Showing 141001 words to 144000 words out of 267381 words
wani irin tsinkewa. A fili ya furta “Ummul.? No.. No no this can’t be.. She can’t get hurt..!” Yana maganar cikin tsananin daburcewa har bai san sanda Haidar yaja motar ya bar wajen ba.
Cikin rikicewa Hisham ya shige nashi motar daga can yanda ya ajeta.
Yana driving yake dialing layin Anisa. Tana d’agawa Hisham ya fara cikin sakin huci “I know where Ummul is.. Tana cikin motar.. Tana tareda Haidar.!”
Anisa tace “So, come up with something.. Kidnap her and runaway.”
A hasale yace “Shut up. Just shut up
.! Kece kika bani shawarin na shirya ma Haidar accident ta haka ne zai leading dina to where he hides Ummul.. Na d’auki shawarinki and tempered with his brakes. And now.. Komai ka iya faruwa da Ummul.. Damn you..! I shouldn’t have listened to your advice..
!”
Cikin daburcewa Anisa ke fad’in “Idiot..! I didn’t say you should temper with his brakes.. Kawai cewa nai Kai causing masa minor accident ka dan bigi bayan motarsa or something.. Amma ni bance Kai causing babban accident ba.. Do you even realize they c
an both die in that car..!” Sai ta fara kuka tana fad’in “Wayyo Haidar.. If something bad happens to Haidar wllhi bazan tab’a yafe maka ba.. And you will answer to me..!”
Hisham ya daka mata tsawa da fad’in “Shut up. Shut your trap..! I can’t lose Ummul
. Bazan rasata ba.. Kuma idan wani abu ya sameta you’ll be the one to pay the price.!”
Bai kuma tsayawa sauraron Anisa ba ya Katse kiran yana mai dukan steering wheel da iyaka k’arfinsa yana tsaki.
**
A b’angaren Daddy kuwa tinda ya koma Office tunanin
abinda Mommy ke masa ne ya sha masa Kai. Da fari ta basa zab’i cewa zai iya datse aurensu Idan yaso.. And now tana nuna masa kaman dai zaman D’anta kawai take a gidan. Kaman dai shid’in baida wani mahimmanci wajenta. Ya sani yaso Kwaise da duka zuciyarsa,
hasalima bai tab’a son wata mace kaman yanda yaso Kwaise ba.. Amma bayan abinda ta masa.. Bayan rabasa da matarsa da sheganta cikin D’ansa da tasa yai yaji ta fita masa a rai. Ba ita kad’ai ba ko wace mace ma ta fice masa.. Yaji baya mararin wani abu mai
suna soyayya because he was betrayed by macen da ya nuna mata zallan soyayya. Wanda hakan yasa ya d’ibi kwaise ya watsar sann bai kuma yunk’urin sake wani aure ba. Kaman yanda tace Kasuwancinsa shine kawai a gabansa shine rayuwarsa shine komai nashi.. Bai
kuma damu ba idan Kwaise bata nuna damuwarta akansa ba. Hasalima yanda taketa Neman attention d’insa zuwa gareta da kuma D’anta tun bayan abinda ya faru sai hakan yake kuma tunzura shi yake nuna mata da ita da d’an nata basu gabansa hasalima babu abinda ya
baiwa rashin mahimmanci irin su… But why’s he feeling this way now..? Meyasa yake ji yanzu da Kwaise ta fara nuna masa baya gabanta abun ke masa zafi sosai..? Meye dalili.. Meyasa yake Jin ciwon hakan bayan abinda yai buri kenan tsawon shekarun nan. Ya d’
an furzar da huci yana aje pen d’in dake hannunsa.
Alhaji Gimba daketa Sallama Daddy baisan da zuwansa ba sabida nisa da yai cikin duniyar tunani k’arasowa yai ya zauna kujera mai kallon na abokin nasa.
Daddy ya d’anyi gajeren tsaki “Yi hakuri Gimba ba
nji shigowarka ba..”
Alhaji Gimba ya murmusa “Ina kuwa zakaji shigowata Madam ta caza maka Kai..” Yai maganar cikin barkwanci irinta abokai.
Daddy ya kuma yin gajeren tsaki “Don’t please.. Don’t bring her up here.. Let’s talk business..”
Girgiza Kai Alh
aji Gimba yai yana juyi cikin kujeran “Abokina kenan. Kana nan a Aliyun ka da na sani.. You know your son Haidar takes after you.. Bai bar maka komai ba.”
Daddy ya kuma yin gajeren tsaki “Are we going to talk about this issue again..?”
“K’warai bazaka iy
a guje ma hakan ba.. Sabida sud’in ahalinka ne.”
Daddy ya kuma lumshe idonsa cikeda k’osawa “Gimba please, my day is bad enough coming to add to it.. Kar ka min maganan D’aya cikin biyun nan..”
“Abinda nake fad’a maka a kullum shi zan sake tunasar dakai.
Bakada Wanda ya fi maka su.. Sud’in ahalinka ne..”
Daddy ya kuma yin tsaki “Gimba, please get out before I ask my secretary to escort you out.!” Ya k’arashe yana nuna masa k’ofa.
Murmushi Alhaji Gimba ya kuma yi “Seems like your pride is speaking for
you again Abokina.” Ya kuma gyara zamansa “Shi rayuwar nan Engr wllhi kyauta ce. Yau dubu nawa basuda daman rayuwa irin namu. Ba wai k’uruciya muka fisu ba.. Ka juya ka duba environment d’inka sosai kaga masu irin shekarun ka guda nawa ne.? A ajiye magana
n arziki na kudi da dama na rayuwa, ka duba masu arzikin lafiya irin naka guda nawa ne.? Ka duba masu ahali irin naka guda nawa ne.? Shin kasan wani ya tara arzikin amma baida lafiyan jin dadin arzikin..? Shin kasan wani ya tara dukiyar amma baida Magaji
.. Shi da za’a amshe duka dukiyar da ya mallaka dan a mallaka masa irin D’an daka mallaka K’wara d’aya tak da ya fiye masa duk wani arzikin gidan duniyar nan da za’a basa..”
Daddy ya girgiza Kai kad’an “So, what are you trying to imply here.. That I’m un
grateful..?”
Alhaji Gimba ya katsesa “Because you are stuck in tha past.. And that destroy your present.” Ya dan gyara zamansa “Kuma kasan ina matsalar take.. A naka tunanin bayan abinda ya faru dakai a baya Kasuwancinka shine abinda yai keeping d’inka mo
ving.. Amma ba haka bane.. Wann ahalin da a kullum kake ik’irarin basuda mahimmanci cikin rayuwarka sune sukai keeping d’inka moving forward.. Your wife and your Son.. Amma ba business d’inka ba kaman yanda Kai kake tunani..” Ya d’an numfasa yana jinjina k
ai “Your company is your distraction not your source of happiness.. Wann ahalin da a kullum kake tashi ka gansu sune sukai healing wann gurbin ciwo dake cikin zuciyarka.”
Katsesa wann karon Daddy yai “Quite the contrary… Ganinsu a kullum da nake shi yake
tuna mun baya.. And maybe that’s why I feel trapped in the past.. Watak’ila da ace bani ganinsu things would’ve been different..”
Alhaji Gimba ya girgiza Kai yana murmushi “So tari zamu so abu amma ba alkhairi bane wajenmu.. Sann so tari zamu k’i abu amm
a alkhairi ne a tattareda mu. Watak’ila D’anka daka rasa tun kafin yazo duniya ba alkhairi bane cikin rayuwarka, Watak’ila D’anka Haidar da Allah ya bar maka shi Watak’ila shine alkhairi a gareka. Barinyi maka tuni da wani k’issa na Annabi Musa (AS) da ma
laminsa Khidr Wanda a k’auli mafi rinjaye shima Khidr Annabi ne. A cikin tafiyarsu da sukai Wanda Annabi Musa(AS) ke Neman ilimi wajen Khidr sunga wani yaro a hanyarsu kuma Annabi Khidr ya kashe yaron Wanda har Annabi Musa ya gaza hak’uri ya tambayesa meya
sa zai kashe ran da baiji ba bai gani ba. Koda suka zo rabuwa Annabi Khidr ya amsa ma Annabi Musa (AS) amsoshin tambayoyinsa da ya gaza hak’uri akansu. Shi wann yaron da ya kashe Iyayensa mutanen kirki ne shi kuma yaron Allah ya k’addari idan ya girma zai
lalace kuma iyayen nasa suna matuk’ar sonsa zasu jarabtu dashi har ya lalatasu dan haka Allah ya masa umarni da ya kashe wann yaron.” Ya dan numfasa yana kallon Daddy da jikinsa yai sanyi sosai “Karatun da zaka d’auka a nan wani sa’in abu ba alkhairi bane
wajenka sai Allah ya d’auke maka shi cikin rahamarsa. Watak’ila wann D’an daka rasa tun yana ciki Watak’ila zaka jarabtu dashi sai Allah ya maka sauyi da wani d’an Wanda ka kasa gani ka kuma kasa appreciating d’insa.” Ya dan kuma gyara zamansa “Ina ka b
ar tawakkali..? Ina ka bar imani da k’addara Abokina.?”
Daddy ya dubesa a sanyaye da idanunsa da suka kad’a ba tareda yace komai ba.
Alhaji Gimba yaci gaba da jinjina Kai “You need to let go of the past and accept what you have kafin lokaci ya k’ure mak
a.. Kafin kai nadama maras amfani Abokina.”
Ya mik’e yana fad’in “Zan koma bakin aiki kafin kasa sakatariyarka ta koreni.. Kai tunani kan abinda muka tattauna dan lokaci baya jiranmu..”
Daga haka ficewa yai ya kyale Daddy nan zaune yana juyi cikin kujera
.
**
A b’angaren su Haidar kaw suna tafe saman kwalta. Gudu yake sosai yana tunanin ahalin da ya girma dasu matsayin iyaye. Wani b’angare na zuciyarsa na tunanin Dareen da abinda tai masa. Meyasa rayuwar sa haka.? Meyasa abubuwa suke zuwa masa yanda suke
zuwa..? Meyasa rayuwarsa gaba d’aya batada alkibla tun tasowarsa.? Why.. Why.. Why.?! Tambayoyin da zuciyarsa ke ta nanata masa kenan ga gudu da yakeyi saman kwalta har baisan gudun nasa ya shige misali ba.. K’ok’arin danna birki yake amma batayi.. Ga gudu
da yake gashi sun fara ratsa tsakiyan motoci..
A razane Ummul take dubansa tana tambayarsa meke faruwa.. Haidar yaci gaba da k’ok’arin danna birki yana fad’in “The brakes.. Is not working..!”
Ummul ta soma salati tana karanto Innalillahi wa inna’ilaih
i raji’un.. A daidai lokacin Haidar yai k’ok’arin kauce ma wata mota Wanda hakan yasa nasu motar ta bar saman kwalta ta fad’a gefen titi.. Haka motar ta dinga juyi har saida ta isa jikin wata bishiya..
SameenaAleeyou
📚
*AUREN WATA UKU..!*
*39*
*©
️
Sameena Aleeyou…✍
🏽
*
Sosai Mommy ke kuka sanda suka iso asibitin Anisa na biye da ita itama matsan k’wallan take. Hankali tashe Mommy ta nufo hospital staff d’in tana tambayar yanda su Haidar suke.
A daidai nan su Daddy da Alhaji Gimba suka fito daga
wani k’ofa. Dan dama sanda accident d’in ya faru company aka k’ira aka sanar dasu.
Daddy yai tsaye yana dubanta yanda take kuka sosai Anisa nata kokarin kwantar mata da hankali bayan hospital staff d’in sun sanar dasu Haidar da matarsa suna cikin ER Lik
itoci na kula dasu.
Wayar Daddy ne ta soma ruri. Daga Kampani ake kiransa. Dafe goshinsa yai yana mai lumshe ido sanda yake amsa kiran. Ga dukkan alamun ba labari mai dad’i yai receiving cikin wayar ba.
Alhaji Gimba Ya dubesa had’ida girgiza kai kad’an
“Akwai wani abu ne.?”
D’an furzar da huci Daddy yai “There’s been an emergency at the company..”
Alhaji Gimba Ya girgiza Kai kad’an “Emergency..? Mai ya faru.?”
Furzar da huci Daddy ya kuma yi “Ban sani ba Gimba.”
Shiru Alhaji Gimba yai yana dubansa.
Tunanin sa d’aya Engr zai iya tafiya ya bar asibitin musamman da yake Haidar ne a asibitin sanin irin alak’ar dake tsakanin Engr d’in da ahalinsa. And especially da yake matsala ne ya kunno a Kampaninsa. Ya sani da za’a ba ma Engr zab’i tsakanin Kampanins
a da D’ansa he’d always choose his company. A halin yanzu ahalinsa suna buk’atar sa fiyeda ko yaushe. Adduarsa Allah yasa kar Engr Ya tafi ya bar ahalinsa cikin yanayin da suka tsinci kansu na jarabawa.
Yana tsaka da tunanin kaman daga sama ya sinkayo mu
ryar Daddy “You go… and take care of things there.”
Alhaji Gimba Ya dubesa da mamaki cikin gaza b’oye farin cikinsa na decision d’in da Engr ya dauka na tsayuwa a asibiti wajen ahalinsa. Hakan na nufin Engr ya zab’i D’ansa sama da kampaninsa da Kasuwancin
sa for the first time. Cikin sauri ya soma jinjina Kai “Kar ka samu damuwa abokina.. zan je na kula da komai a can.. You stay here.. Your family needs you.” Ya k’arashe cikin k’ok’arin k’arfafa ma Daddy gwiwa Wanda Sam k’arfin halinsa ya hana ya nuna tsana
nin damuwarsa.
Kai dubansa ga yanda su Mommy ke zaune yai bayan Alhaji Gimba ya shige. Anisa sai k’ok’arin calming d’inta take da kalamai masu kwantar da hankali cewa Haidar harma da Ummul zasu samu lafiya. Mik’ewa Anisa tai tana duban Mommy wacce har lo
kacin bata cewa komai sai hawaye dake gangaro mata “I’ll.. bring you some water Mommy.” Ta k’arashe tana mai shigewa.
Bayan Anisa ta shige k’uri Daddy yaima Mommy k’uri daga nan yanda yake tsaye. Yana kallon yanda take cazgan kuka mai tsuma zuciya. Tin b
ayan abinda ya faru tsakaninsa da Kwaise zai iya cewa bai sake Jin ya damu da wani damuwa da ya danganceta cikin zuciyarsa ba musamman idan abun ya shafeta ita da D’anta ne. Amma yau d’in sai yaji har k’asan zuciyarsa na jin zafin kukan da Kwaise take. Ha
r cikin zuciyarsa yana so ya k’arasa gareta ya rungumeta cikin jikinsa amma sai yana jin bazai iya hakan ba. Lumshe idanunsa yai yana mai barin wajen cikin sauri dan Sam bai son sauraren kukan da take. It hurts him a lot.
A can waje kuwa koda Anisa ta f
ita sun samu sun keb’e da Hisham. Ta kuma dubansa a hasale “You know your IQ doesn’t work at all. Waima how many gb akan nan naka..?”
Katseta yai kaman zai mak’ureta “Don’t you dare insult me. It was your idea from the very start.. Kece kika kawo shawarin
a shirya masa hatsari.. If there’s someone to be blamed here that should be you.”
Anisa na huci take nuna sa “Kai addu’a kar wani abu ya samu Haidar.. Dan wllhi idan wani abu ya samu Haidar sai na tona maka asiri.!”
Murmushi Hisham yake da gefen baki “I
f that’s a threat, I suggest ki ajiye sa zuwa anjima har muji wani yanayi Ummul ke ciki. Dan na miki alk’awari idan har wani abu ya sameta.. Zakiyi d’andanasanin sanina..!” Ya k’arashe jijiyoyin fuskarsa suna mimmik’ewa.
Anisa ta zaro ido tana duban Hish
am cikeda mamakin irin son da yake ma Ummul. furzar da huci tai hadida rausayar da ido dan bazata basa daman ganin gazawarra ba “Let’s not waste time pointing fingers at each other.. Bazai taimakemu ba.. I thought da ka shirya hatsarin zaka d’auki Ummul k
a gudu da ita.. I thought you said you wanted to be with her so badly. Maiyasa kai wasa da damarka. Maiyasa baka saceta ba kowa Ya huta.?!” Ta k’arashe tana huci.
Murmushi yake da gefen baki yana dubanta “You think I’m stupid.?” Ya kuma murmusawa yana dub
an Anisa “To tell you the truth, I was the anonymous person da ya k’ira company ya sanar da hatsarin nasu.” Ya jinjina Kai yana ci gaba da murmushi “Ina gefe ina kallon komai har yan kwanakwana suka kawo masu dauki.. Daidai da dak’ik’a guda ban bar wajen
ba. I had to make sure sun samu taimako na gaggawa right away.!”
Ya kuma murmusawa yana kallon Anisa da ta zama confused tana duban makirci da ya dama nata. Hisham yaci gaba “Alak’a mai kyau mai tsafta mai cikeda yarda nake son k’ullawa da Ummul Wanda Bab
u algus cikinsa. And believe me na shirya hakan. Bazan tab’a bari ta zargi soyayyar da nake mata ba.. She will come to me willingly.. And she will accept me ba tareda wani ya tilasta mata ba.. Kin fahimta.?!”
Anisa ta tsaresa da ido sai kuma ta girgiza ka
i “I hope it happens very soon.!” Tana ida fad’in haka tasa Kai ta shige tana huci.
A yanda ta bar Mommy nan ta sameta har lokacin matsan hawaye take cikin yanayi mai nunida tsananin tashin hankali.
Anisa tai saurin sauya fuska had’ida daura damuwa sama
n fuskarta. Ta isa ga Mommy jiki a sanyaye ta zauna gefenta tana mai b’alle bottle water d’in da ta shigo dashi. Ta mik’a ma Mommy a hankali tana fad’in “Mommy have some water.”
Girgiza mata Kai Mommy tai cikin zuban hawaye “I can’t Anisa. Bazan iya ba..
Bazan iya saka komai a bakina ba tareda sanin halinda Haidar da Ummul ke ciki ba.!”
Anisa ta maidoda hannunta baya cikin sanyin jiki. Ta d’aura hannunta guda saman na Mommy tana k’ak’alo hawaye “Mommy I know you are strong.. In fact, you are the stronges
t woman I know.. And you are my inspiration.. But sometimes even the strong ones feel vulnerable.. Because we are human beings…” Anisa tasa hannu ta share hawayen da suka zubo mata sai ka rantse har cikin zuciyarta Abinda take fad’i haka ne. Taci gaba “Tad
a hankali da damuwa dole ne.. But what they need the most now it’s our prayers.. Addu’o’in mu suke buk’ata fiyeda komai Mommy.. Especially you.. Sabida ke uwa ce.. Mommy kiyi ma Haidar Addu’a.. In sha Allah zasu samu lafiya daga shi har Ummul kinji Mommy.”
Hawaye na gangaro ma Mommy sai ta rungume Anisa kuka na kuma zuwa mata. Anisa ta saki murmushin cin nasara da gefen baki. A fili kuwa fad’i take “I’m here for you Mommy.. I’m here..!”
A haka Anisa taci gaba da k’arfafa ma Mommy gwiwa Har kawo zuwa fitow
an wani Dr daga hanyar da zai sadaka da ER. Yana tafe yana zame safar hannunsa.
Cikin sauri Mommy ta mik’e Anisa na biyeda ita suka nufi Likitan.
Daddy Wanda shima yaga fitowan Likitan zai nufesa kenan yaga Mommy ta rigasa. Sai yaja Ya dakata Ya tsaya
daga bayansu.
“Dr how’s my son and his wife..? How are they doing..? Can I see them now.. Can I see my son now.. Please tell me..” Ta k’arashe cikin tsananin kid’imewa.
Dr ya dan girgiza Kai yana duban yanda ta rikice sosai. Ga mutum mai shekaru da Ya
d’an soma ja is not good for their health.
Karaf Likitan ya had’a ido da Daddy dake daga gefe. A hankali Daddy ya girgiza masa kai had’ida masa alama da ido alamun kar Ya fad’i wani abinda zai k’ara mata tashin hankali.
Dr ya dan murmusa yace “Kar ki s
amu damuwa Hajiya.. D’anki harma da matarsa na Miki alk’awari suna samu kyakkyawan kulawa. And fortunately matarsa ta riga ta