan motar.

Mommy ta biyo bayansu cikin sauri Har lokacin hawaye take.

Anisa jikinta duk a mace ganin Haidar ya d’auki kucakar nan ya sakata motarsa harma cewa yake ta bud’e masa motar. ‘Kan uba to

h wllhi ka d’auki wofi domin kuwa fanko ce wajen gawa ce Babu rai.’ Ta fad’i haka cikin zuciyarta.

Mommy ce ta shiga bayan motar ta d’aura kan Ummul saman cinyarta yayinda Anisa tai maza ta shige gaban Motar Haidar ke driving.

Yanda hankalin Mommy ya tas

hi dole ta baka tausayi. Dan kuka take da gaske tana fad’in Ummul ta tashi kar ta tafi ta barsu ga mijinta Ya dawo gareta.

Daga Anisa Har Haidar d’in sumbatun Mommy ya cika masu kunnuwa cikin motar. Allah Allah suke a isa asibiti ko sun huta da sunbatun

Mommy.

Suna isa Ya kuma d’aukanta suka nufi cikin asibitin da ita. Take Likitoci suka amsheta aka nufi ER da ita.

Nan suka zauna suna jiran ba’asi daga Drs. Har lokacin Mommy kuka take yayinda Anisa ke addu’an Allah yasa a fito da sakamako mai dad’in

sauraro a kunnuwarta ma’ana ta mutu.

Ganin Mommy bazata daina kuka ba yasa Haidar mik’ewa Ya zira hannayensa cikin aljihun wandonsa. Kukan da Mommy take irritates him musamman idan yaji tana ambaton yarinyar ta tashi mijinta ya dawo gareta. Gaba d’aya ji

yake zuciyarsa a cunk’ushe. Meyasa ma bazai tafi ba.? Zaman me yake a asibitin.? He did what he had to do sanda yaga yarinyar kwance lifeless. Ya kawota asibiti. Toh zaman mai zaici gaba da yi.? Yai gajeren tsaki sanda ya kuma duban Mommy dake ci gaba da

matsan hawaye. Wani b’angare na zuciyarsa na sanar dashi ka zauna ko dan mahaifiyarka. Ya kuma yin tsaki wai shi Haidar ke yin abu dan mahaifiyarsa matar da bata da wani buri bayan taga ta k’untata masa. Ya kuma yin gajeren tsaki yana mai duban k’ofan ER d

in.

Can gefe ya matsa dan baya son sauraron kukan da Mommy take.

Anisa sai satan kallonsa take da duk wani motsinsa.

Wayarsa ce ta soma ruri Ya fito da ita daga aljihu nan yaga Dareen ke kiransa. Bai amsa ba sai Ya maida wayar aljihu Har ta k’arashi

ringing d’inta.

Hankalin Anisa sosai ya kuma tashi ganin Haidar baibi takan wayarsa ba sann ga damuwa k’arara Ya nuna saman fuskarsa. Mai hakan yake nufi .? Ba dai Haidar damuwa yai da wann kucakar ba Wanda ko wayarsa Ya kasa amsawa. Dan ita duk a nata t

unanin damuwar halinda Ummul ke ciki ne ke d’awainiya da Haidar d’in tsaban abinda ta raya ma ranta kenan. Zuciyarta sai wani irin k’una yake mata tana ci gaba da addu’an Allah yasa a fito masu da gawan Ummul kowa ya huta.

A can gidan Haidar d’in kuwa h

ankalin Dareen yayi dubu Ya tashi. Haidar d’inta ne ke ignoring calls dinta yau. Mutumin da ko important meeting yake zai excusing kansa ya d’aga kiranta musamamn da taga an d’auki lokaci bai returning call din ba. Ita kad’ai sai safa da Marwa take tana ji

n zuciyarta na mata d’aci. Tana a haka taga wayan Shadow na shigo mata.

SameenaAleeyou

📚

*AUREN WATA UKU..!*

*31*





Sameena Aleeyou…✍

🏽

*

Tana d’aga kiran ta sinkayo muryarsa daga d’aya b’angaren “I heard that you’re back in the coun

try.. Ya akai banji hakan daga bakinki ba..?”

Shiru batace dashi komai ba sai hucin da take dan gaba d’aya zuciyarta a cunkushe take tinda ta kasa samun Haidar a waya. Muryar Shadow ya kuma dakan dodon kunnenta “Dareen are you sure you are not hiding some

thing from me.?”

“Toh mai zan b’oye maka. Yes mun dawo amma ban samu chance na sanar dakai hakan ba. After all, jiya ne kawai muka dawo k’asar. Is not as if na shafe kwanaki ne da dawowa bakaji daga gareni ba.”

Katseta yai “Don’t you dare take me for a f

ool. I know you so well. Na sani idan kina shirya wani abun.. Let me warn you Dareen. Idan kika shirya wani abu a bayan ido na believe me zaki d’and’ani kud’arki.”

Tai murmushin takaici “Is that a threat.?”

Murmushin shima yai “You know me so well. I don

’t keep people around with threats. Idan har zanyi abu lokaci d’aya nakeyi ke kinfi kowa sanin hakan.”

Yai gyaran murya kafin yaci gaba “Ina Haidar..?”

Ta kuma furzar da huci “How would I know.? Ya fita bai sanar Dani ba.”

“You should know Dareen. Becau

se that’s what you are there for. Ban ajiyeki tareda dashi ba just for you to have fun with him kin fahimta.”

“Oh excuse me! You don’t own me.. And you are not the one calling the shots here. Ni ce nake rayuwa da Haidar a halin yanzu… Barazana kawai kake

da kake cewa tulun da aka d’aure kurwar Haidar aka shata layin k’iyayya tsakaninsa da iyayensa na wajenka.. Kuma bari kaji from now henceforth bazan bari ka cutar da Haidar ba. Babban kuskuren da ka tapka shine da ka min sanadin shiga rayuwarsa. A halin ya

nzu Haidar dani are one.. He’s my husband da nake sonsa da duka zuciyata.. Bazan bari kai ko wani ya cutar dashi ba. So if I were you zan maida makaman yak’ina.”

Murmushi yai daga d’aya b’angaren “Haka kika ce.?!”

Bata bashi amsa ba sai sakin huci da tak

e.

Ya kuma murmusawa “Fine. Zamu gani tsakanin mu biyun Who owns Haidar..!” Yana Ida fad’in haka ya katse kiran.

Dareen taci gaba da kallon wayar tana sakin huci.

**

A can asibiti kaw suna nan zaune jiran tsammani Mommy ta dubi Anisa wacce dama saura

su biyu ne zaune wajen “Idan likitocin Sun fito kimin magana.”

Jinjina mata kai Anisa tai had’ida amsawa. Tabi bayan Mommy da kallo wacce hankalinta ke ga wayar salularta. Mommy tana ficewa wani corridor d’in ta soma waya da ‘yaruwarta Asshe. Nan take sa

nar da Asshe abinda ke faruwa.

Baki har na rawa Asshe ke tambayarta “Haidar..? Haidar fah..? Ina Haidar Haidar yana lafiya.?” Dan ita duk a tunaninta aikin gama ne Ya riga Ya gama tsakanin Haidar da Ummul.

Mommy ta girgiza Kai kad’an “Asshe Haidar lafiy

a yake. Hasalima shi yai driving namu to hospital. Amma meyasa kike tambayar lafiyar sa.?”

Sauk’e ajiyan zuciya Asshe tai tana jin gumi da ya tsartsafo mata na bin jikinta yana sauk’a. Lokaci guda tai k’ok’arin saita kanta “Toh amma Aunty Kwaise is possib

le asirin ne yai aiki. Is possibile amfanin yarinyar ya kare ne. Tinda ita d’in makarin asiri ce.”

Kaman Asshe na ganinta haka Mommy ta girgiza kai “Ta ya hakan zai kasance bayan Haidar shigowarsa gidan kenan. Babu wata alak’a data shiga tsakaninsa da yar

inyar. Ko kin mance mai Malam Ya sanar damu. Har sai wata alak’a ta auratayya ta gifta tsakaninsu kafin ta karya asirin.”

Daga d’aya b’angaren Zuciyar Asshe yaci gaba da tsinkewa. Toh ko dai Anisa tayi shashashancinta ne ta bama yarinyar turaren bata zu

bar ba kaman yanda ta umarceta. Kodai har mai aukuwa ya auku ne ba tareda Kwaise tayi la’akari ba. Wann abu da d’aure kai yake. Toh amma idan Har illan dake jikin yarinyar bai shafi Haidar ba kaman yanda Dije ta sanar da ita. Ta iya yuwa da gaskiyar Suwaib

a Dije fansarta kawai take son d’auka kan yarinyar da uwarta tinda gashi yarinyar ce ke kan gargarar mutuwa kaman yanda bokansu Ya sanar dasu ba Haidar ba. Idan Har hakan ta kasance zatafi kowa farin ciki.

Muryar Mommy ya kuma katseta “Kaina Ya k’ulle gab

a d’aya Asshe. Shin idan yarinyar nan ta mutu a haka wann na nufin asirin dake jikin D’ana Ya karye ne kokuwa dai Har yanzu da asirin jikinsa.?”

Asshe ta sauk’e ajiyan zuciya tace “Aunty Kwaise bakida tabbacin idan Haidar bai shiga b’angaren yarinyar nan

ba a tsakanin shigowarsa gidan. Kinsan abu ne da aka had’a da asiri kuma wann turaren da Malam Ya bamu ya tabbatar mana shi d’in tamkar magnet ne Wanda zai janyo Haidar zuwa gareta..”

Mommy tai Shiru kaman mai nazari sai kuma ta girgiza kai “Asshe al’amar

in nada rikitarwa amma inada tabbacin a lokacin da muka tsinceta kwance k’asa kaman gawa a wann lokacin Haidar ya soma sanyata a idonsa.. Tabbas tayi amfani da turaren inada tabbacin hakan amma bana tunanin amfani da turaren kawai zaisa ta Mutu kafin Haida

r ya samu kusanci da ita.”

Haidar da isowarsa wajen kenan yai tsaye Cak yana sauraren kalaman Mommy na k’arshe. ‘Turare.? Mutuwa kafin shi Haidar ya samu kusanci da yarinyar.?’ Ya nanata kalaman da yaji Mommy tace cikin zuciyarsa.?

A razane Mommy ta juy

o tana dubansa duk a birkice. Kana ganinta kaga maras gaskiya. Tai saurin canza maganar da take cikin wayar tana mai katse kiran. Ta k’ak’aro murmushin da yafi kama da yak’e ta sakar masa “Em.. Em.. Haidar ashe kana nan baka tafi ba..? Na zata ai ka tafi.

.?”

Ya girgiza mata kai kad’an alamun a’a “Ina nan Mommy.. Naje sallah ne. Why.? Is there something I should know.?” Yai tambayar yana tsareta da idonsa.

Tai saurin girgiza masa kai alamun a’a.

Ya jinjina Kansa a hankali ba tareda ya nuna mata yaji kod

a word d’aya daga wayan da ta gama ba. Ya d’an ci gaba da takowa kusanta har lokacin Mommy a tsarge take. Haidar na hankalce da ita.

“Any news about the girl’s condition.?” Ya tambaya yana tsare Mommy da ido.

Zuciyarta Ya kuma tsinkewa tana tuhumar kant

a mai hakan yake nufi.? Kenan Haidar Ya damu ne da Ummul.?

Bata kai ga samo amsa ba suka hango wani Dr ya fito daga ER d’in. Mommy ce ta nufe shi cikin sauri tana tambayarsa Ya jikin Ummul. Yayinda Anisa ma ta taso daga yanda take zaune ta nufo su.

Hai

dar kaw daga can yanda yake tsaye yana karantar yanayin Mommy. Meyasa take nuna damuwa gameda yarinyar bayan ga abinda yaji a waya kaman mutuwa take nema ma yarinyar.? Meye nufin Mommy akan yarinyar.? Mecece manufarta na aura masa yarinyar.? Tunani daban d

aban cikin zucjuarsa. Muryar Dr ya sinkayo yana fad’in “She’s still not out of danger. A halin yanzu bazamu iya bada shaida akan komai ba. Anything can happen.” Ya numfasa kafin ya dubi Mommy “Is she your Daughter.?”

Kafin Mommy ta bada amsa Anisa tai tsu

lum ta bud’i baki tace “No she’s not her daughter.”

Mommy ta k’ara da “She’s my Son’s wife.. Dr meke faruwa da ita ne.?”

Dr ya d’anyi Jim sai yace “Where’s her husband then.? I’d like to speak with him.”

Mommy ta juyo a d’arare tana duban direction din

da Haidar yake. Anisa ma shi take duba tana jira taji yayi rejecting hakan amma sai taji akasin hakan. Abun mamaki muryar Haidar suka sinkaya yana fad’in “I’m here. I am her husband.”

Daga Anisa Har Mommy cikin tsananin shock suke duban Haidar Wanda tuni

ya soma takowa kusansu.

Dr yace “May I have a word with you.?”

Haidar ya jinjina masa kai alamun eh “Sure.. After you.” Ya k’arashe yana alama ma likitan da hannu.

Dr ya jinjina masa kai kafin yasa kai ya nufi ofishinsa Haidar na take masa baya. Daga M

ommy har Anisa mamaki ya hanasu rufe baki. Babu Wanda ya tasammaci haka daga Haidar. Ko ita kanta Mommy da takeda yak’inin maganin bokansu ka iya tasiri akan Haidar tinda ya sanar dasu turaren da suka ba ma Ummul ta dinga amfani dashi zai janyo Haidar gare

ta batai zaton abun zaizo da sauk’i haka ba. Kenan Watak’ila d’aukanta da yai cikin hannunta har ya shak’i turaren.? Gaba d’aya kan Mommy ya k’ulle ta rasa fahimtar tunanin da take. Gaba d’aya duk abubuwan dake wakana Sun k’ulle mata kai.

Anisa ta sauk’

e ajiyan zuciya a hankali tana tinanin kiran k’awarta Leenah dan sanar da ita halinda ake ciki.

**

Dr ya dubi Haidar kafin yace “Amma kana ina har ake barazanar d’aukar rayuwar matarka..?”

Haidar ya jinjina kai lamun nuna rashin fahimta “Ban fahimceka

ba Dr. Barazanar d’aukar rayuwarta kaman yaya.?”

Dr ya jinjina kai yace “Sakamakon gwaje gwajen da mukai mata na gaggawa ya tabbatar cewa she’s being poisoned… Guba ne da ta shak’esa ta numfashi Wanda ya harba huhunta. Most likely cikin turare aka saka gu

ban.”

Haidar yai shiru yana had’a maganganun Likitan da wayan da yaji Mommy nayi. Sai girgiza kai kad’an yace “Turare.?”

Dr ya jinjina kai alamun eh kafin yaci gaba “Irin wann guban akan sanya shi ne cikin wani scent da mutum ke amfani dashi slowly yake

lalata lungs d’in mutum ba tareda an ankara ba. Shi irin wann guban anfi amfani dashi ne idan ana so mutum ya samu slow and painful death. Fortunately guban baiyi wani tasiri jikin matarka ba. But we can’t say she’s completely out of danger har sai mun mat

a minor aiki a lungs d’insa munyi flushing sauran wann guban to prevent it from spreading. Muna buk’atan saka hannunka Shiyasa na buk’aci ganinka a sirrance. Sann abu ne da Ya danganci criminal act kaga dole ai taka tsantsan tinda ba’a tantance waye perpet

rator din ba. Koda tana k’ark’ashin kulawarmu a asibiti rayuwarta na cikin had’ari Har sai an kama mutumin dake k’ok’arin ganin bayan rayuwarta.”

Shiru Haidar yai Zuciyarsa Ya kasa aminta da abinda Likitan nan ke fad’i da maganar da yaji Mommy tayi cikin

waya. Idan ya had’a maganan Mommy da maganan Likitan nan. The whole thing yanada alak’a da turare kaman yanda yaji Mommy tace sann ta ambaci mutuwa a ciki. Ga turare ga mutuwa. Ga kuma abinda Dr ya sanar dashi cewa anyi poisoning yarinyar ne ta cikin turar

e. Toh idan Har Mommy kashen yarinyar takeda niyya meyasa ta aura masa ita.? Meyasa zatai poisoning d’inta.? Shin kodai Mommy shi take so tai poisoning shine ta b’ullo ta wann hanyar ta aura masa wann yarinyar ta saka poison din cikin turarenta dan shima y

a shak’a su hadu su Mutu gaba d’aya tinda gashi ta matsa sai yazo ya zauna da yarinyar. Shin wann shine shirin Mommy na k’arshe akan shi ta kashe shi ba tareda kowa ya zargeta ba.? Shin har haka Mommy ke masa k’iyayya.? Shin Anya Mommy ita ta haifeshi.? An

ya shi d’aya ne daga cikin wann ahalin.? Muryar Likitan ne Ya dawo dashi daga duniyar tunanin da Ya tafi yanda Likitan Ya d’an murmusa dan dik shi a tunaninsa Haidar tunanin aikin da za’ai ma matarsa a lungs yake kar aje a tab’a mata lungs dinta sabida san

in Had’arin irin aiki da Ya danganci organs.

“Look Engr. It’s just a minor surgery. We call it Minimally invasive thoracic surgery.” Ya d’an numfasa kafin yaci gaba “Is a way of performing surgery in the chest through small incisions, without making larg

e cuts in the body, and it does not require spreading apart of the ribs. We use camera and instruments to get to the lung through small incisions in between the ribs. Kaman ma ba’ayi wani aiki ba haka jikin matarka zai zauna. But it’s necessary a dakatar d

a guban daga yad’uwa cikin jikinta.” Ya k’arashe yana mik’a ma Haidar pen da form.

Haidar ya jinjina kai a hankali kafin ya karba yai signing a yanda aka buk’aci Ya saka hannu. Har lokacin ya kasa yarda da abinda ke faruwa. Ya dubi Dr yace “Dr I want this

to stay between us please. Ban jima da dawowa k’asar ba so bansan waye ke farautar rayuwar matata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login