Showing 102001 words to 105000 words out of 267381 words
naka Ya iso.. Gashi dai da alama har yanzu bai iso ba.. Lallai da alama zai dare.” Ta kuma duban Hilal tana tsimewa “Waima mai ya shigo da Kai nan ne. Mai kake nema.?”
“Dama na shigo ne na fad’a Miki zan d’an kwanta kafin la’asar tinda naga har yanzu A
bban bai iso ba.”
Ta jinjina Kai tana dubansa “Idan ya iso zan tada Kai.” Ta fad’i tana nufan k’ofa yayinda Hilal ya take mata baya.
*
Fitowan Hilal sallar la’asar bayan an Ida sallah a masallaci a hanyar sa ta dawowa gida ya hangi Umma tana sallah ji
kin wani gini dake manne da karantar gidansu. Kasancewar akwai interlocks wajen. Mamaki ya cika Hilal. Ikon Allah yanzu dama ashe matar nan bata tafi ba. Lallai ba k’aramin Abu ya zaunar da ita ba.
Ya k’araso gefenta daga can ya tsuguna kan k’afafunsa ha
r ta Ida addu’arta. Hilal ya tayata shafawa.
“Umma.” Ya ambaci sunanta daga nan yanda yake tsugune kaman dai yanda yaji Khulsum na kiranta.
Umma ta d’ago ta dubesa sai ta sakar masa murmushi “Hilal d’an albarka.” Ta fad’i tana dubansa dan bazata tab’a
mance alkhairan yaron ba koda kuwa ita mahaifiyarsa suna buga dabi. Kaman yanda nata yaran basuyi halinta ba haka zalika Hilal baiyi halin mahaifiyarsa ba a cewarta.
Hilal ya gaisheta kafin ya k’arada “Umma mai kikeyi a nan.? Mai ya zaunar dake nan.?” Ya
dan numfasa kiyi hak’uri da tambayar da zan Miki “Shin akwai wani matsala ne tsakaninki da mahaifiyata.? Meke faruwa tsakanin ku biyun.?”
Umma ta girgiza Kai kad’an “Babu komai Hilal. Amma Kai hakuri bazan bar k’ofar gidan nan ba har sai mahaifiyarka ta
saurareni.”
Hilal ya zuba ma sarautar Allah ido yana tuno yanda sukai da Amminsa. Ya d’an kuma girgiza Kai “Amma.. Kiyi hak’uri da tambayarta da zan Miki.. Wani abu ne kike nema wajen mahaifiyata.? Ki sanar dani dan Allah idan wani Abu ne da zan iya taima
kawa.”
Umma ta kuma murmusawa “A’a Hilal. K’arshen abinda zanyi shine na saka ka cikin matsalolinmu. Kai d’in kanada zuciya mai kyau. Ina rok’on Allah yasa D’anuwanka dake auren Ummul d’ina ya zama mai kyaun hali da d’abi’u irin naka..” Ta k’arashe cikin
rawar murya irin na mai kuka hawaye na gangaro mata dan a koda yaushe cikin tunanin Ummul d’inta take da halinda zata iya kasancewa ciki. A gaggauce tai k’ok’arin goge fuskarta kafin ta kuma duban Hilal tace “Mahaifiyarka nake son magana da, sabida wajenta
nazo. Domin dani da mahaifiyarka munada alak’a mai kyau.” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta.
Mamaki ya kuma cika Hilal. Kansa ya kuma k’ullewa. Tabbas wad’ann mata wato Amminsa da Umma al’amarinsu abin dubawa ne sann yanada rikitarwa. A b’angare guda
mahaifiyarsa tana ikirarin datse alak’a da Umma da ahalinta. A b’angaren Umma tana fad’in itada mahaifiyarsa sunada alak’a mai kyau. Shin na waye zai d’auka cikin su biyun.?
Juyin duniya Hilal yayi Umma ta hakura ta koma gida amma fir fir tak’i ta kafe l
allai lallai sai Asshe ta saurareta. Ganin yamma nayi yasa Hilal d’aukan mota ya fice daga gidan. Dan yasan watak’ila maganarta kawai Umma zata saurara ta amince ta bar k’ofar gidansu.
A bakin ward din ya hangeta tana k’ok’arin shiga. Sauri sauri ya k’ar
asa ya cimmata.
Kaman Wanda aka jefo shi haka Khulsum taga Hilal gabanta.
Da mamaki take dubansa.
“It’s a good thing that I found you here. You need to come with me.” Abinda kawai Hilal yace kenan.
Khulsum ta girgiza Kai cikeda mamaki “Malam lafiya.
?”
Yai gajeren tsaki “Wai ke ko yaushe haka kike ne. Abun fad’a baya Miki kad’an ne.?” Ya kuma girgiza Kai “I need you to come with me right away. And please you alone. You don’t need to inform that aunt of yours… She might stop you.” Dan bai mance ba kwa
nakin can da suka shige ita ce ta hana Khulsum bin Umma Akan idonsa. Daga haka sa Kai yai ya soma tafiya yana fad’in tai sauri ba lokaci.
Takaici ya cika Khulsum, mai wann D’an rainin hankalin ya d’auketa da zaice tazo ta bisa. Ina ma zata bisa.? Mai ya m
aidata.?
Ganin ya soma tafiya ya nufi mota yasata bin bayansa da sauri tana fad’in “Kai Malam.. D’an dakata.? Kana tunanin kai waye.? Mai ka d’auke ni.. Mai ka maidani da zaka tako har yanda nake kace nazo na bika kuma kar na sanar da Innata.. Ce maka aka
i..”
Bata Kai aya ba Hilal ya kaikaito yana dubanta cikeda takaicin kuskuren fahimtar da tai masa “Hey cut it out will you.!” Ya katseta da fad’in haka kafin yaci gaba “Seriously, is that what you think of me.?” Har lokacin da mamaki yake dubanta kafin ya
ci gaba “If that’s what I wanted I’d have gone straight to a hotel or club, and not a hospital.” Ya dan girgiza Kai “Look, ni ba irin wad’ann mutanen bane. And I’m not kidnapping you.. Idan na zo nan kawai nazo ne sabida mahaifiyarki dake zaune k’ofar gid
anmu through out the day. Idan Ammi na ta fito ta taddata wajen it would be a disaster. Idan akwai girman mahaifiyarki da kike gani kike ji a cikin Zuciyar ki koda kad’an ne zaki taho tare Dani dan na tabbata ke zata iya sauraronki.” Ya k’arashe yana bud’e
motar.
Jikin Khulsum yai sanyi ta dubesa da mamaki “Umma ce take k’ofar gidanku.?”
Hilal ya zuba mata ido yana dubanta. Baice komai ba sai tada motar da yai “Zakije ne ko nai tafiyata.?”
Ta hareresa sai kuma tai still a wajen kaman mai tunani. Shin ta
sanar da Inna Dije ne.? Toh amma idan ta sanar da Innah Dije wani wutan zata kunna tinda tasan Ummanta da Inna Dije basa jituwa. Sann Inna Dije zata iya hanata zuwa. Tana tsaka da tunanin taji sautin horn ya cika mata kunne alamun Hilal na jiran decision
dinta. Harara ta b’alla masa kafin ta bud’e marfin motar ta shige.
Ya soma driving babu mai ce da kowa komai cikin su biyun har suka iso k’ofar gidansu Hilal. Can Khulsum ta hangi Umma rakub’e jikin gini tana lek’en gate din gidansu Hilal kaman wata maba
raciya. Sosai abin ya mata ciwo ganin mahaifiyarta a haka. Hilal na Ida parking ta fito ta nufi Umma.
“Umma.!” Khulsum tace daga nan yanda take tsaye kusan Umma.
Umma ta d’ago tana dubanta. Khulsum tai saurin k’arasowa ta duk’a gaban Umma “Umma Mai kike
a nan. Dan Allah mai kike haka a nan.? Umma wann fah zubda mutunci ne. Dan Allah ki tashi ki bar k’ofar gidan nan. Duba fah kiga mutane masu shigewa suna kallonki.. Umma dan Allah ki tashi haka nan.”
Hawaye Umma ta soma tana girgiza Kai “A’a Khulsum bani
tafiya sai Hajiya Asshe ta sauraren.”
Khulsum ta juya ta dubi Hilal dake can jikin motarsa yana tsaye. Shid’in ma su yake duba. Ko ba’a ce ba damuwan halinda Umma ke ciki ne saman fuskarsa dukda baya iya sauraron mai uwa da ‘yar ke cewa.
Khulsum ta maid
oda dubanta ga mahaifiyarta “Umma matar nan tareda ita ina nufin keda ita kuka k’ulla auren ‘Yaruwata. Bansan dalilinta na juya Miki baya ba. Bansan meye ku biyun kuka bisne ba. Bansan meye a tsakaninku ba. Amma ke mahaifiyata ce kuma bazan so ki walak’ant
a ba. Dan Allah Umma ko mai kike nema wajen matar nan kiyi hak’uri ki bar k’ofar gidan nan.”
Umma ta kuma girgiza Kai tana hawaye “Khulsum idan na tafi mai zanje nace da Tani. Na mata alk’awarin zan nemo kud’ad’en belinta. A nan ne kawai nake da yak’inin
zan samu kud’in fiddo Tani Khulsum.”
Baki sake Khulsum ke dubanta. Da mamaki tace “Umma wai dama kan kud’ad’en belin Mama kike nan.?”
Umma ta jinjina mata Kai alamun eh.
Shiru Khulsum tai na d’an lokaci kafin ta dubi mahaifiyar tata tace “Umma kece zak
iyi belin Mama. Wai Mama Tani dai da ta saida shagon Abba.?”
Umma ta kuma jinjina mata Kai “Dukkanmu masu kuskure ne Khulsum. Tani ta salwantar da dukiyar Malam ni kuma na salwantar da rayuwar ‘yarsa. Cikin mu biyun idan akwai Wanda tafi girman laifi toh
ni ce Khulsum. Ni yafi cancanta na tafi gidan kasu ba Tani ba. Idan har zan zuba ido ni ina shak’an iskan ‘yanci yayinda Tani ke gark’ame kurkuku bana tsammanin nayi ma kaina adalci. Sann bana jin ‘yancin iskan da nake shak’a a mak’oshi na. Tani ta tuba Kh
ulsum. Dukanmu mun gane kurakurenmu. A halin yanzu bamuda wani buri da ya wuce mu koma ga mijinmu mu kula dashi mu masa jinya mu samu aljannarmu.” Ta k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka.
Jikin Khulsum yai sanyi. Tasan mahaifiyarta tanada zuciya ma
i kyau Wanda da yawan mutane suna amfani da wann damar su shashashantar da ita. Kaman dai yanda takeda kokonto Akan tuban Mama Tani. Dan tasan kad’anda aikin Mama ne ta shashantar da mahaifiyarta ta samu ta fito daga prison.
Muryar Umma ta kuma sinkayo s
anda ta tallafo fuskar Khulsum d’in cikin zuban hawaye take fad’in “Nayi kewarku Khulsum daga ke har ‘yaruwarki. Ina zaman kad’aici a gidan.. Babu ke.. Babu Ummulkhair.. Babu mahaifinku.. Tani ma bata nan.” Tai shiru tana tinanin daga ita sai su Azeema Wan
da suka maidata wofi cikin gidan barikinsu kawai suke bugawa. Su fita sanda suka so su dawo sanda suka so. Idan tai masu abincin da bai musu ba su mata tatas. Har wankin kaya Badia ke sakata. A cewarsu idan batai ba zata fice ta bar masu gidan uba tinda gi
dan na ubansu ne.
Ganin tayi shiru ta tsunduma tunani yasa Khulsum kamo hannayenta “Umma.” Ta kirawo sunan Umman a hankali.
Umma ta d’ago tana duban Khulsum.
“Zaman kad’aici yasa kike so ki fiddo Mama Tani.?”
Shiru Umma bata ce komai ba sai hawaye dak
e kuma gangaro mata.
Khulsum ta janyo mahaifiyarta ta rungume sai dukansu biyun suka fashe da kuka.
Cikin muryar kuka Khulsum ke fad’in “Umma kiyi hak’uri ki koma ki zauna. Nayi ma Abba alk’awari bazan sake barin kusansa ba bayan abinda ya faru.” Cikin
rawar murya taci gaba da fad’in “Umma ba zama da Inna Dije na zab’a ba. A’a zama da Abba na na zab’a. Inna Dije bazata kuma barinki kije kusan mahaifina ba Umma. Zanfi kowa so naga ahalinmu ya kuma cika amma a halin yanzu Abu ne mai matuk’ar wuya Umma. Ki
koma kici gaba da addua ma Abba har Allah ya bashi lafiya iyakacin soyayyar da zaki nuna masa kenan a halin yanzu. Da sannu Allah zai duba Zuciyar Wanda yai tuba na gaskiya ya yaye masa matsalarsa kinji Umma na.” Ta k’arashe cikin rawar murya.
Umma ta sh
iga jinjina mata Kai a hankali har lokacin tana hawaye. Cikin zuciyarta kaw cewa take ita kanta bazata so ta bar Malam k’ark’ashin kulawar Dije kawai ba. Gwara ace Khulsum d’in na tare dasu. Zatai hak’uri kuma zataci gaba da addua kaman yanda ‘yar nata ta
shawarceta.
Hannunta Khulsum ta kamo suka nufo Motan Hilal. Hilal na ganin su ya isa ya bud’e back seat Khulsum suka shige tareda Umma hannayensu rik’e cikin na juna suna Jin d’umin juna da suka jima basu samu hakan ba.
Ta mirror Hilal yake dubansu yanda
suka shige jikin juna. Kan Khulsum na kwance gefen kafad’an mahaifiyarta yayinda Umma ta rik’e hannun Khulsum d’in k’am cikin nata tamkar kar wani Abu ya rabasu. Murmushi ne yaji out of nowhere na zuwa fuskarsa. Shi a duniyar sa duk yanda yaga shak’uwa da
soyayya mai tsafta tsakanin iyaye da ‘ya’yansu ba kowa yake hasashowa ba face D’an Uwansa Haidar. A kullum addu’arsa kenan yaga irin wann bond d’in tsakanin Haidar da iyayensa.
Har gida Hilal ya kawo Umma. Khulsum ta fito taima Umma rakiya zuwa cikin gi
da ta kuma tausarta had’ida kwantar mata da hankali amma fah dukda haka bata ji cikin zuciyarta zata iya baro Abba ta dawo ta zauna da Umma musamman idan ta tuna abinda matan Abban nata suka masa.
Tana fitowa ga mamakinta ta tadda Hilal na nan na jiranta
.
Daga can yanda take tsaye ya zuba mata “Rankidad’e jirana ake gida muje mana.”
Ta had’e fuska sosai “Toh ce maka nai ka jirani. Kai tafiyarka mana.” Tace tana canza hanya.
Furzar da huci yai kad’an ga wayarsa da ta kasa shiru sakamakon kira da Mahai
fiyarsa ke jero masa. Yasan bazai wuce Abbansa ne ya iso ba. Baisan mai zaice mata ba dan shi dai bai iya k’arya ba amma muddin ya sanar da ita Umma ya kawo gida ya taro match ne tsakaninsa da Ammi.
Ya k’arasa da mota gaban Khulsum yai rolling glass “Zak
i shiga ne ko sai na fito na shigar dake da k’arfi.? Be thankful, albarkacin Umma kikace idan na maidake.alk’awari na daukar mata zan maidaki yanda na d’aukoki.” Yace a mugun tsare.
Khulsum ta dubesa dan yanzu gadararsa da k’arfin halinsa ya daina bata ma
maki. Bata son dogon hira dashi dan kaf zuri’arsu haushi suke bata. Sann ga magarib ya k’arato hasalima batasan yanda za’ai ta koma ba tinda ba kud’in abun hawa wajenta. Ta kauda fuska gefe cikeda takaici zata bude backseat ya saka motar a lock.
Fitowa ya
i daga mazauninsa yana fadin “You must be kidding. D’azunma albarkacin Umma kikaci na barki kika zauna baya.” Ya bud’e mata front seat “Shige muje.”
Ta hararesa kafin ta shige.
Tana shiga ya sakar mata murmushi had’Ida kashe mata ido kafin ya zaga ya sh
ige. Takaici ya kuma cika Khulsum.
Suna tafe babu mai cewa komai. Khulsum ta saci kallonsa. Yanzu wai godiya ya kamata ta masa ko hakurin kuskuren fahimtar da tai masa zata basa.? Kai ina ita dai bazata basa hakuri ba dan bataga laifin da tai masa ba. Ta
saci kallonsa suka had’a ido.
Sai ta wayance dan bata so ya fahimci tana dubansa. tai kaman bata kalli b’angaren da yake ba. Saida tai gyaran murya da kyar kafin tace “Idan kana jira na baka hak’uri ne kan abinda ya faru ni dai bazan baka ba. Abinda Kai k
uma shima Kai ka saka kanka shima bazan maka godiya ba.” Ta k’arashe tana kauda fuska.
Hilal ya murmusa “Guilty conscience.? Kar ki damu na yafe miki.” Yace idonsa naga kwalta.
Bata amsa shi ba sai kuma tace “Toh mai za’a tsammata daga wanda yake sallah
babu alwala.?”
Ya kuma murmusawa “Allah yasa dai ba kece mai karb’an tuba ba balle ki k’i karb’an nawa tuban.”
Ta kuma hararsa “Ka fad’a ma wann D’anuwan naka mai sallah babu alwala ‘Yaruwata musulma ce bazata zauna dashi ba. Ni Khulsum sai na datse wa
nn auren.”
Hilal ya jinjina Kai “Why not ask your sister to tell him. After all su biyun sunfi kusa a halin yanzu.”
Ya d’an dubeta a kaikaice kafin ya k’ara “And remember they say, Wanda ya shiga tsakanin mata da miji shi zaiji kunya.”
Ta hareresa mu
samman da taga murmushin dake bisa fuskarsa.
Yana ida parking tasa hannu ta bude marfin motar a fizge ta fice. Ko kallon yanda yake bataiba balle tai masa sallama balle ya samu arzikin godiya.
Bayanta yabi da kallo yana murmushi. Cikin zuciyarsa yake j
in yanzu yanada k’wakk’waran dalilin da zaisa ya k’ara delaying lokacin komawarsa makaranta koda hutunsa ya k’are. Bazai tafi ba har sai ya tabbata baida wani pending matters. Saida ta b’ace ma ganinsa kafin yaja motarsa ya bar wajen.
**
Cuba…
Waya ma
nne b’angaren kunnensa na dama. Dareen na hankalce dashi tinda ya soma wayar.
Daga d’aya b’angaren Hisham yaci gaba “You know I still can’t get over her. I don’t know why.. But I find it difficult to forget about her. Dukda cewa mun hadu ne na d’an wani l
okaci. Nayi tunanin zan cireta a zuciyata cikin sauk’i kaman yanda na cire sauran. But then I realise she’s different. So different.” Ya d’anyi fasali “Haidar na kasa hana zuciyata tunanin matar wani. I dream about her every night. And worse part d’in shi
ne zuciyata tak’i ta karbi k’addaran. Haidar ji nake zata dawo gareni.. Astagfirullah.” Ya k’arashe jikinsa duk a mace.
Sosai Haidar yaji tausayin abokin nasa. Shi ire iren abun nan ba layinsa bane. Hasalima bai tab’a soyayya ba. Dareen ma bazaice ga yan
da akai har ya fara sonta ya aureta ba. So baisan wani shawari zai ba ma abokin nasa ba. Ya d’an numfasa kafin yace “Just.. Just try to distract yourself.. Engage in activities that require your full attention… Like work.. Zaka gani in no time zaka mance d
a ita. And you’ll find someone better than her.”
Hisham ya d’an furzar da huci “What if my mind gets stuck here Haidar.? What if I couldn’t move on.? What if banida wani future dangane da abinda ya shafi Aure.? What if this is my destiny.?”
Haidar yai s
hiru cikin sanyin jiki ba tareda ya iya cewa komai ba.
Hisham yai murmushi mai ciwo “Sorry I shouldn’t be telling you all this. Kayi tafiya ne dan ka rage damuwar dake kanka bai kamata na k’ara maka da nawa ba. Anyways, I guess this is life for us. Ba ko
yaushe muke samun abunda muke so ba.” Ya d’an murmusa kafin yace “Let’s talk business maybe this will keep me busy.” Yai maganar da gajeren murmushi kafin yaci gaba “Ya kamata ka dawo haka work is getting hampered because you are not here. Komai so yake ya
tsaya. And kasan lokaci baya jiranmu.”
Ya d’anyi gajeren tsaki “I’m still on my vocation. Zanje Pennsylvania daga nan.”
Daga d’aya b’angaren Hisham Ya girgiza kai “Wai kana nufin hutun naka bai k’are ba.. Ko wani business d’in kakeda a can US d’in.?”
Gajeren tsaki ya kuma yi “Ka