Showing 234001 words to 237000 words out of 267381 words

Chapter 79 - AUREN WATA UKU COMPLETE

ita ka jefar da ita gashi nan Nima na faruwa akaina.. Ban tab’a ganin azzalumin mu

tum macuci irinka ba Hisham.. Kuma nayi alk’awari ma Haidar sai yanda k’arfina Ya k’are wajen bankado gaskiya da bayyana true color dinka. Bazaka sake samun dama akaina ba Hisham.!”

Murmushi yai kad’an had’ida gyara zamansa “Neesa kenan. Kina magana kaman

baki san wane irin serious crime ake tuhumar Ki dashi ba.. Tuhumarki ake da kisan kai Anisa. Bana jin akwai Wanda zai iya wankeki daga wann babban tuhuma da ake Miki koda kuwa Haidar ne.” Ya kuma gyara zama “You are alone in this Anisa. Ahalin ki Sun juya

Miki baya.. Ina nufin mahaifinki da mahaifiyarki.. Sann Haidar da kika dogara dashi ki yarda dani yana yin komai ne to win Ummulkhair back.” Ya kuma karkacewa yana gyara zamansa “For your information Neesa.. An maida Auren Ummulkhairi da Haidar kinga kuwa

Haidar baida sauran dalili da zaisa Ya taimaka Miki Ya cireki daga cikin wann tuggu.”

Anisa ta saki baki da mamaki tana dubansa “An maida Auren Ummul da Haidar.?”

Ya dan tab’e baki kad’an kafin Ya kuma gyara zamansa “Abu d’aya zai cireki daga wajen nan

Anisa shine Ki amince zaki Aureni..!”

Kaman sauk’ar aradu haka taji batun. Ta d’ago da mugun mamaki tana dubansa “Ni Aneesa kake cewa na Aureka.?!”

Hisham ya murmusa “Ba don Ina sonki zan Aureki ba Anisa.. Sai don kawai ina so na taimaka Miki na cireki d

aga cikin wann k’ulli mai wuyan warwarewa da kike ciki.!”

Girgiza kai Anisa take tana dubansa cikin shock “You have no shame Hisham.. You are a demon.! Baka da zuciya cikin k’irjinka.. Tir da D’anAdam irinka..! Ta nan ka b’ullo..? Toh ka sani ni Anisa baz

an tab’a auren mutum irinka ba.. Never.!”

Hisham ya mik’e yana gyara zaman suit d’insa “Think about my offer Neesa.. Wann shi kad’ai ne hanyar tsira da Ya rage Miki if you don’t want to rot in here.!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice.

SameenaAlee

you

📚

*AUREN WATA UKU..!*

*60*





Sameena Aleeyou…✍

🏽

*



A parlour Hisham ya iske Daddy after dinner. Mommy na zaune gefensa suna tattauna yanda auren Haidar ya kasance. Da yanda Daddy da Abba suka shammacesu gaba d’aya da al’amarin auren.

Ya sh

igo da Sallama saman bakinsa. Suka amsa masa da sakin fuska Dddy yana masa iso da ya shigo ciki ya zauna. Can bakin carpet Hisham ya zauna had’ida risinawa kaman dai yanda yakeyi gaban Daddy a ko Yaushe.

Daddy ya dubesa cikeda kulawa dan ya kula da yanayi

n D’an nasa kaman dai babban Al’amari ke tafe dashi koda bai furta ba.

“Son, lafiya dai koh..? Inji komai lafiya..?”

Hisham ya jinjina Kansa kad’an “Lafiya Daddy.. Dama..” Sai ya d’anyi fasali ba tareda yaci gaba ba.

Mommy ta soma k’ok’arin mik’ewa tana

fad’in “Bari dai na baku waje.”

Hisham yai saurin dakatar da ita da fad’in “No Mommy.. You should also stay.. Please...”

Mommy ta dan yi still sai tace “Shikenan ba damuwa.” Ta koma mazauninta.

Hisham ya dan gyara zamansa kad’an sanda Daddy yace “Muna

sauraronka.”

“Daddy dama.. Ina so na nemi Auren Anisa ne idan babu damuwa. Idan hakan ya muku.. Ina nufin both you and Mommy.”

Da mamaki Daddy da Mommy suka dubi juna.

Mommy ta girgiza Kai kad’an “Wace Anisar.? Kana nufin Anisa my niece.?”

Hisham ya

jinjina Kai kad’an “Eh Mommy.. Idan har babu wani damuwa.”

Daddy ya katsesa da fad’in “Ka kuwa san mai kake fad’a Hisham.. Auren Anisa fah kace. Anisa dake facing court case.?”

Hisham ya jinjina Kansa cikeda risinawa “Eh Daddy.. Kasancewar akwai court c

ase akanta bazai hana Aurenmu ba. In fact wann shine dalilin da yasa na yanke hukuncin neman Aurenta. Dan na fitar da ita daga cikin situation d’in da ta tsinci kanta ciki Wanda ba komai bane face jarabawa daga Ubangiji.” Ya dan numfasa kafin yaci gaba “Da

ddy Anisa tayi kuskure amma ta fahimci kuskuren ta kuma ta gyara.. Dukanmu munga yanda tai repenting bayan ta fahimci kuskurenta.. We shouldn’t abandon her.. Ina nufin dukanmu munyi kuskure a baya.. Kuma mun yafi juna. Bai kamata mu kyale Anisa ita kad’ai

cikin wann ba. Daddy ni zan Auri Anisa matuk’a hakan yayi muku.”

Muryar Haidar suka sinkaya Wanda shigowarsa parlorn kenan yana fad’in “Did I hear that right.? Zaka nemi Auren Anisa.?” Yai tambayar cikin tsananin shock yana duban Hisham d’in.

Hisham ya

murmusa had’ida jinjina Kai yana duban Haidar d’in “Eh Haidar.. You heard that right.. Ina so zan Auri cousin d’inka Anisa… I hope kaima na Sami goyon bayanka D’anuwa.”

Murmushin takaici ne ya kufce ma Haidar “You are unbelievable.! You really have no sh

ame.! Ta nan ka b’ullo..? Zaka auri Anisa..Just what are you up to this time around.? Mai kake shiryawa Hisham.?!”

Daddy ya dakatar da Haidar “Haidar ya isa haka.. Kar ka fara.”

Girgiza Kai Haidar yake yana duban Daddy “Daddy don’t tell me har yanzu baka

gane wann makaryaci mai fuska biyun ba..! Daddy I’m sure idan ya shirya Auren Anisa wata manufa yake dashi amma ba don yana son Anisa ko yana so ya fiddata daga situation da take ciki ba Wanda shi ya jefata.. Daddy this monster here only think of himself.

. If he says he wants to marry Anisa that’s because yanada wata manufa da yake so ya cimma.! I’m very sure he’s up to no good.!”

“Enough Haidar.!” Daddy ya dakatar dashi kafin yaci gaba “Kai a rayuwa ba’a yafiya aka yafe maka.? Meyasa kullum kakeda negat

ive thought Akan D’anuwanka Wanda ba abinda yai maka face alkhairi..! Ka fad’a mun abu d’aya da yayi na cutar dakai..! Idan aka Ummulkhair ne ya maka bayani ya kuma janye idon shi Akan iyalinka a lokacin da ya fahimci Kai take aure. Sann na d’auka an rufe

wann babin a jiya da aka maida aurenka da iyalinka.! Yanzu yazo da batun yana Neman Auren Anisa kace ba haka ba.! Toh mai kake so yayi Haidar.? Ka sanar Dani mai kake so ya aikata kuma.!”

Shiru Haidar yai ba tareda ya kuma cewa komai ba. Yayinda Hisham y

a soma bama Daddy hakuri cikin kwantar da murya da k’ok’arin kwantar masa da hankali. Ya dubi Haidar da idanunsa suka kad’a sosai. Ya sassauta murya “Haidar, ina fata mu samu daidaiton fahimta watarana. I hope a day will come.. Ranan da zaka sake amincewa

Dani. Ka amince bani nufinka da komai face alkhairi.” Ya dan numfasa “Ka yarda Dani, da kyakkyawan manufa nace zan nemi Auren Anisa. Amma idan kanaga bata cancanci miji kaman ni ba.. Ba matsala sai na hakura.After all, ba yau ne rana na farko da na fara ne

man Aure ana rejecting dina ba.”

Kalamansa sai ya tuno ma Daddy labarin da Hisham d’in ya basu lokacin da yaita Neman aure ana rejecting d’insa sabida rashin cikakken asali. Wanda Daddyn yake ganin hakan kaman laifinsa ne. Now is the right time for him to

be a father to his son.

Daddy ya dubi Hisham yace “Ya isa haka Son. Just don’t mind your brother. A hankali wataran zai fahimceka. Idan Kana so ka auri Anisa zan nema maka Aurenta. Ba Anisa kawai ba. Kai Ko ina kake so kaje neman Aure ni mahaifinka Aliyu

Maitama zan tsaya maka.. Ko ‘Yar gidan waye kuwa. Ba Wanda zai sake maka gorin asali.”

Hisham ya murmusa cikeda Jin dadi. Kaman zai kuka yake furta “Thank you Daddy..! For the first time in my life.. Naji a raina Nima inada mahaifi kaman ko wani D’a.”



Ya kamata kaji haka koda yaushe. Because your Dad will always be here for you kaji koh.”

Girgiza Kai kurum Haidar keyi kafin yasa kai ya fice daga parlorn dan bazai jure kallon Kayan bak’in ciki irin wann ba. Mommy ta mik’e tabi bayansa.

Daddy ya dubi H

isham yace “Amma wani hanzari ba gudu ba.. Kanaga za’a bada belin Anisa cikin sauk’i musamman yanzu da iyayen yarinyar can Dareen suka bayyana kuma suke Neman hakkin Ran ‘yarsu.?”

Hisham ya jinjina Kai “K’warai Daddy. Da ace Anisa bata amsa cewa da gangan

ci tabi kan Dareen da mota ba Tabbas da abin yafi zuwa da sauk’i. Babban abinda zaisa a bada belin Anisa a halin yanzu shine rashin ganin gawar Dareen Wanda ganin gawar Dareen ne kad’ai zai tabbatar da mutuwar ta. Kaga zamuyi amfani da hakan a court. Da ta

imakon k’wararren Lauya kotu zata amince ta bada beli koda za’a ci gaba da Shari’ar. Daddy ita kanta Anisa da ta bige Dareen batada tabbacin Dareen ta Mutu ko bata Mutu ba tinda bataga gawar ta ba balle ta tabbatar kaman yanda ta fad’i a statement dinta. S

o bazai yuwu a yanke ma Anisa hukunci ba tareda k’wakk’waran dalili ba. Anisa ta cancanci second chance kaman kowa a rayuwa Daddy. Kuskuren da ta aikata bazai zama dalili da zaisa a juya mata baya ba. Daddy idan ka amince min zan tsaya tsayin daka har sai

na tabbata Anisa ta Sami freedom din data cancanta. Dan rashin adalci ne a barta a rufe ba tareda an tabbatar da ta aikata laifin kisan ba. Idan har daga baya wani abu ya bayyana.. Ina nufin aka samu gawan Dareen ko wani k’wakk’waran dalili da zai tabbatar

da mutuwar Dareen.. Ka yarda dani Daddy ni da hannuna zan mik’a Anisa ma hukuma, Alk’ali yai hukunci koda bayan ta zama matata. Zan kuma d’auki hakan matsayin k’addara Daddy dan D’anadam bazai wuce k’addararsa ba. Daddy I believe Anisa ta cancanci Rayuwar

farin ciki mai cikeda ‘yanci a Gidan Aurenta koda na dan lokaci kad’an ne. Ina fata ta Sami wann opportunity d’in a rayuwa ta samu wann experience din koda na dan lokaci kad’an ne.. Balle ma in sha Allah baza’a sameta da laifin kisan ba.” Ya k’arashe cike

da kulawa.

Mommy dake tsaye bayan parlorn duk sai jikinta yai sanyi. Sai ta rasa tausayin waye zataji. Anisa dake tsare ne ko kuwa Hisham d’in ne dake kokarin nema mata ‘yanci Wanda take ji kaman dukkansu sunyi failing Anisar sai Hisham ne zai sadaukarwa

mai girma ga d’iyar ‘Yaruwar tata.

Daddy ya dafa kafad’an Hisham “I’m proud of you Son. Kanada zuciya mai kyau kuma mai yalwa. Allah ya maka albarka da wann sadaukarwa mai girma da kake k’ok’arin yi. Amma ina so ka fara tuntubar mahaifyarka da batun. Mu

nyi waya ta kuma sanar Dani gobe ‘yanuwanta zasu mata rakiya zuwa nan Abuja. Yanada kyau kaji nata ra’ayin da shawarin.”

Hisham ya amsa da “Shikenan Daddy zanyi kaman yanda kace in sha Allah.”

Daddy ya amsa da “Maddallah. Allah yayi jagora.”

Hisham ya s

ake amsawa da Ameen kafin yai Sallama ma Daddyn ya fice zuciyarsa wasai.

Washe gari kuwa Hajja ta samu tarewa zuwa gidan mijinta Engr Aliyu Maitama a nan birnin tarayya tareda rakiyan tsirarun ‘yanuwanta. Daddy yaso ya raba musu gida ita da Mommy amma sai

Mommyn harma da Hajjan suka zab’i zaman tare a gida d’aya. Hakan yasa tuni aka gyara ma Hajjan nata sashen a nan cikin gidan.

**

Anisa bataji mamakin ganin Haidar ya kawo mata ziyara ba dan tasan izuwa wann lokacin labari ya isa masa cewa Hisham naso y

a aureta.

Haidar ya tsareta sosai da ido kafin ya gyara zamansa yace “Tell me, is it true… Da gaske ne wann D’aniskan ya miki tayin aurensa.?”

Ta furzar da huci kad’an had’ida rausayar da ido “Believe me I couldn’t believe it either.. I mean how shamele

ss of him. Ta ya zai soma cewa zai aureni bayan ukuban da ya jefani ciki..! Ka yarda dani, Ya b’ullo ta wann salon ne bayan da yaji an maida Aurenka da Ummulkhair. Na tabbata wani abun yake son shiryawa.”

Haidar yai shiru kaman mai nazari “And you.? What

are you suggesting.?”

Anisa taci gaba da jinjina Kai tana dubansa “Zan amince da Tayinsa. Zan aure shi.”

Da tsananin mamaki Haidar ke dubanta “Did you hear yourself. Kin kuwa ji mai kika fad’a.? Zaki amince ki amshi tayinsa.? Zaki amince ki aure shi..?

Are you going to let him use you for the second time.?!”

Murmusawa tai kad’an “You might know Hisham as a friend.. Amma ni na sanshi ne a matsayin mugu. Hisham is a very coning person. Idan yace zai Aureni kaman ya sadaukar da wani portion ne na soyayyar

da yake ma Ummulkhair. Knowing Hisham bazai tab’a sadaukarwa mai girma irin wann ba ba tareda ya samu wani babban outcome ba. Idan har yace zai Aureni ka yarda dani akwai wani shiri babba da yake kullawa ta k’ark’ashin k’asa. Kar ka mance Hisham ya kawo ma

ce cikin rayuwarka har ta aureka kukai rayuwar aure ba tareda ka ankare ba. Wanda duk zai aikata abu makamancin wann ba k’aramin shed’ani bane. So na sani Hisham ba mutum bane da za’ayi under estimating d’insa. Duk abinda yake yi is well calculated. Amma k

a yarda dani aurena da yace zai yi wann karon shine babban miscalculation mafi muni da zai tapka a rayuwarsa. Ni ba wann shashashar Anisa da ka sani a baya bane. Bazan Auri Hisham dan na bashi dama yai amfani Dani ba. Saidai ni nayi amfani dashi. Wann karo

n zai tone ramin da zai rupta ne a ciki da Kansa ba tareda ya ankare ba. Zan tabbatar mishi da cewa ni mace ce kuma yayi kuskuren underestimating dina. Ni yafi cancanta na bayyana asalin waye Hisham sabida Dani yai amfani. Kuma aurensa da zanyi shi zai ban

i dama na samu duk wani kusanci dashi sann na yaye rufin fuskarsa kowa yasan waye shi. Ka yarda dani Hisham bazai tab’a barinku ku samu peace ba kaida Ummulkhair matuk’a yana nan a kura lullub’e da fatan akuya.”

Haidar ya girgiza Kai kad’an “No.. No Anisa

. I won’t let this happen. Ina nufin bazan bari ki jefa rayuwarki cikin had’ari ba dan kawai asirin Hisham ya tonu. Kin kuwa san mai ake nufi da kalmar Aure.? Ta ya zaki amince ki auri mutumin da ke kanki kinsan ba mutum bane. Anisa Aure is a life time com

mitment.. Ke ‘Yaruwata ce kuma k’anwata. Koda ace bamu had’a alak’a ta jini ba bazan bari wann devil d’in ya kusanceki ba balle har akai ga maganar Aure. Aure is serious commitment. Na d’auki al’amarin Aure da wasa a farko naga yanda ya juya mun. Bazan bar

ki ki d’auki wann path din ba. Bazan bari kiyi gambling da rayuwarki ba dan kawai kina so ki tona asirin Hisham.” Ya dan furzar da huci yana jinjina Kai kad’an “Akwai ways da yawa da za’a Kama shi. Yanzu haka nasa ana bincike kan iyayen Dareen.I believe a

hankali through wad’ann mutanen zamu samu wani haske gameda gaskiyar al’amarin mutuwar Dareen ko nace b’acewarta. If she’s alive ita kad’ai ce zata iya kawo k’arshen yaudarar Hisham.”

Anisa ta murmusa “And what if she’s dead.? Zan tabbata ne kawai a nan g

idan yari babu ranar fita. Sann Hisham bazai tab’a biyan duk abubuwan da ya aikata ba. Uwa uba bazai tab’a bari ku Sami kwanciyar hankali ba kaida Ummulkhai.” Ta dan numfasa “Na gode da kulawarka a gareni D’anuwa. Amma Hisham ya wuce tunanin mutum.. Bana

tunanin akwai wani bincike da zaisa a Kama Hisham dumu dumu dan shi d’in k’wararre ne. Sann baya barin wani shaida da zai tracing back to him. Abu d’aya da zaisa a Kama Hisham shine abi ta hanyarsa. Ina nufin makirci.! Aurensa ne kawai zaisa na samu kusanc

i dashi.” Taci gaba da jinjina Kai a hankali “I might not be innocent. Kuma nasan in one way or the other dole zan biya abubuwan da na aikata a rayuwa. Tabbas ni nake driving motar. Ni na bige Dareen da Mota but under the influence of Hisham. Ka yarda dani

bansan ina hankalina yake ba lokacin da na bige Dareen maganganun Hisham ne kawai suke yawo a kwanyata. K’ok’ari kawai nake na dakatar da ita kar isa gareka kaman yanda Hisham keta tunzura ni da na dakatar da ita. Dan idan ta isa ta sanar dakai komai zaka

tsaneni koma ka hukunta ni. Ashe amfani kawai yake Dani dan na zame masa garkuwa na aikata laifin da zai amfani ya rufe bakina dashi. While I’m stuck here Hisham bazai tab’a biyan abubuwan da ya aikata ba. Ina buk’atan ficewa a nan dan na tabbata ya biya

duk abubuwan da ya aikata.”

Haidar ya furzar da huci kad’an yana jinjina Kai “Idan haka kika zaba. Fine.! Kowa yanada ‘yancin yin yanda yaso da rayuwarsa. Amma bana so ki saka ma ranki sabida ni Haidar zaki sadaukar da farin cikinki da rayuwarki ki auri

mutum irin Hisham. Idan duk abinda kike fad’a gaskiya ne Anisa. Then Do it for yourself.. For your own freedom.. For you to clear your name...!” Yana ida fad’in haka ya mik’e yai ficewarsa.

Anisa ta bisa da kallo har ya bace mata. Ta lumshe idanunta hawa

yen nadama suka gangaro mata.

**

A cikin satin maganan Auren Anisa da Hisham ya kankama. A b’angaren Hajja sai bata kawo komai a ranta ba tafi alak’anta hakan da Jin k’ai da taimako da D’anta ya saba tsakanin Al’umma tinda d’abi’ar taimako shaidarsa ce.

Sann hankalinta ya kwanta da maganan Ummulkhair musamman da yake an maida Auren Ummul d’in da D’anuwan Hisham d’in wato Haidar. Ga Hisham ma zai nasa auren ya samu natsuwa. Itakam maganar Auren sosai tai na’am dashi dukda can cikin zuciyarta bata Jin wani

abu mai Kama da farin ciki gameda auren. Sann Sam bata samu natsuwa hundred percent ba sai kawai tai k’ok’arin kawar da tunanin dan tasan bazai shige aikin shed’an ba tinda shi Sam baya fatan a k’ulla alkhairi musamman a batu irin na Aure. Bugu da k’ari b

ayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login