Showing 249001 words to 252000 words out of 267381 words
mata hannayensa daga nan yanda yake kishingide “Come here.”
Ta d’an fito da ido tana dubansa. Sai ta soma ‘yan waige waige.
Haidar yace “What..! Taho mana.”
Ta d’an langab’e kai kad’an “Wasa kake.. Ka mance ina muke ne.”
Gyara zamansa yai k
ad’an had’ida furta “Fine.. Kin sama min mai zanci.?” Yai maganar yana mai janyo hannunta.
Ta d’an girgiza kai “Gidan gaba d’aya cike yake.. Barin kira kitchen naji mai suke dashi.”
Tabe baki yai kad’an “Banson abincin Chefs din gidan nan.. Sun Faye cik
a yaji…”
Ta d’an marairaice fuska “Toh ya kake so ayi Rankaidade.? Mu fah bak’i ne a nan. Kai hakuri kaci haka.. Idan munje gida sai na girka maka abinda kake so.” Cikin sigan lallashi take maganar.
Sosai suka birge Hajja har taji dama bata sauko parlor
n ba dan kar ta katse musu soyayyarsu.
Ummul ta d’an matsa baya kad’an daga kusan Haidar tana ma Hajja sannu da sauk’owa. Haidar ma gaisar da Hajja yai kafin daga bisani Hajja ke musu tayin Burabusko miyan taushe da ta dafa ma Daddy. Ta k’arashe tana fad
’in Ummul ta taho ta kawo ma Haidar.
Haidar ya dan shafa kansa kafin ya katse hanzarin da fad’in “But.. I don’t eat Burabusko..”
Hajja ta dan murmusa tace “Lallai kace zamu maida Kai Yerwa Haidar. Ya zaace Kanuri bai cin Burabusko.? Kuma naga favorite
din Daddy kenan. Ya kamata ace ka iya ci.”
Daga k’ofa suka sinkayo murya na fad’in “My brother is more Shuwa arab… Abincin larabawa yake ci.”
Gaba d’aya suka waigo suna duban mai maganar ba kowa bane illa Hilal.. Ya kara girma da k’warjini kaman ba shi
ba.
Ya k’araso cikin parlorn yana gaida Hajja da Ummul lokaci guda Ya k’araso ga Haidar suka gaisa Hilal na hugging d’insa kad’an na yaushe rabo.
Hajja ta shige ta basu waje abinta bayan tayi ma Hilal lale da zuwa.
Haidar ya dubi Hilal “Kai kuma daga
ina kaman an jefo ka.?”
“Daga gida Kano.. Tare muke da Ammi.. I arrived in the country yesterday.”
Haidar ya jinjina Kai yana tambayarsa ya sch. Allah sa dai ya tab’uka abin arziki wann karon. Ya k’arada “Kasan ban tab’a ganin unserious human being ir
inka ba. Gaba d’aya baka d’auki rayuwarka da mahimmanci ba Hilal.”
Hilal ya Dara kad’an “Sanin da ka mun da ne D’anuwa. Well, I can finally say it with full chest.. I’m a graduate now. Kana magana da cikakken accountant ne a nan.”
Jinjina Kai Haidar ya
ke yana dubansa “Idan gaskiya kake fad’i, I’ll hire you.”
Suka dan murmusa gaba d’aya. Hilal na fad’in Lallai shi D’angata ne gashi daga dawowa ya samu aiki.
Ummul da ta b’ace b’at kaman bata a wajen muryar Hajja ta sinkayo tana fad’in maza ta taho ta
shige kitchen dinta dake bangarenta ta samar ma Haidar abinci. Dan ta kula kaman abincin matarsa yake son ci.
Hilal yai karaf ya dakatar da Ummul da fad’in “Addarmu ina Baby yake.? Ni fah shi nazo gani.. Naji ance takwara akai ma Yaya na Haidar. Meyasa b
a’a min ba.
Haidar ya dalla masa harara “Waye zai maka takwara.? Ba dai ni Haidar ba.”
Hilal na murmushi yake Shafa Kai “I’m a changed person fah.. Zaka sha mamaki. Ni fah yanzu na zama responsabile Human being.. Na jima da daina sallah ba alwala..”
Hai
dar ya kuma aika masa wani duba dan baiso a d’ago yarintar su gaban Ummul.
Murmushi Ummul take tana fad’in bari ta kawo masa yaron. Saidai kafin tai shiru ta hangi su Khulsum dasu Badia suna sauk’owa downstairs ga Baba Ali cikin hannun Khulsum d’in. Sam
Khulsum bama ta kula da mutumin dake zaune gefen kujeran Haidar ba.
Shi kaw Hilal mutuwar zaune yai yana dubanta. It’s been long.. So long rabonsu da su saka juna a ido.. Ta k’ara masa girma da kyau.. Saidai ya hangi wani abu mai Kama da salihanci saman c
ute grumpy face dinta.
Sam bata kula ba sai wasa take ma Baba Ali. Bataji sanda Ummul ke introducing Hilal masu Aunty Salima. Bata Ankara ba sai sinkayo muryarsa tai yana fad’in “May I please.. see him..”
Cak ta dakata da abinda take bugun zuciyarta na
k’aruwa. Ta ina zata mance muryarsa. Ta d’ago a hankali tana dubansa. Shi d’in ne dai.. Saidai wann karon ya k’ara mata girma fiyeda sanin da tai masa a baya. Wann sumar tasa mai laushi da tsantsi irinta asalin k’abilar shuwa arab ya tara shi wann karon. H
arda jiki ya k’ara saidai girman yasa ya k’ara duhu kad’an. Har Hilal ya amshi Baba Ali daga hannunta bata dawo daidai ba. Sam bama ta kula har su Azeema Sun wuce sashen Mommy ba. Gaba d’aya sai ta daburce.. Ga Hilal kusan k’ofa yake tsaye rik’eda Baba Ali
yana fad’i ma Haidar yaron dashi yake kama ba da Haidar ba. Harda cewa za’a basa yaron he’s his Godfather.
Ai kawai sai Khulsum tabi bayan Ummul ta nufi kitchen.
Ummul ta dubeta da mamaki yanda ta shigo duk a daburce “Ke kuma fah.? Mai kikeyi a nan..
Na zata kun tafi sashen Mommy gaba d’aya..”
Kasa amsata Khulsum tai sai ma dibi dibi da take. Ummul dai d’an tabe baki tai kadan Ta d’auko carrots zata pilling Khulsum tai karaf ta amshe tana fad’in zata fere mata.
Ummul ta tsareta da ido yanda take kom
ai sauri sauri ba natsuwa. Ta aje chopping board din dake hannunta tana kuma tsare Khulsum da ido “Khulsum.” Ta k’ira sunanta cikeda kulawa.
Khulsum ta amsa tana dubanta.
“Fad’a mun.. Meke faruwa ne.?”
Khulsum ta d’an girgiza Kai “Ba.. Ba komai.. Mai ki
ka gani Adda Ummul.?”
Ummul ta jinjina Kai “Idan zaki b’oye ma wani nidai kinsan bazaki b’oye min ba.. Ki fad’a min meke faruwa.?”
“Da gaske ba komai fah Adda Ummul..”
Daidai lokacin suka soma sinkayo kukan Baba Ali daga parlor.
Ummul ta zame apron di
n dake jikinta tana nuna Khulsum “Ni dake bamu gama ba.. K’arasa fere mun carrot d’in ki yankasu k’anana ina zuwa.”
Daga haka Ummul ta fice sauri sauri.
Ta tadda Hilal ya mika yaron ma Babansa yana fad’in ya kamata ya sanshi dan shine Godfather d’insa.
Ba maganan k’iwa tsakaninsu.
Haidar ya amshe yaron yana fadin “Come to Paapa.” Ya shiga jijjiga yaron yana fad’in yai shiru Maama is here. Daidai sanda Ummul ta zauna gefen Haidar tana k’ok’arin amsar yaron.
Yanda gaba d’aya attention d’in iyayen ya ko
ma kan yaron sosai hakan ya birge Hilal ya kuma basa sha’awa. Sai ya dan murmusa yana k’ok’arin barin parlorn. Hanyar da yaga ta nufa yabi. Nan ya hangeta tsaye cikin kitchen din tana dicing carrots. Ya jima yana dubanta sihirtaccen murmushi saman fuskarsa
kafin Ya soma takowa cikin kitchen din a tsanake.
Sam bataji alamun mutum ba sai taji gyaran murya daga bayanta yana fadin “Hello.. Excuse me..”
Ta dan razana Wanda hakan ya sata saurin aje knife d’in da take yanka carrots din dashi had’ida rintse idanu
nta alamun ta razana.
Hilal ya dan leko yana duban fuskarta. Murya a hankali yace “Sorry..! I didn’t mean to scare you.”
Huci Khulsum keyi ba tareda ta dubesa ba. Lokaci guda tana dunk’ule knife din cikin hannunta. A fusace ta waigo tana fad’in ya kuwa
bazataji tsoro ba mutum yana shiga waje ba Sallama kaman goyon yahudu. Tana maganar a fusace tana juya wuk’ar dake cikin hannunta.
Kallon yanda take juya wukar kawai Hilal yake ya d’ago hannayensa sama alamun surrender lokaci guda yake jada baya yana fad
in “Easy.. Easy..!” Yanda yake ja da baya kaman zai auna a guje sai ya kuma tsorata Khulsum. Ta soma waigawa baya tana duba mai ya gani yake shirin guduwa. Hilal bai daina jada baya ba ai kawai sai itama ta nufo k’ofa a guje dan ta zata wuta ne ya gani a
kitchen din ko wani abu mai Kama da haka.
Kafin tai aune Hilal ya tare k’ofan kitchen d’in wanda hakan ya hanata k’arasawa. Bai daina nunata ba bai daina daukan saiti na gudu ba bai daina furta easy ba.
Ta kuma waigawa cikeda tsoro wann karon “Wai meye
ne.. Meye ka gani.?”
Ya nuna mata hannunta mai rik’eda knife “Pleae keep that away..” Yai maganan yana rik’eda k’ofar kitchen din gam. K’afarsa d’aya na waje d’aya na kitchen din.
Sai ta d’ago wukar dake cikin hannunta tana kallo. Gajeren tsaki tai had
’ida sauk’e ajiyan zuciya kafin ta koma bakin aikinta.
Hilal ya murmusa kad’an kafin ya kuma takowa gareta. Wann karon Sallama yai. Kaman bazata amsa ba sai kuma ta amsa da kyar.
Hilal ya k’arada “You haven’t changed a bit.” Ya fad’i da murmushi saman fu
skarsa. Bata ko dubesa ba balle ta kulasa. Saima ci gaba da tai da abinda take.
Ya dan langab’e Kai yana dubanta “Wai ko darajan gaisuwa bazan samu ba balle sannu da zuwa.?”
Ta dan dubesa a dak’ile sai ta tabe baki had’ida janye idonta “Wanda yai Sallama
idan zai tafi shi ake ma sannu da zuwa.”
Hilal ya dan murmusa dan ya tuna sanda zai tafi bai mata sallama ba. Dikda lokacin itama tana Jigawa gidan Inna Dije amma ko a waya bai kira ya sanar da ita tafiyarsa makaranta ba. Sann tinda ya tafi bai sake nema
nta ba. Alk’awari yai ma Kansa zai natsu yai abinda ya kaisa once and for all ya k’arasa karatunsa ko dan ya share hawayen Amminsa ya kuma tabbatar ma Abbansa bazai sake asaran kudi Akan karatunsa ba. Above all, zaiyi ne ma Kansa ta yanda idan yazo ma Abba
nsa da batun Aure zai tsaya ya sauraresa.
Gyaran murya ya d’anyi yace “Lallai ban kyauta ba amma kiyi hak’uri.” Ya d’anyi shiru kafin ya ambaci sunanta cikin wane irin siga da ya haifar mata da sanyin jiki.
“Khulsum.”
Ta d’ago ta d’an dubesa. Hilal yaci
gaba “Tafiyar da nai ba Sallama yanada dalili wanda nasan idan muka samu time na miki bayani zaki fahimta.Ki yarda Dani nayi hakan ne for us.”
Sai ta d’an kuma dubansa. Yayinda Hilal yaci gaba da jinjina Kai “Believe me, Ban manceki ba daidai da dak’ik’
a guda. A koda Yaushe kina nan a nan..!” Ya k’arashe yana nuni da b’angaren k’irjinsa yanda zuciyarsa take bugawa. Yayinda Khulsum taci gaba da dubansa jiki a sanyaye. Kyakkyawan murmushi saman fuskar Hilal yaci gaba “I never stopped loving you my cute cut
e miss grumpy.!”
Daidai lokacin sukaji alamun ana shigowa kitchen d’in.
Khulsum tai saurin juyawa tana ci gaba da yanka carrot din sanda Ummul ta shigo kitchen d’in.
Shi kaw Hilal saurin daukan glass cup yai yana fadin “I.. I will have a glass of wate
r.!” Ya k’arashe da murmushi yana daukan ruwan gora dake wajen. Ya dubi Khulsum ya kashe mata ido yayinda Khulsum d’in ma ta bisa da wani kallo sihirtaccen murmushi saman fuskarta.
Ita dai Ummul dubansu kawai take. Ta dubi wann ta dubi wancan har Hilal ya
fice sai waigowa yake yana duban Khulsum.
Bayan Hilal ya fice Ummul ta tsare Khulsum da ido wacce ke ta faman sakin murmushi a hankali.
Ummul tai gyaran murya tace “Toh ai ya fice sai ki daina wann murmushin da kike.”
Khulsum ta dan zaro ido “Na’am
Adda Ummul..!”
Tsareta Ummul tai da ido sai ta murmusa tana aje Kayan miyan dake hannunta cikin roba a sink “Zama kimin bayani ne dalla dalla yarinya. Bari dai mu k’arasa da kitchen din nan.”
Dan darawa Khusum tai tana fad’in “Adda Ummul ba fah abinda k
ike tunani bane.”
Ummul tace “Toh ni mai kikaji nace.. Kin Kama kanki tin baaje ko ina ba yarinya..”
Khulsum ta sanne Kai tana dariya.
Bayan Sun gama girkin ne kuma suka soma shirin shagalin. Tuni masu kwalliya Sun iso sunyi mata light make-up da ya mat
uk’ar mata kyau. Shima Haidar d’in saida ya k’ara shiryawa sabida pictures da zasuyi da jariri. Haka kowa ya dinga santinsu dan ba k’aramin kyau sukai ba. Daga bisani Ummul da jaririnta sukaita hotuna da ‘yanuwa da abokan arziki.
**
Wasa wasa har rana t
a kusa k’arewa su Hisham basu iso ba. Har akaci taron shagalin suna aka watse basu Anisa ba dalilinsu.
Izuwa lokacin hankulansu ya soma tashi dan tuni anyi conforming jirginsu ta jima da landing.
Ana haka wayar Sadis ya shigo ma Daddy yanda yake sanar d
a Daddy sun kalla daga security footage na airport Hisham da Anisa Sun shiga wata mota mai d’auke da fake plate number na Kampaninsu. Akwai possibility din kidnapping dinsu akai daga Airport.
Daddy yaci gaba da karanto Innalillahi wa inna’ilaihi ilairaji
’un.
Daidai lokacin da su Hajja da Mommy harma da Aunty Asshe suka shigo parlorn a kid’ime dan tare Sadis da Hilal suka tafi airport binciko abinda ke faruwa kuma tuni Hilal ya kira mahaifiyarsa yayi updating d’inta.
Aunty Asshe kuka kawai take tana fa
d’in anyi kidnapping su Anisa ne dan ance tun rana jirginsu ta sauk’a ga kuma shaida wani mota da ba’a tantance ba ya d’auke su.
Kwantar musu hankali Daddy keyi da fad’in in sha Allah ba komai dan idan ma kidnappers ne dole zasu kira su nemi ransom kuma
ko nawa sukai demanding zai bayar dan ya ceto yaransa.
Girgiza Kai Haidar yake yana duban Daddy “Na tabbata this is one of his games Daddy.. There’s nothing like kidnapping here.. Hisham shi ya shirya wann wasan kwaikwayon. And he used Anisa as a bait.!
”
A fusace Daddy ya daka masa tsawa da fad’in “Ka rufe mun baki Haidar.!” Cikin b’acin rai Daddy yaci gaba “Your brother is kidnapped.. Ba shi kad’ai ba harda iyalinsa wacce ta kasance Yaruwarka.! And you are here blabbing nonsense..!” Yaci gaba da girgi
za Kai yana duban Haidar cikin rashin yarda “For once in your life Aliyu, call a truce with your brother.! If you can’t do anything to help. Then just shut your mouth and get hell out of my house.! Fitar mun a gida nace.!” Ya k’arashe yana nuna ma Haidar k
’ofa cikin tsananin b’acin rai.
Idanun Haidar Sun kad’a sunyi ja yake duban Daddy. Meyasa Daddy bazai yarda dashi ba.! Meyasa idonsa ya rufe Akan d’aya D’ansa.?! Ya soma girgiza Kai yana jada baya lokaci guda ya fice daga parlorn kaman zai kifa.
Mommy t
abi bayansa da kallo tana kiransa amma inaa bai tsaya ba. Hajja kaw tashin hankalinta ne ya ninku. Duk yanda taso ta hana zuciyarta yarda da abinda Haidar ke fad’i gameda D’an nata meyasa taji yau d’in kaman ta yarda da Haidar. Addu’a take a cikin zuciyart
a Allah yasa Haidar kuskuren fahimta kawai yake ma D’anuwansa. Allah ya bayyana Hisham da Anisa cikin k’oshin lafiya ya warware komai ya kuma kawo k’arshen matsalolin Ahalinsu.
Haidar na fitowa sashen Mommy ya nufa kaman zai kifa. Ya shige su Salima a pa
rlor Wanda tuni suma sunyi jigum jigum dan sunga ficewar su Mommy dasu Aunty Asshe hankali tashe.
A d’aki ya iske Ummul tana bama Baba Ali nono.
“Tashi mu tafi.!” Ya fad’i babu walwala.
Ta dan dubesa da mamaki. Dan tin shigowarsa bata gane yanayinsa b
a.
“Ban.. Ban gane ba.. Na tashi mu tafi kuma.? Amma meyasa zamu tafi yanzu.?”
“Kar ki bata mun rai Khairy.! Ki tashi nace mu tafi.!” Ya kuma fad’i cikin tsananin b’acin rai.
Itakam sai taji k’walla na zuwa mata. Ga Baba Ali da tuni ya rigata fara kuka
ciresa da tai yana tsaka da shan nono.
Haidar ya amshesa ya izasa bisa kafad’a “Ki same mu a mota.. Kar ki bata lokaci.!” Daga haka ficewa yai cikin sassarfa.
Mamaki da tsoro suka cikata. Haidar ya juye mata tashi daya. Tasan bai iya fushi ba amma mai
ya bata masa rai irin haka. Toh kodai ta masa laifi ne.? Bata ida tunanin ba ta sinkayo sautin horn kaman zai daga gidan alamun ita yake jira.
Kuka ta fashe dashi tana mai zira mayafinta.
Koda ta nufo k’asa hankulan su Khulsum bai ta b’angaren da take.
Hakan yasa ta nufi k’ofa tana danne kukanta.
Khulsum da ta hangeta tai saurin mik’ewa ta nufeta tana ambaton sunanta.
Bata iya amsa ta ba sai kawai tasa Kai ta shige cikin sauri wani kukan na kuma zuwa mata.
Hakan ya janyo hankulan sauran ‘yanuwan . W
ann ta kalli wann wancan ta kalli wann gidan dai da alama ba lafiya. Aunty Asshe ta fice tana kuka.. Su Mommy sun fice hankula tashe yanzu ga Ummul ta fito tana kuka.
Badia ta rapka tagumi tana fad’in “Oh ni Badi’atu yau meke faruwa ne a gidan nan.?”
Salima tace “Gaskiya ba lafiya.. Toh amma meke faruwa ne.?”
Badia ta tsaida wata ma’aikaciyar gidan tana tambayarta meke faruwa a gidan.
Matar ta girgiza kai tace “Naji securities da suke gate suna cewa yaron Alhaji da zai dawo daga SouthAfrica aka kidn
apping together with his wife Anisa.”
Azeema ta saki baki tace “Anisa dai.?” Sai ta rangad’a guda tana fad’in Alhamdulillah an gama taro lafiya ba Anisa dan ta iso kafin a gama taron da ta wargaza komai.
Salima ta girgiza Kai tace “Kedai bazakiyi hankal
i ba Azeema. An ce Miki an sace mutane kina shewa. Toh gashi bata zo d’in ba amma taro ya tashi ba dad’i. Ki gaya min hankalin waye ke kwance.?”
Azeema ta tabe baki tace “Wllhi Anty Salima dan dai baki zo bane lokacin bikin tariyar Ummul da ke kanki sai
kin tsani wann anisar.”
Salima ta girgiza Kai “Toh yanzu dai duk ba wann ba. Mu had’a hannaye mu tayasu da addu’a Ubangiji ya bayyanasu cikin aminci.”
Suka amsa da Ameena gaba