Showing 6001 words to 9000 words out of 267381 words

Chapter 3 - AUREN WATA UKU COMPLETE

10 Sep 2026

31

/>
zaka proving mun cewa zan iya mallaka maka ragamar jagorancin Kampanin nan in three months time.. But I was wrong.. You are not capable of anything good..!”

Cikin kwantar da murya yake furta “Dad believe me, I have no idea how our new development plan g

et disclosed.. I believe someone is sabotaging our company..”

“Shut up.!” Mahaifinsa ya katsesa kafin yaci gaba “Dama ta ya za’ai ka sani.. Kana can kana shashashancinka other companies are doing great..” Yaci gaba da nunasa da d’an yatsa “Ban d’auraka a

matsayin Head of Marketing development department ba saida na tabbata na turaka k’asar Amurka na musamman domin ka karanci course na musamman a fannin Business Management.. Don’t make me regret this Aliyu.!” Yatsansa har rawa take sanda yake pointing D’an

nasa dashi.

Wani gauron numfashi Haidar yaja had’ida lumshe idanunsa cikin k’ok’arin nitsa zuciyarsa. Muryar mahaifinsa ya kuma sinkaya yana ci gaba “Our website is is.. is just a photo catalog and nothing more.. Tell me waye zai tsaya b’ata lokacinsa a

nan.. A kasuwanci irin namu your website is often the first place potential costumers will go to find more information about your company and its services. Therefore, it should be well designed and offer them exactly what they are looking for.!”

Haidar ya

kuma furzar da huci “Dad, you please listen to me first.. Na sani our company hits a bit of a marketing plateau. But that doesn’t mean we should simply give up..” Ya d’an sassauta muryarsa kafin yaci gaba “Daddy, I believe we can come up with a new market

ing strategy that would help us to not just get our business back in the game but ahead of the game. Aikin da Kampanin mu zaiyi zai tabbatar da hakan.”

“Shut up.. Rufe mun baki..!”

Haidar ya Had’iye k’uncinsa yana furzar da huci mai d’umin gaske.

Cikin

karaji yaci gaba da nunasa da d’an yatsa “How could you have failed in accomplishing a simplest of tasks.. How could you have let our business rivals get ahead of us.. Because of your foolishness now, our company is at risk of going bankrupt.. kana can k

ana shashancinka other companies are doing great.. A haka ne kake tunanin ni Aliyu Maitama zan d’auki project d’in da ci gaban Kampani ya ta’allak’a a Kai ka jagoranta cikin watanni uku.. Bari kaji na fad’a maka.. I did not build this company to hand it o

ver to a pathetic loser like you..” Yai fasali kafin yaci Gaba da nunasa “You are a disgrace to me Aliyu.. Kai baka cancanci sunana ba.. Mahaifiyarka tayi kuskure da tayi zaton zaka zamto kaman ni.. Har abada Kai bazaka tab’a zama kaman ni ba.. Kasan dalil

i..?” Ya k’arashe yana mai kuma takowa sosai gaban Aliyun “Sabida Kai baka saka komai a gabanka ba face shashanci… Ina nan ina Fad’i tashi to make a proper man out of you kana can kana shashanci da abokan banza.. Kana so kace mun duk kudaden da sukaita fit

a under your department a banza suka fita babu result a k’asa..? Ya jinjina Kai yana sakin huci “Ina sakamakon aikin..? Nace ina sakamakon aikin..?! Chacha kake da Kampanina..? Answer me, are you gambling with my company.!” Ya k’arashe yana cakumosa da han

naye biyu yana jijjigasa da iya k’arfinsa.

Izuwa lokacin Zuciyar Aliyu ya gama tafarfasa. D’agowa yai sosai suna fuskantar juna shida mahaifin nasa. Lokaci guda ya murmusa kad’an kafin yace “Oh really Dad. Is that the only problem..?”

Cikin huci mahaifi

nsa ya katsesa “Ya isheka haka.. Kar ka soma. Kar ka kuskura.”

“It has always been like this Daddy.. Hatred..! Eh tsana.!” Haidar ya katsesa cikin tsananin huci. Lokaci guda yaci Gagaba “Why do you always look down on me Daddy.? Despite all the good thin

gs that I’ve done for this company.. The only thing you can see are my mistakes.. Haven’t I done everything you told me to.. Shin bana aikata duk abubuwan da kake umurta na ne. Wanne ne banayi ciki..? Tell me Daddy..!”

Idanunsa suka kuma rinewa zuwa ja,

lokaci guda yaci gaba da girgiza Kai yana furta “Of course bazaka ce komai ba.! Because you don’t have the answer.. I’m sorry if I’m not as smart as you Dad.. I’m sorry if I’m not as skillful as you.. And I’m really sorry if I’m a disappointed..!”

Cikin k

araji mahaifin nasa ma ya katsesa “Yes that’s what you are.. A disappointment.. I gave you everything so you can be the best.. The best schools, the best trainings.. The best of everything.. I invested so much in you to make sure I groom you well.. Amma du

k a banza.. You are nothing but a pathetic loser.”

Idanunsa na kallon k’asa yake furtawa a hankali “That’s enough Daddy. Enough please.!” Yai maganar yana murza tafin hannunsa cikin k’ok’arinsa na danne zuciyarsa dake zillo kaman zai fito daga cikin k’irj

insa sabida b’acin rai.

“I don’t want see your face in my company ever again..! Get out now.. You are fired.” Mahaifinsa ya fad’i yana nuna masa k’ofa.

Kansa na kife k’asa ya saki murmushi. Lokaci guda ya d’ago idanunsa ya sauk’e su tar cikin na mahaifi

n nasa “And do you actually think I’d give you this satisfaction..?”

Ya kuma murmusawa kafin ya girgiza Kai yace “No Daddy bazan jira ka koreni ba. Kasan me..? I’m sick and tired of trying to impress you all the time.. I’m done being your puppet… I quite

.. You don’t need to fire me.. To hell with your damn company… Daddy.!”

Cikin huci mahaifinsa ya dago hannunsa dake rawa zai Kai masa Mari “How dare you talk to me like that..!” Rawan da hannunsa keyi yasa hannun ya gaza sauk’a saman fuskar Haidar. Sai ha

ki yake da kyar irin na Wanda zuciyarsa yakai matuk’a wajen baci.

Haidar ya finciki ID d’insa na Kampanin dake mak’ale jikin suit d’insa yai jifa dashi a wajen kafin yasa kai ya fice a fusace.

A daidai k’ofa ya kusan cin karo da aminin mahaifinsa Alhaj

i Gimba. Kallo d’aya kurum Haidar yai masa kafin ya watsar yasa kai ya fice cikin sassarfa.

Alhaji Gimba ya k’arasa shigowa cikin ofishin yana duban abokinsa dake zaune saman kujera guda yana sakin hakin b’acin rai.

Cikin kwantar da murya ya soma fad’in

“Abinda nake nusar dakai a koda Yaushe yana gab da faruwa Engr.”

Daddy ya d’ago idanunsa masu cikeda ba’cin rai yana dubansa dasu “Kaga Gimba dan Allah kar ka mun maganan yaron nan a nan.. Na riga na Sallama shi..”

Alhaji Gimba ya murmusa irinta manya “

Abokina kenan. D’a d’aya tilo ai ya wuce gaban a sallamashi.. Ai Kai Sallama d’ah ba naka bane..”

“I don’t care if he’s my only son.. Baka ganin abinda ya gama min yanzu ne.. Ban haifi dan da zaiga bayana ba..!”

Alhaji Gimba ya kuma murmusawa had’ida gi

rgiza kai kad’an “Yara ko dubu Allah ya baka bazaka ce ka Sallama guda ba dan hannunka baya rub’a ka yanke..”

“Saidai idan bai rub’e d’in ba..” Daddy ya basa amsa a fusace.

Alhaji Gimba ya tsaresa da idanu kafin yace “Wai kasan matsalar ka kuwa..?”

“Ai

idan Akan Haidar ne ni da Kai bazamu tab’a samun daidaito ba..” Daddy ya basa amsa Kai tsaye.

Ya d’an girgiza Kai kad’an “You are putting in a computation with your Son, and neither of you want to lose.”

Daddy yai saurin dubansa “Mai kake nufi..?”

“B

aka so Aliyu ya taso ya fika k’wazo Shiyasa har kullum kake gani a idanunka shi bai daidai ba.. You refuse to see his potentials. Da zaka basa dama yaron nan ba k’aramin asset bane ma Kampanin ka.. Ka bashi dama koda na k’arshe ne ka k’yalesa yai project d

’in nan at least koda na k’arshe kenan kafin kace ka koresa.. Inaga dan yayi failing business plan ba yana nufin yayi failing project d’insa bane.. Ina nufin bridge project dake gabanmu..”

Da tsananin mamaki Daddy ke duban aminin nasa wann karon “Alhaji G

imba, ka kuwa ji abinda kace..? Shin ka mance cewa the company’s future defends on this very project.. Ta ya zan mallaka ma Aliyu ya jagoranta.. Do you want us all to go down..?”

Alhaji Gimba zai kuma magana Daddy ya mik’e yana gyara zaman business suit d

’insa “This conversation is taking us to nowhere Alhaji Gimba.. Kamata yai yanzu ka tayani mu san mai zamu sanar da Board members sabida shashashncin d’anah.” Daga haka ficewa yai cikin sassarfa.

Alhaji Gimba ya girgiza Kai kurum kafin ya take masa baya.

SameenaAleeyou

📚

*AUREN WATA UKU*

*04*





Sameena Aleeyou…✍

🏽

*

Tafiya yake cikin mota sautin Marin da mahaifinsa ya shata masa bai daina k’uwa a dodon kunnuwansa ba. Shi ba wai zafin Marin bane ya tsaya masa a rai, Marin nasa da yai gaban

employees d’in Kampanin kuma masu aiki under department d’in da yake running shine abinda yafi komai k’ona masa rai. Ya sani shi dai a idanun mahaifinsa baya yin komai daidai sabida haka wann ba sabon abu bane wajensa. Ba a wajen aiki ba a gida ba.. Amma m

eyasa zai wulak’antasa gaban ma’aikatansa irin haka..? Ya cije labb’an bakinsa kad’an zuciyarsa na kuma k’una. Mahaifinsa ya tsanesa baya k’aunarsa, kai duka iyayen sa guda biyu basa sonsa basa k’aunarsa. Shi zai iya cewa tun tasowarsa baida wani good memo

ries da both mahaifansa wato mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa. Mahaifiyarsa tin tasowarsa cikin tilasta masa da tsaurara masa take wajen ganin yayi abinda zai burge mahaifinsa ya kumayi alfahari dashi. Saidai duk abinda yayi baya burge mahaifin nasa. Kullum

cikin nuna masa baiyi daidai yake ba. Kullum cikin kusheshi yake da jifansa da kalamai masu muni. Tsakaninsa da iyayensa akwai wani Katanga da yai ma soyayya shamak’i dashi. Baisan soyayyan iyaye ba. Ya taso ne cikin tilastawa da k’ok’arin burge mutanen d

a bai tab’a birgewa ba a cewarsa. Yai gajeren tsaki yana mai kokarin kauda tinanin.

A farfajiyan gidan yai parking motarsa jikin wani tapkeken roundabout da furanni suka k’awata tsakiyarsa ga ruwa na kwaranya daga tsakiya. Cikin sassarfa ya nufi cikin gi

dan har lokacin zuciyarsa bai daina masa zafi ba.

Zaune ya taddata a parlornsa ta mik’e santala santalan fararen k’afafunta da suka sha ado da k’unshi . Sai faman karkad’a k’afafun nata take tana tururi ita kad’ai alamun dai isowarsa take jira.

Baiji

mamakin ganinta a parlorn tinda yasan kullum cikin controlling rayuwarsa take.

Baice komai ba sabida ransa da yake a mugun b’ace.

Har yasa Kai zai shige ya sinkayo muryarta “Ai na zaci daga can bazaka dawo nan ba tinda ka zama sallamamme .”

Cak ya ts

aya yana saita numfashinsa a hankali “Couldn’t you wait for me first to at least do something wrong kafin ki fara aibatani.” Ya k’arashe daidai sanda mahaifiyarsa ta k’araso gabansa ta tsaya suna fuskantar juna.

Ganin ciwo a fuskarsa ya sanya yanayinta c

anzawa. Alamun rauni ya bayyana saman fuskarta “Haidar.. Me ya sameka.. Ina ka samo rauni..?” Ta tambaya cikin nuna kulawa.

Murmushi mai ciwo ne saman fuskarsa. Lokaci guda ya girgiza Kai yace “Don’t act like you care Mom. Kin San hakan zai faru. Am I rig

ht.?”

Ta d’an tsare fuska “Wani irin magana ne nasan haka zai faru.. Had’arin mota Kai ko me.. Tinda dai nasan baka shiga sabgan mutane balle nace fad’a Kai da wani..”

“Babu ko d’aya Mommy..” Yai fasali yana mai shafa raunin da mahaifinsa yaji masa a la

bb’ansa “Meyasa ciwo a jikina zai d’aga miki hankali da girma na idan bai d’aga miki hankali a lokacin k’uruciya na ba.?”

Ya kafeta da idanu. Jin tayi Shiru batace komai ba yasa shi murmusawa kad’an da gefen bakinsa “Of course you don’t have the answer. W

ell, zaki iya kiran wann a matsayin tukuici na mahaifina. All thanks to you, your Majesty, Mommy.!”

Ta furzar da huci kad’an “Mai ya had’aka da mahaifinka..?”

“A usual stuff.. Banyi daidai ba, Dikda bana tunanin Akan wann ne kawai..” Ya d’an daidaita tsa

yuwarsa kafin yaci gaba “Nafi zaton kece kika bashi shawarin yai mun wulak’ancin da ya mun.. A naki tunanin ta haka ne kawai zaisa ki fahimci mai kike son fahimta gameda D’anda kika dasa rashin yarda da daidaito a tsakaninku tun yana k’aramin yaro. Na sa

ni ku biyun baku zama on the same page with each other unless wann abun will hurt me deeply. Ko ba haka bane Mommy.?” Ya k’arashe yana dubanta.

Furzar da huci tai had’ida girgiza Kai “It’s for your own good Aliyu.. Dik Fad’i tashin da nake inayi ne domin

ka zama mutumin K’warai sann rayuwarka ta inganta.. Bazai yuwu bayan tsayin dakan da nake Akan D’ah na na zuba

ido rana daya komai ya rushe ba. Aliyu ka daina kwana a gida.. Ka tsiri wasu d’abi’u da ba naka ba.. Some strange behaviors wanda a baya bakayi.

A baya baka tab’a maida mun magana kan duk abunda zan umarceka.. But now.. You’ve changed.. Completely Haidar.. Ina kake kai kudaden da kake fitarwa daga kampanin mahaifinka.. So kake ka hadani fada dashi..? A nashi tunanin nice nake daure maka gindi kake

abinda ka so.. A nashi tunanin nasan duk halinda kake ciki.. What he was wrong about shine yanzu Aliyun da ya sani ya banbanta da Aliyu na wanda baya boye mun komai.. D’ah na mai biyayya a gareni koda na kasance mai tsauri akanshi.. Haidar din da baya mun

musu koda munada banbancin ra’ayi..” Ta danyi fasali muryarta na rawa tana kuma matsowa kusansa “Aliyu nasan ba shaye shaye kake ba tunda bakayi ba a lokacin da tak’ura da tsanani zasusa kayi. Sann bana tunanin mata ne suka d’auki hankalinka tinda shima b

akayi a baya ba lokacin da ya kamata ace kayi idan kai me yi d’in ne… Toh menene ya dauki hankalinka a duniyar nan.. Haidar please..”

D’aga mata hannu yai alamun dakatarwa “Kin rasa wann daman akan D’anki Mommy tuntuni..

Ya dan juyo yana dubanta kafin ya

ci gaba cikin rarrabewar kalmomi “What I do with my life is none of your Business… You said it right. Ni ba wann k’aramin yaron da kike kullewa a d’aki ki hana masa lokutansa na k’uruciya ki tilasta masa cinye takardu koda baya so..” Ya d’anyi fasali kafin

yaci gaba “Kin mance ne na tuna Miki Mommy.? That unhappy little boy ya girma Mommy. Kuma zai yanda yake so da rayuwarsa ba yanda ke kike so ba.. After all, duk abinda kike yi kinayi ne sabida benefits d’inki.. Ba abu guda da kikeyi domin ci gaba na.. Kin

ayi ne kawai domin amfanin kanki.. Burinki shine ya mallaka min company sabida watak’ila akwai abinda kike tsoro ko kuma yake Miki barazana da rasa dukiyarsa wanda ni ban sani ba.. Shiyasa kike amfani Dani domin na zame miki makamin ki.. D’anki ba komai ba

ne a wajenki face weapon. Yes, I am nothing to you face makaminki. Haka ne Mommy..?” Jinjina kansa yai jin bata amsa ba “Wace irin uwa ce take haka ma d’anta Mommy.? Ya k’arashe idanunsa cikin nata.

Dikda zuciyarta dake harbawa bata bari tsoro ya bayyana

saman fuskarta ba. Saima girgiza Kai da take “Don’t you dare question my motherhood.. You’ve no idea what it takes to be a parent..!” Ta k’arashe tana sakin huci.

Jinjina mata kai yai “Eh bansan mene zama iyaye ba kuma bana so nai experiencing daidai da

dak’ik’a guda. Kinsan dalili sabida ban taso naga misali mai kyau wajen mutanen da ya kamata na gani daga garesu ba.. “ Ya d’an kuma matsowa had’ida sassauta murya “Kin gama sanin duk abinda ke faruwa cikin rayuwar D’anki.. Do you know why..?” Ya tsare mah

aifiyar tasa da idanu kafin yaci gaba “Because I’m not that scary little cat da kikai traumatizing d’inshi da son zuciya irin naki. Bazaki sake amfani dani domin cimma burinki ba.!” Daga haka sa kai yai ya shige cikin huci.

Tabi bayansa da kalamansa na k

uma dakan dodon kumnuwanta har zuwa tsakar kanta. Salati kawai take.. Meke faruwa da ita..? Meke faruwa da D’anta. Ko zamanin yarinta zamanin da take kulle Haidar cikin d’aki mai duhu bai mayar mata da maganganun irin haka. Hasalima duk abinda zata masa sh

iru yakeyi. Ya koma kaman mai tsoron mutane, dik yanda mutane suke baya zama baya kuma cewa um balle um um. Akwai lokacin da har sukai zaton ko ya kurmance ne har saida aka had’a masa da therapy kafin maganarsa ya dawo. Ita tsoro abun ya soma bata. Yafi ka

ma da aikin asiri.

Yana tura k’ofan d’akinsa ya hangi Anisa ‘yar k’anwar mahaifiyarsa dake aure garin Kano tsaye closet d’insa rungume da rigarsa ta lumshe idanu. Jin an turo k’ofa ya sanyata bud’e idanunta suka kuwa had’a idanu.

“What are you doing i

n here..? And can you explain why you are holding that..?” Yai mata nuni da rigarsa dake cikin hannunta da idanunsa.

Ta saki murmushin yak’e “Na shigo na gyara maka d’akin ne.. Mommy tace kwana biyu baka kwana a gida.. Nima d’in jiya da dare na shigo ga

rin..”

Baiyi mamaki ba dan Mommy ta turo Anisa d’akinsa. Yasan kad’an ne da aikin Mommy ta turo Anisa tai mata binciken k’wak’waf cikin d’akinsa dukdai dan ta gane what’s been going on cikin rayuwarsa.

“Get out.. I need to change..” Ya fad’i yana mai s

higewa cikin d’akin lokaci guda yana k’ok’arin undressing Kansa. Suitcase ya ciro Anisa tana gani ya shiga ciro kayansa yana sakawa ciki.

Mamaki ya cika Anisa da ganin yanayinsa. Tasan bai iya fushi ba dukda kuwa ba kasafai kake gane normal days d’insa ba

. Definitely dai wani abu na faruwa dashi. Ta girgiza kai kad’an. Sauri sauri ta fito

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login